Podcasts about cikin

  • 22PODCASTS
  • 181EPISODES
  • 15mAVG DURATION
  • 1EPISODE EVERY OTHER WEEK
  • Nov 1, 2025LATEST

POPULARITY

20172018201920202021202220232024


Best podcasts about cikin

Latest podcast episodes about cikin

Mu Zagaya Duniya
Bitar muhimmn labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Nov 1, 2025 20:09


A cikin wannan shiri tare da Nura Ado Suleiman, kamar kowanne mako ya kan yi bita ne kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka faru a makon da muke shirin yin bankwana da shi. Cikin waɗannan labarai kuwa akwai yadda aka sanar da sakamakon zaɓen Kamaru wanda ya kai ga ɓarkewar zanga-zangar adawa da wannan sakamako da ke nuna shugaba Paul Biya mai shekaru 92 a matsayin wanda ya yi nasara da fiye da kashi 53 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa. Ku latsa alamar sauti don auraron cikakken shirin.

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu saurare kan janye wasu daga cikin jerin mutanen da Tinubu ya yi wa afuwa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Oct 30, 2025 10:38


Wataƙila sakamakon matsin lamba daga al'umma, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake bitar afuwar da ya yi wa mutane sama da 170 da ke ɗaure a gidajen yari saboda laifukan aikata kisan kai, fataucin miyagun ƙwayoyi da dai sauransu. Shin me za ku ce dangane da wannan sabon mataki na shugaba Tinubu da ke tabbatar da cewa mafi yawan waɗanda aka yi wa afuwar a farko wannan wata, a yanzu za su ci gaba da kasancewa a gidan yari? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai cikin shirin Ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan rana. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

Lafiya Jari ce
Yadda Cholera ta kashe mutane kusan dubu 5 a sassan Najeriya cikin shekaru 5

Lafiya Jari ce

Play Episode Listen Later Oct 13, 2025 10:26


Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan yawaitar samun cutar Kwalara ko kuma amai da gudawa  a sassan Najeriya, cutar da a baya-bayan nan ta kashe ɗimbin al'umma a ƙasar mafi yawan jama'a a Nahiyar Afrika. Wasu alƙaluma da hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasar NCDC ta fitar sun nuna cewa mutane kimanin dubu biyar (5,000) cutar ta kwalara ta halaka a sassan Najeriyar daga shekarar 2020 zuwa 2025 da muke ciki. Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu.............

Tambaya da Amsa
Wasu daga cikin tambayoyi masu sauraren Rfi a shirin Tambaya da amsa

Tambaya da Amsa

Play Episode Listen Later Sep 6, 2025 20:11


A cikin shirin Tambaya da amsa na wannan mako,Nasiru Sani ya mika tambayoyi masu saurare ga masana,daga cikin tambayoyi da aka aiko ,mai saurare ya bukaci karin haske dangane da batun rufe sararin samaniya. A yi saurare lafiya.................

Mu Zagaya Duniya
Najeriya ta sha alwashin shigar da ƴan ƙasar aƙalla miliyan 44 cikin tsarin inshorar lafiya

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Sep 6, 2025 19:54


Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin shigar da ƴan ƙasar aƙalla miliyan 44 cikin tsarin inshorar lafiya nan da shekara ta 2030,Iftila'in zabtarewar ƙasa ya lakume rayukan mutane fiye da dubu 1 a Sudan,wasu kenan daga cikin manyan labarun makon jiya da Nura Ado Suleiman zai kawo muku a cikin shirin Mu zagaya Duniya.

Bakonmu a Yau
Farfesa Balarabe Sani Garko kan rage farashin wanke ƙoda a wasu asibitocin Najeriya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Aug 20, 2025 3:34


