POPULARITY
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yai kaddamar da aikin fara binciken man fetur da iskar gaz a yankin Kolmani da ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe. Alkaluma dai na nuni da cewa akwai kusan ganga bilyan daya nan danyan mai tare da samar wa Najeriya sama da dala bilyan 73 matukar aka fara aikin hako shi. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yaki sanya hannu akan sabuwar dokar zaben da majalisa ta amince da ita wadda zata baiwa jama'a damar tsayawa zabe ba tare da neman Ubangida ba da kuma aikewa da sakamakon zaben kai tsaye daga tashoshin da aka gudanar da zabe. Sashen hausa na rfi ya tattauna da Tsohon Dan Majalisar Dattawa kuma tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP na kasa Sanata umar Ibrahim Tsauri, kuma ga tsokacin da yayi a kai. Daukar wannan mataki na biyo bayan cikar wa'adin sanya hannu akan daftarin da Majalisa ta mika masa a jiya lahadi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yara sama da miliyan 12 ne ke fargabar zuwa makaranta a kasar saboda tsanantar ayyukan ‘yan ta'adda da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane. Bayanai sun nuna cewa ‘yan ta'adda sun yi garkuwa da dalibai sama da dubu 1 a Najeriya cikin kasa da shekara, daya, abinda ke jefa yaran cikin halin ni ‘ya su. Ga tattaunawar Dr.Idris Salisu Rogo na jami'ar Bayero da ke Kano, da Rukayya Abba Kabara.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci taimakon Amurka wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi nahiyar Afirka baki daya, inda ya roke ta da ta dawo da Cibiyar rundunar ta da ke kula da Afirka daga Jamus zuwa nahiyar. A tattaunawar da suka yi da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken Buhari ya ce dawo da Cibiyar rundunar Afirka zai taimaka wajen dakile matsalolin tsaron da suka mamaye nahiyar. Dangane da wannan bukata, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Mai Martaba Sarki Gwandu na 19 Manjo Almustapha Haruna Jokolo, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci taimakon Amurka wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi nahiyar Afirka baki daya, inda ya roke ta da ta dawo da Cibiyar rundunarta da ke kula da Afirka daga Jamus zuwa nahiyar. A tattaunawar da suka yi da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken Buhari ya ce, dawo da Cibiyar Rundunar Afirka zai taimaka wajen dakile matsalolin tsaron da suka mamaye nahiyar. A game da wannan batu Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. El Harun Muhammed, masanin siyasar duniya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dibawa ‘yan bindiga da suka hana sukuni a jihohin arewa maso yammacin Nigeria musamman Jihar Zamfara, wa’adin watanni biyu da su bada kai ko kuma ya sanya kafar wando daya da su. Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya gabatar da sakon shugaban kasar a jawabi ga al’ummar jihar. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Alhaji Tukur Mamu, dan Jarida, kuma mai sharhi gameda harkokin yau da kullum ko yaya yake kallon matakin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabbin manyan hafsoshin sojin kasar, domin maye gurbin wadanda ya nada shekaru 5 da suka gabata. Nadin sabbin hafsoshin na zuwa ne a wani lokaci da matsalolin tsaro suka addabi kasar daga kowane bangare. Dangane da sauyin da aka samu, mun tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya, wanda yayi tookaci akai kamar haka.
A karon farko gwamnatin Najeriya ta ce babu ko da mutum guda da jami`an tsaro suka kashe a shingen karbar harajin ababen hawa a hanyar Lekki da ke Legas, a lokacin zanga-zangar EndSARS. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya musanta zarginda ake yiwa sojan kasar cewa sun kashe masu zanga-zangan ENDSARS a kwanan baya. Shugaban yace, bayanan da aka yi ta yadawa ta kafafen sada zumunta jita-jita ne kawai, babu gaskiya a ciki. Masu zanga-zangar da wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi zargin cewa an kashe a kalla mutane 12 a harabar ta Lekki. Kan haka ne muka tattauna da Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasa Mohammadu Buhari, kuma ga abinda yake cewa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar mutane 69 suka mutu sakamakon tarzomar da aka samu lokacin zanga zangar adawa da cin zarafin yan Sanda, yayin da 37 suka samu raunuka, kuma adadin ya hada da fararen hula da jami’an Yan Sanda da kuma soji.Garba Aliyu Zaria ya mayar da hanakali a cikin shirin Mu zagaya Duniya.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan nasarar da dan Najeriyar nan, Kamaru Usman ya samu a babbar gasar damben zamani da aka gudanar a Amurka. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa dan wasan saboda bajintar da ya nuna. Kazalika shirin ya yi nazari kan kalubalen da ke gaban Real Madrid bayan ta lashe kofin La Liga karo na 34 a Spain.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa karamin ministan ayyukan kasar Festus Keyamo umarnin cigaba da shirin dibar ma’aikata dubu 774 bayan takaddamar da ta kaure tsakanin sa da 'yan Majalisun kasar da suka nemi a dakatar da aikin. Ministan ya ce shugaba Buhari ya bashi umurnin cigaba da aikin kamar yadda doka ta tanada, yayin da kungiyoyi daban daban za su taka rawa wajen dibar ma’aikatan a matakan kananan hukumomi 774 da ke fadin Najeriya a shirin da ake saran ya lakume naira biliyan 52. Dangane da wannan cigaba mun tattauna da Mallam Abdullahi Umar, kuma ga tsokacin da ya yi akai.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada matsayin gwamnatin sa na aiwatar da gina bututun iskar gas wanda zai tashi daga Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano domin saukakawa jama’a samun sinadarin cikin lokaci kuma kamar yadda aka tsara. Yayin da yake kaddamar da fara aikin ta kafar bidiyo a Ajaokuta dake Jihar Kogi da kuma Rigachikum dake Jihar Kaduna, jiya Talata, Buhari yace aikin na da matukar muhimmanci ga ‘Yan Najeriya saboda haka ya zama dole a samu nasarar sa. Dangane da wannan shiri, Umaru Dembo, tsohon ministan albarkatun manfetur a Najeriya ya bayyanawa Ahmad Abba tasirin wannan shirin a tattaunawar da suka yi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci manoman kasar da su kara azama don wadatar da kasar da abinci, saboda a cewarsa, Najeriya ba ta da kudin da za ta yi amfani da su domin sayo abinci daga ketare. Sai dai sakataren yada labaran kungiyar manoman Najeriya, Alhaji Muhammad Magaji, ya ce akwai abubuwan da ya kamata gwamnati ta yi domin ganin cewa manoma sun wadatar da kasar da abinci.
DW Hausa Shirin Safe 01.03.2019 [1] Masana tattalin arziki da hada-hadar kudi a Najeriya, sun bada shawarar cewa ya kamata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta bada himma wajen raya tattalin arzikin kasar musamman a yankin arewacinta domin magance matsalolin da ke addabar yankin. Hosts: Muntaqa Ahiwa Nigeria: Cikin shirin za'a ji yadda masana suka soma baiwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shawara kan buƙatar zaburar da harkokin tattalin arziƙi, musamman ma na arewacin ƙasar da ke fama da matsaloli. Cameroon: Yara ne da ke fama da cutar nan ta HIV mai karya garkuwar jiki da ke cikin mummunar yanayi na rashin maganin rage raɗaɗin wannan cuta. Senegal: Zaɓen da aka kammala. North Korea: Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin sake zama da Amurka bayan tashi taron birnin Hanoi da aka yi ba tare da wata nasara ba. Amurka ta taya Najeriya murnar kammala zaɓe cikin kwanciyar hankali. Somalia: Wani harin ƙunar baƙin wake, ya salwantar da rayuka a ƙasar Somaliya.
Shirin Dandalin siyasa na wannan mako ya mayar da hankaline kan dakatar da babban mai shari'ar Najeriya Walter Onnonghen da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi.