Ilimi Hasken Rayuwa

Follow Ilimi Hasken Rayuwa
Share on
Copy link to clipboard

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin i…

Rfi - Nura Ado Suleiman


    • Jun 10, 2025 LATEST EPISODE
    • weekly NEW EPISODES
    • 10m AVG DURATION
    • 192 EPISODES


    Search for episodes from Ilimi Hasken Rayuwa with a specific topic:

    Latest episodes from Ilimi Hasken Rayuwa

    Dalilan da ya sa manasa ke neman ayi taka tsan-tsan wajen amfani da fasahar AI

    Play Episode Listen Later Jun 10, 2025 9:33


    Shirin Ilimi na wannan mako ya yi duba ne kan muhawarar da ake ci gaba da tafkawa kan fasahar nan ta kimsawa na'ura irin basirar ɗan Adam wadda aka sani da AI, wasu masana dai na cigaba da gargaɗin cewa ya zama dole a yi taka tsan-tsan domin bai kamata a saki jiki da wannan Fasaha ta AI ba, duk da amfanin da ta ke tattare da ita wajen sauƙaƙa ayyuka masu wahala da ɗan Adam ke yi. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna.................

    Yadda faɗuwar jarabar JAMB ta shafi ɗalibai da ke neman gurbin ƙaratu a Najeriya

    Play Episode Listen Later Jun 3, 2025 10:32


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar da aka samu ta faɗuwar jarabar sharar fage ta shiga jami'o'in Najeriya JAMB, da hukumar shirya jarabawar ta ce hakan ya faru ne a sakamakon tangarɗar da aka samu ta na'ura a lokacin rubutawa. Matslar da ta hana shafi ɗalibai dubu 300 da suka rubuta jarabawar.   Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.........

    Yadda Malaman makarantu suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a Abujan Najeriya

    Play Episode Listen Later May 27, 2025 9:47


    Shirin na wannan mako ya ba da hankali ne kan bikin ranar yara ta duniya wanda aka saba gudanarwa a ranar 27 ga watan mayun kowacce shekara, a Najeriya yayin da ake bikin wannan rana Malaman Makarantun firamare a Abuja babban birnin ƙasar ne ke shiga watanni na uku da fara yajin aikin sai Baba ta gani, sakamakon rashin fara aiwatar da sabin tsarin mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70 kamar yadda ƙungiyarsu ta Malaman makarantu ta bayyana. lamarin da ya ta da yajin aikin gargaɗi a baya kafin su tsunduma cikin wanda suke kai a yanzu.

    Yadda satar amsa tsakanin dalibai ke yiwa ilimi illa musamman a Najeriya

    Play Episode Listen Later May 20, 2025 9:40


    Shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali kan Illonlin satar amsa tsakanin Dalibai a yayin rubuta jarabawa. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna

    yadda amsa najeriya
    Shirin gwamnatin Najeriya na dawo da tsarin koyarawa da harshen uwa

    Play Episode Listen Later May 13, 2025 10:07


    A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan, shawarar gwamnatin tarayyar Najeriya ta dawo da tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare da ke fadin kasar. Tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare, wani tsari ne da aka gabatar a shekarar 2022, wadda ke da nufin inganta amfani da harsunan uwa a matsayin harshen koyarwa a makarantun firamare. Sai dai, a wancan lokaci da aka kaddamar da manufar za a yi amfani da ita ne akan Yara yan aji daya zuwa na makarantun firamare.Hakan kuwa ya biyo bayan bincike-bincike da aka gudanar wanda ya nuna cewa rashin fahimtar darusan da ake koyarwa da harshen Ingilishi ya bada gudunmowa wajen barin Yara makaranta da kuma haifar da koma-bayan ilimi a Najeriya.Sai da masana sun bayyana wasu ƙalubale da za a iya fuskanta da suka hadar da rashin wadatattun kayan koyarwa, da matsalolin zabar babban yare a cikin al'ummomi da ke amfani da harsuna da yawa.

