Dandalin Siyasa

Follow Dandalin Siyasa
Share on
Copy link to clipboard

Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen…

Rfi - Abdurrahman Gambo Ahmad


    • May 8, 2019 LATEST EPISODE
    • infrequent NEW EPISODES
    • 13m AVG DURATION
    • 23 EPISODES


    Search for episodes from Dandalin Siyasa with a specific topic:

    Latest episodes from Dandalin Siyasa

    Dandalin Siyasa - Majalisar Najeriya ta gayyaci Buhari don yi mata bayani kan tsaro

    Play Episode Listen Later May 8, 2019 10:12


    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari kan kiran da Majalisar Tarayyar Najeriya ta yi shugaba Muhammadu Buhari don yi mata bayani kan tabarbarewar tsaro a kasar.

    Dandalin Siyasa - Rikicin shugabancin Majalisar Wakilai a Najeriya

    Play Episode Listen Later Apr 17, 2019 10:27


    Shirin dandalin siyasa a wannan makon ya sake yin duba kan dambarwar neman shugabancin Majalisar Najeriyar karo na 9 da sabbin zababbun 'yan Majalisar wakilan kasar ke tafkawa. A yi sauraro lafiya.

    Dandalin Siyasa - Dambarwar Jam'iyyar APC kan shugabancin Majalisun Najeriya

    Play Episode Listen Later Apr 10, 2019 11:11


    Har yanzu Jam'iyyar APC ta gaza shawo kan matsalolinta da suka shafi 'yan majalisun da za su jagoranci majalisar Dattijai da ta wakilai, dai dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar rarrabuwar kai.

    Dandalin Siyasa - Fatan yan Najeriya dangane da sabuwar Majalisa bayan zabe

    Play Episode Listen Later Apr 3, 2019 10:58


    Bayan wata daya da kawo karshen zaben Shugaban kasa da na wasu yan majalisu a Najeriya,hankulan yan kasar da dama ya koma zuwa zauren Majalisa . Haka zalika wasu daga cikin yan majalisun da suka samu goyan bayan jama'a sun sheidawa Bashir Ibrahin Idris a cikin shirin Siyasa fatan su da kuma irinn  rawar da za su iya takawa a Majalisa don kawo sauyi  a siyasar kasar,banda haka wasu sun bayyana damuwa  a kai.

    Dandalin Siyasa - Dambarwar zabukan Najeriya na 2019

    Play Episode Listen Later Mar 20, 2019 10:45


    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan dambarwar zabukan Najeriya, in da Jam'iyyar adawa ta PDP ta garzaya kotu domin kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari na APC a zaben 2019, yayinda ita ma APC a jihar Bauchi ta ruga zuwa kotu duk dai akan batun na zabe.

    Dandalin Siyasa - Nazari kan zaben Gwamnoni a Najeriya

    Play Episode Listen Later Mar 7, 2019 9:57


    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari ne game da zabukan Gwamnoni na 'yan majalisun jihohin Najeriya da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa, in da ake fargabar cewa, da dama daga cikin Gwamnoni masu ci ba za su koma kan kujerunsu ba saboda wasu dalilai na siyasa.

    Dandalin Siyasa - Shugaba Buhari ya lashe zaben Najeriya wa'adi na biyu

    Play Episode Listen Later Feb 28, 2019 11:01


    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne game da nasarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu ta sake lashe kujerar shugabancin kasar wa'adi na biyu bayan doke babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar. Tuni Jam'iyyar PDP ta bayyana sakamakon zaben a matsayin mara inganci tana mai zargin tafka magudi a zaben,yayinda ta ce, za ta shigar da kara a kotu.

    Dandalin Siyasa - 2019: Hankulan kasashen duniya sun karkata zuwa zabukan Najeriya

    Play Episode Listen Later Feb 13, 2019 10:37


    Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako da Bashir Ibrahim Idris ya gabatar, yayi nazari kan halin da siyasar Najeriya ke ciki, yayinda ya rage kwanaki kalilan a gudanar da zabukan kasar na 2019 a matakai daban daban. Sai kuma tsokaci da shirin ya yi kan yadda hankulan kasashen duniya ya karkata zuwa kan zabukan Najeriyar.

    Dandalin Siyasa - Yadda Siyasa ke gudana a Jihar Kano gabanin zaben shugaban kasa

    Play Episode Listen Later Feb 8, 2019 10:20


    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon, ya leka jihar Kano da ke tarayyar Najeriya, ida yayi nazari kan yadda al'amuran Siyasa ke gudana, yayinda ake gaf kada kuri'a a zaben shugabancin kasar na 2019 a ranar 16 ga watan Fabarairu.

    Dandalin Siyasa - Dambarwar siyasar dakatar da Onnoghen

    Play Episode Listen Later Jan 31, 2019 10:40


    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan dambarwar siyasar da ta kunno kai a Najeriya bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dakatar da alkalin alkalai, Walter Onnoghen bisa zargin sa da bayar da bayanan karya kan kudaden da ya mallaka.

    Dandalin Siyasa - Shiri kan dakatar da Babban mai shari'ar Najeriya

    Play Episode Listen Later Jan 30, 2019 10:40


    Shirin Dandalin siyasa na wannan mako ya mayar da hankaline kan dakatar da babban mai shari'ar Najeriya Walter Onnonghen da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi.

    Dandalin Siyasa - 'Yan siyasa na sauya sheka a Najeriya

    Play Episode Listen Later Jan 17, 2019 10:33


    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan yadda 'yan siyasa ke ci gaba da sauya sheka a Najeriya a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben gama-gari a cikin watan gobe.

    Dandalin Siyasa - Kun san abin da Buhari ya fada a Akwa Ibom?

    Play Episode Listen Later Jan 6, 2019 10:27


    Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari da ya kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Akwa Ibom, ya bayyana nasarorin da ya samu tun bayan darewarsa kan karagar mulki a shekarar 2015, in da yake cewa, gwamnatinsa ta murkushe mayakan Boko Haram duk da cewa kungiyar kan kaddamar da hare-hare jifa-jifa a yankin arewa maso gabashin kasar. Shugaban ya kuma bayyana irin nasarar da ya samu a fannin yaki da cin hanci da rashawa. Kuna iya latsa kan hoton don sauraren cikakken shirin kan yakin neman zaben Buhari a Akwa Ibom.

    Dandalin Siyasa - Taron sulhunta yan siyasar Najeriya daga Tsohon Shugaban kasar

    Play Episode Listen Later Dec 12, 2018 10:00


    A wani taro da Tsohon Shugaban Najeriya Abdusalami Abubakar ya shirya,taron da ya hada yan siyasa da suka hada da Muhammadu Buhari shugaban kasar,wanda kuma ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin sa da sauran masu karawa da shi a zaben shekara mai zuwa. Wasu na bayyana cewa ba a gayyaci dan takara Atiku Abubakar a wannan taro,cikin shirin dandalin siyasa Bashir Ibrahim Idris ya samu tattaunawa da yan Najeriya.

    Dandalin Siyasa - Takaddama ta kaure a wasu jam'iyyun siyasar Najeriya

    Play Episode Listen Later Nov 28, 2018 10:00


    A cikin shirin dandalin Siyasa, Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali zuwa takaddama da ta kaure a yankin arewa maso gabacin Najeriya. Datijen wannan yankin sun bukaci a goyawa daya daga cikin yan takara a zaben Shugabancin kasar baya,labarin da wasu suka musanta. Bashir Ibrahim Idris ya samu zantawa da wasu daga cikin datijen yankin a cikin shirin  Dandalin siyasa daga nan Rfi.

    Dandalin Siyasa - Rashin kasancewar mata a fagen siyasar Najeriya

    Play Episode Listen Later Nov 14, 2018 10:58


    A cikin shirin dandalin siyasa,Bashir Ibrahim Idris ya samu tattaunawa da wasu mata dangane da rashin samun mata a fagen siyasar Najeriya,wasu daga cikin yan kasar mata musaman sun bayyana aniyar su ta kasancewa daga cikin yan takara a zaben shekarar 2019.

    Dandalin Siyasa - Tasirin Na'urar Tantance Kuri'u a zaben Najeriya

    Play Episode Listen Later Nov 8, 2018 10:04


    Sashen Hausa na RFI na farin cikin gabatar muku da sabon shirin Dandalin Siyasa da zai rika nazari game da al'amuran da suka shafi siyasar Najeriya, Nijar, Afrika da sauran kasashen duniya. Shirin na makon farko tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari ne game da tasirin na'urar tantance masu kada kuri'u a zaben Najeriya, abin da masana ke cewa, ta na taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar magudi.

    Dandalin Siyasa - Dalilin yin watsi da jekadun Buhari a Majalisar Dattijai

    Play Episode Listen Later Nov 19, 2016 20:09


    Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna game da batun yin watsi da amincewa da jekadu 46 da Majalisar Dattiajan Najeirya ta yi da rikicin shugabannin Jamiyyar PDP mai adawa a Najeriya da ta dare gida biyu inda wasu ‘yan jam’iyyar ke neman a raba-gari wasu kuma ke bukatar sake lale.

    Dandalin Siyasa - Sharhi akan nasarar Trump

    Play Episode Listen Later Nov 14, 2016 20:17


    Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna game sakamakon zaben Amurka inda masana suka yi sharhi akan nasarar da Donald Trump dan takarar Republican ya samu bayan ya doke abokiyar takararsa Hillary Clinton ta Democrat.

    Dandalin Siyasa - Manufofin Clinton da Trump a zaben Amurka

    Play Episode Listen Later Nov 8, 2016 20:01


    Shirin Dandalin Siyasa ya yi nazari ne game da 'Yan takarar shugabancin Amurka guda biyu Donald Trump na Republican da Hillary Clinton da Democrat tare da tattauna manufofinsu. Sannan shirin ya yi tsokaci akan tasirin zaben Amurka ga Afrika.

    Dandalin Siyasa - An ci mutunci da zage-zage a Siyasar Amurka

    Play Episode Listen Later Oct 31, 2016 20:04


    Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne akan dambarwar siyasar Amurka inda ya rage kwanaki a kada kuri’ar zaben shugaban kasa. A cikin shirin za a ji yanayin zaben Amurka da kuma yadda zaben na bana ya zo da sabbin abubuwa da ake ganin sun sabawa demokuradiyar kasar.

    Dandalin Siyasa - Jihohin da Abacha ya kirkiro sun yi shekaru 20

    Play Episode Listen Later Oct 15, 2016 20:04


    Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da bikin cika shekaru 20 da jihohi 6 suka gudanar wadanda Marigayi Janar Sani Abacha ya kirkiro a shekarar 1996. Shirin ya mayar da hankali a Jihohin Gombe da Zamfara. Shin kwanliya ta biya kudin sabulu? Sannan shirin ya tabo muhawarar da ake a Majalisar Dattijai kan wani kudirin doka na Daidaiton jinsi wato kudirin doka da zai ba mata damar yin kafada da kafada da maza wanda ke yin karo da addini.

    Dandalin Siyasa - Shirin Zabe a Ghana

    Play Episode Listen Later Oct 9, 2016 20:07


    Shirin Dandalin Siyasa ya yi nazari kan shirin babban zaben kasar Ghana da za a gudanar a watan Disemba. Shirin kuma ya leka Najeriya game da batun fasa kwan da Hon Abdulmumin Jibril ke yi a Majalisar dokokin kasar.

    Claim Dandalin Siyasa

    In order to claim this podcast we'll send an email to with a verification link. Simply click the link and you will be able to edit tags, request a refresh, and other features to take control of your podcast page!

    Claim Cancel