Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…
A Najeriya, wasu alƙaluman hukumar kare hakkin ɗan adam ta ƙasar sun ce adadin mutanen da ƴanbindiga suka kashe a cikin watanni shida na farkon wannan shekarar ya zarce na ilahirin shekarar da ta gabata, inda a watan da ya gabata kawai mutane 606 ne masu ɗauke da makamai suka halaka. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
Ambaliyar ruwa na ci gaba da yin ɓarna a wasu biranen ƙasashen Afrika, inda ko a baya-bayan nan ta laƙume rayuka fiye da 600 a ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar Nejan Najeriya yayin da tituna suka fara cika da ruwa a wasu ƙananan hukumomin jihar Kano, baya ga babban birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar da aka samu iftila'in ambaliyar a kwanakin baya. Ya ya matsalar ta ke a yankunan ku, ko wani mataki kuke ɗauka don ganin kun kare kanku daga iftila'in ambaliyar ruwan yayin da daminar bana ta sauka? Shin ko akwai wasu matakai da gwamnatocinku ke ɗauka?
A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Wasu fitattun ƴansiyasa a Najeriya, sun sanar da kafa wani sabon ƙawance da zummar ƙwace mulki daga hannu shugaba Bola Tinubu a shekara ta 2027. To sai dai abin lura a nan shi ne, waɗanda suka ƙulla ƙawancen mutane ne da suka taɓa riƙe muhimman muƙamai ƙarƙashin gwamnatoci daban-daban ciki har da ta APC. Abin tambayar shine, ko waɗanne irin alƙawura ne da za su sake gabatar wa 'yan ƙasar domin samun ƙuri'aunsu? Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
A Najeriya, ga alama sabon salon da hukumomin tsaro na tarayya da kuma na jihar Zamfara su ɓullo da su, sun fara yin tarisi a yaki da ayyukan ƴanbindiga da suka addabi jama'ar yankin. Bayanai sun ce farmakin da ƴan sa-kai suka kai ƙarshen makon jiya, ya yi sanadiyyar mutuwar ƴanbidigar kusan 200 ciki har da manyan kwamandojin Bello Turji. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyin jama'a mabanbanta...
Shirin na yau ya baku damar tofa albarkacin bakinku game da tsagita wuta da aka yi tsakanin Iran da Isra'ila bayan kwashe kusan kwanaki 12 ana gwabza yaƙi. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.
Babban hafsan sojojin Najeriya ya bayar da shawarar gina katanga kan iyakokin ƙasar da maƙotanta don magance matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da su. Janar Christopher Musa ya bayar da misali da ƙasashen Pakistan da kuma Saudiyya, waɗanda ya ce sun gina irin wannan katanga tsakaninsu da maƙota saboda dalilai na tsaro.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Karon farko a tarihi, ƙungiyar Paris Saint Germain ta Farnasa ta yi nasarar lashe kofin gasar Zakarun Turai ta wannan kaka bayan da ta doke Inter Milan ta Italiya, inda ta zama ta biyu da ta taɓa cin wannan kofidaga Faransa. Wani abin lura a game da wannan wasa, shi yadda PSG ta lallasa abokiyar karawarta da ci 5 da banza.Me za ku ce a game da wannan nasara da PSG ta samu?Ko meye ra'ayoyinku a game da yadda gasar ta Zakarun Turai ta wannan kaka ta gudana?
A wannan talata, al'ummar Kamaru na bikin cika shekaru 53 da haɗewar yankunan da ke amfani da Faransanci da masu amfani da harshen Ingilishi, waɗanda kafin nan suna zaune da juna ne a ƙarƙashin tsarin tarayya. To sai dai a daidai yayin da ake wannan biki, yanzu haka akwai masu gwagwarmaya da makamai don samar wa yankunan da ke turancin Ingilishi ƴanci.Shin ko me za ku ce a game da wannan haɗewa?Ko waɗanne matakai ku ke ganin cewa sun dace a ɗauka domin dawo da yarda a tsakanin bangarorin biyu?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
Matsalar barace-barace a kan titunan manyan birane a Yammavin Afirka sai daɗa yin ƙamari take, to sai dai bisa ga dukan alamu mahukunta a ƙasar Ghana sun ƙuduri aniyar kawo ƙarshen wannan ɗabi'a. Domin a cikin makon jiya, jami'an tsaro sun cafke mabarata sama da dubu biyu a birnin Accra kawai, kuma yawancinsu ƴan asalin ƙasashen Najeriya, Nijar, Burkina Faso da Mali ne.Shin ko akwai dalilan da za su sa jama'a su mayar da bara a matsayin sana'a?Ko waɗanne matakai ya kamata a ɗauka domin kawo ƙarshen wannan ɗabi'a ta bara?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Shamsiyya Haruna...
