A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban…

Da sanyin safiyar yau Juma'a aka wayi gari da sanarwar gwamnatin Najeriya da ke tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankunan ƙananan hukumomin Tambuwal da Tangaza, da ke jihar Sokoto a yankin arewa maso yammacin ƙasar. Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar, ya ce Amurka ta kai hare-haren ne tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasar, a wani ɓangare na ƙawancen da suka ƙulla da zummar murƙushe ta'addanci. Dangane da wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Yahuza Gesto masanin tsaro da ke tarayyar Najeriya. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawar...

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinibu ya ƙaddamar da ababen hawa na sufuri masu amfani da lantarki guda dubu 3 da 620 da gwamnatin jihar Borno ta tanadar domin sauƙaƙa sufuri a tsakanin al'ummarta. Motocin sun haɗa ne da Kekuna dubu 3 da babura masu ƙafa 3 ko kuma adaidaita sahu guda 500 sai kuma ƙanana da manyan Motocin safa ko kuma bas bas masu ɗaukar mutum 20 da 42 guda 100, kari ga wasu motoci 650 masu amfani da lantarki da gwamnati ta samar don sufuri. Dangane da wanna ne Faruk Muhammad Yabo ya tattauna da Dauda Iliya mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Borno a fannin watsa labarai inda ya fara da tambayarsa yadda ababen hawan suke da kuma yawansu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar...

Majalisar wakilan Najeriya ta gudanar da wasu sauye-sauye ga dokar zaɓen ƙasar yayin zaman da ta yi a jiya Alhamis. Kuma daga cikin batutuwan da suka fi ɗaukar hankali akwai ƙara yawan kuɗaɗen da doka ta ƙayyade ɗan takara zai iya kashewa a yaƙin neman zaɓe, da kuma tilasta amfani da na'urorin tantance masu kaɗa ƙuri'a, gami da watsa sakamakon zaɓe kai tsaye. Sauyin dai na nufin daga yanzu masu neman shugabancin ƙasa na iya kashe Naira biliyan 10, saɓanin Naira biliyan 5, yayin da aka ƙara kasafin ‘yan takarar gwamna daga Naira Biliyan 1 zuwa biliyan 3. Domin jin yadda masana doka ke kallon wannan mataki, Nura Ado Suleiman ya tuntuɓi Barista Al-Zubair Abubakar da ke Najeriya. Latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana...

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Engr Faruk Ahmed da Aliko Dangote ya zarga da hana ruwa gudu wajen harkokin kula da kasuwancin mai da kuma bada lasisi ta NMDPRA, tare da shugaban hukumar NUPRC. Fadar shugaban Najeriya ta ce jami'an biyu sun sauka daga mukaman su ne bisa dalilai na ƙashin kan su. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ibrahim Garba Wala kan lamarin. Ku latsa alamar sauti don jin yadda tattaunawarsu ta gudana...

A farkon wannan Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar wa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ƙarfin ikon kafa dokoar ta ɓaci a kowace jiha da ke faɗin ƙasar, idan buƙatar hakan ta taso, domin tabbatar da zaman lafiya. Yayin yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatocin jihohin da ke ƙarƙashin jam'iyyar PDP suka shigar, Kotun ta ce shugaban ƙasa na da ikon dakatarwar wucin gadi ga zaɓaɓɓun shugabannin jihar da dokar ta ɓacin ta shafa. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Ibrahim Bello Rigachikun da ke Najeriya.

Ƙasashen AES da suka hada da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso, sun ƙalubalanci Najeriya sakamakon saukar gaggawar da jirgin sojin ta da ya yi a Burkina. Waɗannan ƙasashe na zargin Najeriya da keta haddin sararin samaniyar yankin su. Domin tattauna wannan batu da kuma yunkurin juyin mulkin da ya gudana a Benin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Amb Abubakar Cika, tsohon Jakadan Najeriya a Iran. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana...........

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjinawa sojojin ƙasar saboda rawar da suka taka wajen murkushe yunkurin juyin mulkin da aka samu a Jamhuriyar Benin. Tinubu ya ce hare haren sojin sama da kuma tura sojojin ƙasa cikin ƙasar, sun bada gagarumar gudumawa wajen kawar da sojojin da suka sanar da kwace ikon. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu................

