Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka'ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyarsu na sake jifasu cikin damuwa. A cikin 'yan watannin nan, koke-koke sun mamaye kafofin sada zumunta, sakamakon rashin karin bayani kan yawaitan kudaden da bankunan ke cirewa.. Duk da cewa bankuna sun dage cewa hakan tsari ne da kuma sahalewar haka daga babban bankin kasar CBN, kwastomi na diga ayar tambaya kan cirewa fiye sau ɗaya kan, ko kuma daga wanda ya tura da kuma wanda ya ƙarba, yayin da wasu ke kokawa kan rashin maida musu kudinsu nan take idan aka samu masalar sabis kudi bai je ga wanda aka tura ba da dai sauransu... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsadar sufuri. ‘Yan kasuwa, na kukan samun wagegen gibi tsakanin uwar kudin jarinsu da abinda suke kashewa na safarar kayansu zuwa kasuwanni, saboda tsadar kudin sufuri da kuma rashin ciniki saboda halin rashin kudi da ‘yan kasar ke ciki. Kasancewar kowane sasshen Nigeria na da nau'in kayayyakin da yake da su a wadace, ‘yan kasuwa daga arewacin kasar, kan saro kayayyaki irin su Manja da Man Gyada da Garin Kwaki da makamantan su, daga kudancin kasar, yayinda ‘yan kasuwa daga kudanci, kan sayi hatsi, dabbobi da makamantan su daga arewacin kasar. Bayanan hukumar kididdiga ta Nigeria, sun yi nuni da cewa damar ikon sayen kayayyaki a kasuwanni wato purchasing power a turance, da ‘yan Nigeria ke da ita, ta ragu da kashi 21, a sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kayayyakin suka yi, da koma-bayan kudin shigar masu karamin karfi a kasar.

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon, ya duba ƙalubale da kuma damammaki a ɓangaren noman albasa a arewacin Kamaru. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Shirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama'a. Babban Bankin Nigeria, ya fito da bakin alƙalamin adadin kuɗaɗen da ke bankuna da waɗanda ake hada-hada da su a cikin ƙasa tare da waɗanda jama'a ke jujjuyawa a hannunsu. Adadin wannan kudi dai a cewar bankin na CBN, ya kai Naira Triliyan 123 da biliyan 15, a watan Fabareiru, inda aka samu raguwar adadin madarar kuɗi da ke hannun jama'a akan na watan Janairu, wanda ya kai Nera Triliyan 123 da biliyan 36. Haka ma adadin kudaden kasar a asusun ajiyarta na ketare ya ragu zuwa Nera Triliyan 28 da biliyan 41 daga Nera biliyan 29 da biliyan 61. Ku latsa alamar sauti don sauti don sauraron cikkan shirin tare da Ahmad Abba.............

Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka. Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka. To sai dai Kuma irin wannan tsarin na fuskantar cikas ko koma baya, alal misali ga yan kasuwa a jihar filato dake arewacin Najeriya, sakamakon munanan halaye na wasu bata gari marasa tausayin rayuwar Dan Adam, dake tare Yan tireda ko Kuma matafiya inda suke Kai musu farmaki, tare da yi musu kisan gilla. A kwanakin baya wasu Bata gari sun tare wasu Yan kasuwa da ke fatauci daga garin Jos zuwa yankin kudancin Jihar, inda suka kashe biyar daga cikinsu, Wannan al'amari ya Sanya Yan Kasuwar da sauran matafiya shiga hali na fargaba a kowane yanki dake jihar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Matasa a Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar na cike da fatan cin moriyar sabuwar dangatakar da aka kyautata tsakanin kasar da makwabciyarsu Aljeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba a wannan mako ya ɗora ne kan inda ya tsaya a makon jiya, game da gagarumin koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki da duniya ke fuskanta masamman a bangaren makamashi, sakamakon yaƙin da kawancen Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran, da kuma martinin jamhuriyar musuluncin kan Isra'ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo. A makon jiya, shirin ya tattauna wannan batu ne da malaman da muka gayyato, wato Dr. Aminu Idris Harbau masamanin tattalin arziki a tarayyar Najeriya, da Dr. Ibrahim Adamu na sashin nazarin yankin gabas ta Tsakiya a jami'ar Havard da ke Dubai na haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai Mohammad Qaddam Sidiq Isa, mai sharhi kan al'amuran Yau da Kullum shima a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai kuma Isma'il Albabawee ɗan jarida kuma ɗalibi a jami'ar Karbala a ƙasar Iraki. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

A yau shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne a kan yadda Yaƙin da kawancen Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran, da hare-haren mayar da martini na jamhuriyar musuluncin kan yahudun Isra'ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo gagarumar koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin duniya masamman a bangaren makamashi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan taron taron tattalin arziki da ya gudana a farkon watan Fabarairun da ya gabata a jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan tasirin tattalin arziki dangane da alaƙar China da Najeriya da a makon jiya aka yi bikin cika shekaru 55 da faro hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Najeriya da China sun sake jaddada karfafa dangantakar diflomasiyya da ke tsakaninsu yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 55 da fara huldar diflomasiyya a bikin baje kolin sabuwar shekarar kalandar kasar China da aka gudanar.

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za'a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki tsakanin kasashen biyu. Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi, ya sake jaddada aniyar Hukumar na sauƙaƙe cinikayya a yankin, ta hanyar saukaka jigilar kayayyaki da kuma haɓaka haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka da su, musamman Jamhuriyar Nijar. Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata, yayin wani babban taron haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam ta Najeriya da takwararta ta Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Muhammadu Yaqouba, da aka gudanar da hedikwatan Kwastam da ke Maitama a Abuja. Tawagar Nijar ta kunshi shugabannin cibiyar inganta kasuwanci na Nijar wato Chamber des Commerce. Cikin mahimman abubuwan da aka duba a ganawar akwai saukaka zirga-zirga a kayan a iyakokin kasashen biyu ciki harda jigilar man metur na kamfanin Dangote, hakazalika za'a bada damar wucewar wasu kayayyaki da suka makale a bodar Kamba na jihar Kebbi, tireloli 1,600, da suka kwashe sama da watanni 2. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan gina kasuwanni na zamani da Gwamnatin Jihar Yobe ta sake ginawa a wasu sassan jihar domin karfafa harkokin kasuwanci da suka fuskanci koma baya, saboda matsaloli na Boko Haram. Shiga alamar sauti domin sauraron karin bayani.......

Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane gagarumar yarjejeniyar cinikayya mafi girma da ba'a taba ganin irinta ba, da aka cimma tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turain ƙasar India. Yarjejeniyar da aka cimma yayin ziyarar da shugabannin Turai suka kai New Delhi na ƙasar India, za ta bada damar kasuwanci mara shinge tsakanin ƙasashe mambobin EU 27 da kuma ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya, waɗanda suka kaɗai suka mamaye kusan kashi 25% na jimillar hada-hadar kasuwancin cikin gida na duniya da kuma cinkayyar mutane biliyan biyu. Domin ko a shekarar 2024 kaɗai, an yi cinikin sama da Euro biliyan 120 a tsakanin ɓangarorin biyu. Masu sharhi na ganin cewa kalaman wannan yarjejeniya da ɓangarorin biyu suka cimma, alaƙa da manufofin Shugaban Amurka, Donald Trump, musamman duba da yadda Tarayyar Turai ke ƙoƙarin faɗaɗa abokan hulɗar kasuwancinta, ba tare da dogaro da Amurka kaɗai ba. Yarjejeniyar dai na nufin cewa daga yanzu, India za ta soke ko kuma zaftare haraji kan hajoji da dama da take shigarwa yankin Turai, da suka haɗa da motoci daga kaso 110% zuwa 10% kachal, matakin da zai shafi kayan abinci da barasa da tufafi da kayan ado da dai sauransu. An dai ƙulla yarjejeniyar ce a daidai lokacin da mafi yawan ƙasashen duniya ke takun-saka da Amurka sakamakon haraji babu ƙaƙƙautawa da Donald Trump ke amfani da shi don tursasawa abokan hulɗa. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole"na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan sabbin kiraye-kirayen da Bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni na Duniya (IMF) suka yi ga gwamnatin Najeriya wajen ganin ta ɗauki matakab da suka kamata don ƙara rage hauhawar farashin kayayyaki domin al'umma ta amfana a zahiri da kuma ci gaban tattalin arziki ƙasar. Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF, sun bayyana cewa har yanzu tattalin arziƙin Najeriya bai kai matsayin da za a ce ya daidaita ba, duk da wasu sauye – sauye da gwamnati ke aiwatarwa. Hukumomin sun ce rashin daidaiton tattalin arziƙin na ci gaba da shafar rayuwar jama'a, musamman ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki. Masana tattalin arziƙi sun goyi bayan gargadin da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF, ya yi kan cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin da ake aiwatarwa a ƙasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya, na iya fuskantar barazana idan ba a tabbatar da dorewarsu ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali kan ikirarin gwamnatn Najeriya na samun rarar kuɗi da ya kai tiriliyan 12 kuma kashi 21 daga ciki ta same su ne daga bangarorin da ba na man fetur ba a cikinn watanni 6 na farkon shekarar 2025. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin man fetir dangane da tasirin kama shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro da Amurka ta yi zai yi ga tattalin arzikin duniya.

Shirin "Duniya Akai Miki Dole" tare da Faruk Muhammad Yabo a wannan mako ya yi duba ne kan sabbin harajin da gwamnatin Najeriya ke shirin karɓa a hannun jama'ar ƙasar, a wani yanayi da ƙasar ke fatan tattara wani ɓangare na kuɗaɗen tafiyar da harkokinta. Shirin a wannan mako ci gaba ne na makon da ya gabata dangane da wannan dokar haraji wadda al'ummar Najeriya ke ci gaba da suka akanta. A cikin shirin akwai tattaunawa da ƙwararru a fagen na tattalin arziƙi waɗanda da dama suka yi suka ga sabon tsarin harajin na shugaba Tinubu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

A wannan mako shirin zai tattauna ne kan sabuwar dokar harajin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya wa hannu, wadda kamar yadda na ambata ba da jimawa, za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan gobe na shekara mai zuwa. Tun a watan Yunin da ya gabata shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar harajin da ake sa ran za ta sauya fasalin tsarin karɓa da tattara kuɗaɗen shiga ga gwamnati daga ɓangaren haraji a Tarayyar Najeriya.

Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda a shekarun baya bayan nan, hada hadar kuɗi ke neman yin ƙaura daga bankuna zuwa manhajojin wayar salula da ake kira da Mobile Money a Turance, da ake amfani da tsarin wajen aikewa da kuɗi ko karɓarsu a ciki da wajen ƙasar ta Nijar. Samun damar aika kuɗaɗe ta hanyar amfani da manhajojin wayar hannu ba tare da yankar kuɗin haraji masu dama ba, dai tuni ya kawo sauyi dangane da hada-hadar kuɗi a Jamhuriyar ta Nijar, lamarin da ya zo a daidai lokacin da aka takaita fitar da kuɗaɗe daga Bankuna bayan juyin Mulki, tsarin da ya sa mutane da dama masu asusun ajiya a bankuna rungumar mahajojin na zamani a matsayin sabbin wuraren adana kuɗaɗen nasu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.........

Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan gina katafaren kamfanin tono da kuma sarrafa ƙarafu da duwatsu masu daraja da wani matashi ya ƙaddamar a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, irinsa mafi girma a Afirka, wanda zai laƙume dalar Amurka miliyan 400.

Shirin Kasuwa a kai Miki Dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan binciken da majalisar wakilan Najeriya ta ƙaddamar bayan ƙorafin ƴan ƙasar game da yawan haraji da bankuna ke cirewa a asusun su na ajiya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

A 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan karon, ya mayar da hanhali ne kan binciken da Majalisar Walikan Nigeria ta ƙaddamar dangane da ƙorafin ƴan ƙasar kan maban-banta haraji da Bankuna ke yawaita cirewa a asusun ajiyarsu. A ƙarshen watan oktoban da ya gabata ne, Mjalisar Wakilan Najeriya ta kaddamar da wani kwamitin da ta dorawa alhakin bin diddigin korafe-korafen da masu ajiya a bankuna ke yi kan yawan cire musu kudade da ake yi daga asusun ajiyarsu na banki. Kaddamar da kwamitin, ya biyo bayan tarin korafe korafen da ƴan Nigeria ke yi, musamman masu ajiyar kudi a bankunan kasar, game da yawan cire musu kudade ba-gaira ba dalili da bankunan ke yi, da sunan wasu ayyuka da bankunan ke ikirarin gudanarwa. Masana na alakanta wannan batu, da nau'o'in harajin da ake da su a kasar, a matakin kananan hukumomi da jihohi da kuma tarayya, yayinda wasu ma'aikatan gwamnatin kasar, ke kukan cewa wasu kudaden da ake cire musu, musamman na gidaje da na pansho, ba a tura su ga hukumomin da suka dace. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........

