Manufar wannan shiri shi ne koya wa masu sauraronmu girke-girke na Sinawa masu sauki, wadanda kuma ake iya samun kayan hadasu a kasashen Afrika, musamman inda muke da rinjayen masu sauraronmu a harshen Hausa. Sanin kowa ne Sinawa suna da wasu dabaru masu ban sha’awa na sarrafa abinci mai dadin gaske…