Makonni kaɗan gabanin bukukuwan Sallar Layyah, mahukuntan jamhuriyar Nijar sun bayar da umurnin hana fitar da dabbobi zuwa ƙetare. Ga alama dai an ɗauki matakin ne don hana tashin farashin dabbobi a wannan lokaci, yayin da wasu ke cewa matakin zai iya cutar da tattalin arzikin ƙasar.Abin tambayar shine, menene amfani ko kuma illar wannan mataki ga ƙasar?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Hare-haren ƴanbindiga na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Najeriya, inda a baya-bayan nan suka tsananta kai farmaki hatta akan sansanonin soji, kusan a iya cewa haka take a sauran yankin sahel musamman Burkina Faso, lamarin da kanyi sanadin mutuwar jami'an tsaro masu tarin yawa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a kan wannan maudu'in.......
Shin ko kun san muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa kuwa? Wannan tambaya ce mai matuƙar muhimmanci, lura da cewa yanzu haka akwai ɗimɓin mutane da ke fama da wannan matsala a sassan duniya. Yayin da wasu ke kira wannan lalura a matsayin hauka, masana kuwa na cewa hatta shiga yanayi na damuwa ko da ƙuncin rayuwa na iya haddasa wannan matsalar.Shin ko wace irin kulawa ku ke bai wa lafiyar ƙwaƙwalwa?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Shamsiyya Haruna...
Kamfanin Meta da ya mallaki Facebook, Instagram da Whatsapp ya yi barazanar ficewa daga Najeriya bayan da aka lafta masa biyan tarar dala miliyan 290 saboda karya ƙa'ida. To sai dai gwamnatin Najeriya ta ce ko da kamfanin ya janeye daga ƙasar, to dole ne sai ya biya wannan tarar. Za mu so jin ra'ayoyinku a game da wannan takun-saka tsakanin Najeriya da kuma wannan shahrarran kamfani na sadarwa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a bisa al'ada ya kan baiwa masu saurare damar fadin albarkacin bakinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna
Kamar dai kowace shekara, yau 1 ga watan Mayu, ita ce Ranar Ma'aikata ta Duniya, bikin da a bana ana iya cewa ana gudanar da shi ne a cikin wani yanayi na tsadar rayuwa a mafi yawan ƙasashen duniya. Abin tambayar shine, shin ko a cikin wanne yanayi ake gudanar da bukukuwan na bana, musamman a kasashen Afirka?Waɗanne irin manyan buƙatu ma'akata suke son cimma wa?Shiga alamar sauti, diomin sauraron ciakken shirin.
Bisa ga dukan alamu Maroko na ƙara samun kusanci da ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da alaƙa ke ƙara yin tsami tsakanin waɗannan kaasashen da Aljeriya. Ministocin Harkokin Wajen ƙasashen uku sun ziyarci Maroko tare da ƙulla yarjejeniyar da ke ba su damar yin amfani da tashoshin ruwa ƙasar, alhali ba ɗaya daga cikinsu da ke da iyaka da Marokon.Ko yaya ku ke kallon wannan alaƙa tsakanin Maroko da AES, yayin da suka juya wa makociyarsu Aljeriya baya?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda wasu fitattun mutane mambobin kungiyar farar hula a Najeriya suka nuna takaicinsu kan yadda gwamnatin mai ci ke neman mayar da kasar tsarin jam'iyya daya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani
A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Yayin da a yau aka ƙaddamar da makon rigakafi a duniya, Hukumomi a Najeriya da kuma Unicef, sun yi gargaɗin cewa yanzu haka nau'ukan cutar shan'inna har guda 17 da suka yaɗu a cikin jihohi 8 na ƙasar. Wannan dai babban ƙalubale ne ga sha'anin kiwon lafiya, bayan da aka shelanta kawo ƙarshen cutar tun 2020.Shin ko meye dalilan sake ɓullar wannan cuta a Najeriya?Waɗanne matakai ya kamata a ɗauka domin shawo kanta?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin masu saurare.
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani kamfanin hada-hadar kudi ta Internet a Najeriya mai suna CBEX ya tsere da kudaden jama'a. Danna alamar sauarre domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan mako ya mayar da hankali ne kan gargaɗin gwamnatin Najeriya na yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihohi 30 a daminar bana. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu.