Shirin a wannan makon ya yi dubi ne akan batun sabon harajin kashi 15 da gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanya kan tataccen man fetur da dangogin sa da ake shigo da su ƙasar daga ketare, ala'marin da ya fara jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasar kan yuwuwar tashin farashin litar man na fetur. A ranar Jumma'ar da ta gabata ce, fadar gwamnatin Najeriya, ta sanar da cewa tuni shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da harajin fito na kashi 15 kan man fetir da dizal da za a shigo da su ƙasar daga waje, yana mai bayyana tsarin, a matsayin matakin bunƙasa matatun mai na cikin gida da kuma dogaro da kai a fannin makamashi. Sai dai, tuni dilllalan man fetur a ƙasar suka fara gargaɗin cewar muddin karin ya tabbata to akwai yuwuwar farashin man fetur da dangoginsa ya yi tashin da zai fi ƙarfin da yawa daga cikin al'ummar ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........

Shirin a wannan makon ya yi dubi ne kan zare sunan Najeriya da cibiyar da ke sanya idanu kan almundahanar kuɗaɗe da ɗaukar nauyin ta'addanci a duniya ta yi cikin baƙin kundinta. A makon da ya gabata ne, Cibiyar nan ta Yaƙi da Masu Safarar Kuɗi da Ɗaukar Nauyin Ta'addanci ta duniya (FATF), ta sanar da cire sunan Najeriya daga jerin ƙasashen da take ɗaukarsu a matsayin masu wanan ɗabi'a. Wannan mataki ba iya Najeriya ta shafa ba, harma da ƙasashen Burkina Faso da Afrika ta Kudu da ma Mozambique duk a nahiyar Afrika. Cibiyar wadda ke da hedikwata a birnin Paris na ƙasar Faransa, wadda ke gudanar da binciken kwakwaf kan yadda ake hada-hadar kuɗaɗe tsakananin ma'aikatun gwamnati da hukumomi ko kuma cibiyoyin gwamnati ta ce duk da cire waɗannan ƙasahe cikin baƙin littafinta, har yanzu za'a ci gaba da sanya idanu akan waɗannan ƙasashe. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba................

A wannan makon shirin na 'Kasuwa Akai Miki Dole' tare Ahmed Abba zai tattauna ne kan taron ƙoli na ƙasa da ƙasa domin bunƙasa zuba jari da harkokin kasuwanci na farko da jihar Bauchi da ke tarayyar Najeriya ta karɓi baƙunci. Ɗaya daga cikin matsaloli da ke nakasa ci gaban harkokin kasuwanci a Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa ita ce matsalar janyewar masu zuba jari daga fagen harkokin kasuwanci, saboda haka ne ma gwamnatin jihar Bauchi da ke yankin arewacin Najeriya ta shirya wannan taro kan zuba jari irin sa na farko a tarihi. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba.....................

A wannan makon shirin na Kasuwa Akai Miki Dole tare Abdulƙadir Haladu Kiyawa zai tattauna ne a kan yawaitar matasan Najeriya masu muhimman sana'o'in hannu da ke yin ƙaura ko kuma tafiya ci rani zuwa wasu ƙasashen Afrika domin neman na rufin asiri, abin da ake alaƙantawa da dalilai da dama da ke sanya matasan ficewa daga ƙasar tasu ta haihuwa. A shekarun baya ba haka lamarin yake ba, inda Najeriyar ke matsayin wajen da ɗimbin ƴan ƙasashen ƙetare ke kwarara don neman kuɗi musamman ƴan kasashen Afrika kamar Jamhuriyar Nijar, da Ghana, da Jamhuriyar Benin, har ma da Kamaru. To Sai dai a yanzu, waɗannan ƙasashen ne ƴan Najeriyar ke tururuwar zuwa cikinsu duk da kasancewar ƙasashen ba su da ɗinmbin arziƙi kamar Najeriyar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

