POPULARITY
Gwamnonin Arewacin Najeriya tare da Sarakunan yankin sun gudanar da wani taro na musamman domin sake duba matsalolin tsaron da suka addabi yankin, a dai-dai lokacin da mayaƙan Boko Haram da ƴanbindiga ke ci gaba da hallaka jama'a ba tare da ƙaƙƙautawa ba. Bayan kammala taron, Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto. Kula latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana akai...........
Dalilan da suka sanya 'yan Najeriya ke ƙara faɗawa cikin mawuyacin hali sanadiyyar talaucin da ya yi musu katutu. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziƙi a Najeriya Dr Kassim Garba Kurfi.Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar...
Majalisar dokokin ƙungiyar ƙasashen ECOWAS ta gudanar da taron ta a Lome da ke ƙasar Togo, wanda ya mayar da hankali kan tsadar sufurin jiragen sama a yankin. Bayan taron, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sanata Ali Muhammed Ndume, daya daga cikin shugabannin taron. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar tasu.............
Yau manyan limaman dariƙar Katolika na duniya sama da 130 ke fara gudanar da zaɓen Fafaroma domin maye gurbin Francis da ya rasu a makon jiya.Domin sanin yadda ake gudanar da zaɓen, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Archpishop Ignatius Kaigama, daya daga cikin manyan limaman Katolika a Najeriya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta bai wa hafsan sojojin ƙasar umarnin cewar babu wanda zai tafi ritaya a cikin wannan shekarar, sakamakon wasu matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta. Dangane da wannan umarni, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Sani Yahya Janjuna, mai sharhi akan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai.
Katafaren kamfanin sadarwar Meta da ya mallaki Facebook da WhatsApp ya yi barazamar ficewa daga Najeriya, saboda cin tararsa da hukumomin ƙasar suka yi na Dala miliyan 290, sakamako karya ƙa'idodin aikinsa. Najeriya ta samu kamfanin ne da laifin talla ba bisa ƙa'ida ba, da kuma rashin alkince bayanan asiri na jama'ar dake hulɗa da shi.Dangane da wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Samaila Muhammed, masanin tallalin arziki da kuma sadarwa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar
Yau shugaban Amurka Donald Trump le cika kwanaki 100 a karagar mulkin ƙasar, tun bayan rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairun shekarar nan. A tsawon wannan lokaci, shugaban na Amurka ya ɗauki mabanbantan matakai da suak girgiza sassan duniya.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir na Jami'ar Kaduna, don jin yadda masana ke kallon salon kamun ludayin Donald Trump ga kuma tattaunawarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar..
Kungiyar Amnesty International ta tabbatar da mutuwar mutane 26 sakamakon harin ƴan bindiga a wurin hakar zinaren da ke jihar Zamfara. Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Malam Isa Sanusi ne ya tabbatar da haka a tatatunawar da suka yi da Bashir Ibrahim Idris. Ku latsa alamar sautin don sauraron cikakkiyar tattaunawar tasu...........
Yayin da ƙungiyar ECOWAS ke cika shekaru 50 a wannan mako, mun shirya muku rahotanni da hirarraki daban-daban dangane da gudunmawar da ƙungiyar ta bayar a cikin waɗannan shekaru. Daga cikin su akwai rawar da dakarun ECOMOG suka taka wajen magance rikice-rikice da aka samu a ƙasashen Liberia da Saliyo.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya, ɗaya daga cikin sojojin da suka yi aikin samar da zaman lafiyar. ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya ta bayyana rashin amincewar ta da matakin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka, na dakatar da gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar, tare da naɗa kantoman soji. Kungiyar tare da jam'iyyun adawa da kuma wasu masu sharhi na cewa matakin ya saba dokar ƙasa. Dangane da wannan matsayi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin shari'a Barr Solomon Dalung. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..........
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce an fara samun saukin karancin man fetur da aka fuskanta a kwanakin da suka gabata, abinda ya jefa jama'a da dama cikin halin kunchi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Muhammadu Gamatche, shugaban gamayyar kungiyoyin masu motocin sufuri ta kasa a Nijar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana
Hukumar EFCC dake yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sanar da kwato kuɗaɗen da suka kai naira Triliyan guda a shekarar da ta gabata, abinda ke nuna irin nasarar da ta samu, baya ga samun nasara a kotu a shari'o'in da suka kai sama da 4,000.Dangane da wannan nasarar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Isa Sanusi, Daraktan Ƙungiyar Amnesty a Najeriya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiya hirar...........
