Mu Zagaya Duniya

Follow Mu Zagaya Duniya
Share on
Copy link to clipboard

Wannan Sabon Shiri ne da ke tattauna Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya. Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Rfi - Abdoulaye Issa


    • May 31, 2025 LATEST EPISODE
    • weekly NEW EPISODES
    • 20m AVG DURATION
    • 246 EPISODES


    More podcasts from Rfi - Abdoulaye Issa

    Search for episodes from Mu Zagaya Duniya with a specific topic:

    Latest episodes from Mu Zagaya Duniya

    Menene ya sauya a yammacin Afrika tun bayan kafa ECOWAS shekaru 50 da suka gabata

    Play Episode Listen Later May 31, 2025 20:01


    Shirin na wannan mako ya duba bikin cikar kungiyar ECOWAS shekaru 50 da kafuwa, da sauran manyan labaran da suka wakana a wannan mako. Ku danna alamar saurare domin jin cikaken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

    Bitar labaran mako: Bukin cikar RFI Hausa shekaru 18 da kafuwa

    Play Episode Listen Later May 24, 2025 19:52


    Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wanan makon tare da Nura Ado Suleimane, ya mayar da hankali kan wasu manyan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi ciki harda bukin cika shekaru 18 da gidan radiyon RFI ta yi.

    Ƙungiyar JNIM ta kashe sojojin Burkina Faso kusan 200

    Play Episode Listen Later May 17, 2025 20:00


    Shirin Mu zagaya Duniya na wanan mako tare da Nura Ado Suleimane, ya maida hankali kan wasu munanan hare hare da kungiyoyi masu dauke da makamai su kai a Burkina Faso da wasu sassan Najeriya. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken bayani.....

    Rasha ta karɓi baƙuncin taron bikin cika shekaru 80 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu

    Play Episode Listen Later May 10, 2025 20:03


    Shirin  Mu Zagaya Duniya  na wanan makon tareda Nura Ado Suleimane, ya yi duba ne kan nasarar kashe ‘yan ta'adda fiye da dubu 13 da jami'an tsaron Najeriya suka yi. Shirin kuma ya  sake waiwayar wani rahoton ƙwararru da ya ce dubun dubatar mutane ne ke rasa rayukansu a dalilin cutuka masu alaka da abincin da suke ci.Haka zalika ya taɓo batun yadda a Sudan ta Kudu kazamin rikicin da ke faruwa a yankunan da ke kusa da kogin Nilu, ya hana jami'an agaji tallafa wa yara ƙanana kimanin dubu 60 da ke fama da cutar yunwa.Akwai kuma labarin yadda Rasha ta karbi bakuncin taron ƙasashe a bikin cika shekaru 80 da samun nasarar murƙushe sojojin Nazi na Jamus abin da ya kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Ma'aikata a sassan duniya sun gudanar da bikin ranarsu a cikin mumunan yanayi

    Play Episode Listen Later May 3, 2025 20:02


    Shirin  Mu Zagaya Duniya  na wanan makon tareda Nura Ado Suleimane, ya yi duba ne kan  mai'aikata a sassan Duniya suka gudanar da bikin rana ta musamman da aka ware musu a daidai lokacin da wani adadi da dama daga cikinsu ke fuskantar ƙalubale iri-iri.  Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......

    Tasirin ziyarar ministan wajen Najeriya a Nijar ga rikicin ƙasashen biyu

    Play Episode Listen Later Apr 19, 2025 19:23


    Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman, kamar kowannen mako kan yi bitar muhimman labaran da suka faru cikin makon da muke ban kwana da shi, kuma kamar kodayaushe a wannan karon wasu daga cikin labaran da ke ƙunshe a shirin sun ƙunshi ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Najeriya ya kai Jamhuriyar Nijar, wadda a karon farko kenan tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum da sojoji suka yi. A Najeriya shirin ya leƙa Filato aka samu hasarar ɗimbin rayuka, sakamakon hare-haren da aka kai a wasu yankunan jihar, a Najeriyar za a ji yadda wata shu'umar cuta ta janyowa manoman Tumatir hasarar ɗimbin amfanin gonar, sai kuma yadda ‘yan damfara suka yi awon gaba da sama da naira tiriliyan 1 a Najeriyar.A Sudan kuwa ƙungiyar bayar da  agaji ta Redcross ce ta aƙalla mutane dubu 8000 suka bace a yakin kasar.Sai kuma Kenya inda aka cafke wasu mutane da ke shirin fasa kaurin dubban tururuwa zuwa ƙasashen ƙetare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    kenya sudan red cross ku sai nijar najeriya jamhuriyar nijar amurka faransa
    Matakin Trump na janye haraji ya farfado da tagomashin kasuwannin duniya

    Play Episode Listen Later Apr 12, 2025 19:55


    Shirin Mu Zagaya Duniya na wanan makon tareda Nura Ado Suleimane ya duba  yadda matakin shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da harajin da ya shafe kayayyakin dukkanin kasashe ya farfado da tagomashin kasuwannin duniya, duk da cewar Gogan ya ce sassauncin na kwanaki 90 bai shafi ƙasar China ba. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

    Ƙasashen Duniya sun lashi takobin mai da martanin ƙaƙaba wa kayayyakin Amurka haraji

    Play Episode Listen Later Apr 5, 2025 19:50


    ƙasashe da dama ciki har da na Ƙungiyar EU, suka sha alwashin mayar da martanin ƙaƙaba wa kayayyakin Amurka haraji, kamar yadda shugaba Trump ya ƙaddamar da sabon tsarin karɓar harajin da ya ce ya shafi duniya baki ɗaya.

    Ana gudanar da bukukuwan sallah bayan kammala azumin watan Ramadana

    Play Episode Listen Later Mar 30, 2025 19:42


    Saudiyya da wasu kasashen Duniya da suka hada da Najeriya da Nijar na gudanar da bukukuwan Idin ƙaramar Sallah bayan kammala azumin watan ramadana. A jiya Asabar ne ,ƙotun kolin Saudiyya ta yanke hukuncin cewa yau Lahadi 30 ga Maris, 2025 ita ce ranar farko ta Idin Al-Fitr, a cewar wata sanarwa da kotun masarautar Saudiyya ta fitar ta kafafen yada labarai.Ana dai kayyade lokacin da za a gudanar da bukukuwan, wanda ke nuna karshen azumin watan Ramadan, bisa ga ganin jinjirin wata, kamar yadda kalandar musulunci ya tsara.Sai dai ƙasashen Oman da Jordan da ke makwabtaka da ita da kuma Iran masu rinjayen mabiya Shi'a sun ce ba za a fara sallar Idi ba har sai ranar litinin saboda har yanzu ba a ga jinjirin wata ba. Masar da sauran kasashen Arewacin Afirka sun bi sahun.A duk fadin duniyar musulmi, shagulgulan watan Ramadan na bana ya ci tura, bayan da Isra'ila ta sake kai hare-hare a zirin Gaza, inda yakin da ta ke yi na ƙawar da ƙungiyar Hamas ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta Hamas ta bayyana.

    Sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya ta fara aiki a Jamhuriyar Nijar

    Play Episode Listen Later Mar 29, 2025 19:42


    Sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya ta fara aiki a Jamhuriyar Nijar, bayan da aka kaddamar da fara aikin ƙudurorin da taron ƙasar na watan Fabarairu ya bayar da shawarar aiwatarwa.A Najeriya hukumar Kwastam ta janaye haraji a kan dukkanin kayayyakin asibiti da magungunan da ake shigar da su ƙasar daga ƙasashen ƙetare.Mummunar girgizar kasa ta rutsa da gwamman mutane a ƙasashen Myanmar da Thailand.

    thailand myanmar aiki nijar najeriya jamhuriyar nijar
    Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci a jihar Rivers, ya kuma dakatar da gwamna da mataimakiyarsa

    Play Episode Listen Later Mar 22, 2025 20:03


    Masu sauraro Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haɗuwa cikin shirin Mu Zagaya Duniya, wanda ke waiwayar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana da shi. A farkon makon da muka yi bankwana, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci a jihar Rivers, ya kuma dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da kuma dukkan ‘yan majalisun dokokin jihar na tsawon watanni shida.Tinubu ya ce ya ɗauki matakin ne biyo bayan rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jihar, lamarin da ya kai ga karya doka da oda da kuma fara kai hari kan butun mai.

    Ƙungiyar ECOWAS ta bijiro da fara aikin rundunar soji mai zaman ko-ta-kwana

    Play Episode Listen Later Mar 15, 2025 20:04


    Shirin Mu Zagaya Duniya'na wanan makon tareda Micheal Kuduson ya kuma duba batun watsi da wasu kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Nijar suka yi da rahoton taron ƙasa da ta shawarci shugaban mulkin sojin ƙasar ya  ci gaba da zama kan karagar  mulki har nan  da shekaru biyar. Latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin....

    zaman ecowas soji jamhuriyar nijar micheal kuduson
    Manyan hafsoshin tsaron Najeriya da Nijar da Burkina Faso da kuma Mali sun tattauna

    Play Episode Listen Later Mar 8, 2025 19:19


    Mu Zagaya Duniya,bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana,cikin labarun da shirin ya waiwaya aƙwai tattaunawar da aka yi tsaƙanin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da Nijar da Burkina Faso da kuma Mali,sai danbarwar da aka shafe makon da ya ƙare ana gani tsakanin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya da ɗaya daga cikin Sanatoci zauren majalisar Mata, bayan da ta zarge shi da ƙoƙarin cin zarafinta ta hanyar nemanta da lalata.

    Majalisar Ƙoli ta Musulinci ta gargaɗi malaman Najeriya akan tada husuma

    Play Episode Listen Later Mar 1, 2025 20:02


    Daga cikin labarun da shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya ƙunsa akwai gargaɗin da Majalisar Ƙoli kan Shari'ar Musulunci ta Najeriya ta yi wa Malamai kan cewa su yi taka tsan-tsan yayin gabatar da wa'azi, musamman a cikin watan Azumin Ramadana mai alfarma. Sojojin Somaliya sun halaka mayaƙan Al Shebaab a ƙalla 70.Muna kuma ɗauke da bitar rahoton da ya gano yadda wata muguwar ƙwaya mai ta kashe dubban mutane (Tare da ci gaba da aika wasu dubban zuwa asibiti) a wasu ƙasashen yammacin Afirka.

    akan tada muna tare daga najeriya afirka majalisar
    Babangida ya nemi afuwar 'yan Nijeriya a kan soke zaɓen Abiola

    Play Episode Listen Later Feb 22, 2025 19:46


    Kamar yadda aka saba a kowane mako, a wannan karon ma shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya waiwayi wasu daga cikin manyan labaru a kan lamurran da suka wakana a cikin satin da muka yi wa bankwana. Daga cikin labarun da shirin ya ƙunsa kuma akwai, afuwar 'yan Nijeriya da tsohon shugaban ƙasar Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nema a kan soke zaɓen ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.Shirin ya kuma yi bitar labarin nasarar halaka mayaƙan Boko Haram kusan 300 da sojojin Chadi suka samu.

    Matakin ƙarin haraji kan kiran waya da sayen data a Nijeriya

    Play Episode Listen Later Feb 15, 2025 19:34


    Shirin Mu zagaya Duniya na wannan mako matakin ƙarin haraji kan kiran waya da sayen data da kuma na cirar kuɗi daga na'urorin ATM da aka fara aiwatarwa a Nijeriya.Shirin zai kuma yi bitar yadda bukukuwan ranar Radiyo ta Duniya suka gudana a Najeriyar da Nijar.

