POPULARITY
Kamar dai kowace shekara, 1 ga watan Disamba ita ce ranar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta keɓe don yaƙi da cuta mai karya garkuwar jikin ɗan Adam wato HIV ko kuma SIDA. Bikin na bana ya zo ne a cikin wani yanayi da shugaba Donald Trump ya katse tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashe masu tasowa ciki har da na ɓangaren yaƙi da wannan cuta. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Nasir Sani Gwarzo ƙwararren likitan yaƙi da annoba a Najeriya, wanda ya fara da bayyana halin da ake ciki game da yaƙi da HIV a ƙasar. Ga zantawarsu.
Dr. Murtala likitan yara ne dan asalin jihar Adamawar Najeriya da ya rikide ya zama kwararren masanin lafiyar al'umma musamman mata da yara, wanda a yanzu haka ma'aikaci ne a wata kungiya mai zaman kanta da ta ke tallafawa harkokin lafiyar iyali a duniya ciki har da kasashen Afirka mai suna Pathfinder International da ke kasar Amurka.Murtala Mai | Madubin Usman Kabara #11
‘Yar Nijar kuma masaniyar kimiyyar ruwa da doron kasa da ke aiki a hukumar sama-jannatin Amurka ta NASA. Dr. Fadji Maina tana cikin wacce mujallar tereren arziki ta Forbes ta wallafa sunanta a cikin matasan duniya guda 30 ‘yan kasa da shekara 30 da suka sami nasara a rayuwa. Yanzu haka ma'aikaciya ce a hukumar sama jannatin Amurka ta NASA da ke aiki bisa kwarewar ta a fannin ruwa da kimiyyar doron kasa.
A shekarar 1984 a Najeriya an sami wani saurayi dan jihar Kano da ya fi kowane dalibi a Najeriya cin makin jarrabawar gama sakandaren kasashen Afirka ta WAEC a takaice. Yanzu haka dai wannan dalibin mai suna Farfesa Sarki Abba Abdulkadir farfesa ne a bangaren haddasuwar cututtuka a Jami'ar Northwestern University da ke Chicago a Amurka.
Adamu Hamza Bamalli ya sha gwagwarmaya a Najeriya da Amurka kama daga zama direban babbar mota zuwa rikidewa ya zama kwararren Injiniya a jihar Maryland ta Amurka.
Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako kamar yadda ya saba ya yi bitar muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi daga ɓangarori daban-daban na duniya. A Najeriya shirin ya faro da batun Siyasa inda a cikin makon da muka yi wa bankwana rikicin cikin gidan babbar Jam'iyyar adawar Najeriyar wato PDP ya zama ɗaya daga cikin batutuwan da suka ɗauki hankali. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Na ziyarci Dr. Sabo Tanimu a jihar Wisconsin ta Amurka. Yana daya daga cikin kwararrun likitocin kayan cikin bil'adama a kasar inda yake shugabantar bangaren cutar dajin da ta shafi kayan ciki. Dan asalin Najeriya ne daga jihar Benue a tsakiyar Arewacin Najeriya. Shin yaya aka yi Likita Sabo ya fara daga Najeriya har ya tsinci kansa a Amurka inda ya shafe shekaru da dama yana aikin Likita a can.
Na yi hira da Ali Nuhu Mohammed jarumin fina-finan Hausa da Turanci na Najeriya a lokacin da ya ziyarci birnin Washington DC da ke Amurka,, in da na tambaye shi darussan da ya koya a cikin shekaru 20 da ya kwashe yana harkar shirya finafinai.
Yayin da hukumomin Najeriya suka yi watsi da barazanar shugaban Amurka na kai wa ƙasar hari saboda zargin kashe Kiristoci, ƴan kasar da dama na ci gaba da bayyana ra'ayi a kan matsayin na shugaba Donald Trump. Daga cikin waɗanda suka bayyana ra'ayin su a kan wannan barazana har da tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran, Ambasada Abubakar Cika, kamar yadda za ku ji a tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris.