    Ɓangaren ilimin wasu jihohin Najeriya sun gaza samun tallafin gwamnatin ƙasar

    Play Episode Listen Later May 6, 2025 10:08


    Shirin na wannan mako ya duba dalilan da suka sanya bangaren ilimi a matakin farko a Najeriya na matakin jihohi ya gaza samun gajiyar tallafin da zai taimaka wajen bunkasa karatun kananan yara, duk da makudan kudaden da gwamnatin ƙasar ta ware a matsayin tallafi. Bisa ga kididdigar da aka yi a baya-bayan nan, akwai yara fiye da miliyan 10 da ya kamata a ce suna makaranta a Nigeria amma a halin yanzu yawo su ke yi loko-loko ba tare da samun kowani irin nau'in ilimi ba.‘Yan kalilan din da suke samun halartar makaranta, mafi yawan su na fama da rashin wadatattun kayan karatu, kama daga azuzuwa, kayan koyarwa, kujeru da kuma uwa uba kwararrun malamai.

    Ƙalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar magana- Kashi na 2

    Play Episode Listen Later Apr 29, 2025 10:29


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya ɗora ne akan shirin makon jiya sai dai a wannan karon shirin ya karakata ne ga ɓangaren yadda matasa ke sauya wasu kalmomin Hausa ta hanyar yi musu ƙawance da wasu yaruka su bayar da wata kalma da za ta bayar da ma'anar da za a fahimci abin da ake nufi cikin sauƙi. Idan mai sauraro na biye da shirin na Ilimi Hasken Rayuwa a makwannin baya-bayan nan yana ci gaba da bibiyar dokoki ko kuma ladubban rubutu da karatu baya ga magana da harshen na Hausa, harshen da ake ci gaba da ganin bunƙasarsa ba kaɗai a nahiyar Afrika ba, harma da sauran nahiyoyi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Kalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - kashi na 2

    Play Episode Listen Later Apr 22, 2025 10:00


    Shirin na yau, ya ɗora ne akan kashi na farko da muka gabatar a makon jiya, wanda ya yi duba game da yadda harshen Hausa ya bunkasa a lokutan baya, da muhimmacinsa, baya ga matsalolin da yake fuskanta da ma kalubalen da Rubutun Hausa ke fuskanta a kafofin sada zumunta.  Masana sun bayyana ka'idojin rubutun Hausa, a matsayin wani yanayi na lura tare da kiyaye ka'idojin harshen Hausa a rubuce domin samun damar isar da sakon da marubuci ke nufi zuwa ga mai karatu daidai ba tare da dungushe ko sauya ma'anar da marubuci ke nufi ba. A cewar masanan kiyaye ƙa'idodin rubutun yana kuma samar da saukin fahimtar karatu daga mai karantawa.Ko da a kafafen yada labarai, rashin kiyaye ka'idojin rubutun Hausa yakan taka rawa wajen sauya ma'anar labari, to ko ya masu bibiyar shafukan  yanar gizo na kafafen watsa labarai ke ji idan suka ga ba a yi amfani da harufa masu lanƙwasa ba kamar Ɓ da Ɗ da kuma Ƙ? Ga abinda wasu ke cewa. 

    Ƙalubalen da suka dabibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - Kashi na 1

    Play Episode Listen Later Apr 15, 2025 9:49


    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon shirin ya sauya salo zuwa mai dogon zango ta yadda zai tattauna da masu ruwa da tsaki a kan bunƙasar harshen Hausa da matsalolin da ya ke fuskanta da dalilan da suka haifar da matsalolin, da dai sauran muhimman batutuwa da suka shafi harshen na Hausa. Harshen Hausa, harshe ne da yake da tsohon tarihi wanda ya shafe ɗaruruwan shekaru ana magana da shi, wanda alƙaluma suka tabbatar da cewar zuwa yanzu miliyoyin mutane ne ke magana da harshen a sassan duniya.Wani rahoto da aka wallafa a shekarun baya bayan nan ya nuna cewar a halin yanzu Harshen Hausa ne Harshe na 11 da aka fi amfani da shi a duniya, zalika an yi ƙiyasin cewar mutane miliyan 150 ne ke magana da shi a sassan Duniya.Masana na kallon waɗaccan alƙaluma a matsayin dallilan da suka sanya harshen na Hausa yin shaharar ta kai ya yi gogayya da dukkanin manyan harsunan duniya, lura da yadda harshen ke da yalwar kalmomi da za a iya sarrafa su gami da bayyana kowanne irin tunani da su, walau a litattafai, kafofin yaɗa labarai da sauran hanyoyi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Yadda yaran 'yan makarantun firamare suka koma haƙar ma'adanai a Najeriya

    Play Episode Listen Later Apr 8, 2025 10:05


    Shirin na wannan mako ya duba yadda ƙananan yara 'yan makarantun firamare suka karatu domin aikin haƙar ma'adanai saboda cimma bukatun yau da kullum a jihar Bauchin Najeriya. A latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.