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da shirin dawo da illahirin makarantun na tsangaya guda 157 da ke sassan ƙasar zuwa ƙarƙashin cikakkiyar kulawarta ma'aikatar ilmin ƙasar. Ƙarƙashin sabon tsarin, duknannin ɗaliban da ke cikin irin waɗannan makarantu ba za a kira su da suna jahilai ba. Khamis Saleh ya zanta da Imam Bukhari Maraban Jos, shugaban gamayyar makarantun tsangaya a jihar Kaduna, wanda kuma ke da masaniya dangane da tsarin, ga kuma zantawarsu.

Sabon ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa mai ritaya ya sha alwashin murƙushe barazanar ƴan ta'adda tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin jama'ar Najeriya, inda ya ce nan gaba kaɗan jama'a za su ga gagarumin sauyi. Janar Musa wanda ya yi rantsuwar kama aiki a cikin makon nan, ya sanar da wasu daga cikin tsare-tsaren da zai yi amfani da su a sabon salon yaƙi da ta'addancin da zai faro, ciki har da mayar da ilahirin sojoji bakin daga don fatattakar ɓatagari da kuma hana biyan ƴan ta'addan fansa dama kawo ƙarshen sulhu dasu. Dangane da wannan ne Azima Bashir Aminu ta tattaunawa da masanin tsaro Squadron Leader Aminu Bala Sokoto. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

Babban Bankin Najeriya ya sanar da cire shingen kuɗaɗen da jama'a ke ajiyewa a bankuna da kuma ƙara yawan kuɗin da ake ɗauka a bankin. Bankin ya ce daga yanzu an ƙara yawan kuɗin da mutum ka iya cirewa daga naira 100,000 zuwa naira 500,000, yayin da bankin ya ci gaba da riƙe naira N100,000 a matsayin kuɗin da mutum guda ka iya cirewa a ATM a rana guda. Domin duba tasirin wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dakta Isa Abdullahi, na Jami'ar Kashere, da ke jihar Gombe a Najeriya. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da sunan Janar Christopher Musa mai ritaya ga majalisar Dattawa domin amincewar ta ya zama ministan tsaro. Christopher Musa ya yi aiki a matsayin babban hafsan tsaron Najeriya daga ranar 23 ga watan Yunin 2023 zuwa 30 ga watan Octoban 2025, lokacin da shugaban ƙasar Bola Ahmad Tinubu ya yi masa ritaya. Idan majalisa ta amince, Janar Musa zai maye gurbin Badaru Abubakar da ya yi murabus a ranar Litinin. Bayanai sun nuna cewa fannonin da Musa ya fi ƙwarewa a kai shine fatattarkar ƴan ta'adda, da dubarun yaƙi, kasancewar ya yi aiki a matsayin jagoran rundunar sojojin Najeriya da ke kula da tsaron iyakokin Najeriya ta arewa maso gabashi da kuma yankin tafkin Chadi, haka nan ya kuma yi aiki a matsayin guda daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Sierra Leone, da kuma wasu ayyukan a Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya.. Domin sanin tasirin wannan nadin da kuma kalubalen dake gaban Janar Musa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon kakakin rundunar sojin kasa ta Najeria, Janar Sani Usman Kukasheka mai ritaya. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

Ƴan Najeriya na ci gaba da neman bayani a kan yadda wasu kuɗaɗen da aka tara, da yawan su ya kai dala miliyan 30 domin samar da tsaro a makarantu suka shiga, sakamakon sake dawowar satar ɗalibai a yankin arewacin ƙasar. A ƙarƙashin wannan shirin da ya fara a shekarar 2014, kasashe da dama suka tallafawa Najeriya, cikin su har da ƙasar Norway da ta bada dala miliyan guda, da wata dala miliyan guda daga Bankin Raya ƙasashen Afirka na AfDB, sai kuma Fam miliyan guda daga gwamnatin Birtaniya. Gwamnatin Switzerland ta bada taimakon dala miliyan takwas, yayin da Amurka ta bada dala miliyan biyu, sai kuma Qatar da ta bada dala miliyan biyu, yayin da ƴan kasuwan Najeriya su kuma suka bada taimakon dala miliyan 10. Ganin yadda aka kasa samar da tsaron a makarantu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abubakar sadiq Umar Gombe. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

Kamar dai kowace shekara, 1 ga watan Disamba ita ce ranar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta keɓe don yaƙi da cuta mai karya garkuwar jikin ɗan Adam wato HIV ko kuma SIDA. Bikin na bana ya zo ne a cikin wani yanayi da shugaba Donald Trump ya katse tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashe masu tasowa ciki har da na ɓangaren yaƙi da wannan cuta. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Nasir Sani Gwarzo ƙwararren likitan yaƙi da annoba a Najeriya, wanda ya fara da bayyana halin da ake ciki game da yaƙi da HIV a ƙasar. Ga zantawarsu.