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a faɗin ƙasar. Daniel Bwala, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan Bayanan da suka shafi tsare-tsaren gwamnati ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntansa na X, inda ya ce matakin zai sauƙaƙa wa dubban marasa lafiya masu fama da ciwon ƙoda. An fara aiwatar da wannan mataki a manyan asibitoci kamar FMC Ebute-Metta da ke Lagos da FMC da ke Jabi a Abuja da UCH Ibadan da FMC Owerri da UMTH Maiduguri, yayin da za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara domin samun damar amfani da su a duk faɗin ƙasar. Sai dai da safiyar Laraba bayan rahotannin RFI, Gwamnatin Najeriya ta ɗan daidaita jerin sunayen manyan asibitocin ƙasar da za su ci gajiyar sabon tallafin domin sauƙaƙawa majinyta wanke ƙoda, inda aka ƙara asibitin koyerwa na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano. Cikin sanarwar da ma'aikatar lafiyar ƙasar ta fitar, ta ce za'a ci gaba da ƙara wasu asibitocin ne dama sannu a hankali, amma ba mantawa da wani sashin ƙasar akayi ba. Ga asibitocin da za su amfana da sabon ragin farashin ƙudin wankin ƙoda 1. Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano 2. Asibitin koyarwa na Maiduguri 3. Asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi 4. Asibitin koyarwa na Jos 5- Babban Asibitin tarayya da ke Abuja 6. Cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Ebute Metta a Lagos 7. Asibitin jami'ar Ibadan 8. Asibitin koyarwa na Benin. 9.Cibiyar lafiya ta tarayya da ke Yenagoa a Bayelsa 10.Asibitin koyarwa ta Owerri da ke Imo 11. Asibitin koyerwa na Abakaliki da ke Ebonyi.

AWR in Hausa - Adabin Duniya Rediyo

HIDIMAR MATA A CIKIN LITTAFI MAI TSARKI

AWR Hausa - هَوْسَ
MATA CIKIN HIDIMA

AWR Hausa - هَوْسَ

Play Episode Listen Later Aug 13, 2025 29:00


HIDIMAR MATA A CIKIN LITTAFI MAI TSARKI

Wasanni
Yadda shugaban Najeriya ya tarbi tawagar Super Falcons bayan lashe gasar WAFCON

Wasanni

Play Episode Listen Later Aug 4, 2025 9:43


Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan karramawar da gwamnatin Najeriya ta yi wa tawagar Super Falcons na lashe gasar WAFCON. A makon da ta gabata ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karrama ƴan wasan tawagar ƙungiyar kwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Falcons, bayan nasarar lashe kofin WAFCON karo na 10 daga cikin 13 da aka yi. Cikin kyautukan da gwamnati ta baiwa waɗannan ƴan wasa akwai lambar girmamawa na ƙasa wato OON da shugaban Tinubu ya baiwa dukkan ƴan wasan da masu horar dasu, hakazalika kowacce ƴar wasa ta samu dalan amurka dubu 100, da kuma karin naira miliyan goma-goma daga ƙungiyar gwamnonin Najeriya. Tuni dai shugaban hukumar wasani a Najeriya Shehu Dikko ya yaba da wannan nasarar da kuma irin karramawar da shugaban ƙasar ya yiwa ƴan wasan. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.

Muhallinka Rayuwarka
Samun ƙaruwar yin noman cikin gida musamman a arewacin Najeriya

Muhallinka Rayuwarka

Play Episode Listen Later Jul 13, 2025 20:00


Shirin Muhallinka Rayuwa na wannan mako yayi duba ne kan yadda ake ƙara samun ƙaruwar yin noman cikin gida musamman a yankin Arewacin Najeriya, yankin da hukumomi suka dade suna kiraye kiraye kan a rungumi harkar noman. Za mu kuma duba yadda hakan zai taimaka wa wadata ƙasa da abinci da kuma fa'idarsa ga muhalli.

no man za gida najeriya cikin
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu saurare kan mutanen da 'yanbindiga suka kashe a cikin watanni 6

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Jul 9, 2025 10:12


A Najeriya, wasu alƙaluman hukumar kare hakkin ɗan adam ta ƙasar sun ce adadin mutanen da ƴanbindiga suka kashe a cikin watanni shida na farkon wannan shekarar ya zarce na ilahirin shekarar da ta gabata, inda a watan da ya gabata kawai mutane  606 ne masu ɗauke da makamai suka halaka. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...

suka masu najeriya cikin
Lafiya Jari ce
Uku cikin Ma'aurata goma a Najeriya na fama da matsalar haihuwa - Rahoto

Lafiya Jari ce

Play Episode Listen Later Jun 30, 2025 9:53


Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani binciken ƙwararru da ke nuna cewa duk 3 cikin ma'aurata 10 a Najeriya na fama da matsalar haihuwa, alƙaluman da ke nuna tsanantar matsalar a wannan ƙasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika.