    Yadda ɗalibai a Bauchi ke watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai

    Play Episode Listen Later Apr 1, 2025 10:05


    Shirin wannan makon zai yi dubi ne akan yadda ɗalibai a jihar Bauchi ke yin watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai.Jihar Bauchi, ta yi ƙaurin suna a baya a matsayin wadda ke sahun gaba wajen yawan yaran da suka yi watsi da makarantunsu tare da rungumar harkar tonon ma'adinai don samun dogaro da kai.Dalili ke nan da fiye da rabin daliban wasu makarantun firamare a jihar, suka bar zuwa makaranta inda suka karkatar da hankali kan harka haƙon ma'adanan.

    Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin ɗaukar nauyin karatun ƴaƴa mata zuwa PHD

    Play Episode Listen Later Mar 25, 2025 9:29


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan shirin da gwamnatin jihar Jigawa ta ƙaddamar, na ɗaukar nauyin karatun ‘ya'ya mata daga Firamaren har zuwa karatun Digirin Digirgir, shirin da  ta ce tana fatan zai zaburar da ƙarin mata da iyayensu wajen duƙufa neman ilimi, ba tare da fargabar fuskantar ƙalubale na rashin ƙarfi ta fuskar tattalin arziƙi ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman.........

    Gwamnatin Ghana na nazarin yiwuwar fara bayar da ilimin Sakandire kyauta

    Play Episode Listen Later Mar 4, 2025 9:52


    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan shirin gwamnatin Ghana na fara bayar da ilimin Sakandire kyauta, kodayake an faro da sauraren ra'ayin jama'a kan wannan shiri wanda ma'aikatar ilimin ƙasar ta bijiro da shi. Bayanai sun ce baya ga bayar da ilimin kyauta, tsarin zai kuma kawo gyara a yanayin bayar da ilimi musamman a manyan makarantun ƙasar ta Ghana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

    Yadda matasa a Najeriya suka ƙirƙiri injin da ke tsince tsakuwa daga Shinkafa

    Play Episode Listen Later Feb 25, 2025 9:59


    A wannan makon, shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara ya mayar da hankali kan yadda wasu matasa suka ƙirƙiri wani nau'in inji da ke cire tsakuwa daga jikin shinkafa, wanda zai taimaka matuƙa wajen samar da tsaftatacciyar shinkafa. Kafin wannan hoɓɓosa daga matasan, akan shigo da irin injinan ne daga ƙasashe irin China don sauƙaƙawa Manoma.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Gwamnatin Najeriya ta ɗaga likafar Kwalejin Kimiyyan Lafiya ta Tsafe zuwa Jami'a

    Play Episode Listen Later Feb 18, 2025 9:58


    Shirin “Ilimi Hasken Rayuwa” namu na wannan mako, ya  yada zango ne a tarayyar Najeriya, inda shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudurin samar da sabuwar jami'a kimiyyan lafiya da fasaha ta tarayya wato Federal University of Health Science and Technology a garin Tsafe na Jihar Zamfara, bayan tsallake dukkan matakan majalisa dokokin ƙasar. Wannan saka nannu na shugaban ƙasar ya yi zai bada damar ƙara inganta harkan kiwon lafiya ta hanyar samar da kwararru.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.........

    Matsin rayuwa na barazanar gurgunta karatun ƙananan yara a Najeriya

    Play Episode Listen Later Feb 11, 2025 9:38


    Shirin ''Ilimi Hasken Rayuwa'' tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yadda halin matsin rayuwa ke yin tasiri a kan karatun yara ƙanana lamarin da ya sa kaso mai yawa daga cikinsu ba sa samun cikakkiyar fahimta a kan darussan da ake koya musu, saboda dalilai da dama masu alaka da matsin rayuwar. Baya ga batun ci a koshi dai, yanyayin da yara ƙanana ke tafiya makarantunsu a yanayin da ake ciki ma lamari ne da ya kamata a mayar da hankali akai, la'akari da cewar a wasu lokutan ɗan hakin da ka raina kan tsone maka ido.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    Yadda za'a koya wa yara iya karatu tun daga matakin farko a Najeriya

    Play Episode Listen Later Feb 4, 2025 10:14


    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan lokaci ya mayar da hankali kan yadda za'a bi ƙa'idoji da hanyoyi domin koya wa yara iya karatu a matakin farko a Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...

