POPULARITY
Yawaitar yajin aikin likitoci na neman kassara ɓangaren kiwon lafiya a Najeriya, domin kuwa yanzu haka likitocin da suka kammala karatu sannan suke cikin asibitoci don sanin makamar aiki, sun tsunduma yajin aiki saboda neman a biya su haƙƙoƙinsu kamar dai yadda yake ƙunshe a yarjejeniyar da ke tsakaninsu da hukuma. Shin ko yaya wannan yajin aiki ke shafar sha'anin kiwon lafiya a yankunan da ku ke rayuwa? Wace shawara za ku bai wa ɓangarorin don warware saɓanin da ke tsakaninsu? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Ra'ayoyi sun sha bambam a tsakanin al'umma dangane da matakin zaftare kuɗaɗe don tallafa wa Gidauniyar Ceton Ƙasa da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kafa. Ƙarƙashin wannan gidauniya, kusan kowane rukuni na jama'a, tun daga ƙusoshin gwamnati, zuwa ma'aikata da kamfanoni, na gwamnati da masu zaman kansu, kai har ma da masu zaman kashe wando, ala dole sai kowa ya bayar da nasa tallafin. Shin me za ku ce a game da wannan Gidauniya, da har ake cewa har yanzu ba wanda ke da hurumin gudanar da bincike dangane da kuɗaɗen da ake tarawa a cikinta? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Wataƙila sakamakon matsin lamba daga al'umma, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake bitar afuwar da ya yi wa mutane sama da 170 da ke ɗaure a gidajen yari saboda laifukan aikata kisan kai, fataucin miyagun ƙwayoyi da dai sauransu. Shin me za ku ce dangane da wannan sabon mataki na shugaba Tinubu da ke tabbatar da cewa mafi yawan waɗanda aka yi wa afuwar a farko wannan wata, a yanzu za su ci gaba da kasancewa a gidan yari? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai cikin shirin Ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan rana. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
Shirin a wannan makon ya yi dubi ne kan zare sunan Najeriya da cibiyar da ke sanya idanu kan almundahanar kuɗaɗe da ɗaukar nauyin ta'addanci a duniya ta yi cikin baƙin kundinta. A makon da ya gabata ne, Cibiyar nan ta Yaƙi da Masu Safarar Kuɗi da Ɗaukar Nauyin Ta'addanci ta duniya (FATF), ta sanar da cire sunan Najeriya daga jerin ƙasashen da take ɗaukarsu a matsayin masu wanan ɗabi'a. Wannan mataki ba iya Najeriya ta shafa ba, harma da ƙasashen Burkina Faso da Afrika ta Kudu da ma Mozambique duk a nahiyar Afrika. Cibiyar wadda ke da hedikwata a birnin Paris na ƙasar Faransa, wadda ke gudanar da binciken kwakwaf kan yadda ake hada-hadar kuɗaɗe tsakananin ma'aikatun gwamnati da hukumomi ko kuma cibiyoyin gwamnati ta ce duk da cire waɗannan ƙasahe cikin baƙin littafinta, har yanzu za'a ci gaba da sanya idanu akan waɗannan ƙasashe. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba................
Ga alama yajejeniyar tsagaita wutar da Isra'ila ta ƙulla tsakaninta da Hamas, wadda Amurka ta tsara ta kama hanyar rugujewa, sakamakon umarnin da Firaminista Benjamin netanyahu ya bayar na ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza. Wannan ya biyo bayan abinda ya kira ƙin bada gawarwakin sauran Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su. Domin tattauna wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris, ya tuntuɓi Dakta Abdulhakin Garba Funtua, mai sharhi a kan harkokin Gabas ta Tsakiya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.........................
Shirin wannan makon zai tare ne a jihar Kano dake Tarayyar Najeriya, inda aka samu manoma da dama a wasu yankuna da suka duƙufa wajen noman barkono a wannan shekarar. Ba shakka sun yi aiki tuƙuru, kuma haƙarsu ta cimma ruwa duba da ɗimbim barkono da suka girba. Wannan lamari dai ya tayar da hankalin waɗannan manoma, waɗanda sun sauya alƙibla ne saboda ganin yadda farashin amfanin gona dangin hatsi ya faɗi warwas a kasuwanni, kuma sun yi haka ne domin su more daga ribar da aka yi ta ci daga barkono, amma sai gashi lamarin ya yi musu ta leƙo ta koma. A kusan ilahirin kasuwannin kayan gwari, gani za ka yi ga barkono, wanda kafin yanzu yake tamkar gwal, sai ga shi yanzu masu saye su na mai tayin da suka ga dama. Masana sun yi ittifakin cewa, ba shakka rashin tsari da alƙibla wajen noma da kuma binciken halin da kasuwa ke ciki sun taka rawa ainun a wcikin wannan matsala da aka samu. Sai dai kuma, matsaloli na yanayi ma sun taka irin nasu rawar, domin akwai matsin lamba daga yadda tsarin ruwan sama ya sauya, da sauraan matsaloli da suka addabi ƙasar noma. Matsalar yanayi da muhalli na mummunan tasiri akan ko wane irin nau'i na noma. shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin, tare da Michael Kuduson.
Gwmanatin Jamhuriyar Nijar ta kafa kwamitin ƙwararru wanda ta ɗora wa alhakin sake rubuta tarihin ƙasar, lura da cewa yawancin abubuwan da ake faɗa game da ƙasar a halin yanzu Turanwan mulkin mallaka ne suka rubuta su. Shin ko meye muhimmanci rubuta sabon tarihin wanda aka ɗanka wa masana ƴan ƙasar a maimakon wanda aka gada daga ƴan mulkin mallaka? Anya abu ne mai yiyuwa a iya sauya bayanan da ke rubuce a game da ƙasar waɗanda tuni suka karaɗe duniya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Mahukunta a Najeriya sun tasa ƙeyar ƴan asalin ƙasashen waje su 192 da aka tabbatar da sun shahara wajen aikata damfara ta yanar gizo a cikin ƙasar. Mutanen waɗanda aka kama a birnin Lagos, sun haɗa da China, Philippines, Malaysia, Pakistan, Tunisia da dai sauransu, waɗanda tuni kotu ta tabbatar da laifukansu. Shin me za ku ce a game da yadda ƴan damfara a yanar gizo ke neman mayar da Najeriya a matsayin tunga domin baje kolinsu? Shin ko kun gamsu da irin matakan da mahukunta ke ɗauka domin daƙile wannan matsala? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
Malaman Jami'o'in Najeriya sun kare matakin ƙungiyarsu na tsunduma yajin aikin gargaɗi na makwanni 2, inda suka zargi gwamnati da yaradara. Wannan kuwa na zuwa ne duk da gargaɗin da gwamnatin ƙasar ta yi na amfani da dokar nan ta babu aiki babu biya duk malamin da ya shiga yajin aiki na ASUU. Shugaban ƙungiyar Malaman reshen Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Haruna Jibril ya yiwa Bashir Ibrahim Idris ƙarin bayani a tattaunawar da suka yi kamar haka... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
A Najeriya yajin aikin malaman jami'o'i ya shiga rana ta biyu, lamarin da tuni ya fara haifar da cikas musamman ga ɗalibai da mafi yawansu na tsakiyar zana jarrabawa. Yayin da ƙungiyar Malaman ASUU ta ce ta shiga yajin aikin ne domin neman gwamnati ta cika aiwatar da yarjejeniyar da ɓangarorin biyu suka rattaba wa hnnu tun 20009, yayin da a gwamnati ke cewa tuni aka aiwatar da abubuwan da kunshe a yarjejeniyar. Shin ko yaya ku kallon wannan yajin aiki? Wace shawarar za ku bai wa bangarorin biyu domin gaggauta wannan saɓani da ke tsakaninsu. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Ra'ayoyi na ci gaba da bayyana dangane da afuwar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wa mutane 175 da aka kama da laifuka daban daban. Daga cikin waɗanda aka yi wa afuwar har da waɗanda aka yankewa hukuncin kisa, da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi da dai sauransu. Shin ko me za ku ce a game cancanta ko kuma rashin dacewar yin wannan afuwar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
A ƙasar Kamaru, yanzu haka ana ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar da za a yi ranar lahadi mai zuwa, inda ƴan takarar 9 za su fafata da shugaba mai-ci wato Paul Biya. Kawo yanzu dai yaƙin neman zaɓen na gudana a cikin kwancin hankali, yayin da tuni mahukunta suka yi gargaɗi domin kauce wa duk wani abu da zai iya haifar da matsala a wannan marra. Shi me za ku ce a game da wannan zaɓe da ake shirin gudanarwar a Kamaru? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Rundunar Ƴansandan Najeriya ta sanar da karɓar umarnin kotu na dakatar da kama motocin dake ɗauke da bakin gilashi, inda ta umarci jami'an ta da su dakatar da kamen har zuwa lokacin da za'a kammala shari'ar. Wannan ya biyo bayan rugawa kotu da wasu lauyoyi suka yi domin hana aiwatar da dokar da suka ce za ta take haƙƙin Bil Adama. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barr Suleiman Muhammed, lauya mai zaman kansa. Ku latsa alamar sauti domin jin tattaunawarsu...
