POPULARITY
Yau juma'a, kamar yadda aka saba muna baku damar tofa albarkacin bakinku, domin bayyana mana ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga fannin tattalin arziƙi, ƙasuwanci, tsaro da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Shamsiyya Haruna...
Gwmanatin Jamhuriyar Nijar ta kafa kwamitin ƙwararru wanda ta ɗora wa alhakin sake rubuta tarihin ƙasar, lura da cewa yawancin abubuwan da ake faɗa game da ƙasar a halin yanzu Turanwan mulkin mallaka ne suka rubuta su. Shin ko meye muhimmanci rubuta sabon tarihin wanda aka ɗanka wa masana ƴan ƙasar a maimakon wanda aka gada daga ƴan mulkin mallaka? Anya abu ne mai yiyuwa a iya sauya bayanan da ke rubuce a game da ƙasar waɗanda tuni suka karaɗe duniya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Mahukunta a Najeriya sun tasa ƙeyar ƴan asalin ƙasashen waje su 192 da aka tabbatar da sun shahara wajen aikata damfara ta yanar gizo a cikin ƙasar. Mutanen waɗanda aka kama a birnin Lagos, sun haɗa da China, Philippines, Malaysia, Pakistan, Tunisia da dai sauransu, waɗanda tuni kotu ta tabbatar da laifukansu. Shin me za ku ce a game da yadda ƴan damfara a yanar gizo ke neman mayar da Najeriya a matsayin tunga domin baje kolinsu? Shin ko kun gamsu da irin matakan da mahukunta ke ɗauka domin daƙile wannan matsala? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
A wannan makon shirin na Kasuwa Akai Miki Dole tare Abdulƙadir Haladu Kiyawa zai tattauna ne a kan yawaitar matasan Najeriya masu muhimman sana'o'in hannu da ke yin ƙaura ko kuma tafiya ci rani zuwa wasu ƙasashen Afrika domin neman na rufin asiri, abin da ake alaƙantawa da dalilai da dama da ke sanya matasan ficewa daga ƙasar tasu ta haihuwa. A shekarun baya ba haka lamarin yake ba, inda Najeriyar ke matsayin wajen da ɗimbin ƴan ƙasashen ƙetare ke kwarara don neman kuɗi musamman ƴan kasashen Afrika kamar Jamhuriyar Nijar, da Ghana, da Jamhuriyar Benin, har ma da Kamaru. To Sai dai a yanzu, waɗannan ƙasashen ne ƴan Najeriyar ke tururuwar zuwa cikinsu duk da kasancewar ƙasashen ba su da ɗinmbin arziƙi kamar Najeriyar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Valdība akceptē valsts nākamā gada budžetu ar deficītu 3,3% no IKP. Valdība atbalsta izmaiņas Dabas resursu nodokļa likmēs, kas paredz jaunu nodokli neapstrādātai koksnei un lielāku nodokli kūdras nozarei. Neskatoties uz panākto vienošanos, kas ļauj NATO valstīm iegādāties Ukrainas vajadzībām ieročus no ASV rezervēm, kopējais militārais atbalsts Ukrainai vasaras izskaņā piedzīvojis strauju kritumu. No 17. oktobra dzelzceļa līnijā Rīga-Tukums gaidāmas būtiskas izmaiņas pasažieriem. Latvijas vīriešu futbola izlase šovakar Daugavas stadionā aizvadīs Pasaules kausa kvalifikācijas maču, pretiniekos - šī sporta veida izgudrotāju mantinieki Anglijas futbola izlase. Masu demonstrācija, slēgtas lidostas un traucēta sabiedriskā transporta satiksme – tā ir daļa no 14. oktobra nacionālā streika Beļģijā.