    Gasar HIFEST karo na bakwai a Najeriya

    Play Episode Listen Later Jan 28, 2025 10:05


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne, kan yadda wata kungiya a Najeriya, ke karfafa gwiwar daliban sakandire kan yadda za su bayyana baiwar da suke da ita, musamman a bangaren ilimin fasaha.

    karo najeriya
    Mahimmancin kwalejojin fasaha a Najeriya wajen bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya

    Play Episode Listen Later Dec 24, 2024 10:02


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya yi nazari ne kan mahimmancin kwalejojin fasaha na Najeriya ga bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya da fasaha a ƙasar, da kuma kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu, sai kuma duba hanyoyin da za a bi don farfaɗo da martabarsu. Ku latsa almar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman............

    ku asar najeriya
    Tasirin da salon koyarwa ke da shi wajen baiwa ɗalibai ingantatcen ilimi

    Play Episode Listen Later Dec 10, 2024 10:01


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan mako, ya tattauna ne a kan salon koyarwa tun daga matakin makarantu na ƙasa wato ‘Method of Teaching' a turance, da tasirin da wannan salo ke da shi kan bayar da ilimi. Salo ko kuma dabarun koyarwa matakai ne ko tsarin da malamai ke amfani da su wajen koyar da ɗalibai darussa, a kuma tabbatar da cewa ɗaliban sun fahimci darasin da ake yi musu. A mafi yawan lokuta waɗannan dabaru sukan bambamta a tsakanin darussa, zalika ya danganta da matakan ilimi daga ƙasa, da na tsakiya zuwa na sama.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.......

    Rashin malamai ya tilasta iyaye janye yaransu daga makarantu a kudancin Najeriya

    Play Episode Listen Later Nov 6, 2024 9:16


    Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda iyaye a yankin kudancin ƙasar ke janye yaransu daga Makarantu saboda ƙarancin makarantu a yankin. Jihar Abia na sahun ƴan gaba gaba da ke fama da wannan matsala inda a baya-bayan nan aka tarin yaran da suka daina zuwa makaranta.

    daga rashin najeriya
    Gwamnatin Bauchi na shirin mayar da yara fiye da miliyan 1 makarantu

    Play Episode Listen Later Oct 29, 2024 9:45


    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ke yunƙurin mayar da yara fiye da miliyan guda makaranta a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar. Tuni masu ruwa da tsaki a wannan yanki suka yi maraba da matakin gwamnatin ta Bauchi, lura da yadda yunƙurin zai taimaka matuƙa wajen rage ɗimbin yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba a Arewacin na Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

    Ɓanagrorin ilimi sun koka da matakin JAMB na durkusar da harshen Faransanci

    Play Episode Listen Later Oct 24, 2024 10:00


    Sannu a hankali darussan nazarin harshen faransanci na kara karbuwa a manyan makarantun Nigeria, sai dai kuma, wani matakin da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a Nigeria, ta aiwatar, na cire takardar shaidar share fagen shiga jami'a ta karatun  harshen faransanci, daga cikin darussan da hukumar ta JAMB ke bayar da guraben karatunsu a manyan makarantu ya daga hankalin masu ruwa da tsaki.

    Yadda wasu gwamnoni a Najeriya ke biris da yaran talakawa da suka tura karatu wasu kasashe

    Play Episode Listen Later Oct 15, 2024 10:42


    Shirin na wannan rana ya duba yadda wasu gwamnonin a Najeriya ke daukar alhakin tura yaran talakawa wasu kasashe domin karatu amma kuma daga bisani sai gwamnatin ta yi biris da sha'aninsu.

    Yadda jami'o'i a Najeriya ke neman tallafin inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI

    Play Episode Listen Later Oct 8, 2024 10:00


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami'o'i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.......

    ai ku yadda tuni turai najeriya faransa
    Yadda ake ƙara samun yawaitar masu karatun yaƙi da jahilci a Adamawa

    Play Episode Listen Later Oct 1, 2024 9:54


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna ne akan yadda makarantun manya ko kuma na yaƙi da jahilci kamar yadda akan kira su, ke fuskantar ƙalubalen ɗauka ko ilimantar da ɗaliban da yawansu ke ƙaruwa a kullum, adadin da ya zarta na makarantun manyan da ake da su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara......