Yau ake cika shekaru biyu cif da ƙazamin harin da Mayaƙan Hamas suka kai Isra'ila wanya ya hallaka Yahudawa fiye da dubu guda sanadiyyarsa ne kuma aka faro wannan yaƙi na Gaza da ya kashe Falasɗinawa fiye da dubu 60. Wannan yaƙi shi ne mafi muni da duniya ta gani a wannan ƙarnin wanda ya rushe fiye da kashi 90 na gine-ginen yankin. Dangane da wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin siyasar ƙasashe don jin tasirin wannan yaƙi ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar...
A jiya ne aka gudanar da bikin ranar malamai ta duniya cikin yanayin ƙuncin rayuwa da ƙarancin albashi, musamman a wasu ƙasashen Afirka da malaman ke ɗanɗana kuɗarsu. An ware wannan rana ne, domin nuna goyon baya ga irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban rayuwar al'umma a fannoni da dama. Wanne hali malamai ke ciki a yankunanku? Shin kun gamsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a yankunanku. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Tambari kayan kida ne na kaɗe-kaɗe da ke kunshe da ganga wanda aka shimfiɗa fata ɗaya ko fiye da haka. Ana buga shi da makidi a wasu wuraran ma da hannu a cikin masarautu. Wannan shi ne abinda shirn wannan lokaci ya kunsa.
A Najeriya ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin matatar Dangote da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas wato PENGASSAN. Tun daga lokacin da matatar Dangote ta fara aiki kawo yanzu, an samu takaddama irir-iri daga kungiyoyin da ke da alaka da man fetur da kuma iskar gas. Ko me yasa takun saka tsakanin Dangote da masu ruwa da tsaki a harkar mai, yaki ci yaki cinyewa? Me ku ke ganin ummul aba'isin wannan dambarwa da take bullowa daga kusurwa-kusurwa, wanda ake ganin zai haifar da tashin farashin mai a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai........ Ku latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin na ku.....................
An ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar Kamaru, inda mutane 12 ciki har da shugaba mai-ci Paul Biya za su kara da juna a ranar 12 ga watan gobe na Oktoba idan Allah ya kai mu. Yayin da Paul Biya ke fatan sake samun yardar al'umma don ci gaba da mulki karo 8, a nasu ɓangare kuwa 'yan adawa na kallon zaɓen a matsayin wata dama don samar da sauyi a ƙasar. Shin me za ku ce a game da wannan yaƙin neman zabe? Ko wane fata ku ke yi wa al'ummar Kamaru? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da rage kuɗin ruwan da ake sanyawa masu karɓar bashi daga kaso 27.50 zuwa kaso 27 karon farko cikin shekaru huɗu. Wannan ci gaba na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar tattara haraji ta Najeriya ke cewa ta sami ƙarin kuɗaɗen shiga da kaso 411%, amma hakan ba zai hana ci gaba da ciyo bashi da Najeriya ke yi ba. A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara, Dr Ahmad Bolori masanin tattalin arziki a Najeriya ce, ragin kwabo 50 kachal yayi matuƙar kaɗan duk da cewa babu wani abu da talaka zai mora a wannan ci gaba. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance.
Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewa daga Kotun Hukunta Laifuka ta Duniya da ke birnin Hague, bisa zargin kotun da kasancewa ƴar amshin ƴan mulkin mallaka. To sai dai wasu na ganin cewa shugabannin ƙasashen uku sun ɗauki matakin ne don kauce wa bincike ko tuhuma daga wannan kotu. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacinku a yau cikin shirin na Ra'ayoyinku masu saurare. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Gwamnatin Jamhuriya Nijar ta ɗage haramcin shigar da siminti a ƙasar, sakamakon yadda ake fama da ƙamfarsa, lamarin da ya haifar da tsadarsa a kasuwa. Wani lokaci a can baya ne dai mahukunta suka sanar da haramta shigar da simintin don kare kamfanonin da ke sarrafa shi a cikin gida, amma kuma aka wayi gari na cikin gidan sun gaza wadatar da masu buƙatar sa domin yin gini. Shin ko me za ku ce a game da cire haramcin? Wannan shine maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
A Najeriya, gwamnatin Neja ta umarci ilahirin limaman masallatan Juma'a a faɗin jihar da su riƙa miƙa mata bayanan da ke ƙunshe a cikin huɗubar da za su gabatar don tantancewa, matakin da Gwamna Muhammadu Umar Bago ke cewa yunƙuri ne na kaucewa duk wata barazana ta cusa ƙiyayya ko kuma haddasa rikici da malaman ka iya yi. Yaya kuke kallo wannan mataki na Gwamnan jihar Neja? Shin kuna ganin akwai buƙatar shigowar gwamnati don daidaita yadda malamai ke gudanar da khuɗubobi da sauran karatuttuka? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
Hukukumar Yaƙi da Rasha ta ICPC a Najeriya, ta ce yanzu haka tana ƙara sa-ido dangane da yadda ake kashe kuɗaɗe mallakin ƙananan hukumomi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ke shan matsin lamba domin ganin ta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya buƙaci a zuba wa ƙananan hukumomin kuɗadensu kai-tsaye a maimakon bi ta hannun gwamnonin jihohi. Ko me za ku ce a game da jan ƙafa wajen aiwatar da wannan umarni da kotu ta bayar tun watan Yulin shekara ta 2024 da ta gabata? Wace irin rawa ya dace ICPC ta taka don kare dukiyar ƙananan hukumomi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakin ku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Sabon firaministan Faransa Sebastien Lecornu ya karɓi ragamar tafiyar da mulkin daga hannun Francois Bayrou, wanda ƴan Majalisar dokokin ƙasar suka tsige a ranar Litinin ta gabata.Wannan dai shi ne Firaminista na 5 bayan da Emmanuel Macron ya karɓi ragamar mulki domin yin wa'adi na biyu, lamarin da ke nuni da cewa ƙasar na fama da rikici a fagen siyasa. Dr Mubarak Muhammad, mazauni Faransa kuma masani a game da salon siyasar ƙasar, ya bayyana wa Nura Ado Sulaiman mahangarsa a game da wannan batu. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu..................
A Najeriya, an shiga takun-saƙa tsakanin Ƙungiyar NUPENG ta direbobin motocin dakon mai da iskar gas da kuma Ɗangote wanda ya sanar da sayo motoci dubu 4 da zai yi amfani da su don rarraba man fetur a sassan ƙasar. Yayin da NUPENG ke cewa magoya bayanta ne ke da hurumin raba mai da iskar gas a ƙasar, sai dai manazarta na cewa Ɗangote, na da damar raba hajarsa sakamakon sakin mara da aka yi wa ɓangaren kasuwanci a ƙarƙashin dokokin Najeriya. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi....
Kotun ƙasar Finland ta ɗaure Simon Ekpa mai fafutukar kafa ballewar Biafra daga Najeriya shekaru 6 a gidan yari, saboda samun sa da laifufukan ta'addanci. Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin ake ci gaba da tsare ɗaruruwan mutane a gidajen yarin Najeriya bisa zargin aikata ta'addanci, amma kotuna sun gaza hukuntar da su. Shin ko me za ku ce a game da wannan hukunci da kotun ƙasar Finland ta yanke? Meye ra'ayoyinku a game da gazawar kotunan Najeriya wajen hukunta waɗanda ake tuhuma da aikata irin waɗannan laifuka a cikin gida? Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu
Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Afrika sun bayyana aniyar aiki tare a tsakaninsu domin tunƙarar matsalolin tsaron da suka addabi nahiyar, musamman ayyukan ta'addanci. Wannan ya biyo bayan taron da suka halarta a Najeriya. Dangane da wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya dangane don jin alfanun wannan sabin yunƙuri , ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana akai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
Hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka a taron da suka yi a birinin Abujan Najeriya, sun ƙuduri aniyar haɗa gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta. Wannan taro dai ya samu halartar wakilan ƙasashe sama da 50, waɗanda suka yi imani da cewa la'akari da girman matsalar, akwai buƙatar ƙasashen su yi aiki a tare don tunkarar ta. Shin ko meye ra'ayoyinku a game da wannan yunƙuri na ƙasashen Afirka? Waɗannan shawarwari za ku bayar domin samun nasarar wannan fata? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
A jamhuriyar Nijar, dubban mutane ne suka rasa ayyukansu yayin da ɗimbin ƴan gudun hijira suka daina samun tallafi, bayan da mahukunta suka kori mafi yawan ƙungiyoyin agaji daga gudanar da ayyukansu a cikin ƙasar. Bayan korar waɗannan ƙungiyoyi da ke taimaka wa ƴan gudun hijira, a mafi yawan yankuna har yanzu gwamnatin ta gaza samar da tsarin da zai maye gurbin waɗannan ƙungiyoyi don agaza wa jama'a. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin....
A Najeriya muhawara ta ɓarke game da buƙatar sulhu da ƴan ta'adda maimakon amfani da ƙarfin Soji, kodayake an samu mabanbantan ra'ayoyi daga ɓangaren masana a fannin na tsaro lura da yadda suka ce irin wannan sulhu ya gaza amfanarwa a yankuna da dama duk da cewa anga alfanunsa a wasu yankunan. Yaya kuke kallon wannan batu? Shin kuna ganin sulhu ko kuwa amfani da ƙarfin soji shi ne mafi a'ala wajen yaƙi matsalolin tsaron Najeriyar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkaci bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza....
Lura da yadda jama'a ke ɗari-ɗari a game da kayan abincin da aka sauya wa ƙwayoyin halitta da ake kira GMO, wannan ya sa mahukunta a Najeriya ke neman yin amfani da malaman addini domin gamsar da jama'a su rungumi irin wannan abinci. Abin neman sani a nan shi ne, shin ko kun fahinci abin da ake kira GMO? Ko a shirye ku ke domin karɓar nau'in abincin da aka canza wa ƙwayoyin halitta? Anya yin amfani da malaman addini zai sa jama'a su amince da shi a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Mai Bai wa Shugaban Najeriya Shawara kan Sha'anin Tsaro Nura Ribaɗo ya tabbatar da kama jagororin ƙungiyar Ansaru da ake kira Ƴan Mahmuda su biyu, waɗanda suka jima suna addabar yankunan ƙasar. Ana dai bayyana wannan ƙungiya a matsayin babbar barazana ga matsalar tsaron ƙasar, saboda alaƙarta kai-tsaye da Alqa'ida. Shin ko wane sauyi wannan kame zai samar ta fannin tsaro a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Kusan a kowacce shekara, dai-dai wannan lokaci ne ake samun faruwar ambaliya sakamakon saukar ruwan sama mai yawa da ke haddasa asarar rayuka da kuma dukiyoyi masu tarin yawa. A daidai wannan lokaci, ko wane hali ake ciki a yankunanku dangane da batun ambaliya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a wannan rana. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ƴanbindiga sama da 100 a ƙaramar hukumar Bukkuyum dake jihar Zamfara, sakamakon wasu hare haren sama da suka kaddamar a kan su. Rahotanni sun ce sojojin sun yi amfani da bayanan asiri ne wajen kai harin kan ƴanta'addan waɗanda aka ce yawansu ya kai 400 a dajin a Makakkari. Wannan na daga cikin nasarorin da sojojin Najeriya suka samu a ƴan kwanakin nan. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ad Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Danfodio dake Sokoto, wanda ya ce wannan shi ne labarin da ƴan Najeriya ke farin cikin ji. Ga yadda tatatunawar su ta gudana a kai.
