POPULARITY
Categories
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya yi duba ne kan irin koma bayan da ake gani na faruwa a tsakanin tawagogin kwallon kafar Najeriya, kama daga bangaren mata mata da maza, har ma da yan wasa masu tasowa. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
A Najeriya, Gwamnan mai ci kuma ɗan takarar jam'iyyar Accord Ademola Adeleke ya lashe zaɓen jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar da sama da kuri'u dubu 511, yayin da abokin karawarsa na APC mai mulkin ƙasar Bola Oyebamiji ya zo na biyu da banbancin kuri'u 66,252. Kafin ranar zaɓen dai an fuskanci dambarwar siyasa da rikece-rikece da suka yi sanadin mutuwar kusan mutum 40. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar da Ahmad Abba ya yi da Farfasa Kamilu Sani Fage, masanin siyasa kan zaɓen..
A Najeriya, Gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam'iyar Accord Ademola Deleke ya lashe zaɓen jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar da ƙuri'u sama da dubu 511, yayin da ɗan takarar jam'iya APC mai mulkin ƙasar Bola Oyebamiji yazo na biyu da ƙuri'u dubu 444,815. Kafin ranar zaɓen dai an fuskanci dambarwar siyasa da rikice-rikice da suka yi sanadin mutuwar mutane sama da 40. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
A ranar Asabar 15 ga watan Agustan 2026 ake sa ran gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun, wanda tuni ya yi sanadin halaka mutane sama da 30 a lokacin yaƙin neman zaɓe. Rundunar 'Yansanda dai ta tura muƙaddashin Sifeto Janar Isyaku Muhammmad da Kwamishinoni 30 da kuma wasu ƙarin jami'ai dubu 15,000, domin tabbatar da tsaron masu kaɗa ƙuri'u da jami'an zaɓen. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Zainab Aminu Abubakar, mai magana da yawun hukumar zaɓen ta Najeriya.
A Najeriya, Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Kasa ta roƙi gwamnonin jihohi da su yi wa Allah su gaggauta karɓar sama da Naira biliyan 332 na kuɗaɗen tallafin daidaita tsarin ilimi. Shugabar Hukumar Aisha Garba wanda ta yi wannan kira, ta ce bayaga Naira biliyan 65 da aka ware akwai kuma wasu Naira biliyan 267 da aka ware domin inganta makarantun firamare a ƙananan hukumomin faɗin ƙasar. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.
Hukumar kula da ilimin Firamare a Najeriya ta roƙi gwamnonin ƙasar da su yiwa Alla su je su karɓi naira biliyan 332 waɗanda yanzu haka ke ajje a Banki, domin inganta ilimi a jihohinsu. Shugabar hukumar Aisha Garba ta ce baya ga naira biliyan 65 da aka ware domin kai ɗaukin gaggawa, akwai kuma naira biliyan 267 da ke ajje domin amfanin jihohin. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Muhammad Dukku, tsohon shugaban hukumar kula da ilimin Firamare a jihar Gombe ga kuma tattaunawarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.......
A Najeriya, ƙungiyar G –100 ta gamayyar wasu fitattun ƴan ƙasar kimanin 100 ta jagorancin wani sabon yunkurin ganin lallai sai jam'iyyun adawa sun yi haɗin guiwa domin fitar da ɗantakara ɗaya tilo da zai fafata da shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekara mai zuwa. Ku danna alamar sauraro dimin jin cikakken shirin tare da Oumar Sanni.
A ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau. Masana tattalin arziki sun alakanta wannan gagarumin ci gaba da kasuwar ta samu da sauye-sauye masu tsauri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi a fannin tattalin arziki.
Yan adawar Najeriya sun fara wani sabon yunkuri na hadin kai a tsakanin su domin fidda dan takara guda da zai fafata da shugaban kasa Bola Tinubu a zaben shekara mai zuwa. Wata kungiyar dake kiran kan ta G100 ke jagorancin wannan sabon yunkuri, yayin da ta sanar da taron da za ta yi a makon gobe. Dr Ibrahim Modibbo na daya daga cikin shugabannin ta, kuma ya yi wa Bashir Ibrahim Idris a tattaunawar da suka yi kan lamarin
Ga alama ƴan Najeriya da dama sun fusata da yadda ƙungiyoyin kwallon ƙafa na ƙasa ke cigaba da samun nasara a wasannin da suke a nahiyar Afirka. Bayana gazawar da ƙungiyar Super Eagles ta yi na kasa zuwa gasar cin kofin duniya da aka kammala a Amurka da Canada da kuma Mexico, yanzu kuma Super Falcons ta mata ta gaza samun nasara a gasar WAFCON Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Alhaji Yusuf Musa Sakatare a ma'aikatar wasanni ta jihar Nasarawa.....
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sake ɓarkewar cutar kwalara ko kuma amai da gudawa a jihar Borno, lamarin da ya jefa ɗimbin jama'a a yanayi na matuƙar damuwa damuwa musamman bayan da rahotanni ke cewa an samu yaɗuwar annobar cutar har a yankunan da ake ajje da ɗimbin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.
“Shugabanci na Gari a Tsarin Dimokuraɗiyya.” Shugabanci ba mulki kawai ba ne, illa amana ce, nauyi ne, da kuma hidima ga jama'a. A tsarin dimokuraɗiyya, ana bai wa 'yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu, amma tambayar ita ce: ta yaya za mu tabbatar da cewa wannan zaɓe yana haifar da shugabanci mai adalci, gaskiya, amana da bin doka? A yau za mu duba ginshiƙan shugabanci na gari, rawar shugabanni da jama'a, da kuma manyan ƙalubalen da ke hana samun kyakkyawan shugabanci a Najeriya da Afirka.
Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da dazuka ke bayar wa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Shirin Muhallinka rayuwarka na wannnan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da ganzun daji ke bayarwa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Fitaccen attajirin Najeriya Aliko Ɗangote yau ya zama fuskar Afrika a harkokin kasuwanci, da zuba hannayen jari, inda shugabannin ƙasashen Duniya ke nemansa ruwa a jallo domin zuba jari a ƙasashensu ta hanyar samar da masana'antu. Bayan samar da gagarumar matatar man fetur a Najeriya, a kan dala biliyan 20, wadda a yau kimarta ya zarce Dala biliyan 40, yanzu haka ya fara aikin faɗaɗa ta domin zama mafi girma a Duniya, baya ga shirinsa na gina wata sabuwar matatar man a Gabashin Afrika. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziƙi, Hon Sama'ila Muhammad, a kan wannan shahara ta Ɗangote. Sai a latsa alamar sauti da ke sama domin sauraron wannan tattaunawa.
Masu ruwa da tsaƙi a harkokin tattalin arziki sun yabawa Najeriya dangane da ci gaba da kasuwar hannayen jarin ƙasar da ta zama ta farko a duniya, wajen zarce ta Seoul da London da kuma New York, sakamakon wasu sauye sauye da aka aiwatar. Domin sanin irin matakan da suka samar da wannan ci gaba, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. Umar Kwairanga shugaban majalisar gudanarwar hukumar kula da hada-hadar hannayen jarin Najeriya, lokacin wata ziyara da ya kawo ofishin RFI Hausa a Lagos.
Shirin samar da kudin bai ɗaya na ƙasashen ECOWAS ya sake samun koma baya saboda sanarwar ƙasar Guinea na ficewa. Domin sanin tasirin matakin da kuma abinda ke iya haifarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Dauda Muhammad Kontagora, masanin tattalin arziki a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar.
Shirin samar da kuɗin bai ɗaya na ƙasashen ECOWAS ya sake samun koma baya saboda sanarwar da ƙasar Guinea ta bayar da ficewa da shirin. Domin sanin tasirin matakin da kuma abinda ke iya haifarwa , Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. Dauda Muhammad Kontogora, masanin tattalin arziki a Najeriya, ku danna alamun saurare domin jin yadda zantawar tasu ta kasance.