    Hukumar JAMB ta shirya taro kan bai wa naƙasassu dama

    Play Episode Listen Later Sep 24, 2024 10:00


    Shirin namu na wannan mako zai yi dubi ne kan yadda  hukumar kula da harkar jarabawan shiga jami'o'i a  Najeriya wato JAMB da hadin guiwan kungiyar zabiya na kasa ta shirya taron nahiyar Afrika na farko kan baiwa nakasassu ko masu larura ta musamman dangane da  harkar ilimi kamar kowani dan adam. Taron an shirya shi ne dai la'akari da irin kalubalen da masu larura ta musamman ke fama da ita a kasashe masu tasowa kamar Najeriya,kama daga kyama,nuna musu banbanci da dai sauransu.

    Fannin ilimi a Najeriya na fuskantar barazana sakamon matsin tattalin arziki

    Play Episode Listen Later Sep 17, 2024 10:06


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya yi duba ne a kan yadda matsin tattalin arziki da kuma tsare-tsaren gwamnati suka kassara fannin ilimi a tarayyar Najeriya. Daga ɓangaren mahukunta jami'o'in suna ganin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su a fannin ilimi sune suka sanya a wannan lokaci ko da gyare-gyare a jami'o'in basa iya aiwatarwa. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara........

    Har yanzu tsarin jagoranci da bada shawarwari na tasiri a makarantu?

    Play Episode Listen Later Aug 27, 2024 9:21


    Shirin a wannan mako ya duba yadda tsarin jagoranci da bada shawarwari a makarantu, tsarin da ke taimakawa dalibai zabar irin fannin da suke son kwarewa akai, inda sun kai matakin jami'a da sauransu. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara

    Tsarin ilimin Sakandire kyauta a Ghana ya ƙarfafa gwiwar dubban ɗalibai

    Play Episode Listen Later Aug 20, 2024 9:55


    Shirin ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon ya mayar da hankali kan tsarin bayar da ilimin Sakandiren kyauta a Ghana, wanda ya taimaka matuka wajen ƙara yawan Ɗaliban da ke halarta karatu a wannan mataki. Duk da cewa shirin ya laƙume kuɗaɗe masu tarin yawa amma gwamnatin ƙasar ta Ghana ta ce ko shakka babu kwalliya ta biya kuɗin sabulu cikin shekaru 5 da fara tsarin.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shiri.

    Tasirin da shirin gwamnatin Ghana na ilimin sakandare kyauta ya yi

    Play Episode Listen Later Aug 13, 2024 10:09


    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa'  na wannan makon zai yi duba ne kan shirin bayar da ilimin sakandare kyauta da gwamnatin Nana-Akufo Addo ta ƙasar Ghana ta bullo da shi. Bincike ya nuna cewa wannan shiri ya yi tasiri, duba da yadda aka samu ƙaruwar adadin ɗaliban da ke karatun sakandare a cikin shekaru biyar da suka gabata. Shirin ya tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan faannin, inda suka fayyace bayanni filla-filla a kai. 

    Yadda tsarin koyo da koyarwa a karni na 21 ke saukakawa wurin fahimtar karatu

    Play Episode Listen Later Jul 30, 2024 9:59


    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimtar da ɗalibai, sannan ɗalibai su ma su ji sauƙin fahimtar abin da ake koyar da su a aji. A wannan mako, mun dubi yadda tsarin yake aiki tare yadda ya sauƙaƙa wa malamai da ɗalibai wurin fahimtar karatu a wannan zamani musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

    Karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana

    Play Episode Listen Later Jul 23, 2024 9:57


    Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana. Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai.Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.

    Yadda tsadar lantarki ke kassara harkokin karatun manyan makarantun Najeriya

    Play Episode Listen Later Jul 16, 2024 10:00


    A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya.Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki. To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a kusan manyan makarantun Najeriya, wata matsalar kuma ita ce ta tsadar wutar a sakamakon ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ta yi.Wannan dalili ne ya sanya ƙungiyar shugabannin jami'o'in Najeriya, ta yi kashedin cewa jami'o'in tarayyar ƙasar aƙalla 52 ka iya durƙushewa nan ba da jimawa ba, a sakamakon tsadar kuɗin wutar.Shugabannin Jami'o'in na Najeriya, sun yi wannan gargaɗi ne bayan wani sabon ƙari na kashi 300 da aka yi musu a kwanakin baya.Kuna iya latsa alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...

