Podcasts about najeriya muhammadu buhari

  • 5PODCASTS
  • 11EPISODES
  • 7mAVG DURATION
  • ?INFREQUENT EPISODES
  • Dec 28, 2021LATEST

POPULARITY

20172018201920202021202220232024


Best podcasts about najeriya muhammadu buhari

Latest podcast episodes about najeriya muhammadu buhari

Bakonmu a Yau
Mustafa Fanandas: Game da gazawar mulkin Buhari a Najeriya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Dec 28, 2021 3:36


Kungiyar masu hankoron kare shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta koka kan yadda gwamnatinsa ta gaza wajen samar da tsaro da kuma walwala ga talakawan kasar. Shugaban kungiyar Mustafa Salisu Musa Fanandas ya ce, abubuwan da ke faruwa a Najeriya sun sha bam-bam da abin da shugaba Buhari ya shaida musu kafin hawansa kan karagar mulki. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsa da Abdurrahman Gambo Ahmad.

game ku buhari najeriya shugaban najeriya muhammadu buhari
Bakonmu a Yau
Tattaunawa da Aminu Bala Sokoto kan tsanantar hare-haren 'yan bindiga

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Dec 13, 2021 3:31


A Juma'ar da ta gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da wata tawaga mai karfi da ta kunshi shugaban hukumar tsaro ta DSS da babban sufeto janar na ‘yan sandan kasar zuwa jihohin Sokoto da Katsina sakamakon tsanantar hare-haren ‘yan bindiga wadanda a cikin makon da ya gabata suka kone fasinjoji sama da 30 wadanda ke kan hanyar balaguro a motar safa. Dangane da wannan Michael Kuduson ya tattauna da Aminu Bala Sokoto, masanin tsaro a Najeriya ga kuma zantawarsu.

bala dss juma haren sokoto katsina najeriya najeriya muhammadu buhari
Kasuwanci
Kasuwanci - Karin bayani kan sabon kudin eNaira da Najeriya ta kaddamar

Kasuwanci

Play Episode Listen Later Oct 27, 2021 9:53


Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan makon tare da Ibrahim Malam Goje ya duba sabon kudin yanar gizo na eNaira da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar, domin dacewa da zamani wajen farfado da tattalin arziki Najeriya da kuma saukaka hada-hadar kudade a yanar gizo.

dole enaira najeriya najeriya muhammadu buhari
Bakonmu a Yau
Bakonmu a Yau - Najeriya ta kaddamar da Nairar da za a rika hada hadar-ta, ta intanet wato eNaira

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Oct 25, 2021 3:41


Yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da Nairar da za a rika hada hadar-ta, ta intanet wato eNaira, a fadarsa dake birnin Abuja, kuma eNairar za ta fara aiki ne daga lokacin da aka kaddamar da ita. Matakin na zuwa ne bayan da aka jinkirta kaddamar da Nairar a farkon wannan wata na Oktoba.  Dangane da wannan batu Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Kasim Kurfi, masanin tattalin arzikin a Najeriyar, ga kuma yadda zantawarsu ta kaya.

tata abuja rika hadar enaira wato oktoba najeriya najeriya muhammadu buhari
Kasuwanci
Kasuwanci - Alfanun sabuwar dokar man fetur da Buhari ya sanyawa hannu

Kasuwanci

Play Episode Listen Later Aug 18, 2021 10:02


Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi nazari kan sabuwar dokar man fetur da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu.  Za ku iya latsa alamar sauti don sauraron shirin.

za shirin buhari hannu ahmed abba najeriya muhammadu buhari
Ilimi Hasken Rayuwa
Ilimi Hasken Rayuwa - Dakatar da harkokin kamfanin Twitter da gwamnatin Najeriya ta yi

Ilimi Hasken Rayuwa

Play Episode Listen Later Jun 8, 2021 11:14


A cikin shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon , Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali ne a kan dakatar da harkokin kamfanin sadarwa na Twitter da gwamnatin Najeriya ta yi biyo bayan goge wani sako da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa. Masana harkar sadarwa sun tofa albarkacin bakinsu.

najeriya masana bashir ibrahim idris najeriya muhammadu buhari
Bakonmu a Yau
Bakonmu a Yau - Haruna Jakolo kan shawarar shugaban Chadi na sake fasali yaki da ta'addanci

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Mar 29, 2021 3:35


Shugaban Kasar Chadi Idris Deby ya bayyana cewar rashin kai hare-hare da rundunar sojin hadin kai ta kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi ke yi na daga cikin matsalolin da suka hana samun nasarar yakin. Bayan ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Deby ya bukaci sake fasalin yakin da kuma kaddamar da Karin hare-hare. Dangane da wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sarkin Gwandu na 19, Manjo Mustapha Haruna Jokolo mai ritaya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

sake bayan kamaru yaki chadi haruna nijar najeriya shugaban bashir ibrahim idris najeriya muhammadu buhari
Bakonmu a Yau
Bakonmu a Yau - MDD ta bukaci Buhari ya yi amfani da tattaunawa wajen shawo kan matsalar tsaro a Najeriya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Aug 25, 2020 3:37


Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da yayi amfani da tattaunawa da kuma tafarkin siyasa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar. Babban Jakadan Majalisar dake Najeriya Edward Kallon ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar shugaban, inda yake cewa matsalolin tsaron da suka addabi kasar dake da sassa daban daban na da wahalar magance su. Dangane da wannan shawara Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon ministan ayyuka na musamman a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

buhari najeriya majalisar dinkin duniya bashir ibrahim idris najeriya muhammadu buhari
Bakonmu a Yau
Bakonmu a Yau - Sarkin Gwando na 19 Alhaji Mustafa Haruna Jakolo kan koma-bayan sha'anin tsaro a Najeriya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later May 22, 2020 4:11


Matsalolin rashin tsaro a yankunan jihohin arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da ciwa ‘yan asalin yankin tuwo a kwarya, kasancewar a duk rana sai kara samun munanan hare-hare ake daga ‘yan bindiga duk da matakan tsaron da ake dauka. Kan sha’anin tsaron ne Garba Aliyu Zaria ya tattauna da mai martaba Sarkin Gwandu na 19, kuma tsohon mai tsaron lafiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a zamanin mulkin soja, Alhaji Mustapha Haruna Jokolo, wanda yayi tsokaci kan halin da ake ciki da kuma mafita daga matsalar tsaron.

koma bayan haruna najeriya najeriya muhammadu buhari garba aliyu zaria
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyi kan kashe jami'an kungiyar agajin Faransa da Boko Haram tayi

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Dec 16, 2019 15:33


Kungiyar agajin kasar Faransa ta Action Against Hunger ta sanar da kashe jami’an ta guda 4 da kungiyar Boko Haram tayi garkuwa da su tun a watan Yuli. Kisan ya gamu da suka daga Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma kungiyar agajin dake taimakawa mutane 300,000 da rikicin Boko Haram ya tagayyara. Kan wannan batu muka baku damar tattaunawa a wannan litinin.

boko haram yuli kisan masu action against hunger faransa majalisar dinkin duniya najeriya muhammadu buhari
Dandalin Siyasa
Dandalin Siyasa - Shugaba Buhari ya lashe zaben Najeriya wa'adi na biyu

Dandalin Siyasa

Play Episode Listen Later Feb 28, 2019 11:01


Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne game da nasarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu ta sake lashe kujerar shugabancin kasar wa'adi na biyu bayan doke babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar. Tuni Jam'iyyar PDP ta bayyana sakamakon zaben a matsayin mara inganci tana mai zargin tafka magudi a zaben,yayinda ta ce, za ta shigar da kara a kotu.

pdp buhari atiku abubakar najeriya bashir ibrahim idris najeriya muhammadu buhari