afrika fama goma najeriya cikin
Mu Zagaya Duniya
Bitar labaran mako: Hatsarin jirgin India da harin da Isra'ila ta kai Iran

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Jun 14, 2025 19:38


Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman, ya yi bitar wasu daga cikin labaran da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi, masamman haɗarin jirgin saman da ya yi sanadin salwantar rayukan mutane kusan 300 a India sai kuma munanan hare-haren da Isra'ila ta kai Teheran babban birnin ƙasar Iran. Cikin makon da ya ƙare ne kuma Najeriya ta yi bikin ranar Dimokaradiyya (Tsarin mulkin da ƙasar ta shafe shekaru 26 tana ƙarƙashinsa ba tare da katsewa ba).shirin zai waiwayi bayanan da masana suka yi wajen auna cigaba da kuma matsalolin Najeriyar a Sikeli. shirin ya kuma leƙa Masar don jin yadda jami'an tsaro suka tasa ƙeyar ‘yan Sudan da ke neman mafakar gudun hijira zuwa hanyar Libya.

Bakonmu a Yau
Ƙungiyar Amnesty ta zargi sojojin Najeriya da kashe ƴan-sa-kai a Zamfara

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Jun 3, 2025 3:18


Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta yi zargin cewa jirgin sojin saman ƙasar ya yi ruwan bamai-bamai kan jami'an sakai tare da kashe akalla 20 da jikkata wasu da dama a ƙauyukan Maraya da Wabi da ke ƙaramar hukumar Maru na jihar Zamfara. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar jiya Litinin, ta ce lamarin kai tsaye ya shafi jami'an sakai da suka taru domin tunkarar ƴan bindiga da suka kai hare-hare a ƙauyukan nasu ranar Asabar.  A tattaunawarsa da Ahmad Abba, Daraktan Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sunusi, ya fara da bayani kan yadda lamarin ya auku.

Tambaya da Amsa
Waɗanne dalilai ne ke hana ɗan Adam samu isasshen barci cikin dare

Tambaya da Amsa

Play Episode Listen Later May 31, 2025 20:09


A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan wasu dalilai  dake haifar da rashin samun isasshen barci a cikin  dare. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson, don jin sauran tambayoyin da kwararru suka amsa a wannan mako.

dare samu cikin micheal kuduson
Mu Zagaya Duniya
Ma'aikata a sassan duniya sun gudanar da bikin ranarsu a cikin mumunan yanayi

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later May 3, 2025 20:02


Shirin  Mu Zagaya Duniya  na wanan makon tareda Nura Ado Suleimane, ya yi duba ne kan  mai'aikata a sassan Duniya suka gudanar da bikin rana ta musamman da aka ware musu a daidai lokacin da wani adadi da dama daga cikinsu ke fuskantar ƙalubale iri-iri.  Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......

Wasanni
Tasirin masu horarwa na cikin gida wajen ɗaga likafar tawagogin ƙasashen Afirka

Wasanni

Play Episode Listen Later Mar 24, 2025 9:59


Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya mayar da hankali kan tasirin masu horarwa na cikin gida a ci gaban ƙwallon ƙafar nahiyar Afirka. A baya-bayan nan ƙasashen na nahiyar Afirka sun mayar da hankali wajen ɗaukar masu horarwa na cikin gida tun bayan rawar da Morocco ta taka a gasar cin kofin Duniya ta 2022 karon farko da aka ga irin hakan daga wata ƙasa a nahiyar ta Afrika.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Muhallinka Rayuwarka
Yadda masu aiki a cikin teku ke rayuwa har ma da yadda za a yi amfani da teku

Muhallinka Rayuwarka

Play Episode Listen Later Mar 9, 2025 20:00


Shirin Muhallinka Rayuwarka na wanan makon tareda Micheal Kuduson wanda  kashi  na uku ne ya dora akan kashi na biyu wanda ya gabata a makon jiya. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata shirin ya mayar da hankali ne kacokam akan yadda masu aiki a cikin teku ke rayuwa har ma da yadda za a yi amfani da teku, tafki, rafi ko kogi domin gudanar da harkokin noma da kuma kyautatawar muhalli.

idan yadda masu aiki najeriya cikin micheal kuduson
Kasuwanci
Yadda ake samun sauƙin farashin kayayyakin masarufi a sassan Najeriya