    Mu Zagaya Duniya: 'Yan tawaye ssun yyi shelar kafa gwamnati a Goma

    Play Episode Listen Later Feb 8, 2025 19:42


    A cikin shirin 'Mu zagaya Duniya',  wanda ke kawo bitar mahimman abubuwan da suka wakana a makon da ya gabata, za ku ji cewa:‘Yan tawayen M23 tare da haɗin giwar mayaƙan AFC sun yi shelar kafa gwmnati a birnin Goma, ‘yan kwanaki bayan ƙwace shi da suka yi daga hannun sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyar CongoGwamnatin sojin Nijar ta dakatar da da ayyukan hukumar bayar da agajin gaggawa ta RED Cross a ƙasar

    Wasu daga cikin labarun mako a cikin shirin Mu Zagaya Duniya

    Play Episode Listen Later Feb 1, 2025 19:52


    Daga cikin labarun da shirin ya sake waiwaya a wannan makon, akwai cikar wa'adin ficewar kasshen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar daga cikin ƙungiyar kasashen yammacin Afirka CCOWAS, da kuma abinda ya biyo baya.

    Wasu daga cikin labarun mako a cikin shirin Mu Zagaya Duniya

    Play Episode Listen Later Jan 25, 2025 20:04


    Cikin makon da ya ƙare, Zaratan sojin Najeriya dake fatattakar ‘yan ta'adda a yankin arewa maso yammacin ƙasar, suka samu nasarar kashe kwamandojin riƙaƙken ɗan fashin dajin nan Bello Turji wanda ya zame wa jama'a Batoyi. Jami'in kula da watsa labaran rundunar ta ‘Operation Fansan Yamma' Lafatanar Kanar Abubakar Abdullahi yayi mana ƙarin bayani kan nasarorin da suka samu.

    An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin Isra'Ila da Hamas

    Play Episode Listen Later Jan 18, 2025 19:31


    Wasu daga cikin muhimman labaran da za ku ji a wannan shiri sun ƙunshi nasarar cimma yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Hamas sai kuma wutar dajin Los Angeles wadda ta cinye faɗin yankin da ya zarta girman birnin Washington DC fadar gwamnatin Amurka akwai yadda

    Chadi ta daƙile yunƙurin da ‘yan ta'adda suka yi na afkawa fadar shugaban kasa

    Play Episode Listen Later Jan 11, 2025 19:19


    Daga cikin abubuwan da shirin Mu Zagaya Duniya na wanan makon ya yi waiwaye akai akwai yadda  gobarar daji ce ke cigaba da tafka barna a birnin Los Angeles inda ta raba mutane kusan dubu 200 da muhalansu bayan kone fadin kasa da gine-gine masu yawan gaske.

    Gudunmawar da marigayi Jimmiy Carter ya bai wa Afirka da Gabas ta Tsakiya

    Play Episode Listen Later Jan 4, 2025 20:08


    Daga cikin labarun da shirin wannan makon ya waiwaya akwai yadda ɗaruruwan mutane mazauna ƙauyuka aƙalla 50 suka tsere daga muhallansu saboda barazanar da ƙasurgumin ɗan ta'adda Bello Turji yayi na kai musu farmaki, a ranar 1 ga watan Janairun da ya gabata. Sai kuma waiwayar rawar da tsohon shugaban Amurka marigayi Jimmiy Carter ya taka wajen samar da zaman lafiya a Yankin Gabas ta Tsakiya. 

    sai daga afirka amurka
    Bitar labaran mako: Nijar ta nanata zargin Najeriya kan shirin wargaza mata ƙasa

    Play Episode Listen Later Dec 28, 2024 19:58


    Shirin Mu Zagaya Duniya ta wannan makon tare da Nura Ado Sulaiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi, masamman nanata zargin Najeriya da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi na hada kai da wasu ƙasashen wajen yi musu zagon ƙasa ta fuskar tsaro sun haifar muhawara a tsakanin ‘yan ƙasashen, yayin da su kuma makuntan Najeriyar suka yi watsi da zarge-zargen da suka bayyana a matsayin marasa makama. A Mozambique kuwa fursunonin akalla dubu 6000 ne suka tsere daga gidan Yari ta hanyar amfani da rikicin siyasar da ya barke biyo bayan hukuncin kotun koli kan zaben shugaban ƙasar da jam'iyya mai muli ta lashe.