A Najeriya yajin aikin malaman jami'o'i ya shiga rana ta biyu, lamarin da tuni ya fara haifar da cikas musamman ga ɗalibai da mafi yawansu na tsakiyar zana jarrabawa. Yayin da ƙungiyar Malaman ASUU ta ce ta shiga yajin aikin ne domin neman gwamnati ta cika aiwatar da yarjejeniyar da ɓangarorin biyu suka rattaba wa hnnu tun 20009, yayin da a gwamnati ke cewa tuni aka aiwatar da abubuwan da kunshe a yarjejeniyar. Shin ko yaya ku kallon wannan yajin aiki? Wace shawarar za ku bai wa bangarorin biyu domin gaggauta wannan saɓani da ke tsakaninsu. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Ra'ayoyi na ci gaba da bayyana dangane da afuwar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wa mutane 175 da aka kama da laifuka daban daban. Daga cikin waɗanda aka yi wa afuwar har da waɗanda aka yankewa hukuncin kisa, da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi da dai sauransu. Shin ko me za ku ce a game cancanta ko kuma rashin dacewar yin wannan afuwar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Kamar yadda aka saba, a kowace ranar Juma'a, sashen Hausa na RFI na baiwa masu sauraro damar tofa albarkacin bakinsu kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama dag siyasa, zamantakewa, tattalin arziƙi da dai sauransu. A yau ma bamuyi ƙasa a gwiwa ba wajen baku wannan dama. Idan kuka latsa alamar sauti, zakuji mabanbanta ra'ayoyi a shirin da Abida Shu'aibu ta gabatar...
A ƙasar Kamaru, yanzu haka ana ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar da za a yi ranar lahadi mai zuwa, inda ƴan takarar 9 za su fafata da shugaba mai-ci wato Paul Biya. Kawo yanzu dai yaƙin neman zaɓen na gudana a cikin kwancin hankali, yayin da tuni mahukunta suka yi gargaɗi domin kauce wa duk wani abu da zai iya haifar da matsala a wannan marra. Shi me za ku ce a game da wannan zaɓe da ake shirin gudanarwar a Kamaru? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Rundunar Ƴansandan Najeriya ta sanar da karɓar umarnin kotu na dakatar da kama motocin dake ɗauke da bakin gilashi, inda ta umarci jami'an ta da su dakatar da kamen har zuwa lokacin da za'a kammala shari'ar. Wannan ya biyo bayan rugawa kotu da wasu lauyoyi suka yi domin hana aiwatar da dokar da suka ce za ta take haƙƙin Bil Adama. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barr Suleiman Muhammed, lauya mai zaman kansa. Ku latsa alamar sauti domin jin tattaunawarsu...
A jiya ne aka gudanar da bikin ranar malamai ta duniya cikin yanayin ƙuncin rayuwa da ƙarancin albashi, musamman a wasu ƙasashen Afirka da malaman ke ɗanɗana kuɗarsu. An ware wannan rana ne, domin nuna goyon baya ga irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban rayuwar al'umma a fannoni da dama. Wanne hali malamai ke ciki a yankunanku? Shin kun gamsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a yankunanku. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Shirin 'Ra'ayoyin Mai Saurare' na wannan rana tare da Abida Sha'aibu ya tattauna ne kan bukin cika shekaru 65 da samun ƴancin Najeriya daga turawan mulkin mallakar Burtaniya da aka gudanar a wannan Laraba, wato tunawa da ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, kan halin da ƙasa ke ciki ta fannin ci gaba ko kuma koma-baya a tsawon waɗannan shekaru.
A Najeriya ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin matatar Dangote da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas wato PENGASSAN. Tun daga lokacin da matatar Dangote ta fara aiki kawo yanzu, an samu takaddama irir-iri daga kungiyoyin da ke da alaka da man fetur da kuma iskar gas. Ko me yasa takun saka tsakanin Dangote da masu ruwa da tsaki a harkar mai, yaki ci yaki cinyewa? Me ku ke ganin ummul aba'isin wannan dambarwa da take bullowa daga kusurwa-kusurwa, wanda ake ganin zai haifar da tashin farashin mai a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai........ Ku latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin na ku.....................
A Najeriya, wani abu da ke neman ɗaure wa jama'a kai shi ne yadda ƙasa da shekara ɗaya da ƙddamar da ayyukanta, matatar mai ta Ɗangote ke fuskantar rigingimu daban daban, da suka haɗa da tsakaninta da dillalan mai masu zaman kansu, da ma'aikatan dakon mai wato NUPENG sai kuma wannan karo da PENGASSAN wato ƙungiyar manyan ma'aikatan mai da iskar gaz na ƙasar. A game da waɗannan rigingimu ne Abdoulkarim Ibrahim Ibrahim Shikal ya zanta da masani harkar mai a ƙasar wato Alhaji Ɗayyabu Yusuf Garga, domin sanin wasu daga cikin dalilan faruwar hakan. Ga kuma zantawarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
An ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar Kamaru, inda mutane 12 ciki har da shugaba mai-ci Paul Biya za su kara da juna a ranar 12 ga watan gobe na Oktoba idan Allah ya kai mu. Yayin da Paul Biya ke fatan sake samun yardar al'umma don ci gaba da mulki karo 8, a nasu ɓangare kuwa 'yan adawa na kallon zaɓen a matsayin wata dama don samar da sauyi a ƙasar. Shin me za ku ce a game da wannan yaƙin neman zabe? Ko wane fata ku ke yi wa al'ummar Kamaru? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
Shirin Ra'ayoyin mai Saurare na wannan ranar Alhamis 25 ga watan Satumbar 2025, wanda Oumar Sani ya gabatar, ya tattauna ne kan matakin gwamnatin Amurka na hana duk wani ɗan Najeriya ciki har da jami'an gwamnati da aka samu da hannu da rashawa bisar da za ta ba su damar shiga ƙasar.
Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewa daga Kotun Hukunta Laifuka ta Duniya da ke birnin Hague, bisa zargin kotun da kasancewa ƴar amshin ƴan mulkin mallaka. To sai dai wasu na ganin cewa shugabannin ƙasashen uku sun ɗauki matakin ne don kauce wa bincike ko tuhuma daga wannan kotu. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacinku a yau cikin shirin na Ra'ayoyinku masu saurare. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Gwamnatin Jamhuriya Nijar ta ɗage haramcin shigar da siminti a ƙasar, sakamakon yadda ake fama da ƙamfarsa, lamarin da ya haifar da tsadarsa a kasuwa. Wani lokaci a can baya ne dai mahukunta suka sanar da haramta shigar da simintin don kare kamfanonin da ke sarrafa shi a cikin gida, amma kuma aka wayi gari na cikin gidan sun gaza wadatar da masu buƙatar sa domin yin gini. Shin ko me za ku ce a game da cire haramcin? Wannan shine maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Yau juma'a, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar faɗin albarkacin bakinsu, kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tattalin arziƙi, ilimi, lafiya, zamantakewa, siyasa da dai sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare Nasiru Sani...
A Najeriya, gwamnatin Neja ta umarci ilahirin limaman masallatan Juma'a a faɗin jihar da su riƙa miƙa mata bayanan da ke ƙunshe a cikin huɗubar da za su gabatar don tantancewa, matakin da Gwamna Muhammadu Umar Bago ke cewa yunƙuri ne na kaucewa duk wata barazana ta cusa ƙiyayya ko kuma haddasa rikici da malaman ka iya yi. Yaya kuke kallo wannan mataki na Gwamnan jihar Neja? Shin kuna ganin akwai buƙatar shigowar gwamnati don daidaita yadda malamai ke gudanar da khuɗubobi da sauran karatuttuka? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
Hukukumar Yaƙi da Rasha ta ICPC a Najeriya, ta ce yanzu haka tana ƙara sa-ido dangane da yadda ake kashe kuɗaɗe mallakin ƙananan hukumomi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ke shan matsin lamba domin ganin ta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya buƙaci a zuba wa ƙananan hukumomin kuɗadensu kai-tsaye a maimakon bi ta hannun gwamnonin jihohi. Ko me za ku ce a game da jan ƙafa wajen aiwatar da wannan umarni da kotu ta bayar tun watan Yulin shekara ta 2024 da ta gabata? Wace irin rawa ya dace ICPC ta taka don kare dukiyar ƙananan hukumomi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakin ku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
[✐3.Moderato] Volitional Form “I'm thinking of telling the truth.”[00:08]Hi everyone, good morning, good day, good evening. Today, we will learn the volitional form. Let's start from the basics.Repeat after me[00:21]1. go: masu form → volitional form2. sit3. drink4. call, invite5. go back, go home6. meet7. eat8. see, watch, look9. do10. come[01:32]Now, make a sentence as follows.For example,Let's buy a personal computer in Akihabara. [Masu style]→ Let's buy a personal computer in Akihabara. [Plain style]Ready?[01:45]1. Let's go tomorrow. [Masu style] → [Plain style]2. Let's sit here.3. Let's drink this sake.4. Let's call an ambulance.5. Let's go home soon.6. Let's meet again.7. Let's eat supper at home.8. Let's watch a Japanese film.9. Let's clean the toilet.10. Let's come to this restaurant to eat again.[04:16]Next, let's make a sentence with “〜to omoimasu” after listen to the key words [KW].[01:25]For example,[KW] internet/online, buy, think→ I think I will buy it online.OK?[01:37]1. [KW] supermarket, stop by, go home, think→ I think I will stop by the supermarket and then go home.((tachi)yorimasu = stop by, pop in)2. [KW] back seat, sit, think→ I think I'm going to sit in the back seat.3. [KW] go home, medicine, take, think→ I think, when I get home, I'll take medicine.4. [KW] graduation, parents, invite, think→ I think I will invite my parents to the graduation ceremony.(yobimasu : here means = invite, ask to come)=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*= 「しんじつを はなそうと おもっています。」[00:08]みなさん、おはようございます、こんにちは、こんばんは。きょうはVolitional Formをべんきょうします。さっそく、きほんから はじめましょう。Repeat after me[00:21]1. いきます → いこう[volitional form]2. すわります → すわろう3. のみます → のもう4. よびます → よぼう5. かえります → かえろう6. あいます → あおう7. たべます → たべよう8. みます→ みよう9. します→ しよう10. きます→ こよう[01:32]では、つぎのようにぶんつくってください。たとえば、あきはばらで パソコンを かいましょう。[Masu style]→ あきはばらで、パソコンをかおう。[Plain style]いいですか。[01:45]1. あした、いきましょう。[Masu style]→ あした、いこう。[Plain style]2. ここに すわりましょう。→ ここに すわろう。3. このおさけを のみましょう。→このおさけを のもう。4. きゅうきゅうしゃを よびましょう。→ きゅうきゅうしゃを よぼう。5. そろそろ、かえりましょう。→ そろそろ かえろう。6. また、あいましょう。→ また、あおう。7. うちで ゆうはんを たべましょう。→ うちで ゆうはんを たべよう。8. にほんのえいがをみましょう。→ にほんのえいがをみよう。9. トイレをそうじしましょう。→ トイレをそうじをしよう。10. また、このレストランに たべにきましょう。→ また このレストランに たべに こよう。[04:16]つぎは、まずキーワード[KW]をきいてから、「〜とおもいます」のぶんをつくろう![01:25]たとえば、[KW] ネット、かいます、おもいます→ ネットで、かおうと おもいます。いいですか。[01:37]1. [KW] スーパー、よります、かえります、おもいます→ スーパーによってから かえろうと おもいます。((たち)よります = stop by、pop in)2. [KW] うしろのせき、すわります、おもいます→ うしろのせきに すわろうと おもいます。3. [KW]うちに かえります、くすり、のみます、おもいます→ うちにかえったら、くすりをのもうと おもいます。4. [KW]そつぎょうしき、りょうしん、よびます、おもいます→ そつぎょうしきに、りょうしんをよぼうと おもいます。(よびます: here means = invite, ask to come)Support the show=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=*=Need more translation & transcript? Become a patron: More episodes with full translation and Japanese transcripts. Members-only podcast feed for your smartphone app. Japanese Swotter on PatreonNote: English translations might sound occasionally unnatural as English, as I try to preserve the structure and essence of the original Japanese.
Shirin Ra'ayoyin Mai Sauraro na wannan Litinin tare da Nasiru Sani ya tattauna ne kan janye yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar da ƙugiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta sanar a ƙarshen mako, kwanaki bayan fara ta a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ta ƙara wa'aɗin makwanni biyu don a biya musu buƙatunsu. Daga cikin buƙatun ƙungiyar da take nema gwamnati ta biya akwai abinda ya shafi albashi da alawus-alawus da kuma walwalar mambobinta. Ku latsa alamar sauti domin sauraron ra'ayoyin wasu daga cikin masu sauraro da suka aikoma ta manhajarmu ta Whatsapp
A makon da ya gabata ne likitoci da ke neman ƙawarewa a Najeriya suka gudanar da yajin aiki, domin nuna rashin amincewa dangane da yadda gwamnati ke jan ƙafa wajen ƙin biyansu haƙƙoƙinsu.To sai dai bayan da aka fara biyansu wasu daga cikin haƙƙoƙin, sun dakatar da yajin aikin tare da bai wa gwamnati ƙarin makonni biyu domin shafe musu hawayensu. Dr Uzairu Abdullahi, shi ne Editan Mujallar wallafa labarai ta ƙungiyar ya yi ƙarin bayani..... Latsa alamar sauti domin sauraron tattaunawar da Abdoulkarim Ibrahim Shikal........
A karon farko gwamnatin Najeriya ta hannun hukumarta da ke kula da sufurin jiragen ruwa a koguna ko kuma cikin gida, ta shelanta haramta jigilar duk wani jirgi ko kwale-kwale da ba a yi wa rijista da gwamnati ba, Ghana ta karɓi baƙi ‘yan Afirka ta yamma, waɗanda gwamnatin Amurka ta taso ƙeyarsu a ƙarƙashin shirin shugaba Donald Trump na korar baƙin-haure, wasu kenan daga cikin manyan labarun makon jiya da Nura Ado Suleiman zai kawo muku a cikin shirin Mu zagaya Duniya.. Latsa alamar sauti don sauraron shirin..........
A yunƙurin rage yawaitar haɗura akan ruwa, Hukumar Kula da Zirga-zirga a kan Kogunan Najeriya ta haramta yin amfani da jiragen ruwa a kan kogunan ƙasar sai tare da samun izini daga gare ta. Wasu daga cikin matakan da hukumar ta sanar sun haɗa da hana yin lodin fasinja sai a tashoshin da ta amince da su, sai tilasta wa fasinja yin amfani da rigar kariya, da mallakar takardar shaidar ƙwarewa ga illahirin matuƙan jiragen da dai sauransu. Anya waɗannan matakai za su taimaka don rage afkuwar haɗurra a kan kogunan Najeriya? Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyyar Nijar na ci gaba da kamen waɗanda ke sukar lamirinta da suka hadar da ƴan jarida da masu fafutuka har ma da ƴan siyasa. A wani rahoto da ta fitar a baya bayan nan kungiyar kare hakkin bil Adam Human Right Watch ta soki yadda sojojin da suka kwace muki a ƙasar ke tsare jama'a babu gaira babu dalili. Akan wanan abokin aiki Oumarou Sani ya tattaunawa da Mamane Wada shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.
A Jamhuriyar Nijar, batun ƴancin faɗin albarkacin baki, aikin jarida ko kafa ƙungiyoyi da sunan yi fafutuka na ci gaba da fuskantar barazana. Bayan rusa ilahirin jam'iyyun siyasa, daga bisani an ci gaba da kama ƴan jarida da masu fafutukar kare hakkin bil adama, tare da jefa ƙungiyoyin kwadago a cikin fargaba ta hanyar farawa da rusa kungiyoyin alƙalai na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don jin ra'ayoyin jama'a kan wannan batu.
A Najeriya, an shiga takun-saƙa tsakanin Ƙungiyar NUPENG ta direbobin motocin dakon mai da iskar gas da kuma Ɗangote wanda ya sanar da sayo motoci dubu 4 da zai yi amfani da su don rarraba man fetur a sassan ƙasar. Yayin da NUPENG ke cewa magoya bayanta ne ke da hurumin raba mai da iskar gas a ƙasar, sai dai manazarta na cewa Ɗangote, na da damar raba hajarsa sakamakon sakin mara da aka yi wa ɓangaren kasuwanci a ƙarƙashin dokokin Najeriya. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi....
A cikin shirin Tambaya da amsa na wannan mako,Nasiru Sani ya mika tambayoyi masu saurare ga masana,daga cikin tambayoyi da aka aiko ,mai saurare ya bukaci karin haske dangane da batun rufe sararin samaniya. A yi saurare lafiya.................
Kamar yadda aka saba kowacce ranar Juma'a mukan baku dama don bayyana mana ra'ayoyinku game da batutuwa daban-daban da suka shafin fannonin rayuwa daban-daban don kira ga masu ruwa da tsaki da su kawo ɗauki. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu Garba
Masu ruwa da tsaki kan sha'anin Shari'a a Najeriya sun sabunta ƙorafin da suke yi a kan matsalar jinkiri maras tushe, wajen gudanar da shara'o'i ko yanke hukunci kan waɗanda ake tuhuma da aikata manyan laifuka, musamman na ta'addanci. Ƙorafin ya sake bijirowa ne la'akari da yadda cikin ƙanƙanin lokaci mahukuntan ƙasar Finland suka zartas da hukunci kan Simon Ekpa, wani mai iƙirarin neman kafa ƙasar Biafra a Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hirar....
Kotun ƙasar Finland ta ɗaure Simon Ekpa mai fafutukar kafa ballewar Biafra daga Najeriya shekaru 6 a gidan yari, saboda samun sa da laifufukan ta'addanci. Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin ake ci gaba da tsare ɗaruruwan mutane a gidajen yarin Najeriya bisa zargin aikata ta'addanci, amma kotuna sun gaza hukuntar da su. Shin ko me za ku ce a game da wannan hukunci da kotun ƙasar Finland ta yanke? Meye ra'ayoyinku a game da gazawar kotunan Najeriya wajen hukunta waɗanda ake tuhuma da aikata irin waɗannan laifuka a cikin gida? Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu
Hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka a taron da suka yi a birinin Abujan Najeriya, sun ƙuduri aniyar haɗa gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta. Wannan taro dai ya samu halartar wakilan ƙasashe sama da 50, waɗanda suka yi imani da cewa la'akari da girman matsalar, akwai buƙatar ƙasashen su yi aiki a tare don tunkarar ta. Shin ko meye ra'ayoyinku a game da wannan yunƙuri na ƙasashen Afirka? Waɗannan shawarwari za ku bayar domin samun nasarar wannan fata? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
A jamhuriyar Nijar, dubban mutane ne suka rasa ayyukansu yayin da ɗimbin ƴan gudun hijira suka daina samun tallafi, bayan da mahukunta suka kori mafi yawan ƙungiyoyin agaji daga gudanar da ayyukansu a cikin ƙasar. Bayan korar waɗannan ƙungiyoyi da ke taimaka wa ƴan gudun hijira, a mafi yawan yankuna har yanzu gwamnatin ta gaza samar da tsarin da zai maye gurbin waɗannan ƙungiyoyi don agaza wa jama'a. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin....
Shirin Lafiya Jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakin gwamnatin Najeriya na rage farashin wankin ƙoda ko kuma Dialysis, daga Naira dubu Hamsin ko fiye da haka zuwa Naira dubu 12 kacal. Tuni wannan mataki ya Faranta ran ɗimbin ƴan Najeriya musamman waɗanda ke da ƴan uwan masu fama da wannan lalura da ke da matuƙar cin kuɗi, kodayake murna ta fara komawa jiki, bayan cikakken bayani kan wannan tagomashi ya nuna cewa babu kaso mai yawa na jihohin Arewa maso yammacin Najeriya, duk kuwa da yadda suke da ɗimbin masu fama da wannan lalura. Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin....
„Společnost se uzdraví skrze uzdravení jedinců – a v tom je obrovská naděje a potenciál pro celospolečenskou změnu. Tedy ne, že přijmu nějakou jinou ideologii, ale že si uvědomím sám sebe. A to je zpátky individuace nebo sebepoznání, rozpomenutí se sám na sebe,“ říká terapeut Daniel Paulus v rozhovoru pro pořad Kupředu do minulosti. 3. díl, 22.08.2025, www.RadioUniversum.cz
Yau Juma'a rana ce da mukan baiwa masu saurarenmu damar tofa albarkacin bakinsu a cikin shirinmu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Danna alamar saurare domin jin cikaken shirin tare da Nasiru Sani
A Najeriya muhawara ta ɓarke game da buƙatar sulhu da ƴan ta'adda maimakon amfani da ƙarfin Soji, kodayake an samu mabanbantan ra'ayoyi daga ɓangaren masana a fannin na tsaro lura da yadda suka ce irin wannan sulhu ya gaza amfanarwa a yankuna da dama duk da cewa anga alfanunsa a wasu yankunan. Yaya kuke kallon wannan batu? Shin kuna ganin sulhu ko kuwa amfani da ƙarfin soji shi ne mafi a'ala wajen yaƙi matsalolin tsaron Najeriyar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkaci bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza....
Lura da yadda jama'a ke ɗari-ɗari a game da kayan abincin da aka sauya wa ƙwayoyin halitta da ake kira GMO, wannan ya sa mahukunta a Najeriya ke neman yin amfani da malaman addini domin gamsar da jama'a su rungumi irin wannan abinci. Abin neman sani a nan shi ne, shin ko kun fahinci abin da ake kira GMO? Ko a shirye ku ke domin karɓar nau'in abincin da aka canza wa ƙwayoyin halitta? Anya yin amfani da malaman addini zai sa jama'a su amince da shi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Mai Bai wa Shugaban Najeriya Shawara kan Sha'anin Tsaro Nura Ribaɗo ya tabbatar da kama jagororin ƙungiyar Ansaru da ake kira Ƴan Mahmuda su biyu, waɗanda suka jima suna addabar yankunan ƙasar. Ana dai bayyana wannan ƙungiya a matsayin babbar barazana ga matsalar tsaron ƙasar, saboda alaƙarta kai-tsaye da Alqa'ida. Shin ko wane sauyi wannan kame zai samar ta fannin tsaro a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Yau take ranar bayyana ra'ayoyinku kan batutuwa da suke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, zamantewa da sauran abubuwan daban daban na rayuwa. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyin...
Lauyoyi a Jamhuriyar Nijar sun tsunduma yajin aikin kwanaki biyu daga yau Alhamis, domin nuna rashin amincewa da rusa ƙungiyoyin alƙalai da sauran ma'aikatan shari'a da gwamnatin ƙasar ta yi. Kafin rusa waɗannan ƙungiyoyi, tuni aka rusa ƙungiyoyin jami'an kare gandun daji da na kwastam da kuma illahirin jam'iyyun siyasar ƙasar. Shin, ko me za ku ce a game da wannan mataki na gwamnatin Nijar ta ɗauka? A irin wannan yanayi, ko meye makomar ƴancin gudanar da ƙungiyoyi a ƙasar? Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi...
Bankin Duniya ya amince ya ranta wa Najeriya dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 460 don tallafa wa mutanen da suka ƙaurace wa matsugunansu saboda matsaloli a sassa daban daban na Arewacin ƙasar. Yanzu haka akwai mutane sama da milyan 3 da rabi da ke rayuwa a wannan yanayi, kuma mafi yawansu sun dogara da tallafi ne domin rayuwa. Shin ko waɗanne matakai suka kamata a ɗauka don tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen ta hanyoyin da suka dace? Sai ku bayyana ra'ayoyinku a lambarmu ta Whatsapp da kuma shafinmu na Facebook.
Kusan a kowacce shekara, dai-dai wannan lokaci ne ake samun faruwar ambaliya sakamakon saukar ruwan sama mai yawa da ke haddasa asarar rayuka da kuma dukiyoyi masu tarin yawa. A daidai wannan lokaci, ko wane hali ake ciki a yankunanku dangane da batun ambaliya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a wannan rana. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace ilahirin kamfanonin haƙo zinare tare da shelanta cewa sun zama mallakin ƙasar, yayin da a ɗaya ɓangare ta hana fitar da duk wani nau'in dutse mai ƙima zuwa ƙetare sai tare da izinin hukuma. Hakan na zuwa ne watanni bayan ta ƙwace kamfanonin haƙo uranium matsayin mallakin ƙasar. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
In this powerful episode of Conversations with Rich Bennett, Gavin Masumiya shares his emotional journey from a shy, self-conscious child to a confident speaker, coach, and musical artist. Through freestyle rap, public speaking, and deeply personal songwriting—especially after the loss of his mother—Gavin discovered the healing power of voice and vulnerability. Listeners will be inspired by his resilience, creativity, and unique approach to coaching others into authentic expression. Guest Bio: Gavin Masumiya is a voice coach, speaker, and freestyle rapper who helps people unlock their authentic expression through the power of voice. A former behavioral therapist and English teacher in Japan, Gavin now works with clients around the world to overcome self-doubt and step into their truth. Following the passing of his mother, he transformed grief into artistic healing through songwriting, releasing tracks under his artist name, Masu. Gavin also facilitates coaching programs, mentors aspiring speakers, and contributes to purpose-driven organizations that align with his mission of emotional transformation. Main Topics: · Gavin's journey from shy child to confident speaker and coach· Discovering freestyle rap as a tool for healing and self-expression· Using creativity and music to process grief and honor his mother· Launching a music career under the name Masu· Creating “legacy appointments” through recorded conversations· Coaching professionals to unleash their authentic voice· The impact of mastermind groups and the power of asking for help· Future ambitions, including a TEDx Talk and potential book Resources mentioned: · Michael's website: https://www.gavinmasumiya.com/· Supporter: Real Life Prosthetics· Supporter: Full Circle Boards· Supporter: Sincerely Sawyer PhotographySend us a textSupport the showRate & Review on Apple Podcasts Follow the Conversations with Rich Bennett podcast on Social Media:Facebook – Conversations with Rich Bennett Facebook Group (Join the conversation) – Conversations with Rich Bennett podcast group | FacebookTwitter – Conversations with Rich Bennett Instagram – @conversationswithrichbennettTikTok – CWRB (@conversationsrichbennett) | TikTok Sponsors, Affiliates, and ways we pay the bills:Hosted on BuzzsproutRocketbookSquadCast Contests & Giveaways Subscribe by Email
To bylo téma mezinárodní konference, na kterou vás zavedeme. - Mohou být někteří lidé závislí na sportu? Jaké problémy jim může způsobovat? - Připomínají dětskou stavebnici, ale ochrání kritickou infrastrukturu nebo úřady před teroristickými útoky. To je nový typ protibalistického krytu, který lze složit libovolného tvaru. Vyvinuli ho čeští vědci. Moderuje Daniela Vrbová.
To bylo téma mezinárodní konference, na kterou vás zavedeme. - Mohou být někteří lidé závislí na sportu? Jaké problémy jim může způsobovat? - Připomínají dětskou stavebnici, ale ochrání kritickou infrastrukturu nebo úřady před teroristickými útoky. To je nový typ protibalistického krytu, který lze složit libovolného tvaru. Vyvinuli ho čeští vědci. Moderuje Daniela Vrbová.