Kasuwanci

Play Episode Listen Later Feb 26, 2025 10:00


A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda ake kara samun saukar farashin kayan masarufi a sassan Najeriya. Bayanai da muka tattaro na nuni da cewa yawancin kayayyakin da farashin su ya sauka na amfanin gona ne da kuma na kamfanonin kasashen waje, amma na kamfanonin cikin gida har yanzu suna nan a yadda suke.A makon jiya Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce an samu sauƙin matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a ƙasar da a ƙalla kashi 10.3.Cikin sanarwar da ta fitar a Talatar wancan makon, hukumar ta NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriyar ya sauka ne zuwa kashi 24.4 a watan Janairun wannan shekara, saɓanin kashi 34.8 da aka gani a watan Disambar shekarar bara ta 2024.

nbs yadda sassan najeriya cikin hukumar
Lafiya Jari ce
Tiyatar fitar da jarirai daga cikin Uwa na yawaita a sassan Najeriya

Lafiya Jari ce

Play Episode Listen Later Feb 24, 2025 10:15


Shirin Lafiya jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda fasahar cire ɗa ta hanyar CS ke taimakawa wajen ceto rayukan uwa da ɗa da nufin rage asarar rayukan da ake fuskanta a lokacin haihuwa. Duk da cewa haihuwa 3 cikin 100 ce kaɗai ake yi ta hanyar tiyata ko kuma CS a Najeriya bisa alƙaluman 2019, amma a baya-bayan nan ana ganin yawaitar matan da ake yiwa CS gabanin haihuwa kama daga nau'in matan da basa zuwa asibiti da kuma mata masu shekaru da yawa ko waɗanda suka yi haihuwa da dama, duk dai a ƙoƙarin kange yawaitar mace-macen mata ko kuma asarar jariran da ake gani a sassan ƙasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

Bakonmu a Yau
Tattaunawa da Musa Idris kan saukar farashin kayayyaki a Najeriya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Feb 19, 2025 3:29


Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce an samu sauƙin matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a ƙasar da a ƙalla kashi 10.3. Cikin sanarwar da ta fitar a jiya Talata, hukumar NBS ɗin ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriyar ya sauka zuwa kashi 24.4 a watan Janairun wannan shekara, saɓanin kashi 34.8 a watan Disambar shekarar bara ta 2024. Domin jin halin da ake ciki....la'akari da wannan rahoto, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Musa Idris daga jihar Jigawa, magidanci kuma ɗan kasuwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..........

ku domin nbs jigawa najeriya cikin talata hukumar
Mu Zagaya Duniya
Wasu daga cikin labarun mako a cikin shirin Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Feb 1, 2025 19:52


Daga cikin labarun da shirin ya sake waiwaya a wannan makon, akwai cikar wa'adin ficewar kasshen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar daga cikin ƙungiyar kasashen yammacin Afirka CCOWAS, da kuma abinda ya biyo baya.

Mu Zagaya Duniya
Wasu daga cikin labarun mako a cikin shirin Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Jan 25, 2025 20:04


Cikin makon da ya ƙare, Zaratan sojin Najeriya dake fatattakar ‘yan ta'adda a yankin arewa maso yammacin ƙasar, suka samu nasarar kashe kwamandojin riƙaƙken ɗan fashin dajin nan Bello Turji wanda ya zame wa jama'a Batoyi. Jami'in kula da watsa labaran rundunar ta ‘Operation Fansan Yamma' Lafatanar Kanar Abubakar Abdullahi yayi mana ƙarin bayani kan nasarorin da suka samu.

Bakonmu a Yau
Isah Sunusi kan hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza da ke ci gaba da lakume rayuka

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Jan 1, 2025 3:18


Ƙungiyar kare hakkin bil Adama ta ‘Amnesty International', ta fitar da sakamakon binciken da ta gudanar akan zarge-zargen da ake yi wa Isra'ila na aikata kisan ƙare dangi a Gaza. Cikin rahoton wanda aka fitar da shi a birnin Kano dake arewacin Najeriya, Amnesty tace Isra'ila ta kashe mutane sama da dubu 40, ciki harda kananan yara dubu 13 a cikin shekara guda.Wakilinmu na Kanon Abubakar Abdulƙadir Ɗangambo ta tattauna da Daraktan kungiyar ta Amnesty a Najeriya Isa Sunusi.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