A tsakiyar wannan mako, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shelanta kafa dokar ta ɓaci kan sha'anin tsaro a faɗin ƙasar, matakin da a ƙarƙashi ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin jami'an Ƴansanda dubu 50,000 domin murƙushe matsalolin tsaron da ke ta'azzara. Kan wannan, da wasu ƙarin matakai da ake shirin ɗauka a ƙarƙashin dokar ta ɓacin kan tsaro Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kanal Muhd Sani Makiga mai ritaya, masanin tsaro a Tarayyar Najeriyar. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...

A jiya ne sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Umaro Sissiko Embalo, sakamakon rikicin zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a ƙarshen mako, a daidai lokacin da ake shirin gabatar da sakamako yau Alhamis. Shugaban da madugun yan adawa duk sun yi iƙrarin nasara, a kasar da ta yi ƙaurin suna wajen juyin mulki. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir dangane da juyin mulkin, wanda shi ne na biyar a kasashen Afirka ta Yamma, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai.

Gwamnatocin wasu jihohin dake arewacin Najeriya sun sanar da matakan rufe makarantun firamare da sakandare, wasu ma harda jami'oi, domin kaucewa matsalar garkuwa da daliban da ake samu, wanda ya kara ta'azzara a kasar. Domin duba tasirin matakin da kuma halin da yankin ya samu kan sa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin ɗaukar sabbin ƴansanda dubu 30 da kuma janye masu gadin manyan mutane ba bisa ƙa'ida ba. Domin sanin tasirin wannan mataki da kuma yadda zai taimaka wajen inganta tsaro a ƙasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon mataimakin Sifeto Janar na Ƴansandan Najeriya Malam Ahmad Abdurrahaman. Ku latsa alamar sauti donjin yadda zantawarsu ta gudana.............

A Najeriya, ƴan bindiga masu gurkuwa da mutane domin ƙarbar ƙudin fansa, sun tsanata kai hare-hare makarantu tare da sace ɗaibai a baya-bayan nan, lamarin da ya sa gwamnatoci a wasu jihohin ƙasar suka ɗauki matakin rufe makarantu a matakai daban-daban. Hakan ya biyo bayan sace dalibai a jihohin Kebbi da Neja a makon da ya gabata, lamarin da ya sake haifar da fargaba kan tsaron dalibai da makarantu da kuma makomar ilimi a yankin arewacin Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunar Khamis Saleh da tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Sani Usaman Kukasheƙa mai ritaya..........

Ƙungiyar Amnesty International ta zargi hukumomin ƙasar Chadi da gazawa wajen ɗaukar matakan kare mutanen da ake cin zarafin su, sakamakon rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙasar, yayin da ta ce tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, an kashe mutane 98, baya ga jikkata sama da 100 da kuma tilastawa ɗaruruwan iyalai barin muhallin su. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Isa Sanusi Daraktan kungiyar a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai.

Matsalolin tsaro na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Tarayyar Najeriya, bayan da a baya-bayan nan aka ga yadda ƴan bindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar suka sace ɗalibai aƙalla 25 a jihar Kebbi, yayinda ana tsaka da jimamin wannan kuma aka sake ganin yadda suka kai hari wata majami'ar jihar Kwara tare da kashe mutane 2 da kuma sace wasu da dama. Wannan na zuwa ne kwanaki bayan dakarun Sojin Najeriyar sun sanar da samun gagarumar nasara a kan ƴan ta'adda musamman bayan barazanar Trump ta ɗaukar matakin Soji kan ƙasar ta yammacin Afrika. Dangane da wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin tsaro a Najeriyar Dr Yahuza Getso........