Shirin ‘Kasuwa A Kai Miki Dole' na wannan mako zai tattauna ne kan wasu alƙaluma da suka nuna yadda Najeriya ta Kashe Dala Biliyan 2.86 a cikin watanni 8 na farkon shekarar da muke ciki ta 2025, wajen Biyan Kuɗin Ruwan Basukan da ta karɓo daga ƙasashen ƙetare tare da Nura Ado Suleiman..... Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...........

Shirin kasuwa a Kai miki dole na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake gudanar da hada-hadar kayayyakin amfanin gona da ake samu a damina,waɗanda ake shukawa da sauran tsirrai da ake samu a daji saboda saukar ruwan sama.Ɗaya daga cikin falalar ruwa ita ce Allah ya rayar da amfanin gona.Da zarar damina ta yi nisa kayan amfanin gona da sauran tsirrai da ba shukasu aka yi ba, suka fara yabaya, to daga nan za'a fara ganin hada-hadar waɗannan kayayyaki irinsu ɗanyar masara,wake, gujiya,da wasu ƴaƴan itatuwa da ake samu a wannan lokaci kadai, harma halitu irinsu Fara. Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Ahmed Abba............

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya dubi batun ƙarin da aka samu a rabon arzikin ƙasa na wata-wata da gwamnatin Najeriya ke yi tsakaninta da jihohi da ƙananan hukumomin ƙasar, inda alƙaluma su ka nuna yadda wannan kaso ya ƙaru da ninkin abin da aka saba rabawa a baya, tun bayan zuwan wannan gwamnati ta shugaba Bola Tinubu a shekarar 2023. Ɓangararorin gwamnatoci uku a Najeriya, wato ta tarayya da ta jihohi da kuma ƙananan hukumomi sun raba kaso mafi yawa a tarihin rabon tattalin arzikin ƙasa na wata wata wanda ya kai sama da Naira Tiriliyan 2 da biliyan 200 a watan Agustan da ya gabata.... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Shirin a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ake ƙara samun raguwar kayayyakin masrufi a Najeriya. Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, tace watanni biyar jere kenan, ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, inda tace an samu sauƙar farashin kayyaki a watan Agustan da ya wuce, da kaso 1 da ɗigo 76 cikin 100, wanda hakan ke nuna yadda aka samu sauƙi fiye da kaso 21.88 na watan Yuli, yayin da yanzu kuma ya koma kaso 20.12 cikin 100. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin........

Shirin a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin Babban bankin Najeriya CBN da ya umarci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su sanya na'urar bin diddigi ta taswira wato GPS a tashoshin POS a fadin ƙasar, a wani mataki na dakile ɓata gari a bangarori daban-daban masamman ma ayyukan ƴan damfara. Latsa alamar sauti domin sauraaron cikakken shirin......

Shirin kasuwa akai miki Dole na wanan makon tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa ya mayar da hankali ne kan yadda karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi, ke ci gaba da haɓaka tattalin arziƙin ƙasashen da ke maƙwabtaka ita waɗanda ke amfani da kuɗin CFA. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, zai tattauna ne kan ƙalubalen da ake fuskanta na durƙushewar kamfanonin sarrafa shinkafa a Najeriya, duk da zuba jarin dubban biliyoyin Naira da ‘yan kasuwa suka yi wajen kafa kamfanonin sarrafa shinkafar, waɗanda rahotanni suka tabbatar da cewa an rurrufe da dama daga cikin kamfanonin ko kuma an rage adadin shinkafar da su ke sarrafawa. Wani bincike ya ƙiyasta cewa a shekarar 2018, Nigeria kan sayi shinkafar da ba ta gaza ta Nera triliyan 2 da rabi ba, yayin da kuma kusan kashi 90 na hada-hadar cinikin shinkafa da ake yi, na gudana ne ba a hukumance ba. Alƙluma dai sun nuna Nigeria ke kan gaba a faɗin nahiyar Afrika wajen sayen shinkafa daga ƙasashen ƙetare, kamar yadda hukumar kula da hada-hadar fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen na waje ta tabbatar, inda a duk shekara, ake shigar da shinkafa cikin Najeriyar ta zunzurutun kuɗi Nera Triliyan 9 da biliyan 200. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yunkurin da gwamnatin Najeriya Ke yi na ganin ta farfado da tattalin arzikinta, ta hanyar tada masana'antun da suka durƙushe. Ƙaramin ministan kasuwanci na ƙasar Sanata John Owan Enoh ya fara ziyarar wasu daga cikin masakun da suka durƙushe domin ganin sun dawo bakin aiki. Masaka ta UNTL da Ke Kaduna na cikin masakun da ministan ya ziyarta bisa ganin irin gudummuwar da ta ke bayar wa a baya. Ku latsa alamar sauti don saurorin cikakken shirin tare da Ahmed Abba............

To kamar yadda akaji a matashiyar shirin, ra'ayoyin masana tattalin arziki sun banbanta a Najeriya, tun bayan da sananne a harkar tattalin arziki Bismark Rewane ya tabbatar cewa Naira ta daidaita tsakanin 1500 zuwa 1560 kan kowace dala a makonnin baya-bayan nan, yayin da tattalin arzikin ƙasar kuwa ya fara farfadowa sakamakon matakin babban bankin na Najeriya CBN da ya sanya zunzurutun ƙudi har dalar Amurka biliyan 4 da miliyan 100 cikin watanni shida na wannan shekara...ta 2025.

Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan sabuwar dokar Harajin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu a ƙarshen watan Yunin wannan shekara ta 2025 a matsayin wata sabuwar dokar haraji da za ta taimaka wajen sake yi wa tsarin tattara harajin ƙasar garambawul kamar yadda su ka bayyana. Sabuwar dokar ta kuma yi bayani dalla-dalla kan waɗanda za ta shafa tare da cire wasu nau'ukan ƴan Najeriya kama daga ƴan kasuwa da ma'aikata da ma manya da matsakaitan kamfanoni. Kuma domin sanin waɗanda da dokar ta bada damar karɓar haraji a wurinsu da ma waɗanda ta ce a ɗage musu tare da irin tasirin da za ta yi ga tattalin arziƙin ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Yau Shirin zai mayar da hankali ne kan ziyarar kwamitin shugaban Najeriya kan saukaka harkokin kasuwanci a jihohin arewa maso gabas. Ku danna alamar Saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba

Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon, ya maida hankali ne kan taron koli na farko kan ƙarfafa ci gaban tattalin arzkin ƙasashen Afrika ta Yamma da aka gudanar a Najeriya, ta hanyar sauƙaƙa tsarin kasuwanci ga ƴan kasuwar da ke zirga-zirga a tsakani. Ku lasha alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya yi duba ne kan girman asarar da al'ummar Makwa na jihar Naija suka tafka masamman ma ƴan kasuwarsu, sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa garin a ƙarshen watan Mayan wannan shekara ta 2025. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........

Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan wani sabon bashin da Najeriya ta ciwo daga bankin duniya da ya haura sama da dala biliyan ɗaya. Wannan sabon bashin dai ya janyo cece-kuce daga ƴan ƙasar waɗanda suka nuna damuwa kan yadda gwamnati ke ci gaba da ciyo manyan basussuka duk da iƙirarinta na janye tallafin manfetur domin dogaro da kai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba............

Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne kan babban taron da ƙungiyar Matan Arewa ƴan kasuwa mazauna Lagos da ke kudancin Najeriya su ka yi a birnin Lagos, wanda ya mayar da hankali kan karfafawa mata gwiwa kan harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arzikinsu.

Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan makon tare da Ahmed Abba ya yi duba kan irin girman asarar da masau kamfanoni su kace sun tafka saka makon matsalar karancin wutan lantarki da ake fama da ita musamman a arewacin kasar. Ku shiga alamar sauti domin jin cikakken shirin......

Shirin Kasuwa akai Miki Dole na wanan makon tareda Ahmed Abba , ya mayar da hankali kan asarar sama da Naira biliyan ɗaya da ƴan kasuwar Taminus na birnin Jos suka tafka sakamakon konewar wani bangare na babbar kasuwar ta jihar Filato dake Najeriya. Ku latsa alamar sauti domin sauraron karin bayani.......