    Dalilan mummunar faduwar jarabawa da daliban jamhuriyar Nijar suka yi a bana

    Play Episode Listen Later Jul 9, 2024 9:55


    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda dalibai a jamhuriyar Nijar suka yi mummunar faduwa a sakamakon jarabawar karshe ta makarantar Sakandare. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadir Haladu kiyawa

    suka bana shirin nijar jamhuriyar nijar
    Yadda ayyukan ƴan ta'adda suka kassara harkokin Ilimi a Arewacin Najeriya

    Play Episode Listen Later Jul 2, 2024 9:58


    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta'adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar. Bincike ya nuna cewa, tun bayan harin na 2014, 'yan ta'adda sun ci gaba da kai makamancinsa a kimanin makarantu 17, waɗanda suka haɗa da makarantun Firamare da sakandare da ma manyan makarantun gaba da sakandare, inda suka yi garkuwa da dalibai da dama, an sako wasu bayan biyan kuɗin fansa, wasu kuwa suna rike a hannunsu  har zuwa yanzu. Cikin shekaru goma da fara ƙaddamar da irin wannan ta'addanci kan makarantu da ɗalibai, masana sun bayyana shakku kan gwamnatin Najeriya tare da zarginta da nuna halin ko in kula kan ilimi tare da rayukan al'ummar kasar musamman ɗalibai. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...

    Tasirin sabuwar hanyar koyarwa a duniya

    Play Episode Listen Later Jun 25, 2024 9:59


    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan sabuwar hanyar koyarwa, da kuma tasirin da ta ke da shi a harkar ilimi a faɗin duniya, wato Innovative Teaching Method a turance. Ita dai sabuwar hanyar koyarwa wato Innovative Teaching Method, hanya ce da ta sha bambam da hanyoyin koyarwa da aka saba gani a lokutan baya, domin ita ana koyar da ɗalibai ne bisa doron buƙatarsu ta koyo, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da kuma na'urori, batare da malami ya zama shi ne ruwa kuma shi ne langa ba.

    Yadda jaddawalin karatun Najeriya ke haifar ga koma-baya a Fannin Ilimin Kasar

    Play Episode Listen Later Jun 18, 2024 9:59


    A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne a kan yadda tsarin jaddawalin karatun Najeriya ke haifar da koma-baya a fannin ilimin kasar. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...

    Ban-bancin da ke da shi wajen karatun Ilimin kimiyya da fasaha a kasashen Duniya

    Play Episode Listen Later Jun 11, 2024 9:17


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne a kan tsarin ilimin kimiyya da fasaha tsantsa hadi da lissafi, wato STEM Education a turance. Mafi yawancin kasashen Duniya da suka ci gaba, na bawa wannan tsari na Ilimin Kimiyya da fasaha tsantsa hadi da Lissafi fifiko a makarantunsu, la'akhari da yadda kimiyya da fasaha a wannan zamani suka zama ginshinkin ci gaba a sararin wannan duniyar. Kuna iya latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......

    Jami'ar Umaru Musa ta yaye sama da dalibai dubu goma a wannan shekarar

    Play Episode Listen Later Jun 4, 2024 10:14


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake ci gaba da samun ci gaba a bangaren daliban da ke zuwa makaranta a yankin Arewacin Najeriya. Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a da ke jihar Katsina ta samu nasarar yaye sama da dalibai dubu 10 a wannan shekarar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin ta re da Abdulkadir Haladu Kiyawa........

    Yadda Jami'o'in Najeriya suka fara mayar da hankali kan karatun koyon sana'a

    Play Episode Listen Later May 21, 2024 9:37


    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda aka fara mayar dahankali a kan karatun koyon sana'a a Kwalejoji da Jami'o'i a Najeriya.Kuna iya Latsa alamar sauti domin sauraron shirin...

    Yadda Dalibai ke bada gudunmawa wajen sarrafa sinadaran da basa gurbata muhalli

    Play Episode Listen Later May 14, 2024 10:01


    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba yadda Dalibai a kasashen da suka ci gaba ke bayar da gudunmawa wajen sarrafa sinadarin "Hydrogene" da baya gurbata muhalli sosai, ta fuska kere-kere da nufin inganta iskar da ake shaka, bisa tallafin gwamnatocin kasashensu.

    Yadda matasa ke dukufa wajen amfani da Internet don dogaro da kai

    Play Episode Listen Later May 7, 2024 10:16


    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako zai duba yadda matasa suka dukufa wajen amfani da yanar gizo don dogaro da kai. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

    internet shirin yadda najeriya matasa
    Karuwar masu mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya, na barazana ga karewar kwararru

    Play Episode Listen Later Mar 26, 2024 10:00


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama. Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu.Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

    bogi masu najeriya
    An samar da cibiyar sadarwa a jahar Bauchi don saukakawa dalibai wajen bincike

    Play Episode Listen Later Mar 19, 2024 9:47


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al'umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet musamman wuraren da babu irin wannan ci gaba ko kuma wuraren da suke da shi amma bashi da karfi, wanda jama'are ke cikin wannan rukuni. Kungiyoyin da sun sha alwashin samar da irin wannan cibiyar sadarwa guda 20 a shiyoyin Najeriya shida zuwa karshen wannan shekara domin samar da internet a yankunan karkara.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

    Taro kan gudummawar kafafen yada labarai a bangaren tsaro a jami'ar ABU Zaria

    Play Episode Listen Later Mar 5, 2024 9:57


    Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya  sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Ya yi wannan ne da zummar taimaka wa kokarin da al'umma ke yi wajen warware wa kansu matsalar tsaron da ke damun su.

    Yadda dalibai ke barin karatu a Nijar don tafiya neman kudi a wasu kasashe

    Play Episode Listen Later Feb 27, 2024 10:09


    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa kan sanin muhimmancin da ilimi ke da shi. A Nijar kashi 25 na yara ne ke samun zuwa makarantar boko, kuma daga yara 100 da ake sanyawa a makarantun firamare uku kadai ke kaiwa matakin jami'a.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

    Yadda gwamnatin jahar Neja ta fara horas da dalibai sana'oin dogaro da kai

    Play Episode Listen Later Feb 20, 2024 10:05


    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne kan yadda gwamnatin jahar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta samar da shirin horas da dalibai sana'oin hannu don dogaro da kai. Gwamnatin jahar dai ta ware ranar Juma'ar kowane mako don gudanar da darasin koyon sana'oin hannu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

    Yadda amfani da komfuta ya shafi kyaun rubutun dalibai

    Play Episode Listen Later Jan 31, 2024 9:34


    A wannan makon zamu duba yadda ci gaban kimiyya da Ilimi ke zama wani nau'I na koma baya musamman a tsakanin dalibai a Najeriya.Tun bayan samar ko kuma kirkirar na'urar kwamfuta a 1837, da kuma shigowar ta Najeriya karon farko a 1963 sannu a hankali take bazuwa tsakanin jama'a, yayi da kuma ake samun ci gaba ta fannin amfani da ita. 

    Gwamnatin Neja na shirin farfado da tsarin karatun makiyaya

    Play Episode Listen Later Dec 19, 2023 9:56


    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne da tsarin karatun 'yayan makiyaya, wato Nomadic Education. Gwamnatin jihar Neja ce ta yi hobbasa don farfado da shirin karatun 'yayan makiyaya a jihar. Shirin zai bai wa makiyaya damar samun ilimi a duk inda suka yi balaguro don inganta makomarsu. Yanzu haka dai shirye-shirye sun yyi nisa a game dfdaa wannan shirin a jihar Neja  mai fara da matsalar tsaro sakamakon ayyukan 'yan bindiga da ke kashe mutane da satar su don kudin fansa.

    Taimakon da kirkirarren Tabarau ke bai wa masu fama da matsalar raunin gani

    Play Episode Listen Later Nov 28, 2023 10:04


    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan nazarin da masana kimiya suka yi wajen kirkirar Tabaraun hangen nesa, don taimakawa masu raunin gani. A jamhuriyar Nijar, matsalar gani na zama babban kalubale ga al'ummar kasar wacce a yanzu har aka fara samunta a tsakanin matasa. Tuni dai matsalar ta sanya likitoci fara kiraye-kiraye ga al'umma da su tashi tsaye wajen kula da lafiyar idonsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

    Claim Ilimi Hasken Rayuwa

    In order to claim this podcast we'll send an email to with a verification link. Simply click the link and you will be able to edit tags, request a refresh, and other features to take control of your podcast page!

    Claim Cancel