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya buƙaci rundunonin sojin Najeriya na sama da na ƙasa da kuma na ruwa, da su ƙaddamar da gagarumin farmaki kan sansanonin ƴan ta'addan da ke zagayen Yankin Tafkin Chadi, domin murƙushe matsalar tsaron da ta addabi Yankin. Kiran da gwamnan na Borno ya yi a farkon makon nan, na zuwa ne a yayin da matsalolin tsaro ke sake ta'azzara a sassan arewacin ƙasar, ciki har da satar ɗaliban da aka yi jihar Kebbi. Domin jin yadda masana tsaro ke kallon wannan lamari Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kanal Muhammad Sani Ibrahim Makiga mai ritaya, masanin tsaro a Najeriya.

Fatan Najeriya na samun gurbi a gasar cin kofin duniyar da za'a yi a shekara mai zuwa ya gushe, sakamakon rashin nasarar da ƙungiyar Super Eagles ta yi a hannun ƙasar Congo. Wannan shi ne karo na biyu a jere da Najeriya ba zata je gasar ta dunitya ba, bayan gaza zuwa Qatar shekaru 4 da suka gabata, kafin wannan karo. Bashir Ibrahim Idris, ya tattauna da tsohon sakatare janar na Hukumar Kwallon Kafa Najeriya, Hon Sani Ahmad Toro game da wannan koma baya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta gudanar da babban taronta na ƙasa a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke yankin Kudu maso yammacin ƙasar, inda ta zaɓi sabbin shugabanninta a matakin ƙasa. Jam'iyyar ta ɗauki tsauraran matakai yayin taron mai cike da cece-kuce, ciki harda korar wasu manyan jiga-jiganta da suka haɗa da ministan Abuja Nyesom Wike da wasu ƙarin mutum 10. A tataunawarsa da Ahmad Abba, gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP, Sanata Abdulkadir Bala Mohammad, ya ce umurnin kotu suka bi wajen gudanar da wannan taro kuma sun samu nasara. Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawar tasu............

Shugaban kwamitin shirya babban taron Jam'iyyar PDP na ƙasa a birnin Ibadan dake Najeriya, Umar Fintiri, wanda shi ne Gwamnan Adamawa, ya ce babu abinda zai hana su gudanar da taron da suka shirya gobe asabar. Fintiri ya bayyana haka ne bayan wani gagarumin taron da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da suka gudanar yau a birnin Abuja. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Hamisu Mu'azu Shira, ɗaya daga cikin jiga jigan jam'iyyar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.

Kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya ta tafka hasarar Naira Tiriliyan 4 da Biliyan 600 a ranar Talata, sakamakon matakin da masu linƙaya cikin kasuwar suka ɗauka na sayar da hannayen jarinsu cikin gaggawa saboda dalilai da dama ciki har da tsoron faɗuwa. Hasarar ta fiye da Naira Tiriliyan 4, ita ce mafi muni da kasuwar hannayen jarin Najeriyar ta fuskanta cikin shekaru 10. Domin jin dalilan da suka janyo aukuwar hakan da sauran lamura masu alaƙa, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau masanin tattalin arziƙi a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar...

Dai dai lokacin da wasu jita-jita ke nuna cewa mahukuntan Najeriya kan biya kuɗaɗen fansa ga ƴan bindiga gabanin kuɓutar da ɗimbin mutanen da suke garkuwa dasu, ko kuma ga waɗanda suka aje makamansu a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi iƙirarin cewa bai taɓa biyan ko sisin kwabo ga ƴan bindiga ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Gwamna Uba Sani da Khamis Saleh................

An bude traon Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi da ake kira COP 30 a Brazil inda masana muhalli da sauyin yanayi daga kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare muhallin ke halarta a kasar Brazil. Za'a kwashe makwanni biyu ana gudanar da wannan taro wanda zai mayar da hankali a kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a kan wannan matsala. Dakta Abubakar Ibrahim, Malami kuma mai bincike a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ya yi tsokaci a kan matsalar musamman ganin irin illar da take yi a yankin arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawarsa da Bashir Ibrahim Idris.

Gwamnatin Jihar Yobe dake Najeriya tace za ta ƙara gina manya asibitoci a kananan Hukumomi 3 wadda suka hada da Gashua, Potiskum da kuma Nguru, baya ga gina wani wannan sabon asibitin kula da masu fama da cutar ƙoda a Garin Gashua inda cutar tafi ƙamari a jihar. Haka kuma gwamnatin ta ce zata gina wasu makarantu na musamman a kowacce mazaɓa 178 da ake da su a jihar domin ƙara inganta karatun tun daga tushe. Gwamna Jihar, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da wakilinmu Bilyaminu Yusuf. Latsa alamar sauti don jin tattaunawarsu....

Yayin da ake ci gaba da lalubo hanyar warware matsalar barazanar Donald Trump na kai hari Najeriya, wasu masana na bayyana cewar ta hanyar diflomasiya kawai za a iya warware wannan dambarwa. Barr Abdullahi Ibrahim Jalo na ɗaya daga cikin su. Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris ta gudana..............

Barazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan Najeriya na ci gaba da janyo cecekuce a ƙasar da kuma ƙetare, kuma tuni wannan batu ya fara tasiri a musamman kan tattalin arzikin ƙasar. Faduwar hannayen jarin Najeriya da aka gani a wannan mako, ta janyo hankalin mutane yayin da ake ganin kai tsaye yana da alaƙa da barzanar ta Trump. Rukayya Abba Kabara ta tattauna da kwararre kan harkokin tattalin arziki a Najeriya, Alhaji Shu'aibu Mikati kan wannan batu, ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.

Yayin da hukumomin Najeriya suka yi watsi da barazanar shugaban Amurka na kai wa ƙasar hari saboda zargin kashe Kiristoci, ƴan kasar da dama na ci gaba da bayyana ra'ayi a kan matsayin na shugaba Donald Trump. Daga cikin waɗanda suka bayyana ra'ayin su a kan wannan barazana har da tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran, Ambasada Abubakar Cika, kamar yadda za ku ji a tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris.

A Najeriya, babban abin da ya fi ci wa al'ummar yankin Arewacin ƙasar tuwo a ƙwarya ita ce matsalar rashin tsaro, inda hare-haren ƴanbindiga ke ci gaba da haddasa asarar rayukan jama'a, da gurgunta harkar noma da kuma kasuwanci a yankin baki-ɗayansa. Dangane da haka ne Bashir Ibrahim Idris ya zanta da ɗaya daga cikin dattawan yankin Alhaji Shehu Ashaka, ga kuma yadda zantawarsu ta kasance. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

Har yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar Kamaru sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka bayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya samu nasara. Shugaban 'yan adawa Issa Tchiroma Bakary da ya zo na biyu ya ƙi amincewa da sakamakon, inda ya buƙaci jama'a da su sake fitowa zanga zanga a ranakun litinin da Talata da kuma Laraba na makon gobe, yayin da a ɓangare ɗaya gwamnati ke barazanar ladabtar da duk wanda ya saɓa dokokin ƙasar, ciki harda shi Isa Tchiroma. Domin tattauna halin da ake ciki a ƙasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammadu Sani. Ku alatsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...

Yayin da ake shirin fara taron sauyin yanayi na duniya da ake kira COP30 a Brazil, a ranar 10 ga watan gobe, ƙungiyar OXFAM ta fitar da sanarwa inda take sake bayyana damuwa a kan rashin ɗaukar kwararan matakai wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla shekaru 10 da suka gabata a birnin Paris. Game da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da darakatar ƙungiyar ta OXFAM a Nahiyar Afrika Malama Fatima Nzi Hassan. Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.

Ga alama yajejeniyar tsagaita wutar da Isra'ila ta ƙulla tsakaninta da Hamas, wadda Amurka ta tsara ta kama hanyar rugujewa, sakamakon umarnin da Firaminista Benjamin netanyahu ya bayar na ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza. Wannan ya biyo bayan abinda ya kira ƙin bada gawarwakin sauran Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su. Domin tattauna wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris, ya tuntuɓi Dakta Abdulhakin Garba Funtua, mai sharhi a kan harkokin Gabas ta Tsakiya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.........................

A baya-bayan nan ne, gwamnatin Najeriya ta gudanar wani garambawul ga sha'anin tsaron ƙasar, ciki kuwa har da matakin da shugaba Bola Tinubu ya yi na sauya kusan ilahirin manyan hafsoshin tsaron ƙasar, lamarin da ya janyo cece-kuce. Ra'ayoyi sun mabanbanta game da wannan mataki na garambawul ga ɓangaren na tsaro a Najeriya, inda wasu ke ganin batu ne da ya dace lura da yadda matsalolin tsaro ke ci gaba da ta'azzara, yayinda wasu ke alaƙanta batun da siyasa. A gefe guda, Najeriyar ta gamu da jita-jitar yunƙurin juyin mulki, wanda kuma kwanaki bayan tsanantar jita-jitar shugaban ya gudanar da wannan garambawul, Dangane da hakan ne kuma Michael Kuduson ya tattaunawa da masanin tsaro a ƙasar Muhammad Sani Makigal. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....