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya mayar da hankali ne kan halin da ake ciki game da noman zoɓo a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, da kuma yadda ake fita da shi zuwa ƙasashen ƙetare. Duk da cewa ana noman zoɓo a Jihohi irin su Zamfara da Katsina da Kano da Kebbi da Borno da Yobe, bayanai na cewa kusan kaso 70 cikin 100 na zobon da ake fita da shi ƙasashen waje a jihar Jigawa ake nomawa, sai dai a shekaru biyu da suka gabata manoman na zoɓo sun ɗan fuskanci kalubale a harkar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........

Yau shirin ya yada zango ne ƙasar Ghana, inda ya mayar da hankali kan matakin gwamnatin ƙasar na bai wa ƴan ƙasashen waje wa'adin ficewa daga kasuwancin zinare.Ƙasar Ghana ta bai wa ƴan ƙasashen waje da su fice daga harkokinta na kasuwancin zinare a ƙarshen wannan wata na Afirilu a wani mataki na bunƙasa kananan masu hakar zinare na cikin gida da kuma samun ƙudin shiga. Ƙasar ta yammacin Afirka dake kan gaba a samar da zinare a nahiyar na ƙokarin tsaftace harkokin harƙar zinare ta hanyar daidaita cinikin zinari daga kananan masu hakar ma'adinai.

Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan tasirin matakin shugaban Amurka Donald Trump kan shirin sa na sanya gagarumin ƙarin haraji ga kusan ɗaukacin ƙasashen duniya, wanda ya jawo durƙushewar kasuwannin hannayen jari ta duniya da lalata alaƙa tsakanin ƙasar da ƙawayenta, duk da cewa ya yi amai ya lashe wajen dakatar da harajin da watanni uku masu zuwa. Shirin ya duba tasirinsa ga ƙasashen Afirka masamman Najeriya.

Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yi dubi ne kan halin da fannin kasuwanci ke ciki a Najeriya sakamakon barazana ko ƙoƙarin mamaya da ƴan ƙasar China ke yi, wanda aka tabbatar da irin illar da ayyukansu ke haifarwa ga ƴan kasuwa da kuma tattalin arziƙin ƙasar. Ba sabon abu bane yadda ake samun ƴan ƙasar China da ke aikata abubuwan rashin ɗa'a kama daga ɓangaren haƙar ma'adai ba bisa ƙa'ida ba, yin kutse ga ƴan kasuwa, zamba cikin aminci a intanet da sauransu.Sai dai ana zargin har izuwa yanzu, babu wani tsatsauran mataki na azo a gani da gwamnatin ƙasar ta ɗauka wurin kawo ƙarshen irin waɗannan laifuffukan da ake samun ƴan ƙasar na yi a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

Shirin Kasuwa akai miki dole na wanan makon tareda Ahmed Abba ya yada zango ne jihar Maradi dake jamhuriyar Nijar, inda ya mayar da hankali kan rawar da kannan kamfanoni ke takawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar dake yankin Sahel. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......

Shirin KASUWA AKAI MIKI DOLE na wanan makon ya maida hankali ne kan matakin da gwamnatin jihar Neja ta ɗauka na janye haraji kan ƙananan ƴan kasuwa da masu talla a faɗin jihar, a wani mataki na bunƙasa ƙananan ƴan kasuwa tare da samar wa da al'umma sauƙi a jihar. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......

Shirin ‘Kasuwa a kai miki Dole' tare da Nura Ado Suleiman ya tattauna kan farfaɗowar darajar Naira a kasuwar hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare, musamman ma a kan Dalar Amurka, nasarar da wasu ke ganin ta biyo bayan manufofin da babban bankin Najeriya CBN ke aiwatarwa. Bayanai dai sun nuna cewa darajar Naira na ta ƙaruwa ne kusan a kowace rana tun daga watan Janairun wannan shekara da mu ke ciki ta 2025. Nasarar da wasu Magidanta suka ce sun shaida samun ta, la'akari da sauƙin da aka fara samu a harkokinsu na yau da kullum.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....