Ga alama yajejeniyar tsagaita wutar da Isra'ila ta ƙulla tsakaninta da Hamas, wadda Amurka ta tsara ta kama hanyar rugujewa, sakamakon umarnin da Firaminista Benjamin netanyahu ya bayar na ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza. Wannan ya biyo bayan abinda ya kira ƙin bada gawarwakin sauran Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su. Domin tattauna wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris, ya tuntuɓi Dakta Abdulhakin Garba Funtua, mai sharhi a kan harkokin Gabas ta Tsakiya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.........................
Daga cikin labarun da shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan makon ya kunsa akwai labarin matakin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ɗauka na yin tankaɗe da rairaya a manyan hukumomin tsaron ƙasar, inda ya sallami manyan hafsoshin tsaron ƙasar, dai dai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe ‘yan ta'adda fiye da 50 yayin wasu jerin hare-hare da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar kusan lokaci guda a kan garuruwan daban daban a jihohin Borno da Yobe. Shirin ya waiwayi wasu daga cikin lamurran da suka wakana a Kamaru inda ake cigaba da dakoon Kotun Fasalta Kundin tsarin mulki ta tabbatar da sakamakon zaɓen shugabancin ƙasar. A yankin gabas ta tsakiya, Amurka ta hau kujerar naki kan yunƙurin wasu na ganin Isra'ila ta kwace iko ya yankin Falasɗinu na Gaɓar yamma da kogin Jordan.
Shirin a wannan mako ya mayar da hankali ne kan wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya ta 2026 da ƙasashen Amurka, Mexico da Canada za su karɓi baƙunci. A Nahiyar Afrika tuni dai wasu ƙasashe suka sami tikitin zuwa gasar da suka haɗar da Morocco da Tunisia da Aljeriya da Ivory Cost, sai dai ƙasashen Najeriya da Afrika ta Kudu da kuma Senegal na cikin halin rashin tabbas, sai dai a wannan Talata ne za su san makomarsu. Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abubakar Isah Ɗandago..................
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Michael Kuduson a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda aka samar da wata katafariyar cibiyar bunƙasa harkokin noman Damuna dana Rani ga al'ummar jihar Kano wadda aka samar a garin Kadawa da ke ƙaramar hukuamr Garin Malam. bayanai sun ce wannan cibiyar bunƙasa noma na ƙunshe da tarin kayakin buƙata a lokacin noman walau na rani ko kuma na damuna duk dai a ƙoƙarin haɓaka harkar noma a jihar ta Arewa maso yammacin Najeriya. Bankin Musulunci da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kanon ne suka samar da wannan cibiya wadda ta laƙume biliyoyin dalolin Amurka ƙarƙashin shirin KSSB na haɓaka noma bisa kulawar SASAKAWA. Ku latsa alamar tsari don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.....
Daga cikin labarun da shirin 'Mu zagaya Duniya' tare da Nura Ado Sulaiman, ya waiwaya a wannan makon akwai halin da ake ciki a Zirin Gaza bayan yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin da aka samu nasarar ƙullawa tsakanin Isra'ila da Hamas.Shirin ya kuma waiwayi zaɓen shugabancin Kamaru wanda masu fashin baƙi ke ci gaba da tofa albarkacin bankinsu a kai. A najeriya kuma akwai waiwayen afuwar da shugaba Bola Tahmed Tinubu ya yi wa wasu mutane fiye da 170 Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...........
Shirin ‘Kasuwa A Kai Miki Dole' na wannan mako zai tattauna ne kan wasu alƙaluma da suka nuna yadda Najeriya ta Kashe Dala Biliyan 2.86 a cikin watanni 8 na farkon shekarar da muke ciki ta 2025, wajen Biyan Kuɗin Ruwan Basukan da ta karɓo daga ƙasashen ƙetare tare da Nura Ado Suleiman..... Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...........