Hukumar zaɓen Najeriya ta gabatar da jerin sunayen ƴan takarar zaɓen shekara mai zuwa da takardun shaidar ilimin da suka mallaka. Bisa doka ana buƙatar duk mai sha'awar tsayawa takara ya gabatar da shaidar kammala karatun firamare kafin ya shiga a dama da shi, daga muƙamin Kansila zuwa shugaban ƙasa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barrister El-Zubair Abubakar, ga kuma yadda tattaunawar su ta kasance.
Shirin ya duba kungiyar matan zumunta da ke hada kan mata mabiya addinin Kirista a majami'u don tallafa wa juna da hidimta wa ubangiji,
Shirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shrin tare da Abdullahi Isa
Shirin "Mu Zagaya Duniya" tare da Oumarou Sani kamar kowanne mako ya taɓo muhimman labaran da suka faru a sassa daban daban na Najeriya ciki har da zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, kana dambarwar ma'aikatar Bogi a Najeriya sai kuma batun cika shekaru 3 da faro mulkin Soji a Najeriya sannan batun ficewar Chadi daga kotun ICC. Zamu soma shirin daga Najeriya inda batun kirkirar ma'aikatar Bogin nan ta PFIPC karkashin jagorancin Adeniyi Adeyimi Mattew wadda ke habbaka hulda da zuba jari ta sake tayar da kura a kasar . Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Daukacin kasashe 55 dake cikin hukumar kwallon kafar Turai sun kaɗa kuri'ar kin amincewa da shirin sayar da hannayen jarin FIFA, tare da barazanar kauracewa wasannin cin kofin duniyar da za'a gudanar nan gaba. Kasashen sun yi fatali da shirin shugaban FIFA Gianni Infantino na sayar da kashi 20 na hannun jarin kamfanin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Tsohon Sakatare Janar na hukumar kwallon kafar Najeriya, Hon Sani Ahmed Toro. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...
Kungiyar agaji ta ICRC ta rage alkaluman mutanen da ƴan uwan su ke nema a yamkin arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon tashin hankalin boko haram, daga dubu 24,000 zuwa dubu 17,000. Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwar da ta rabawa manema labarai. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan hulda da manema labarai na kungiyar, Aliyu Dawobe wanda ya bayyana mana dalilan rage alƙaluman. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...
Chadi ta zama ƙasa ta biyar da ta bi sahun ƙasashen da suka bayyana aniyar ficewa daga ƙarƙashin kotun hukunci kan manyan laifuka ta Duniya ICC. A jiya Litinin ne dai gwamnatin Chad ta sanar da fara shirin, saboda abinda ta kira gazawar kotun Duniyar wajen sauke nauyin da ke wuyanta, inda ta fi karkata hukunce-hukuncenta kan ƙasashen Afrika. Don jin yadda masana dokoki ke kallon wannan lamari, da kuma makomar Kotun Duniyar, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Umar Usman Ɗanbaito da ke Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata cibiyar da ke sa'ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka. Cibiyar ta ce adaɗin ya zarce jimillar kuɗin da aka ware wa manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya guda bakwai. Batu da ya janyo ce-ce-ku-ce. A cikin rahotonta, Cibiyar ta nuna cewa gwamnatin ta ware kusan Naira biliyan 960 ga ma'aikatun Sufurin Jiragen Sama, Gidaje, Harkokin Mata, Ciniki da Masana'antu, Shari'a, Kiwon Dabbobi da Albarkatun Man Fetur, amma kuma ta ware kusan Naira biliyan 963 domin sayen motoci da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Yan bindiga a Najeriya sun sace wani babban mai shari'a a jihar Kebbi, kwanaa guda bayan kama shugaban karamar hukuma a jihar Zamfara. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da suke cigaba da sace mutane a yankin ba tare da kakautabawa ba. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hira da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Farfesa Bello Bada......
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...
Sau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma. Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la'akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau'in kayan abinci.
Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani ya mayar da hankali kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin wanda ya taɓo dukkanin batutuwa kama da tsaro da tattalin arziƙi, siyasar ƙasashe dama rikice-rikice.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da kama wasu mutane 7 da ake zargin manyan kwamandojin ƴan ta'adda ne na ƙungiyar Boko Haram da ISWAP jim kaɗan bayan da suka sauka a filin jiragen saman jihar Katsina a arewa maso yammacin ƙasar daga Saudiyya. Tuni dai lamarin ya zama batun da ake tafka muhawara akai, musamman kan yadda ‘yan ta'addan suka samu damar sulalewa zuwa wajen Najeriya ba tare da an cafke su ba tun da fari. Shiga alamar sauti don sauraron hirar da Nura Ado Suleiman ya yi da Aminu Bala Sokoto, Squadron Leader mai ritaya....
Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Wasu sabbin alƙaluma da ƙwararru suka fitar, sun nuna cewa adadin amfanin gonar da ake fitarwa daga Najeriya zuwa ƙasashen ƙetare ya ragu da aƙalla kaso 31 cikin 100, sakamakon yadda ƙasashe musamman na Turai da Asiya ke ƙin karɓar kayayyakin abincin, ciki har da Wake da Zoɓo da dai sauransu. Rahoton dai ya bayyana amfani da magungunan kashe ƙwari fiye da kima, a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da ke kan gaba wajen janyowa Najeriya wannan hasara. Shiga alamar sauti don sauraron hirar da Nura Ado Suleimane ya yi da Farfesa Shehu Ado Garki, tsohon shugaban Jami'ar Al-Qalam da ke jihar Katsina, kuma ƙwararre a fannin noma.....
Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan nasarar da jihar Kano ke iƙirarin samu bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu raguwar mace-macen mata a lokacin haihuwa a sassan jihar wadda a baya ke sahun gaba wajen asarar rayukan ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko goyon ciki Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumar Sani ya yi bitar wasu daga cikin manyan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi ciki har da nasarar kuɓutar da dalibai tare da malamansu 40 a jihar Oyo da ke Najeriya bayan sun shafe kwanaki 50 a hannun wadanda su kayi garkuwa dasu.
Matsalar tsaro ta hare-haren da ‘yan ta'adda kan kai wa makarantu ko ɗalibai a sassan Najeriya, na ci gaba da ci wa al'ummar ƙasar tuwo a ƙwarya, la'akari da cewar ko a baya bayan nan, ‘yan bindiga sun kai hari tare da sace wasu ɗaliban wata Sakandare a ƙaramar hukumar Dekina da ke jihar Kogi. Wannan ya zo ne bayan hare-haren da a makwannin baya makarantun suka fuskanta a jihohin Oyo da kuma Borno. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da shugaban ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya, Comrade Audu Titus Amba. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga rundunar sojin saman ƙasar da ta buɗe ɓangaren hanyar Maiduguri zuwa Kano da ta toshe a anguwar Ngomari-Pompomari da ke wajen birnin Maiduguri kusan shekaru 10 wanda ke haddasa asarar ɗumbin rayuka. Ɗan Majalisa mai wakiltar Jere a jihar Borno, Hon. Satomi da ya gabatar da ƙudirin gaban Majalisar a makon jiya, ya yi wa Ahmed Abba ƙarin bayani dangane da girman matsalar da toshe hanyar ya haifar da kuma ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen ceto ɗalibai da malamai da Boko Haram ta yi garkuwa da su a Askira-Uba na jihar Borno. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.
Shin ko addini na da tasiri ga rayuwar Musulmi, wajen hana su yin kabilanci? Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci, ya yi nazari a kan wannan batu.
Yayin da ake ci gaba da jinjina wa rundunar sojin Najeriya saboda nasarar ceto ɗalibai da malamai 44 da ƴanbindiga suka yi garkuwa da su a jihar Oyo, wasu na gani cewa ya kamata mahukunta su ƙara azama don ceto ɗaruruwan mutanen da ake ci gaba da yin garkuwa da su a sasan ƙasar. Ko a jiya lahadi ɗimbin mutane ne suka gudanar da zanga-zangar neman gaggauta ceto ɗalibai da dama da ake yin garkuwa da su a jihar Borno ciki har da waɗanda aka sace rana ɗaya da na jihar Oyo. Abdoulkarim Ibrahinm Shikal ya zanta da Ibrahim Garba Wala da ke bin diddigin wannan batu na taɓarɓarewar tsaro a Najeriya, ga kuma zantawarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
Shirin a wannan makon zai leka Gabas ta Tsakiya inda rikici ya sake barkewa tsakanin Amurka da Iran abin da ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta watanni uku da suka cimma a tsakaninsu. Bayan nan, shirin zai taɓo wasu mahimman lammuran da suka wakana a sassan yammacin nahiyar Afirka, musamman Najeriya, Nijar da Kamaru.