Bakonmu a Yau
Amb Abubakar Cika kan mataki AES na zaman rundunonin sojinsu cikin shirin ko ta kwana

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Dec 24, 2024 3:23


Ƙasashen AES da suka haɗa da Nijar, Mali da kuma Burkina Faso sun yi watsi da ƙarin wa'adin watanni shidda da ECOWAS ta yi musu a makon jiya, kan lokacin ficewarsu daga cikin ƙungiyar a hukumance, rangwamen da zai fara aiki a watan Janairun dake tafe. Cikin sanarwar da suka fitar, ƙasashen uku sun sanar da baiwa rundunonin sojinsu umarnin zama cikin shirin kar ta kwana. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Ambassada Abubakar Cika tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu..................

Bakonmu a Yau
Hajiya Hannatu Musawa kan sanya bikin hawan Daba na Kano cikin manyan al'adun duniya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Dec 18, 2024 3:30


Hukumar da ke kula da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta UNESCO ta damƙawa Najeriya takaddar shaidar sanya bikin hawan Daba na Kano cikin manyan al'adun duniya masu matukar tasiri. Jim kaɗan bayan kammala miƙa shaidar wakilinmu a Abuja Isma'il Karatu Abdullahi ya tattanna da ministar al'adu ta Najeriya Hajiya Hannatu Musawa kan tasirin da wannan zai yi wa ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar ta su......

unesco ku bikin kano sanya daba duniya najeriya cikin hukumar majalisar
Al'adun Gargajiya
UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundinta na al'adun duniya

Al'adun Gargajiya

Play Episode Listen Later Dec 10, 2024 10:35


Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al'adun duniya.Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al'adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa.  Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........

unesco ku kano gado sanya daba duniya dabar sallah babba najeriya cikin masana majalisar abdoulaye issa
Al'adun Gargajiya
Gushewar al'adar tatsuniya a cikin al'ummar Hausawa

Al'adun Gargajiya

Play Episode Listen Later Nov 26, 2024 10:11


Shirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna dangene da gushewar a'adar tatsuniya wadda ke zama hanyar da al'ummar Hausawa ke amfani da ita wajen  ilmantarwa, fadakarwa da kuma tarbiyantar da yara ta hanyar shirya kagaggun labarai masu kunshe da darussa.

gado najeriya cikin hausawa abdoulaye issa
Mu Zagaya Duniya
Wasu daga cikin muhimman lamuran da suka faru a makon da ya ƙare

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Nov 23, 2024 19:59


Masu sauraro Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin sabon shirin Mu Zagaya Duniya, wanda ke waiwayar wasu daga cikin muhimman lamuran da suka faru a makon da ya ƙare.......Akwai tsokaci ko kuma martani daga ɓangarori daban daban  dangane da umarnin kotun duniya ta ICC na bada sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa da kuma ɗaya daga cikin Jagororin  Mayakan Hamas.

Al'adun Gargajiya
Masarautar Keffi a cikin shirin Al'adun mu

Al'adun Gargajiya

Play Episode Listen Later Nov 17, 2024 10:00


Yau shekaru tara kenan da zama Sarkin masarautar keffi da mai martaba Dr alhaji shehu usman chindo yamusa,bayan      rasuwar mahaifinsa mai martaba alhaji Chindo Yamusa na uku 3.A cikin shirin al'adu za ku ji tarihin Sarkin na Keffi.

Lafiya Jari ce
Ƙuncin rayuwa na jefa ɗimbin ƴan Najeriya cikin tsananin damuwa - Rahoto

Lafiya Jari ce

Play Episode Listen Later Oct 28, 2024 9:54


Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan matsalar damuwa mai dankwafarwa ko tsananin damuwa da ake kira Depression, cutar da ake ganin ta'azzararta a baya-bayan nan tsakanin ƙasashe masu tasowa musamman waɗanda ke fama da matsi ko kuma ƙuncin rayuwa. Wasu bayanan ƙwararru yayin bikin ranar lafiyar ƙwaƙwalwa da ya gudana a farkon watan nan, ya nuna yadda matsi da ƙunchin rayuwa ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya a tsananin damuwar ko kuma damuwa mai dankwafarwa, matsalar da likitoci suka yi gargaɗin cewa ka iya kaiwa ga taɓin ƙwaƙwalwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........