    Mu Zagaya Duniya:Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin Najeriya na 2025

    Play Episode Listen Later Dec 21, 2024 19:55


    Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleimaza ya mayar da hankali ne kan mayan labarai da suka fi ɗaukar hanhali a makon da muka yi bankwana da shi, masamman halin da ake ciki a Najeriya bayan da shugaban ƙasar ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.

    gaza duniya najeriya faransa
    Shirin mu zagaya: Rundunar sojin Najeriya tace 'yan ta'dda sama da dubu 129 sun ajiye makamasu

    Play Episode Listen Later Dec 14, 2024 19:59


    Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Nura Ado Sulaiman kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata, ciki kuwa har da batun yaddama'aikatar tsaron Najeriya ta bakin hafsan hafsoshin sojin ƙasar Janar Christopher Musa ta sanar da cewa cikin watanni 6 na ƙarshen wannan shekara adadin ƴan ta'adda dubu 129 da 417 tare da iyalansu ne suka ajje makamai bayan miƙa wuya ga mahukuntan ƙasar, lamarin da ke matsayin gagarumar nasara a ƙoƙarin da Najeriya ke yi na kawo ƙarshen barazanar ta'addancin da ya yi mata katutu. 

    Shirin mu zagaya duniya: Hukumar UNESCO, ta karrama hawan Dabar jihar Kano dake Najeriya

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2024 20:02


    Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Nura Ado Sulaiman kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata, ciki kuwa har da batun yadda  Hukumar Kula da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta sanya hawan Dabar jihar Kano dake Najeriya cikin manyan Al'adun Duniya masu dimbin Tarihi.Da kuma sauran rahotanni da suka gabata.Sai a latsa alamar sauti domin samun cikakken shirin.

    Wasu daga cikin muhimman lamuran da suka faru a makon da ya ƙare

    Play Episode Listen Later Nov 23, 2024 19:59


    Masu sauraro Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin sabon shirin Mu Zagaya Duniya, wanda ke waiwayar wasu daga cikin muhimman lamuran da suka faru a makon da ya ƙare.......Akwai tsokaci ko kuma martani daga ɓangarori daban daban  dangane da umarnin kotun duniya ta ICC na bada sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa da kuma ɗaya daga cikin Jagororin  Mayakan Hamas.

    Mu zagaya Duniya

    Play Episode Listen Later Nov 9, 2024 21:41


    Shirin mu zagaya Duniyaya yi dubi da yadda zaben Amurka ya gudana. Karibullah Abdulhamid na Madobi ya gabatar.

    Mu zagaya Duniya: Yadda katsewar lantarki ta kassara kasuwancin a arewacin Najeriya

    Play Episode Listen Later Nov 2, 2024 20:31


    Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Ƙaribullah Abdulhamid Namadobi kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke shirin bankwana da shi, ciki kuwa har da batun matsalar wutar lantarkin da yankin Arewacin Najeriya ya yi fama da shi, sai kuma shirye-shiryen tunƙarar zaɓen Amurka da ke tafe a makon gobe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin wanda ya taɓo ɓangarori daban-daban na duniya kama daga Afrika da nahiyar Turai, Asiya da kuma tashe-tashen hankulan da ake fama da su a sassan duniyar musamman gabas ta tsakiya.

    Yan t'adda daga Burkina Faso na amfani da wani yanki na kasar Ghana a matsayin mafaka

    Play Episode Listen Later Oct 26, 2024 20:20


    Daga cikin labarun da shirin ya waiwaya akwai, korafin da kungiyar direbobin motocin haya a Najeriya ta gabatar da korafi kan tashin hankalin da mabobinta ke fuskanta, inda ta gabatar da kididdigar da ke nuna cewar, akalla direbobi 50 ‘yan ta'adda suka halaka suka kuma suka yi awon gaba da wasu mutanen da dama daga kan hanyar Gusau zuwa Funtua.Al'ummar Jamhuriyar Nijar na alhinin rashin da suka yi na tsohon Fira Ministan kasar Hama Amadou, wanda ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.

    ghana burkina faso daga wani larabar najeriya jamhuriyar nijar
    Bitar wasu daga cikin muhimman labarai na al'amuran da suka wakana a makon da ya ƙare

    Play Episode Listen Later Oct 19, 2024 19:37


    Yayin da ‘Yan Najeriya da dama ke jin jiki kan matsin rayuwar da suka shiga tun bayan janye tallafin man fetur da kuma fara aiwatar da wasu matakai da sabuwar gwamnatin ƙasar  ta yi, Bankin Duniya yayi gargaɗin cewar, matsalar da ake ciki samin taɓi ce, muddin aka kuskura aka janye ko dakatar da manufofin tattalin arziƙin da shugaba Tinubu ke aiwatarwa.

    Bitar Labaran mako:- Najeriya ta sake ƙara farashin man fetur karo na 4 a jere

    Play Episode Listen Later Oct 12, 2024 19:49


    Shirin Mu Zagaya duniya tare da Nura Ado Suleiman kamar ko yaushe ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi, ciki kuwa har da ƙarin farashin man fetur ta Najeriya ta sake yi karo na 4 cikin watanni 16 duk da matsi da tsadar rayuwa da ta addabi al'ummar ƙasar.

    Kisan shugaban Hezbollah ya janyo wa Isra'ila ɗimbim hare-hare daga Iran

    Play Episode Listen Later Oct 5, 2024 19:59


    Daga cikin  Labarun da suka fi ɗaukar hankali a makon da ya ƙare akwai jerin makamai masu linzamin da Iran ta kai wa Isra'ila hari da su, a yayin da ita kuma Isra'ilar ta karkatar da hare-haren da take kai wa a Gaza zuwa Kudancin Lebanon, h da zummar murkushe mayakan Hezbolla A Najeriya kuwa ɗimbin Iyallai ne suka shiga alhinin rashin da suka yi, biyo bayan nuutsewar da wani jirgin ruwa yayi ɗauki da fasinjoji sama da 300 da ke ƙoƙarin tsallaka kogin Kwara domin zuwa taron Maulidi.

    Bassirou Diomaye ya caccaki kwamitin tsaron majalisar Dinkin Duniya

    Play Episode Listen Later Sep 28, 2024 20:00


    A babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya kuwa, shugaban Senegal ne ya ɓare kwamitin tsaron majalisar, a bisa yadda yake gaza ɗaukar matakan warware matsalolin tsaron da ke haddasa hasarar rayukan da ɗimbin duniya a yankin Sahel.

    senegal sahel duniya majalisar dinkin duniya majalisar
    Tsuguni bata kare ba tsakanin kamfanin Dangote da kamfanin NNPC a Najeriya

    Play Episode Listen Later Sep 21, 2024 20:40


    Har yanzu tsuguni bata kare ba tsakanin kamfanin Dangote da kamfanin NNPC dangane da gabatar da man fetur da yake tacewa a cikin gida. A cikin wannan shirin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Kasum Kurfi, masanin tattalin arziki da kuma Abdulkarim Ibrahim dangane da kalubale da kuma mafita dangane da wannan al'amari.

    bata dangote nnpc najeriya bashir ibrahim idris
    Halin da aka shiga bayan iftila'in ambaliyar ruwa a Maiduguri

    Play Episode Listen Later Sep 14, 2024 20:35


    Daga cikin labarun da shirin makon nan ya waiwaya akwai iftila'in ambaliyar ruwan da ya afka wa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno da kuma halin da aka shiga bayan aukuwar lamarin.A fannin tsaro kuwa, dakarun sojin Najeriya ne suka samu nasarar halaka ɗaya daga cikin manyan jagororin ‘yan ta'addan da suka addabi al'ummar yankin arewa maso yammacin ƙasar.