Kamar yadda aka saba a duk ranar Juma'a, muna kawo muku wasu daga cikin manyan labarun da Jaridar Aminiya da ke Najeriya ta ƙunsa. A wannan karon Nura Ado Suleiman ya tattauna ne da Jamilu Adamu, Editan shafin labarun ban Al'ajabi na wannan jarida.
Jagororin yankin Arewacin Najeriya sun kammala taron yini biyu da duka gudanar a Kaduna, don bibiyar alkawurran da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ɗaukar wa yankin a lokacin yaƙin neman zabe. Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu suka yi zargin cewa an maida yankin saniyar ware duk kuwa da irin gudunmuwar da ya bayar a lokacin zaɓen baya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Khamis Saleh da Barista Abdullahi Jalo...........
Masu saurare barkan mu da safiya Rukayya Abba Kabara ce ke farincikin kasancewa da ku a cikin sabon shirin Mu zagaya Duniya,a cikin shirin zaku ji yadda mutane sama da miliyan biyar ke fama da tsananin yunwa a wasu jihohin arewa maso gabashin Najeriya uku. Wannan mako ne tsaffin jami'an ƴansanda a Najeriya suka gudanar da wata kwarya-kwarayar zanga-zanga a babban birnin tarayyar Abuja.
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce tattalin arzikin ƙasar ya samu ƙarin tagomashi da kashi 3 da ɗigo 13 a rubu'in farko na wannan shekarar ta 2025, saɓanin kashi 2 da ɗigo 27 yake a daidai wannan lokaci a shekarar 2024. Wannan na zuwa ne yayin da talauci ke ci gaba da ta'azzara a tsakanin al'ummar ƙasar, kuma manoma sun gaza yin noma yadda ya kamata saboda matsalar ta'addanci. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Rahotanni daga Najeriya sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon haɗurran motoci da aka samu a ƙarshen mako cikin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da Lagos da kuma jihar Oyo baya ga Lagos da kuma jihar Kogi. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin hanyoyin motoci ke ci gaba da taɓarɓarewa, yayinda wasu direbobin ke tuƙi cikin yanayi na maye ko kuma saɓawa dokokin tuƙi. Dangane da wannan matsala da ke kaiwa ga asarar ɗimbin rayuka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Adamu Idris Abdullahi Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW da ke Abuja ga kuma yadda tattaunawarsu ta kasance. Sai ku latsa alamar sauti don saurare.
A ƙarshen makon da ya gabata aka samu ambaliyar ruwan sama a sassan birnin Kano, a dai dai lokacin da damina ta fara kankama a jihar. Wannan matsalar ta haifar da matsaloli ga mazauna da kuma baƙin da ke zuwa birnin. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƙaramar hukumar Dala, Hon Siraj Ibrahim Imam, Kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti son sauraron cikakkiyar Hirar.
