Barka da Warhaka, shiri ne da ke sakarwa matasa linzamin bayyana ra’ayinsu a siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da sauran batutuwan rayuwa ba tare da takunkumi ba. Zamani...riga
Kilishi, wani abincine na kasaita a kasar Hausa, wanda yake da sunaye daban daban misali a turanci ana kiransa da "Beef Jerky". Kasan cewar Amurka bata bari a shigo da nama Hausawa mazauna yammacin duniyar na fama da rashin Kilishi, Hakan yasa Balkisu Aliyu mai kamfanin Alsutra Kitchen ta fara yin Kilishin ana saida shi a kasashe da dama. Hakan yasa muka gayyato ta shirin Barka da Warhaka don tattaunawa da ita.
A yau mun zanta ne da Sani TY Sha'aban wanda aka fi sani da Freiiboi mawaki dan shekaru 15, kan irin burin shi a rayuwa da kuma irin gatan da yasamu na tallafi da kuma kwarin gwiwa daga waurin mahaifinsa.
A yau mun tattauna da mawakin zamani Abdul Amdaz wanda ke rera waka da salon Hausa Sudaniyya.
Shin ko yawaitar sabbin wayoyin hannu na zamani ya kashewa masu sana'ar daukan hoto kasuwa? Mun tattauna da Lawal Abdullahi Matazu, Mai daukan hoto, gami da zayyanar rubutu (Graphics designing) inda ya warware mana zare da abawa.
A yau munyi duba ne kan Podcast, ma'anarsa da tarihinsa da kuma bukatar karbuwarsa a wurin matasa musamman masu magana da harshe Hausa a fadin duniya.
Ba 'boyayyen abu bane mafi yawancin iyaye basa tallafawa yaransu wajen kara musu kwarin gwiwa a bangaren wasanni da hikimomi na yau da gobe. TY Sha'aban wanda aka fi sane da (Shaba) ya bambamta da sauran iyaye domin kuwa shi yana tallafawa dansa (Freiiboi) wajen yin wakokin zamani. Ko me yasa? ku biyo mu cikin shirin Barka da Warka domin jin dalili.
Matsalar fyade, matsala ce da ta zama ruwan dare musaman a arewacin Najeriya, inda a yan kwanakin nan rahotanni suka yawaita akan fyade musamman ga kana nan yara maza da mata har ma da jarirai. Saboda haka ne a cikin wannan shirin muka gayyato Fakhriyya Hashim 'Yar rajin kare hakkin mata tare da Saratu G Abdullahi, Malamar Jinya da kuma rajin kare hakkin mata domin tattaunawa akan wannan matsala. Asha sauraro lafiya.
A cikin shirin "Barka da Warhaka" kashi na farko mun gayyato Maryam Bugaje, 'Yar Jarida kuma mai fashin bakin akan lamuran yau da kullum inda muka tattauna game da zanga zangar da ta barke a Amurka sakamon cin zarafin bakaken fata da jami'an 'Yan sanda ke yi a Amurka.
"Barka da Warhaka", shiri ne da ke sakarwa matasa linzamin bayyana ra'ayinsu a siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da sauran batutuwan rayuwa ba tare da takunkumi ba. Zamani...riga