Cikin makon nan, kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya, ta kafa tarihin zama mafi ƙarfi gami da bunƙasa a faɗin Duniya, bayan zarta mai riƙe da kambun a baya bayan nan, wato takwararta ta Korea ta Kudu. Rahoton kamfanin Bloomberg ya nuna cewa, zuwa yanzu Kasuwar ta Najeriya ta samu tagomashi ne da kaso 67 cikin 100, yayin da ta Korea ta Kudu ke da kaso 66. Domin jin ƙarin bayanin kan dalilan samun wannan nasara, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Ƙasim Garba Kurfi, ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a kasuwar hada-hadar hannayen jarin ta Najeriya. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawar...
Majalisar dattijan Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta dakatar da shirin yin afuwa ko kuma sauya ɗabi'un tubabbun ƴan ta'adda a wani yunƙuri na dawo da su cikin al'umma, wanda ta ce ba ya taimakawa ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen yaƙi da ta'addancin da ya yi mata katutu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Najeriya na tattaunawa da China wajen ganin ta samu goyon bayan da ya dace a fasahar zamani da kuma makamai domin shawo kan matsalolin tsaro da suka addibi ƙasar. Sabon jakadan Najeriya a ƙasar China Janar Abdurrahman Bello Dambazau mai ritaya ya bayyana haka a tattaunawar da suka kayi da Bashir Ibrahim Idris. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar.
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku, ya ce mutunta addinan juna, daina furta kalaman ƙiyayya ko tsatsauran ra'ayi, abubuwa ne da za su iya taimakawa ta fannin kyautata zamantakewa a tsakanin al'umma. Wannan dai gargaɗi ne da ke ƙunshe a sanarwar da aka fitar bayan ganawar da aka yi a babban masallacin birnin Abuja tsakanin mai alfarma Sarkin Musulmin da kuma tawagar manyan jami'an Fadar Vatican ƙarƙashin jagorancin Archibishop Paul Richard Gallaghera. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Shirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al'ummomi a yankunan ƙarƙara.
A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sabon rahoton hukumar UNICEF ya nuna cewa, jihohin Kano, Katsina, da Jigawa ne ke kan gaba a faɗin Najeriya wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inda a faɗin kasar kuwa, akwai yara sama da miliyan goma sha takwas da dubu ɗari uku da makoma ta iliminsu ke cikin haɗari. Sau da yawa, wannan zargi na komawa ga gwamnati, sai dai abin tambayar shine, shin ko laifin na iyaye ne da al'umma, ko kuwa suma hukumomi akwai nasu kason? Mun ziyarci garin Meshumi da ke karamar hukumar Ungoggo a jihar Kano, inda shirin ya tarar makarantar firamare na nan a gine, amma dakin karatu ya zama kufai. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Shamsiyya Haruna
Shirin na Lafiya Jari ce zai a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
A Najeriya, daidai lokacin da ake neman sanin matsayin shugaba Bola Tinubu dangane da zargin kafawa da kuma tafiyar da wata ma'aikatar jabu a ƙarƙshin gwamnatin tarayya, sai kuma ga wasu bayanai daga Asusun Lamuni na Duniya IMF da ke cewa gwamnatin ta kashe sama da Naira triliyan 8 waɗanda sam kasafin kuɗin ƙasar bai san da su ba. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hira da Abdoulklarim Ibrahim Shikal ya yi da Kwamrad Nasiru Kura mai fafutukar yaƙi da rashawa a ƙasar..........
Ƙungiyar kare hakin bil Adam Amnesty International ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsalolin ta'addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.........
Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsaloli na ta'addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi. Ruƙayya Abba Kabara ta tattauna da daraktan Amnesty a Najeriya, Malam Isa Sanusi kan rahoton nasu. Latsa alamar sauti don sauraren sa....