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon yi duba ne kan gasar sukuwar dawaki da aka gudanar a birnin Zazzau da ke tarayyar Najeriya, inda ƙasashe 5 da suka haɗa da Nijar da Kamaru da Chadi da Burkina Faso da Mali da kuma mai masaukin baƙi Najeriya suka fafata. Wannan ne dai karo na farko da aka gudanar da gasar a a birnin Zazzau bayan kwashe fiye da shekara 12 ba tare da gudanar da ita ba. A wannan karon gasar ta yi armashi sosai ganin yadda jama'a sukayi tururuwar zuwa filin sukuwan dawaki da turawan mulkin mulka suka gina fiye da shekara 100, domin gane wa idonsu yadda za ta kaya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan wani sabon bashin da Najeriya ta ciwo daga bankin duniya da ya haura sama da dala biliyan ɗaya. Wannan sabon bashin dai ya janyo cece-kuce daga ƴan ƙasar waɗanda suka nuna damuwa kan yadda gwamnati ke ci gaba da ciyo manyan basussuka duk da iƙirarinta na janye tallafin manfetur domin dogaro da kai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba............
Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya yi duba ne kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da aka yi a ƙarshen mako tsakanin PSG ta Faransa da kuma Inter Milan, inda PSG ta samu nasarar lashe gasar bayan da ta zazzaga wa Inter Milan ƙwallaye biyar. Wannan ne dai karon farko da PSG ta lashe wannan kofi, kuma karo na farko da wata ƙungiya daga Faransa ta lashe shi tun bayan Marseille a shekarar 1993.Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Khamis Saleh............
Shirin Lafiya Jari Ce a wannan makon shirin ya mayar da hankali kan yadda wani bincike ke gano cewa yawan shan suger ko kuma sikari a lokutan ƙuriciya na taka muhimmiyar rawa wajen haddasawa mutum ciwon suga a lokacin girma. Wannan cuta ta suga ko kuma Diebetes na cikin jerin cutukan da ke barazana ga rayukan ɗimbin mutane musamman a sassan Najeriya da tuni cutar ta fara zama ruwan dare mai gama duniya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............
Wannan shiri zai mayar da hankali ne kan yadda zamani ke tasiri akan salon magana ko gagara gwari a tsakanin al'umar hausawa, musamman ma matasa masana da dattawa da suka jiya suka ga yau sun bayyana dalilai da suka sanya irin wannan salo na zance, wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa a tsakanin al'uma da gudummawar da kowanne ɓangare ke bayarwa wajen disashewar wannan fiƙira ta harshe.
Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta bayyana shirin kafa sabuwar rundunar hadin kai wadda za ta dinga yaki da yan ta'addan da suka addabi yankin. Wannan na da cikin shirin shugabannin yankin na dakile ayyukan ta'addanci, da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Janar Kape Alwali Kazir mai ritaya a dangane da wannan shiri.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Babban Hafsan tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa ya ce baya ga amfani da makamai wajen tinkarar mayakan Boko Haram, farfado da Tafkin Chadi zai taimaka wajen samarwa jama'ar yankin sana'oi. Wannan ya biyo bayan ziyarar aikin da ya kai Maiduguri bayan kazaman hare haren da boko haram ta kai cibiyoyin soji.Dangane da wannan bukatar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mutumin yankin, Farfesa Sheriff Muhammad Almuhajir.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shin ko kun san muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa kuwa? Wannan tambaya ce mai matuƙar muhimmanci, lura da cewa yanzu haka akwai ɗimɓin mutane da ke fama da wannan matsala a sassan duniya. Yayin da wasu ke kira wannan lalura a matsayin hauka, masana kuwa na cewa hatta shiga yanayi na damuwa ko da ƙuncin rayuwa na iya haddasa wannan matsalar.Shin ko wace irin kulawa ku ke bai wa lafiyar ƙwaƙwalwa?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta bai wa hafsan sojojin ƙasar umarnin cewar babu wanda zai tafi ritaya a cikin wannan shekarar, sakamakon wasu matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta. Dangane da wannan umarni, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Sani Yahya Janjuna, mai sharhi akan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai.
Shirin a wannan makon zai tattauna ne a kan Camfi, da kuma yadda ya kasance a zamanin kaka da kakanni, da rawar da ya taka a waccan lokaci da kuma yadda yake shafar rayuwar jama'a a lokacin da muke.Duk da ƙarancin lokaci, shirin Al'adunmu na gado zai yi ƙoƙarin zayyana rabe-raben al'adar ta Camfi ko kuma wasu daga ciki.