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyoyin ta'addanci ke kawowa ilimin yara mata tsaiko a Najeriya. Danna alamar sauarre don jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
Yau ta ke ranar jin ra'ayoyin ku masu saurare kan batutuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga fannin siyasa, ilimi, lafiya, tattalin arziƙi da dai sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
Hukumar Yaƙi da Rashawa a Najeriya EFCC, ta ce a cikin shekarar ta 2024 da ta gabata, ta yi nasarar ƙwato kusan Naira tiriliyan ɗaya daga hannun barayi da masu handame dukiyar al'umma. EFCC ta ce ko a gaban kotu ma, ta samu nasarori sama da sau dubu huɗu akan masu cin rashawa da kuma ƴan damfara cikin shekarar da ta gabata.Abin tambayar shine, ko aikin hukumar na gamsar da 'yan Najeriya?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakakken shirin.
Ƙungiyar direbobin motoci a Najeriya, ta buƙaci mahukunta su ɗauki matakan kawo ƙarshen kisan da ƴan awaren Biafra ke yi wa direbobin manyan motoci a duk lokacin da suke ratsa yankin kudu maso gabashin ƙasar. Ƙungiyar ta ce an kashe mambobinta sama da 50, kuma 20 daga cikinsu an kashe su ne a shekarar 2024, sannan aka kwashe kayayyaki da kuma ƙona motocinsu.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu.
Aƙalla 40% na mazauna yankin arewa maso yammacin Najeriya ne ka tu'ammuli da miyagun ƙwayoyi, kuma kusan 28 cikin ɗari suna zaune ne a jihar Kaduna kamar dai yadda rahoton hukumomin da yaƙi da wannan matsala ya nuna. Hakazalika, mutum 1 cikin 7 a yankin arewa maso yammacin ƙasar suna tu'ammali da miyagun ƙwayoyin a cewar rahoton.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
Hukumar Ƙayyade Farashin Wutatar Lantarki a Najeriya, sanar da sabon tsarin biyan tara a kan waɗanda ke satar makamashin lantarki a ƙasar. Tarar ta kama daga Naira dubu 100 zuwa dubu 300 daidai da irin salon da mutum ya yi wajen sada gidansa da wannan makamashi.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa a Najeriya, ta ce farashin kayan abinci ya sauka a cikin watan Janairun da ya gabata da 10% idan aka kwatanta da na wata Disamba. To waɗannan dai bayanai da hukuma ta fitar, saboda haka za mu so jin ra'ayoyinku a game da wannan rahoto.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Abida Shu'abu Baraza...
Alƙalumma na nuni da cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata, an kashe aƙalla Naira Tiriliyan 7 da bilyan 200 a matsayin tallafi da nufin inganta sanar da wutar lantarki a Najeriya. To sai dai a zahirin ana cewa har yanzu wannan ɓangare na ci gaba fama da matsaloli masu tarin yawa, yayin da a ɗaya ɓangare farashin wutar ya ninka ninkin ba ninkin.
A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
a yau shirin namu na ra'ayoyin ku masu sauraro ya yi dubu ne akan Shin ko menene ra'ayin ku a game da batun tattaunawa da 'yan bindiga.
A yau juma'a kamar yadda aka saba kuna aiko mana da saƙonnin ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya, siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar. Tinubu ya bayyana haka ne wajen taron ƙasashen Afirka wanda ya mayar da hankali akan yadda za a samar wa aƙalla mutane miliyan 300 wutar lantarki a nahiyar baki ɗaya. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
Yau 29 ga watan Janairu wa'adin farko da kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka bayar na ficewa daga kungiyar ECOWAS ya cika, abinda ke tabbatar da raba garin bangarorin biyu dangane da cikar wannan wa'adi, Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
A yau juma'a kamar yadda aka saba kuna aiko mana da saƙonnin ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya, siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Rahotanni daga wasu sassan Najeriya ciki har da babbar kasuwar kayan abinci dangin hatsi ta Dawanau da ke Kano na cewa an fara samun sauƙin farashin kayayyakin abincin, idan aka kwatanta da yadda al'amarin yake a watannin baya. Lamarin dai ya haifar da muhawara akan dalillan da suka janyo saukin farashin kayana abincin da ɗorewar hakan.Abin tambayar shine, ko al'umma sun gamsu da wannan rahoto, ko kuma har yanzu anan nan a gidan jiya?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
A ƙasar Amurka, bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaba ƙasa na 47, Donald Trump, ya rattaba hannu kan wasu gomman dokokin zartawa na ikon shugaban ƙasa, ciki har da janye ƙasarsa daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kamar yadda ya yi a wa'adin mulkinsa na farko, kafin magabacinsa Joe Biden ya maido da ƙasar ciki. Wasu na ganin wannan mataki zai yi illa ƙwarai ga ɗorewar hukumar wajen gudanar da ayyukan ta a duniya, duba da kaso mai tsoka da Amurka ke bayarwa wajen gudanar da ayyukan WHO ɗin.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
A wannan makon ne gwamnatin sojin Nijar ta gabatar da wata sabuwar doka da ke tilastawa baƙi da ke neman zuwa ƙasar da su tabbatar sun samu takardun izini da suka dace, tare da gargadi ga su ma ƴan ƙasar da su yi hattara wajen ƙarbar baƙunci baƙi da ke shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba. Sabuwar dokar ta soji ta tanadi hukunci mai tsauri ga waɗanda suka saɓa umarnin a bangarorin baƙi da su kansu ƴan ƙasar, wanda ya ƙunshi hukuncin ɗauri a gidan yari da kuma tara.Gwamnati da wasu ƴan ƙasar na cewa anyi hakan ne saboda dalilai na tsaro, yayin da wasu ke danganta hakan da tsoro da fargaba, to ku ya kuka kalli wannan mataki?Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.....
A baya-bayan hare-haren sojojin Najeriya kan ƴan ta'adda na shafar fararen hula musamman ƴan sa kai da ke taimakawa wajen yaƙar matsalolin tsaro. Matsalar na ƙara yawaita inda a kwanan nan sojojin suka kai hari a jihohin Sokoto da Zamfara wanda ya halaka fararen hula fiye da 100, yayin da a kowane lokaci sojojin kan musanta hakan , daga baya kuma su ce za su gudanar da bincike.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
A wani yanayi da ba safai aka saba gani ba, mahukuntan Nijar sun sallami tuɓaɓɓun mayaƙan Boko Haram aƙalla 124 ciki har da ƙananan yara 44, waɗanda aka basu horan sauya ɗabi'u don komawa rayuwar fararen hula. Wannan shi ne karon farko da ake ganin irin hakan, tun bayan makamancin yunƙurin da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Muhammad ya yi watanni ƙalilan gabanin hamɓarar da shi.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi a cikin shirin...
Kamar yadda labari ya karaɗe kafafen yada labarai, ƙaasa da mako guda bayan da hukumar kwastan a Najeriya ta sanar da buɗe shafin yanar gizo don aikewa da takardun neman ɗaukar jami'ai kimanin dubu 4, sama da masu neman wannan aiki dubu dari 5 ne suka gabatar da buƙatunsu. Wannan al'amari ne da ke faruwa a kowace ma'aikata a duk lokacin da aka sanar da buƙatar ɗaukar ma'aikata.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.
A wannan talatar ce aka rantsar da John Mahama a matsayin shugaban Ghana, cikin yanayi na tarin kalubale da suka hada da na matsin tattalin arziki biyo bayan lashe zaben da aka yi cikin kwanciyan hankali da lumana. Masu bibiyar siyasa a kasar sunyi ittifakin cewa duk da cewa Mahaman ya taba jagorancin kasar, ya dawo ne a lokacin da lamura suka sauya ainun.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.
A yayin da ake bankwana da shekarar 2024 shuwagabanni daga kasashen Duniya na fuskantar tarin kalubale da suka hada da rikice-rikice,yake-yake harma da wasu matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da matsin tattalin Arziki da sauran su. Wasu abubuwa ne baza ku iya mantawa ba kuke tsoron dakon su zuwa sabuwar shekara?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Hauwa Garba Aliyu Zaria.
A yau juma'a kamar yadda aka saba kuna aiko mana da saƙonnin ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya, siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ana fargabar al'umma da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata sakamakon wani hari da jirgin yaƙi na soji ya kai kan Lakurawa a wasu ƙauyuka da ke Sokoton Najeriya. Ana kallon wannan harin a matsayin na kuskure kuma ba wannan ne karon farko da hakan ke faruwa ba a arewaci da wasu Najeriya.Latsa alamar sauti domin sauraren mababanta ra'ayoyi a cikin shirin da Abida Shu'aibu Baraza ta jagoranta...
Aƙalla mutane 60 suka rasa rayukansu a sassan Najeriya, yayin turmutsitsin karɓar tallafin abinci da kuma taron bikin ƙarshen shekara na yara a jihohin Anambra, da Oyo da kuma birnin Abuja. A yayin da ‘yan Najeriyar ke tofa albarkacinsu kan lamarin wasu na ɗora laifin aukuwar haɗurran akan gazawar mahukunta wajen samar da tsarin bai wa mutane kariya yayin taruka, yayin da wasu ke ganin ɗaiɗaikun masu raba tallafin ke da alhaki la'akari da cewar suna yin hakan ne ba tare da tsari ko sanin hukuma ba.Wannna shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...