Shugaban Ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya ƙaddamar da wani shirin diflomasiya domin shawo kan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, wadanda suka fice daga cikin ƙungiyar ECOWAS.A ƙarshen makon da ya gabata, shugaban ya ziyarci waɗannan ƙasashe guda uku, inda ya gaba da shugabannin su.Dangane da tasirin wannan ziyarar, Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da Dr Elharun Muhammad na Cibiyar kula da manufofin ci gaban ƙasashe dake Kaduna, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Ƙungiyoyin mata daban daban na ci gaba da gudanar da zanga zanga dangane da zargin cin zarafin da Sanata Natasha Uduaghan ke yi kan shugaban Majalisar dattijan ƙasar Godwill Akpabio na neman yin lalata da ita, wanda ya sanya matan miƙa buƙatar murabus ɗinsa, kodayake jami'an tsaro sun yi amfani da hayaƙi mai sanya ƙwalla wajen tarwatsa dandazonsu. Dangane da yadda tarin mata ke fuskantar cin zarafi walau a wuraren ayyuka koma a tsakar gari, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Khadija Suleiman Saulawa wata mai rajin kare haƙƙoƙin mata a Najeriya ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
Majalisar dokokin Ƙungiyar ECOWAS ta sake kafa wani sabon kwamiti da zai ziyarci ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, domin tattaunawa da hukumomin sojin dake mulki a ƙasashen 3 waɗanda suka samar da ƙawancen AES. Mataimakin shugaban Majalisar Ɗattawan Najeriya, Sanata Barau Jibril ya bayyana haka bayan wani zaman na musamman da Majalisar ECOWAS ta gudanar a birnin Lagos, dangane da wannan ne kuma suka zanta da Bashir Ibrahim Idris.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
Gwamnatin Najeriya ta ce shugabannin ƙananan hukumomin ƙasar sama da 700, sun gaza wajen gabatar da asusun ajiyar da za ta rinƙa zuba musu kuɗaɗensu kowane wata. Babbar jami'ar da ke kula da asusun ƙasar Oluwatoyin Sakirat Madein ta ce daga cikin ƙananan hukumomi 774 da ake da su a ƙasar, 25 ne kacal suka gabatar da asusunsu. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tintiɓi Hon Saleh Yahya Taki, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kazaure da ke jihar Jigawa.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..............
Tattaunawa tsakanin wakilan Isra'ila dana Hamas domin amincewa da shiga rukuni na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninsu ta katse a birnin Alqahira na Masar bayan gaza cimma daidaito. Tuni Isra'ila ta dakatar da shigar da kayakin agaji zuwa yankin Gaza da ƙungiyoyi ke jagorantar kaiwa wanda aka tattara daga ƙasashen Larabawa ga Falasɗinawan yankin da ya yi fama da yaƙin kusan shekaru 2, lamarin da ke da nasaba da yadda Hamas ta ƙi amincewa da ƙara wa'adin rukunin farko na yarjejeniyar a gefe guda Isra'ila ta ƙi amincewa da shiga rukuni na biyu, wanda ya sanya tuni Isra'ilan ta fara dawo da hare-hare zuwa wasu yankuna ciki har da Rafah.Dangane da wannan matsala Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Bashir Nuhu Mabai na jami'ar Dutsinma ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
Gobe Asabar ke zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1446 dai-dai da 1 ga watan Fabrairun 2025, abinda ke nufin al'ummar musulmi a faɗin duniya za su fara da gudanar da ibadar azumi, wanda ake gudanarwa duk shekara. A lokacin watan Ramadan al'ummar musulmi kan ruɓanya ayyukan ibadar da suke gudanarwa, domin neman dace wa a wurin Allah SWT, tare da samun falala mai tarin yawa.Kan hakan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Mansur Isa Yelwa fitaccen malamin addinin musulinci a Najeriya.Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar...
A yayin da ake gab da fara azumin Ramadan, Matatar Mai ta Ɗangote da ke Najeriya ta sanar da rage farashin litar man fetur da take sayar wa ƴan kasuwa daga Naira 890 zuwa Naira 825, rahusar da ta fara aiki daga yau Alhamis, 27 ga watan Fabairu. Kan hakan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Shu'aibu Idris.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar...