Tambaya da Amsa
Amsoshin wasu daga cikin tambayoyi masu sauraren Rfi

Tambaya da Amsa

Play Episode Listen Later Oct 26, 2024 20:00


A cikin wannan shirin ,Nasir Sani ya tattaro tambayoyin ku masu sauraren Rfi hausa,wandada a cikin wannan shirin za ku ji amsoshin wasu daga cikin su.Masu saurare sun bukaci samun karin haske dangane da yarjejeniya a bangaren da ya shafi yankinn  Neja Delta da Gwamnatin Najeriya.Shirin Tambaya da amsa na zuwa maku ne a duk karshen mako daga sashen hausa na Rfi.

Mu Zagaya Duniya
Bitar wasu daga cikin muhimman labarai na al'amuran da suka wakana a makon da ya ƙare

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Oct 19, 2024 19:37


Yayin da ‘Yan Najeriya da dama ke jin jiki kan matsin rayuwar da suka shiga tun bayan janye tallafin man fetur da kuma fara aiwatar da wasu matakai da sabuwar gwamnatin ƙasar  ta yi, Bankin Duniya yayi gargaɗin cewar, matsalar da ake ciki samin taɓi ce, muddin aka kuskura aka janye ko dakatar da manufofin tattalin arziƙin da shugaba Tinubu ke aiwatarwa.

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur da kashi 15 cikin 100

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Oct 11, 2024 10:34


Najeriya ta yi sabon ƙarin farashin mai da akalla kashi 15%, wanda kuma shi ne karo na 4 a cikin watanni 16 da shugaba Bola Tinubu ya shafe kan karagar mulki. Babu dai wani dalili da kamfanin NNPCL da ke matsayin wakilin gwamnati a harkar mai ya bayar dangane da wannan farashi, illa kawai jama'a sun gan shi ne haka kwatsam.Kan wannan batu shirin 'Ra'ayoyin Masu Sauraro' na ranar Alhamis ɗin nan ya bayar da  damar tattaunawa akai.

ra sake babu kashi bola tinubu najeriya cikin alhamis
AWR in Hausa - Adabin Duniya Rediyo
SATA A CIKIN DANGANTAKA

AWR in Hausa - Adabin Duniya Rediyo

Play Episode Listen Later Oct 9, 2024 29:00


MU KOMA ZEREFAT

sata cikin
AWR Hausa - هَوْسَ
SATA A CIKIN DANGANTAKA

AWR Hausa - هَوْسَ

Play Episode Listen Later Oct 9, 2024 29:00


MU KOMA ZEREFAT

sata cikin
Bakonmu a Yau
Dokta Abdulhakim Garba Funtua kan hare-haren Isra'ila a Lebanon

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Sep 24, 2024 3:35


Kasashen duniya sun fara mayar da martani dangane da kazamin hare haren da Isra'ila ke kai wa a yankin kudancin Lebanon wanda a jiya kawai ya kai ga hallaka mutane kusan 300. Cikin wadanda suka bayyana damuwa da yadda yakin Isra'ilar ke fadada har da Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres. Dangane da wannan yaki Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua na Babbar Kwalejin Fasaha dake Kaduna, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

lebanon isra antonio guterres haren kaduna garba cikin majalisar dinkin duniya majalisar bashir ibrahim idris
Bakonmu a Yau
Wasu daga cikin muhimman labarai da jaridar Aminiya ta wallafa a wannan mako

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Sep 20, 2024 3:36


Kamar dai kowane mako, a yau juma'a ma jaridar Aminiya da ake wallafa ta a Najeriya ta sake fitowa ɗauke da dimbin labarai da suka shafi fannoni daban nan na rayuwa. Kuma Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Muƙaddashin Editan jaridar Muhammad Amin Ahmed domin jin karin bayani dangane da labaran da suke ɗauke da su a wannan karo. domin sauraron cikakken shirin, a latsa alamar sauti.