A cikin wannan shirin da ke waiwaye kan mahimman labaran wannan makon, za ku ji cewa: Faransa ta jagoranci ƙarin gwamman ƙasashe wajen amincewa da Yankin Falasɗinu a mamtsayin ƙasa ‘Yantacciya a wani yunƙuri na Diflomasiya da ke zama ɗaya daga cikin mafiya girma da aka gani cikin shekaru da dama. Shirin zai kuma waiwayi jawaban wasu daga cikin shugabannin Nahiyar Afrika a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya. Najeriya ta yi fatali da rahoton Amurka da ya zargi mahukuntan ƙasar da gazawa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na aiwatar da ayyukan raya ƙasa da akw warewa maƙudan kuɗaɗe a kasafi duk shekara. Da dai sauran mahimman labarai.
Shirin Ra'ayoyin mai Saurare na wannan ranar Alhamis 25 ga watan Satumbar 2025, wanda Oumar Sani ya gabatar, ya tattauna ne kan matakin gwamnatin Amurka na hana duk wani ɗan Najeriya ciki har da jami'an gwamnati da aka samu da hannu da rashawa bisar da za ta ba su damar shiga ƙasar.
Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewar ƙasashensu daga Kotun Hukunta Laifufuka ta Duniya da ke birnin Hague. A sanarwar haɗin-gwiwa da suka fitar cikin daren litinin da ta gabata, ƙasashen uku sun ce sun ɗauki matakin saboda sun lura cewa kotun ta rikiɗe domin zama ƴar amashin ƴan mulkin mallaka. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani dokokin ƙasa da ƙasa Maitre Lirwanou Abdourahman, domin jin ko wataƙila ya yarda da dalilan da wadannan ƙasashe suka gabatar. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.
Ƙasashen duniya na ci gaba da nuna amincewarsu da samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu, a wata guguwa wadda ba'a taɓa ganin irinta ba. Ƙasashen turai da ake ganin suna da ƙyakyawar alaƙa da Amurka irinsu su Burtaniya, Canada da kuma Australia a wannan Karo sun sanar da amincewar su da baiwa Falasɗinu damar zama ƙasa mai cin gashin kanta amma bisa wasu shariɗoɗi. A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce har yanzu da sauran rina a kaba don kuwa amincewar waɗannan ƙasashe ƙadai a fatar baki bata wadatar ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
Shirin Al'adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la'akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama'ar gari ke tofa albarkacin bakunansu akan karramawar da wata Jami'a mai suna European-American University ta yi wa fitaccen mawaƙin siyasa a Najeriya Dauda Kahutu Rarara, wanda ta bai wa Digirin Girmamawa na Dakta. Reshen Jami'ar da bayanai a yanar gizo suka nuna cewar hedikwatarta na ƙasar Faransa ne ta yi bikin Karrama mawaƙi Raran ne a Abuja, ranar Asabar, 20 ga watan nan na Satumba, taron da ya samu halartar wasu fitattun mutane. Sai dai Kash! ‘yan sa'o'i bayan bikin da aka yi Jami'ar da ake alaƙanta da Turai da Amurka ta ce ba ta fa san zance ba, domin ba da yawunta aka miƙa wa fitaccen mawaƙin siyasar Digirin na Girmamawa ba, zalika dukkanin mutanen da suka yi iƙirarin alaƙanta kansu da ita ta barranta da su, domin sun yaudari mutane ne da sunanta domin samun damar karɓar na goro a huce. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin a wanan mako tare Khamis Saleh, ya yi duba ne kan makomar tawagar Najeriya a ƙoƙarin neman gurbin zuwa gasar lashe kofin duniya, inda a tsakiyar makon da ya gabata aka kammala wasannin na 8 na sharen fagen zuwa gasar lashe kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka za su karɓi bakunci a shekara mai zuwa. Kawo yanzu dai wasanni sun ɗauki zafi ganin cewa wasu daga cikin tawagogin ƙasashen sun fara jin kanshin halartar gasar, amma kuma wasu har yanzu tana ƙasa tana dabo. Latsa alamar sauri domin sauraron cikakken shirin.....
A karon farko gwamnatin Najeriya ta hannun hukumarta da ke kula da sufurin jiragen ruwa a koguna ko kuma cikin gida, ta shelanta haramta jigilar duk wani jirgi ko kwale-kwale da ba a yi wa rijista da gwamnati ba, Ghana ta karɓi baƙi ‘yan Afirka ta yamma, waɗanda gwamnatin Amurka ta taso ƙeyarsu a ƙarƙashin shirin shugaba Donald Trump na korar baƙin-haure, wasu kenan daga cikin manyan labarun makon jiya da Nura Ado Suleiman zai kawo muku a cikin shirin Mu zagaya Duniya.. Latsa alamar sauti don sauraron shirin..........
Wasu daga cikin labarun makon da ya gabata da shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya waiwaya a wannan karon sun haɗa da, nasarar da rundunar Sojin Najeriya ta samu na kashe ‘yan ta'adda kusan 600 da yarjejeniyar sayen makamai da ƙasar ta ƙulla da Amurka. Sai kuma a fannin tattalin arziƙi, inda wata tawaga ta musamman daga ƙasar Qatar ta fara ziyarar makwanni kusan 3 a wasu ƙasashen nahiyar Afrika domin ƙulla yarjeniyoyi gami da zuba hannayen jarin biliyoyin Dalar Amurka a ƙasashen aƙalla 10.
A ranar Jumma'a ake saran shugaban Amurka Donald Trump zai yi wata ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin dangane da yadda za'a kawo ƙarshen yaƙin da ake gwabzawa a Ukraine. Sai dai wasu da bayyana damuwa kan yadda shugabannin suka manta da batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza, ganin yadda ake ci gaba da asarar rayukan ɗimɓin rayuka. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. Abdulhakeem Garba Funtuwa dangane da yunkurin ƙasashe duniyar na samaun tsagaita wuta da kuma watsi da halin da ake ciki a Gaza.
Shirin ya mayar da hankali ne kan yadda matakin Amurka na janye tallafin da take ba wa ɓangaren kula da masu fama da cuta mai karya garkuwa jiki ta HIV da ake fargabar zai iya haifar da koma baya ga shirin yaƙi da cutar. Tuni hukumomi a duniya suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan mataki da shugaban Amurka, Donald Trump ya ɗauka, wanda ake ganin zai fi yin tasiri ne ga nahiyar Afirka. Tuni mujallar Lancet ta Biritaniya ta yi hasashen cewa matakin na Donald Trump na iya haifar da mutuwar mutane sama da miliyan 14 nan da shekarar 2030, ciki har da yara sama da miliyan 4.5 'yan kasa da shekaru biyar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashi Aminu.
To kamar yadda akaji a matashiyar shirin, ra'ayoyin masana tattalin arziki sun banbanta a Najeriya, tun bayan da sananne a harkar tattalin arziki Bismark Rewane ya tabbatar cewa Naira ta daidaita tsakanin 1500 zuwa 1560 kan kowace dala a makonnin baya-bayan nan, yayin da tattalin arzikin ƙasar kuwa ya fara farfadowa sakamakon matakin babban bankin na Najeriya CBN da ya sanya zunzurutun ƙudi har dalar Amurka biliyan 4 da miliyan 100 cikin watanni shida na wannan shekara...ta 2025.
Shirin Tambaya da Amsa na wanan makon tare da Nasiru Sani ya amsa wasu daga cikin muhimman tambayoyin da ku masu sauraro ku ka aiko mana. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkaen shirin....
Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta Najeriya ta ce adadin mutanen da ‘yan ta'adda suka kashe a cikin watanni shidan farko na wannan shekara, ya zarce adadin da aka lissafa a shekarar bara. Ƙungiyar direbobin motocin dakon kaya a Senegal ta koka kan matsalolin tsaro da suka fara shafar yankunan kan iyakar ƙasarsu da Mali, inda ta yi barazar dakatar zirga-zirga zuwa Malin muddin mahukunta suka gaza ɗaukar matakan da suka ɗace. Kakakin majalisar dokokin Kenyan ya goyi bayan bai wa ‘yan sandan Umranin harbe duk mai zanga-zangar da aka samu yana satar dukiyar jama'a da lalata kayan gwammnati. A Amurka kuwa Ambaliyar ce ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 119 Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
Rahotanni daga Amurka na cewa an samu ƙaruwar yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon Iftila'in Ambaliyar ruwan da ya afka wa Jihar Texas, inda zuwa yanzu adadin ya haura mutane 115, yayin da har aynzu aka gaza gano wasu aƙalla 160 da suka ɓace. Domin jin halin da ake ciki da kuma dalillan da suka haddasa aukuwar ambaliyar a Texas, Nura Ado Suleiman ya tattauna da mazaunin ƙasar ta Amurka, Alhaji Garba Suleiman Krako Madakin Saminaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
A ranar Litinin ƙasashe manbobin ƙungiyar BRICS suka kammala taronsu na 17 a Brazil, inda a cikin kwanaki biyu da suka shafe suna ganawa, jagororin ƙasashen suka tattauna a kan yadda manufofin shugaba Trump ke tasiri kan tattalin arziƙi da kasuwancin Duniya. Sai dai tun kafin kammala taron, shugaba Trump ɗin ya yi barazanar lafta harajin kashi 10 kan kayayyakin ƙasashen na BRICS, da ma duk wata ƙasa da ta goyi bayan matakan adawa da manufofin Amurka. Kan wannan batu, da kuma tasirin ƙungiyar ta BRICS Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau, masanin tattalin arziƙi da ke Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..
Yau ake cika shekaru 80 da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da ta samar da Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar a Birnin San Francisco da ke Amurka, a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 1945. Bikin cika shekaru 80 din na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar mai wakilai 193 ke fuskantar kalubale da dama, waɗanda suka hada da makomar ta ko kuma ci gaban tasirinta baki ɗaya. Kan wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Chika, tsohon jakadan Najeriya a Iran. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..........
Shirin Duniyar wasanni na wanan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne akan gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi da aka bude a karshen mako a ƙasar Amurka dama sauye -sauyen da aka samu a bana. Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shiri........
A yau shirin tamabaya da amsa, tare da Nasiru Sani, zai kawo muku bayanai ne akan tasirin tsarin harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙabawa ƙasashen Canada da Mexico da kuma China akan ƙasashe Afirka. Shirin ya kuma zanta da kwararru a fannin lafiya, kan dalilan da ke sanya shan ruwa a kai.Akwai kuma cikakken bayani kan Sultan Makenga, wato jagoran ƙungiyar 'yan tawayen M23 wanda ya hana zaman lafiya a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, musamman ma a gabashin ƙasar.Shiga alamar sauti, domin saurarin cikakken shirin.
Yau shugaban Amurka Donald Trump le cika kwanaki 100 a karagar mulkin ƙasar, tun bayan rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairun shekarar nan. A tsawon wannan lokaci, shugaban na Amurka ya ɗauki mabanbantan matakai da suak girgiza sassan duniya.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir na Jami'ar Kaduna, don jin yadda masana ke kallon salon kamun ludayin Donald Trump ga kuma tattaunawarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..
Gwamnatin shugaba Donald Trump ta gabatar da ƙudurin daina ba da tallafi ga rundunonin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, saboda gazawar da ta ce rundunonin na yi a ƙasashen Mali da Lebanon da kuma Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo.Amurka ce dai ke kan gaba wajen tallafa wa ayyukan wanzar da zaman lafiyar a sassan Duniya, inda take samar da kusan kaso 27 cikin 100 na kasafin da ake buƙata.akan haka ne, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Kamilu Sani Fagge.
Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman, kamar kowannen mako kan yi bitar muhimman labaran da suka faru cikin makon da muke ban kwana da shi, kuma kamar kodayaushe a wannan karon wasu daga cikin labaran da ke ƙunshe a shirin sun ƙunshi ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Najeriya ya kai Jamhuriyar Nijar, wadda a karon farko kenan tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum da sojoji suka yi. A Najeriya shirin ya leƙa Filato aka samu hasarar ɗimbin rayuka, sakamakon hare-haren da aka kai a wasu yankunan jihar, a Najeriyar za a ji yadda wata shu'umar cuta ta janyowa manoman Tumatir hasarar ɗimbin amfanin gonar, sai kuma yadda ‘yan damfara suka yi awon gaba da sama da naira tiriliyan 1 a Najeriyar.A Sudan kuwa ƙungiyar bayar da agaji ta Redcross ce ta aƙalla mutane dubu 8000 suka bace a yakin kasar.Sai kuma Kenya inda aka cafke wasu mutane da ke shirin fasa kaurin dubban tururuwa zuwa ƙasashen ƙetare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan tasirin matakin shugaban Amurka Donald Trump kan shirin sa na sanya gagarumin ƙarin haraji ga kusan ɗaukacin ƙasashen duniya, wanda ya jawo durƙushewar kasuwannin hannayen jari ta duniya da lalata alaƙa tsakanin ƙasar da ƙawayenta, duk da cewa ya yi amai ya lashe wajen dakatar da harajin da watanni uku masu zuwa. Shirin ya duba tasirinsa ga ƙasashen Afirka masamman Najeriya.
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan ƙaruwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki ko kuma HIV AIDS ko sida tsakanin matasan Ghana a shekarun baya-bayan nan, wadda masana ke ɗora alhakin yawaitarta kan rashin ɗaukar matakai. Wannan ƙaruwar alƙaluma na zuwa a dai dai lokacin da duniya ke ganin ƙarancin magunguna rage kaifin cutar sakamakon matakin Amurka na zaftare tallafin da ta ke bayarwa ƙarƙashin ƙungiyar USAID.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.
A Laraba 9 ga watan Afrilu, sabon harajin da ya kama daga kashi 10 zuwa sama, da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙaba wa ƙasashen Afirka zai fara aiki, bayan da harajin da ya shafi sauran ƙasashe ya soma aiki a ranar 5 ga watan na Afrilu. Tun cikin makon jiya ne dai matakin na Trump ya soma tasiri a kasuwannin Turai da Asiya, a yayin da ƙasashen Afirka suka shiga zulumi dangane da makomarsu.Don jin tasirin da sabon harajin na Amurka zai yi a kan tattalin Arzikin arziƙin ƙasashen Afirka, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Ƙasim Garba Kurfi.A latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar zanatawar.
ƙasashe da dama ciki har da na Ƙungiyar EU, suka sha alwashin mayar da martanin ƙaƙaba wa kayayyakin Amurka haraji, kamar yadda shugaba Trump ya ƙaddamar da sabon tsarin karɓar harajin da ya ce ya shafi duniya baki ɗaya.
Ƙasashe da dama ciki har da na Ƙungiyar EU, sun alwashin mayar da martanin ƙaƙaba wa kayayyakin Amurka haraji, kamar yadda shugaba Trump ya ƙaddamar da sabon tsarin karɓar harajin da ya ce ya shafi duniya baki ɗaya.Sabon harajin dai ya kama ne daga kashi 10 zuwa sama, wanda ya shafi hajoji daga kowace ƙasa, matakin da Trump matakin ya ce ya ɗauka ne don kare buƙatun al'ummar Amurka. Don jin yadda masana ke kallon sabon yaƙin kasuwancin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta AbdulHakim Garba Funtua.