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna dake Najeriya Malam Nasir El Rufai ya gabatar da zarge-zarge da dama akan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ciki har da nada mutanen da basu ƙware ba a muƙaman gwamnati, abin da ya ce ke haifar da tarnaƙi wajen tafiyar da gwamnati. El Rufai ya kuma zargi Tinubu da janye sunansa a matsayin minista, tare da kuma zargin Malam Nuhu Ribadu da ƙoƙarin ɓata masa suna.Dangane da waɗannan zarge-zarge, Bashir Ibrahim Idris, ya tattauna da Dakta Abbati Bako, mai sharhi akan siyasar Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A yayinda aka cika shekaru 3 cif da faro yaƙi tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine maƙwabtan juna, dukkanin ɓangarorin biyu sun tafka gagarumar asara marar misaltuwa a wannan ɗan tsakani kama daga Sojojinsu da ke fagen daga da kuma kayakin more rayuwa da kowacce ta lalatawa ƴar uwarta. A baya-bayan nan anga yadda shugaban Amurka Donald Trump ke ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yaƙi ta hanyar tuntuɓar Vladimir Putin na Rasha a wani yanayi da tuni aka faro taron tattaunawa kan kawo ƙarshen wannan yaƙi a Saudiya kodayake batun bai yiwa ƙasashen Turai daɗi ba, ganin yadda basu samu goron gayyata a tattaunawar ba, haka zalika itama Ukraine.Dangane da wannan dambarwa ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua masanin siyasar ƙasashe ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar...
Mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriya na ƙorafi game da yawan kuɗin da aka warewa yankin a kasafin kuɗin ƙasar na wannan shekara domin samar da hanyoyi a yankin. Al'ummar yankin na Arewa maso gabashin Najeriya na zargin cewar anyi watsi da yankin nasu idan aka kwatanta da irin maƙuden kuɗaɗen da aka warewa wasu yankuna na ƙasar.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barrister Abdullahi Jalo guda cikin mutanen wannan yanki ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
Tsoho shugaban Najeriya janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya nemi afuwar ƴan ƙasar a game da matakin da ya ɗauka na soke zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993, wanda aka yi ittifaƙin cewa marigayi Moshood Kashimawo Oalawale Abiola ya lashe, sama da shekaru 30 bayan faruwan lamarin. Kan hakan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Yahya Kwande...
Majalisar Dattawan Najeriya ta kaddamar da bincike domin gano yadda bindigogi dubu 178,459 suka bata daga rumbun aje makaman 'yansanda daga shekarar 2018 zuwa yanzu. Shugaban kwamitin binciken, Sanata Samuel Godwin ya ce daga cikin bindigogin, dubu 88,078 manya ne kirar AK-47, yayin da dubu 3,097 kuma kanana ne.Dangane da wannan labari mai tayar da hankali, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Sule Ammani, Yarin Katsina.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Kamfanin man NNPC a Najeriya ya ce sakamakon kwanciyar hankalin da aka samu, adadin man da yake hakowa kowacce rana ya karu zuwa ganga miliyan guda dubu 750, sabanin kasa da ganga miliyan guda da dubu 250 a baya. NNPC ya kuma ce yanzu haka yana hako cubic biliyan 7 na gas kowacce rana. Dangane da wannan ci gaba, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Babangida Abdullahi na Jami'ar Baze dake Abuja, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.....
Yayinda shugabannin ƙasashen Afrika ke kammala taronsu akan yadda za su tinƙari rikicin ƴantawayen ƙungiyar M23 a Congo, rahotanni sun bayyana nasarar da mayaƙan suka samu na sake kama Bukavu bayan birnin Goma mafi girma a lardin na Kivu. Ganin irin nasarorin da suke samu kan dakarun ƙasar ta Congo dama gazawar shugabannin Afrika wajen daƙile matsalar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Jafar Lawal, masani akan harkokin siyasar Afrika ta gabas, kuma ga yadda tattaunawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
Ƴan Najeriya na ci gaba da gabatar da ƙorafe ƙorafe sakamakon sabbin harajin da aka ɗora musu na cire kudade a bankuna da kuma kirar waya. Kamfanonin sadarwar kasar sun sanar da karin kashi 50 na kudin kirar wayar, yayin da Babban Bankin Najeriya ya sanar da kara harajin da ake cirewa akan cirar kudi ta ATM zuwa naira 100 akan kowacce naira 20,000. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Alhaji Kabir Muhammad Baba, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai
Ƙungiyar Transparency International ta fitar da rahoton ta na shekarar da ta gabata, wanda ya nuna cewar Nijeriyar ta koma matsayi na 140 daga 145 na shekarar da ta gabata , a jerin ƙasashen duniya dake fama da matsalar cin hancin.Domin tattauna wannan sabon rahoto, Bashir Ibrahim Idris ya tuntuɓ Dr. Ladan Salihu, tsohon shugaban Radiyo Nijeriya, sai a latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar.
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta kafa kwamitin musamman da aka ɗora wa alhakin shirya taro maharawa don sake dawo da ƙasar kan turbar dimokuradiyya. Ana kyautata zaton sakamakon ayyukan kwamitin ne za su fayyace tsawon lokacin da ake buƙata don tafiyar da mulkin riƙnon ƙwarya da kuma irin salon mulin da ya kamata a ɗora Nijar a nan gaba.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sani Rufa'i ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.
A Najeriya rahotanni sun bayyana cewar yanzu haka shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkanin ministocinsa da suka fito daga yankin arewacin ƙasar su koma jihohin da suka fito domin kare manufofinsa da kuma bayyana irin ayyukan da yake yi. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban ke ganin matsananciyar suka daga ɓangaren adawa da kuma ganin tarin barazana musamman kan salon kamun ludayin gwamnatinsa.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Harsanu Yunusa Guyaba.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarnin sanya takunkumi akan kotun duniya ta ICC da kuma haramtawa jami'anta dake binciken 'yan kasarsa ko kuma kawayen Amurka irin su Isra'ila. Abin tambayar shine, wanne irin tasiri wannan mataki zai yi?Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru, masanin shari'a a Jami'ar Baze, da ke Nijeriya.
Ƙasashen duniya sun bayyana matukar rashin amincewarsu da buƙatar shugaban Amurka Donald Trump, na ƙwace Gaza da kuma mayar da Falasdinawa wasu ƙasashe domin gina wurin shaƙatawa a ƙasarsu. Wannan matsayi ya gamu da suka daga ƙasashen duniya da dama ciki harda Majalisar Ɗinkin Duniya. Bashir Ibrahim Idris ya tatatuna shirin da Ambasada Abubakar Cika, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Iran. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.........
Ƙasashen duniya na ci gaba da bayyana damuwa dangane da shirin shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da ayyukan hukumar USAID wadda ke taimakawa ƙasashen duniya . Wannan hukuma dai na taka gagarumar rawa a bangarori da dama a ƙasashe masu tasowa irin su Najeriya.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara a kan harkokin noma dangane da tasirin matakin a kan noman ƙasar.Latsa alamar sauti domin sauraren yadda tattaunawar ta kasance....
Duk da nasarorin da sojoji ke samu kan ƴan ta'adda a arewa maso yammacin Najeriya, masu ɗauke da makaman na ci gaba da kai hare-hare a ƙauyuka da dama na jihar Zamfara. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Dr Suleiman Shu'aibu Shinkafi...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake jaddada aniyarsa na inganta samar da wutar lantarki a fadin kasar. Tinubu ya bayyana haka ne wajen taron kasashen Afirka wanda ya tattauna yadda za'a samarwa akalla mutane miliyan 300 wutar a nahiyar baki daya. Ganin irin matsalolin wutar da ake fuskanta a Najeriya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon manajan hukumar samar da wuta a kasar, Comrade musa Ayiga, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Wani bincike ya zargi kwamitin ilimi na majalisun Najeriya ta bukatar naira miliyan takwas takwas daga kowanne shugaban jami'ar tarayya kafin amincewa da kasafin kudinsu na wannan shekarar. Tuni wannan zargi ya haifar da cece kuce a cikin kasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Peter Lassa, tsohon shugaban hukumar gudanarwar manyan kwalejojin ilimin Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana...........
Tsoffin shugabannin Najeriya guda 2 wato Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari sun gurfana a wata kotun sasanta rikicin kwangilla domin bada ba'asi a kan soke kwangilar gina tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ministan Obasanjo ya bayar bada saninsa ba, da kuma kin biyan kudin sasanta matsalar da gwamnatin Buhari ta ki. Dangane da wannan dambarwa Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da daya daga cikin dattawan kasar Alhaji Sule Ammani, Yarin Katsina.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyartattaunawar.
Rahotanni daga sassan Najeriya sun nuna cewar an samu faduwar farashin kayan abinci bayan jama'ar ƙasar suka kwashe dogon lokaci suna fama da tsadarsa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Adamu Tilde, masanin harkar noma kuma ɗan kasuwa dangane da lamarin. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana........
Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa daga cikin mambobin Hukumar Lafiya ta Duniya, matakin da wasu ke ganin na iya illa ga dorewar hukumar wajen gudanar da ayyukan ta a duniya. Dangane da tasirin matakin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Sabon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana manufofin gwamnatinsa bayan karbar rantsuwar kama aiki da ya yi a matsayin shugaba na 47. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua na Babbar kwalejin Fasaha ta Kaduna dangane da wadannan manufofi, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.
Isra'ila da kungiyar Hamas sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen yakin da suka kwashe watanni 15 suna fafatawa, wanda ya yi sanadiyar kashe Falasdinawa sama da dubu 45, bayan harin da ya kashe Yahudawa sama da dubu guda. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin siyasar duniya Dr Abdulhakeem Garba Funtua game da yarjejeniyar, kuma ga yadda zantawasu ta gudana a kai.
Hukumomin sojin Jamhuriyar Nijar sun gabatar da wata sabuwar dokar da zata hukunta baƙin da ke shiga cikin kasar ba tare da halartattun takardu ba. Wannan ya biyo bayan zarge zargen da ake na samun wasu baki da ke yiwa kasar zagon kasa. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mai sharhi a kan Nijar, Abdoul Naseer, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
'Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi daban daban dangane da harin saman da sojoji suka kai a kan 'Yan sakai a Jihar Zamfara, wanda ya hallaka akalla mutane 15. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar tsaro kuma tsohon sojin sama Air Commodore Tijjani Baba Gamawa kan lamarin, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Hukumomin Najeriya sun ce mutane sama da dubu 600 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane suka kashe daga cikin mutane sama da miliyan 2 da dubu 200 da suka yi garkuwa da su, yayin da kuma aka biya kuɗin fansa r da ya kai sama da naira triliyan 2 da biliyan 200. Dangane da wannan rahoto mai tada hankali, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar tsaro Malam Yahuza Getso, kuma ga yadda zantawar tasu ta kasance.sai a latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar.
Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa a kan rashin isassun takardun kuɗaɗe a daidai lokacin da Babban Bankin ƙasar ke cewa akwai sama da naira triliyan 4 a hannun jama'a. Tuni rashin waɗannan kuɗaɗe ya shafi harkokin kasuwanci da kuma na yau da kullum a cikin ƙasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dr Isa Abdullahi. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana......
Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya ta ziyarci matatar man fetur ta birnin Fatakwal bayan gwamnatin ƙasar ta ce matatar ta fara aiki gadan-gadan. Domin jin yadda wannan matata ta fara aiki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Kwamare Nuhu Abayo Toro, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar kwadagon da suka ziyarci matatar.Ku lata alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
Ƙasashen duniya sun fara mayar da martani dangane da nasarar da ƴan tawaye suka samu na karɓe iko da birnin Damascus tare da tserewar shugaba Bashar Al Assad. Yayin da wasu ke murna dangane da kawo ƙarshen Assad a karagar mulki, wasu kuma na bayyana damuwa akan makomar yankin Gabas ta Tsakiya. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran, Ambasada Abubakar Chika. Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawarsu ta gudana........
An kammala zaɓen shugaban ƙasar Ghana, ba tare da fuskantar wata matsala ba, duk da cewa an yi hasashen za'a iya fuskantar tashin tashina a lokacin zaɓen. Sakamkon zaɓen na ƙarshen mako ya nuna cewa tsohon shugaban kasa John Mahama ne ya lashe saben, kuma tuni ɗan takaran jam'iyya mai mulki, Mahamudu Bawumia ya taya shi murya, abin da ke nuni da cewa ya amince da shan kaye.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar Bashir Ibrahim Idris tare da Alh. Irbaɗ Ibrahim, masanin siyasa a Ghana
Mazauna yankunnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na ci gaba bayyana irin halin kuncin rayuwa da suka samu kansu sakamakon yadda suke biyan ƙudi ga ƴan bindiga kafin su yi noma a daminar da suka gabata, yanzu kuma lokacin girbi ƴan bindigar sun hana su zuwa girbi da kwaso amfanin gonar sai sun biya.Wannan matsala ta yi sanadiyar talauta akasarin mutanen da ke wannan yankin. Dangane da wannan batu ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, kuma ga abinda ya shaida masa.
Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ɓacin ransu dangane da satar da wani tsohon babban jami'in gwamnatin ƙasar ya yi, ya kuma gina gidaje sama da 750. Tuni kotu ta ƙwace gidajen da kuma mallakawa gwamnati, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Bala Ibrahim mai sharhi kan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantarwarsu ta gudana.