Bakonmu a Yau
Kwamrade Audu Titus Amba game da hare-hare ta'addanci kan dalibai da makarantu

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Sep 10, 2024 3:23


Majalisar Ɗinkin Duniya ta koka kan yadda aka samu ƙaruwar kashi 20 cikin 100 kan hare-haren da ake kai wa makarantu da sauran cibiyoyin ilimi da kuma ɗalibai a tsakanin shekarun 2022 zuwa 2023 da ta gabata, musamman a ƙasashen da yaƙi ya ɗaiɗaita. Cikin rahoton da ta fitar, hukumar kula ilimi, da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta ce sau dubu 6,000 aka kai wa dalibai da malamansu da kuma cibiyoyin ilimi hari, ciki har da hare-hare dubu 1,000 inda sojoji ke mayarda makarantun sansani. Ganin cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen makarantu da dama ke fuskantar barazanar hare-haren ta'addanci ya sa Nura Ado Suleiman tattauna wa da Kwamrade Audu Titus Amba, shugaban ƙungiyar malaman Najeriyar.

game amba duniya hare hare najeriya cikin majalisar
Kasuwanci
Yadda basuka su ka yi wa ƙasar Ghana katutu a cikin shekara guda

Kasuwanci

Play Episode Listen Later Aug 7, 2024 9:59


A yau shirin zai waiwai kasar Ghana, inda basusukan da ake bin kasar ya karu da dala biliyan 47.4 / Cidi biliyan 658.6 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2024.Babban Bankin ƙasar ta Ghana ne ya fitar da wadandan alkaluma cikin wani rahoton da ya fitar na taƙaitaccen Bayanan Tattalin Arziki da Kuɗi na watan Mayun shekarar 2024. A cewar babban bankin na Ghana, bashin da ake bin ƙasar ya karu ne zuwa Cidi biliyan 658.6 a watan Fabrairun wannan shekarar, tsabanin Cidi biliyan 611.2 da yake a ƙarshen shekarar 2023.

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu saurare kan shigar iyayen al'umma cikin ayyukan garkuwa da mutane

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Jul 30, 2024 10:06


Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya duba yadda rashin tsrao da kuma garkuwa da mutane ke kara yawaita a arewacin Najeriya, inda a baya-bayan nan kwamishin yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ya sanar da cafke 'dan majalisar dokoki da hakimi tare da tsohon shugaban karamar hukumar Kaurar Namoda bisa zarginsu da hannu dumu dumu cikin ayyukan garkuwa da mutane domin karbar kuɗin fansa. Wannan al'amari ya sake tabbatar da zargin da ake yi wa wasu daga cikin shugabanni a Najeriya dangane da taka muhimmiyar rawa a matsalolin tsaron da suka addabi al'ummar ƙasar.Me za ku ce kan wannan lamari?Wane darasi ya kamata al'umma su koya?Wace mafita ce mafi dacewa a bi wajen magance matsalolin tsaron dake tagayyara jama'a?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare da Nasiruddeen Muhammad

Kasuwanci
Yadda Najeriya ke fuskantar tashin farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 30

Kasuwanci

Play Episode Listen Later Jul 24, 2024 10:11


A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al'umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin mafi ƙarancin albashin ma'aikata. Shin ko hakan zai kawo sauƙi kan halin da ake ciki a ƙasar? Kuna iya latsa alamar sauti don jin amsar wannan tambaya tare da masana ta cikin shirin...

Lafiya Jari ce
Hatsarin da ke cikin amfani da maganin ƙwari wajen adana kayan abinci

Lafiya Jari ce

Play Episode Listen Later Jul 22, 2024 9:50


Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai mayar da hankalli ne a kan gargaɗin da hukumar kiyaye ingancin abinci da magunguna a Najeriya, wato NAFDAC ta yi a kan hatsarin da ke tattare da amfani da maganin kashe ƙwari na Sniper a wajen adana kayan abinci domin kare su daga ƙwari. NAFDACdai ta jaddada haramcin da ta yi a kan amfani da wannan magani da ma sshigowa da shi Najeriya, bayan da ce bincikenta ya tabbatar  da cewa maganin yana haddasa cutuka da suka haɗa da cancer.

Mu Zagaya Duniya
Wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare daga Rfi

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Jul 20, 2024 20:07


A ranar Alhamis da ta gabata, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naira dubu 70 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, inda yayi alƙawarin sake nazari kan yiwuwar wani ƙarin a duk bayan shekaru uku, a cikin shirin mu Zagaya Duniya ,Nura Ado Suleiman ya  zaɓo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya ƙare domin bitarsu.

suka daga wasu najeriya cikin alhamis
Wasanni
Yadda El-Kanemi ta lashe kofin ƙalubale na Najeriya na farko cikin shekaru 32

Wasanni

Play Episode Listen Later Jul 15, 2024 10:00


Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan nasarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta El-Kanemi Warriors ta lashe kofin kalubale na Najeriya na shekarar 2024. A karshen watan da ya gabata ne dai ƙungiyar ta Jihar Borno ta samu nasarar lashe kofin kalubale na Najeriya, bayan da doke Abia Warriors da ci 2 - 0 a filin wasa na Mobolaji Johnson da ke Lagos.

lagos yadda najeriya cikin
Tambaya da Amsa
A cikin shirin zaku ji amsar tambaya game da sabon irin masara da aka samar

Tambaya da Amsa

Play Episode Listen Later Jul 13, 2024 20:13


Shirin tambaya da amsa na wannan makon ya amsa tambayoyi da dama da masu saurare suka aiko mana su. Danna alamar saurare don jin masoshin tambayoyin ta cikin shirin tare da Nasiru Sani

Bakonmu a Yau
Dr. Yakubu Mohd Baba kan umarnin gwamnati na kawo ƙarshen Cholera cikin mako 6

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Jul 10, 2024 3:01


Ganin yadda annobar cutar Kwalara ta yaɗu a sama da jihohi 30, gwamnatin Najeriya ta bada umarnin ɗaukar matakan tabbatar da kawo ƙarshen cutar cikin makwanni 6.An dai ɗora nauyin ne akan hukumar duba gari ta kasa.Wakilinmu na Abuja Mohd Sani Abubakar ya zanta da shugaban hukumar Dakta Yakubu Mohd Baba don jin ta yadda za su tunkari wannan aiki. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron zantawar ta su...

Mu Zagaya Duniya
Tattaunawa kan wasu daga cikin tarin matsaloli da suka hadabi Najeriya a fanoni daban-daban

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Jul 6, 2024 18:03


A cikin shirin Duniyarmu a yau,Michael Kuduson ya tattauna Mustapha Salisu Fernandez dan siyasa kuma mai sharhi kan lamuran yau da na kullum a Najeriya.

suka daga tarin wasu najeriya cikin
Ilimi Hasken Rayuwa
Yadda ayyukan ƴan ta'adda suka kassara harkokin Ilimi a Arewacin Najeriya

Ilimi Hasken Rayuwa

Play Episode Listen Later Jul 2, 2024 9:58


A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta'adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar. Bincike ya nuna cewa, tun bayan harin na 2014, 'yan ta'adda sun ci gaba da kai makamancinsa a kimanin makarantu 17, waɗanda suka haɗa da makarantun Firamare da sakandare da ma manyan makarantun gaba da sakandare, inda suka yi garkuwa da dalibai da dama, an sako wasu bayan biyan kuɗin fansa, wasu kuwa suna rike a hannunsu  har zuwa yanzu. Cikin shekaru goma da fara ƙaddamar da irin wannan ta'addanci kan makarantu da ɗalibai, masana sun bayyana shakku kan gwamnatin Najeriya tare da zarginta da nuna halin ko in kula kan ilimi tare da rayukan al'ummar kasar musamman ɗalibai. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...

Mu Zagaya Duniya
Bitar labaran makon da ya gabata ta cikin shirin "Mu zagaya Duniya"

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Jun 8, 2024 20:24


Shirin Mu zagaya duniya bisa al'ada kan yi bitar muhimman labaran da suka gudana a makon jiya, a wannan makon shirin tare da Nasrudden Muhammad, ya duba kan dambarwar yajin aikin NLC a Najeriya sai kuma yadda Jam'iyyar ANC a Afrika ta kudu ke laluben kafa gwamnatin haɗaka. Duk dai a cikin shirin za kuma kuji yadda ta ke ci gaba da kayawa a Gaza, bayan da Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare sassan Rafah ciki har da makarantar da ke ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya.Waɗannan da ma sauran muhimman labarai na ƙunshe a cikin shirin.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin..

gaza wa jam afrika ku isra anc shirin bitar duniya nlc duk najeriya cikin majalisar dinkin duniya majalisar