    Abdulaziz Abdulaziz ''Gwamnatin shugaba Tinubu na iya bakin kokarin''

    Play Episode Listen Later Sep 7, 2024 20:28


    Matsalar tsaro na ci gaba da ta'azzara a yankin arewa maso yammacin Najeriya, musamman a yan makwannin da suka gabata, inda 'yan bindiga ke kai hare hare suna kashewa ba tare da kaukauatawa ba. Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tace tana iya bakin kokarin ta amma kuma jama'a na cewar har yanzu da sauran aiki.

    Bitar labaran mako: Yadda sabon farashin man fetir ya shafi ƴan Najeriya

    Play Episode Listen Later Sep 7, 2024 20:31


    Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Rukayya Abba Kabara ya taɓo halin da aka shiga a Najeriya bayan da mahukunta suka kara farashin man fetur, sai kuma taron Afirka da China da kuma sabon fraministan Faransa.

    china mako bitar shafi duniya yadda najeriya afirka faransa
    Yadda ƙasashen Najeriya da Nijar suka dawo da alakarsu

    Play Episode Listen Later Sep 1, 2024 19:59


    Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya taɓo batun sake dawo da alaka da aka yi tsakanin Najeriya da Nijar, da yadda aka samu karuwan basukan da kasashen Afrika ke ciwowa daga China da kuma batun neman sanyawa wasu ministocin Isra'ila takunkumi da ƙungiyar tarayyar Turai ta nema mambobinta su yi.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh....

    Bitar labaran mako: Yadda ambaliyar ruwa ke ci gaba da ɓarna a arewacin Najeriya

    Play Episode Listen Later Aug 17, 2024 20:03


    Shirin Mu zagaya Duniya da ke bitar labaran mako tare da Nura Ado Suleiman ya taɓo yadda ambaliyar ruwa ke ci gaba da ɓarna a sassan arewacin Najeriya a wani yanayi da hukumar NEMA ke gargaɗi kan yiwuwar ambaliyar ta shafi mutane fiye da miliyan 3 a jihar Kano kaɗai.

    Shirin ya duba manyan labaran da suka faru a wannan mako

    Play Episode Listen Later Aug 10, 2024 19:56


    Shirin mu zagaya duniya na wannan mako ya duba manyan labaran da suka faru a wannan mako ciki kuwa har da addin mutanen da hare-haren ta'addanci suna kashe a cikin shekaru biyar a Najeriya Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman

    Zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa ta rikiɗe zuwa tarzoma a sassan Najeriya

    Play Episode Listen Later Aug 3, 2024 20:00


    Mu Zagaya Duniya, shiri ne da ya saba tacewa gami da zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu tare da Nura Ado Suleiman. Shirin wannan makon ya fi mayar da hankali ne wajen bitar yadda zanga-zanga kan tsadar rayuwa da kuma neman shugabanci nagari ta gudana a sassan Najeriya, inda a wasu sassa zanga-zangar ta lumana ta rikiɗe zuwa tashin hankalin da ya kai ga hasarar rayuka da kuma ɗimbin dukiya.'Mu Zagaya Duniya' zai kuma leka Mali, inda dakarun kasar da dama gami da sojojin hayar Rasha na Kamfanin Wagner suka rasa rayukansu, bayan ƙazamin artabun da suka yi da mayakan Abzinawan da suka samu taimakon masu tayar da kayar bayan dake ikirarin jihadi.

    Wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare daga Rfi

    Play Episode Listen Later Jul 20, 2024 20:07


    A ranar Alhamis da ta gabata, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, inda yayi alƙawarin sake nazari kan yiwuwar wani ƙarin a duk bayan shekaru uku, a cikin shirin mu Zagaya Duniya ,Nura Ado Suleiman ya  zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu.

    suka daga wasu najeriya cikin alhamis
    Najeriya za ta bayar da damar shigar da kayan abinci ba tare da haraji ba

    Play Episode Listen Later Jul 13, 2024 20:00


    Shirin duniya kamar yadda aka saba na duba manyan labaran da suka faru a sassan duniya A cikin shirin zaku ji cewa..............Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin janye biyan kudaden haraji kan wasu muhimman kayayyakin abinci da ta dage haramcin shigar da su kasar, don saƙaƙawa jama'a raɗaɗin tsadar raywar da suke ciki.Matakin sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar, Mali da kuma Burkina Faso na tabbatar da ballaewarsu daga ECOWAS ya tayar da  hankalin kungiyar kasashen ta yammacin Afirka, a yayin da kwararru ke cigaba da bajakolin ra'ayoyinsu kan matakin.A Kenya kuwa, shugaban ƙasar William Ruto ne ya kori rankatakaf din ministocinsa sai fa ƙwaya biyu rak da ya bari, ‘yan kwanaki bayan zanga-zanga kan tsadar rayuwa da dubban matsasan kasar suka gudanar.Danna alamar saurare don jin gundarin shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

    Tattaunawa kan wasu daga cikin tarin matsaloli da suka hadabi Najeriya a fanoni daban-daban

    Play Episode Listen Later Jul 6, 2024 18:03


    A cikin shirin Duniyarmu a yau,Michael Kuduson ya tattauna Mustapha Salisu Fernandez dan siyasa kuma mai sharhi kan lamuran yau da na kullum a Najeriya.

    suka daga tarin wasu najeriya cikin
    Rikicin masarautar Kano ya ɗauki sabon salo

    Play Episode Listen Later Jun 22, 2024 19:43


    Wasu daga cikin labarun da shirin makon nan ya waiwaya sun haɗa da yadda rikicin masarautar Kano ya ɗauki sabon Salo,, bayan da Gwamnatin jihar ta bada umarnin rushe fadar Sarki dake unguwar Nasarawa, inda Aminu Ado Bayero ya ke, matakin da ya zo sa'o'i kaɗan bayan da babbar Kotun Tarayya da ke jihar ta yanke hukuncin rashin amincewa da sabuwar dokar masarautar

    Gwamnatin sojin Nijar ta kwaɓe wa Bazoum rigar kariya

    Play Episode Listen Later Jun 15, 2024 18:59


    Daga cikin Labarun da shirin ya waiwaya a wannan mako akwai matakin mahukuntan sojin Jamhuriyar Nijar na cirewa hamabararren shugaban ƙasar Bazoum Muhd rigar kariyar, abinda ya bude kofar samun damar gurfanar da shi gaban kotu.A Najeriya kuwa  Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zai ci gaba da yi wa tattalin arzikin ƙasar garambawul duk kuwa da yadda hakan ke ta'azzara  wahlhalun da al'ummar kasar ke sha. Sai Kuma Senegal inda shugaban kasar Basirou Diomaye Faye ya sassauta farashin kayayyakin masarufi don saukaka wa jama'a tsadar rayuwar da suke ciki.Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ƙaruwar mutanen da rikici ke tilastawa barin matsugunansu a sassan duniya, adadin da zuwa yanzu ya kai mutum miliyan 120.

    duniya daga bazoum kariya nijar najeriya jamhuriyar nijar majalisar

    Claim Mu Zagaya Duniya

    In order to claim this podcast we'll send an email to with a verification link. Simply click the link and you will be able to edit tags, request a refresh, and other features to take control of your podcast page!

    Claim Cancel