A yayinda aka cika shekaru 3 cif da faro yaƙi tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine maƙwabtan juna, dukkanin ɓangarorin biyu sun tafka gagarumar asara marar misaltuwa a wannan ɗan tsakani kama daga Sojojinsu da ke fagen daga da kuma kayakin more rayuwa da kowacce ta lalatawa ƴar uwarta. A baya-bayan nan anga yadda shugaban Amurka Donald Trump ke ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yaƙi ta hanyar tuntuɓar Vladimir Putin na Rasha a wani yanayi da tuni aka faro taron tattaunawa kan kawo ƙarshen wannan yaƙi a Saudiya kodayake batun bai yiwa ƙasashen Turai daɗi ba, ganin yadda basu samu goron gayyata a tattaunawar ba, haka zalika itama Ukraine.Dangane da wannan dambarwa ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua masanin siyasar ƙasashe ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar...
Shirin na Tambaya da amsa na baiwa masana damar kawo ƙarin haske a wasu daga ciƙin tambayoyinku daga nan Rfi,shin ko wata kasa a doron duniyar nan, ta taba fusƙantar irin gobarar da ta tashi a birnin Los Angeles na Amurka kuma duk da kasancewarta babbar ƙasa mai isassun kayan aiki,ko mai ya hana ya hana Amurka samun nasarar shawo kan gobarar a cikin ƙanƙanin lokaci
Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarnin sanya takunkumi akan kotun duniya ta ICC da kuma haramtawa jami'anta dake binciken 'yan kasarsa ko kuma kawayen Amurka irin su Isra'ila. Abin tambayar shine, wanne irin tasiri wannan mataki zai yi?Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru, masanin shari'a a Jami'ar Baze, da ke Nijeriya.
Ƙasashen duniya sun bayyana matukar rashin amincewarsu da buƙatar shugaban Amurka Donald Trump, na ƙwace Gaza da kuma mayar da Falasdinawa wasu ƙasashe domin gina wurin shaƙatawa a ƙasarsu. Wannan matsayi ya gamu da suka daga ƙasashen duniya da dama ciki harda Majalisar Ɗinkin Duniya. Bashir Ibrahim Idris ya tatatuna shirin da Ambasada Abubakar Cika, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Iran. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.........
Ƙasashen duniya na ci gaba da bayyana damuwa dangane da shirin shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da ayyukan hukumar USAID wadda ke taimakawa ƙasashen duniya . Wannan hukuma dai na taka gagarumar rawa a bangarori da dama a ƙasashe masu tasowa irin su Najeriya.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara a kan harkokin noma dangane da tasirin matakin a kan noman ƙasar.Latsa alamar sauti domin sauraren yadda tattaunawar ta kasance....
Bayan shafe watanni 15 ana gwabza mummunan yaƙi a yankin Gaza tsakanin sojojin Isra'ila da mayaƙan Hamas da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, shugabaan Amurka, Donald Trump ya ce yaƙin ya lalata yankin na Gaza baki daya, don haka ya bayyana wa Sarki Abdallah na Jordan buƙatar kwashe Falasɗinawa daga yankin zuwa ƙasarsa kuma ya ce ya na sa ran tattaunawa da shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi a kan haka. A kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da masanin lammuran da suka shafi Gabas ta Tsakiya, Malam Isma'il Ahmad.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............
A ƙasar Amurka, bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaba ƙasa na 47, Donald Trump, ya rattaba hannu kan wasu gomman dokokin zartawa na ikon shugaban ƙasa, ciki har da janye ƙasarsa daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kamar yadda ya yi a wa'adin mulkinsa na farko, kafin magabacinsa Joe Biden ya maido da ƙasar ciki. Wasu na ganin wannan mataki zai yi illa ƙwarai ga ɗorewar hukumar wajen gudanar da ayyukan ta a duniya, duba da kaso mai tsoka da Amurka ke bayarwa wajen gudanar da ayyukan WHO ɗin.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa daga cikin mambobin Hukumar Lafiya ta Duniya, matakin da wasu ke ganin na iya illa ga dorewar hukumar wajen gudanar da ayyukan ta a duniya. Dangane da tasirin matakin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana manufofin gwamnatinsa bayan karbar rantsuwar kama aiki da ya yi a matsayin shugaba na 47. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua na Babbar kwalejin Fasaha ta Kaduna dangane da wadannan manufofi, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.