Katafaren kamfanin Dangote, ya sanar da shirin faɗaɗa matatar sa mai samar da tacaccen gangar mai 650,000 zuwa miliyan guda da 400,000 a kowacce rana. Shugaban rukunin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya ce za'a kwashe shekaru uku ana aikin faɗaɗa matatar wadda ya ce za ta zama mafi girma a duniya. Dangane da wannan ci gaba ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da babbar manajar rukunonin kamfanin, Fatima Aliko Dangote. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.....

A Cote d'Ivoire, a jajiberin zaɓen shugaban ƙasar, hukumomi sun ɗauki matakan da suka dace na ganin an gudanar da zaɓen ba tare da an fuskanci wata matsala ba. To domin jin ko a ina aka kwana ,Abdoulaye Issa ya tattauna da Usman Ture,wani ɗan ƙasar ta Cote d'ivoire da ya karɓi katinsa na zaɓe. Latsa alamar sauti domin jin yadda tattaunawarsu ta gudana...

Sannu a hankali ƙananan bankuna na bada gagarumar gudumawa wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya, la'akari da yadda jama'a ke komawa hada hada da su maimakon manyan bankunan da aka sani a baya. Ko a jiya Moniepoint ya sanar da samun jarin Dala miliyan 200 domin inganta harkokin sa. Domin sanin tasirin wadannan ƙananan bankunan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Isa Abdullahi na Jami'ar Kashere. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..................

An buɗe taron baje kolin kafafen yaɗa labarai na Afrika da ake kira AFRICAST karo 14 a birnin Lagos da ke Najeriya, inda masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai daga nahiyar da kuma sassan duniya ke halarta.Domin ƙara inganta ayyukan yaɗa labarai, wasu daga cikin mahalarta wannan taro na ganin cewa ya zama wajibi a samar da dokokin da za su sa-ido kan ayyukan kafafen sada zumunta da kuma sauran hanyoyin yaɗa labarai ta yanar gizo. Sanusi Bature Dawakin Tofa, shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Yusuf, kuma wanda ya wakilce shi a taron, a zantawarsa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, ya ce lalle akwai buƙatar samar da gyara a wannan fanni. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar...................

Gwamnatocin jihohin Katsina da Kano da kuma Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya sun kulla haɗakar inganta wutar lantarkin ga jihohin uku. Gwamnonin Kano, Jiagwa da Katsina sun shiga yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa wutar lantarki a jihohin uku da ke arawacin Najeriya, tare da zuba hannun jari a kamfanonin Future Energies Africa (FEA) da na rarraba wutar lantarki a jihohin uku wato KEDCO. Hakan ya fito fili ne bayan wani taro da gwamnonin jihohin uku da suka hada da Malam Umar Dikko Radda da Abba Kabir Yusuf da kuma Umar Namadi suka gudanar a ƙasar Morocco inda suka tattauna da kamfanin Future Energies Africa da Kedco da sauran masu ruwa da tsaki a harkar makamashi. A zantawarsa da RFI Hausa, Gwamnan jihar Katsina Malama Dikko Rada ya ce suna son fito da haryar yin haɗaka a fannin wutar lantarki tsakanin jihohin makwabtan juna ta hanyar zuba jari naira biliyan 50 domin samar da wutar da yankin ke bukata. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar................

Babbar Cibiyar rundinonin sojin Najeriya ta yi watsi da rahotannin dake cewa an yi yunkurin juyin mulkin a kasar, abinda ya kai ga kama wasu hafsoshi guda 16. Daraktan yada labaran Cibiyar janar Tukur Gusau ya shaidawa Bashir Ibrahim Idris a zantawarsu cewar, sojojin da aka kama ana tuhumar su ne da laifin saba dokoki na soji amma ba juyin mulki ba. Ga yadda zantawarsu ta gudana.

Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta shirya wani taro a Lagos domin horar da matasa a kan yadda za su kare haƙƙoƙin jama'a a yankunan da suka fito.Taron wanda zai gudana a shiyoyin Najeriya guda 6 ya ƙunshi matasa daga shiyar kudu maso yammacin kasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Malam Isa Sanusi. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.............

Jiga-jigan Jam'iyyun adawa a Najeriya da suka haɗa da gwamnoni da ƴan majalisun tarayya da na jihohi na rige-rigen komawa jam'iyya mai mulki ta APC. Na baya-bayan nan da ya koma jam'iyyar ta APC shi ne gwamnan jihar Bayelsa yayinda na Taraba ke kan hanya, kan hakan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa Ambasada Ibrahim Kazaure akan wannan lamari ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.......

Kwamitin Majalisun Najeriya da ke yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska ya bada shawarar sake dokar zaɓe ta yadda za a dinga gudanar da zaɓuɓɓuka a watan Nuwamba domin bada damar kammala shari'u kafin lokacin rantsar da waɗanda suka samu nasara. Domin sanin tasirin wannan shiri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Baƙo mai sharhin kan harkokin siyasa ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar....

Malaman Jami'o'in Najeriya sun kare matakin ƙungiyarsu na tsunduma yajin aikin gargaɗi na makwanni 2, inda suka zargi gwamnati da yaradara. Wannan kuwa na zuwa ne duk da gargaɗin da gwamnatin ƙasar ta yi na amfani da dokar nan ta babu aiki babu biya duk malamin da ya shiga yajin aiki na ASUU. Shugaban ƙungiyar Malaman reshen Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Haruna Jibril ya yiwa Bashir Ibrahim Idris ƙarin bayani a tattaunawar da suka yi kamar haka... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....

Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi dangane da wasu daga cikin mutanen da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yiwa afuwa a makon jiya, inda suke bayyana rashin dacewar afuwar da akan wasu waɗanda suka aikata manya laifuka. Daga cikin waɗanda ake muhawara a kan su akwai masu kisan kai da masu safarar ƙwayoyi da kuma masu safarar makamai. Domin tattauna wannan batu Bashir Ibrahim Idris, ya zanta da Ibrahim Garba Wala, guda cikin masu fafutukar kare haƙƙin Bil'Adama a Najeriya.......... Latsa alamar sauti domin sauraron zantawarsu................

A ƙarshen wannan mako ne jama'ar ƙasar Kamaru za su kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, inda ƴan takara 10 ke neman shugabanci, cikin su harda shugaba Paul Biya dake neman wa'adi na 8. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammad Sani game da zaɓen. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawarsu...

Rundunar Ƴansandan Najeriya ta sanar da karɓar umarnin kotu na dakatar da kama motocin dake ɗauke da bakin gilashi, inda ta umarci jami'an ta da su dakatar da kamen har zuwa lokacin da za'a kammala shari'ar. Wannan ya biyo bayan rugawa kotu da wasu lauyoyi suka yi domin hana aiwatar da dokar da suka ce za ta take haƙƙin Bil Adama. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barr Suleiman Muhammed, lauya mai zaman kansa. Ku latsa alamar sauti domin jin tattaunawarsu...

Shugaban Hukumar zaɓen Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya kawo ƙarshen aikin sa a INEC, inda ya miƙa ragamar tafiyar da hukumar ga May Agbamuche.Yayin miƙa ragamar aikin, Yakubu ya roƙi kwamishinonin hukumar da su bai wa Agbamuche haɗin kai wajen gudanar da ayyukan ta na riƙo zuwa lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai naɗa wanda zai maye gurbinsa.Tuni dai tambayoyi suka yawaita game da wanda zai maye gurbin Yabubu a matsayin shugaban hukumar ta INEC, dangane da wannan batu Bashir Ibrahim Idris ya tattaunawa da Malam Ibrahim Garba Wala. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar..........

Yau ake cika shekaru biyu cif da ƙazamin harin da Mayaƙan Hamas suka kai Isra'ila wanya ya hallaka Yahudawa fiye da dubu guda sanadiyyarsa ne kuma aka faro wannan yaƙi na Gaza da ya kashe Falasɗinawa fiye da dubu 60. Wannan yaƙi shi ne mafi muni da duniya ta gani a wannan ƙarnin wanda ya rushe fiye da kashi 90 na gine-ginen yankin. Dangane da wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin siyasar ƙasashe don jin tasirin wannan yaƙi ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar...