Rai dangin goro ne; ruwa ake ba shi. Idan rayuwa ta yi nauyi xan Adam yana buqatar hutu. Idan wahala ta yi yawa ana buqatar sauqi. Wannan littafi an yi shi ne don ya zama “Abokin Fira” ga Maigida da iyalinsa a matsayin taxi da nishaxi da ake yi kafin shiga bacci. Haka kuma ana son ya taimaki matafiyi wanda yake zaune a cikin qosawa yana jiran isowar mota ko saukar jirgin sama, ko zuwan wani baqo, ko kiran likita. Ko kuma yake zaune a cikin mota direba yana keta daji da shi, ko a cikin jirgin sama yana keta sararin samaniya, ko dai wani yanayi makamancin haka. Littafin yana dacewa a karanta shi
Mu daina kallon mutanen da ke qarqashin mu basu da qima ko hikima
Ka da ka raina mutum, kowa na da hikima da fahita da Allah Ya bashi
Duk hali da mutum ya samu kan sa ya gode ma Allah do Allah na da hikimar duk abin da ya yi.
Duniya duk abin da za ka yi, ka tuna gaba.
Lallai wannan labari akwai abin dariya a cikin sa
Idan da zamu laƙanci ɗabi'ar haƙuri, to da lallai mun ci nasara a duk wata himma ko huɓɓasa da zamu yi. Saurara kuji misalin irin ribar da haƙuri ke kawowa.
Duk yadda za ayi, mu guje ma sharri don ko badaɗe ko ba jima, yana biye da mai yin sa kamar kare.
Zina cuta ce mummuna wacce tabon ta ma kawai, abin kyama ne.
Mu riqa kyautata wa junan mu zato don munana zato ba halin kirki ba ne.
Duk mugu, Allaah baya barin sa. Mu guje wa mugunta da duk wani nau'in zalunci
Ilmi ba ruwan sa da shekaru. Dan hakin da ka raina, shi ke tsone maka ido.
Allaah Mai Iko, idan ka ga Allaah Ya hana ka ko Ya jinkirta maka biyan buqata, wallaahi akwai dalili... Saurari watai irin baiwa da Allaah Ya ba wa wani bawan Sa ta hanyar da bai zai taba tunanin cewa taimaka masa aka yi ba.
Wannan maihifin ya karantar da dansa wasu darasi ne masu muhimmanci ta hanyar lurarwa. Saurara ku ji.
Shaidan na cin galaba akan wanda baya iya hadiye fushin sa fa.
Gaskiya ya kamata mutum ya kware akan iya magana da mu'amala
Ikon Allaah, wa'azi fa iyawa ne. Saurari uslubin da'awa da mata tayi wa mijin ta har ya dena shan sigari.
Allaah Sarki mata, maza, ku tausaya wa matan ku masu kishi mana.
Iya zaman Aure da magance matsalolin Aure, darasi ne da ya kamata a koyar.
Duniya fa ba taru duk an zama daya ba. Har yanzu ana samun mutanen kirki.
Ikon Allaah, shi kuma wannan ko me akayi ma sa da har takai ga marin liman?
Ikon Allaah... Ka ji yanda Allaah Ya kama azzalumi...
Wanda ke son sanin wahalalle, lallai na da bukatan sauraron wannan labari.
Allaah Mai kyauta ta yanda Ya ga dama. Ku saurari wannan ku sha mamaki.
Idan zakayi magana, ka san abin da zaka fada, idan ba haka ba, to fa lallai kar ka ji haushi amsar da za a ba ka.
Rayuwar wasu abin tausayi ne amma mai hankali ke gane haka don ba su roqo sannan mutane gama gari, suna mu su kallon banza.
Wato Shaidan babban Maqiyin mu ne, amma kash, sai ka ga mutane da yawa suna biye ma waswasin shi. Ku ji wannan labari
Kun taba sanin labarin Gamon Katar kuwa? Ku dai saurari wannan