Wasanni

Follow Wasanni
Share on
Copy link to clipboard

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Rfi - Nura Ado Suleiman


    • Jun 2, 2025 LATEST EPISODE
    • every other week NEW EPISODES
    • 10m AVG DURATION
    • 258 EPISODES


    Search for episodes from Wasanni with a specific topic:

    Latest episodes from Wasanni

    Sharhi kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da PSG ta lashe

    Play Episode Listen Later Jun 2, 2025 10:00


    Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya yi duba ne kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da aka yi a ƙarshen mako tsakanin PSG ta Faransa da kuma Inter Milan, inda PSG ta samu nasarar lashe gasar bayan da ta zazzaga wa Inter Milan ƙwallaye biyar. Wannan ne dai karon farko da PSG ta lashe wannan kofi, kuma karo na farko da wata ƙungiya daga Faransa ta lashe shi tun bayan Marseille a shekarar 1993.Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Khamis Saleh............

    Yadda bukin wasanni na ƙasa ke gudana a Abeokutan Najeriya

    Play Episode Listen Later May 26, 2025 10:00


    Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon tare da Khamis Saleh yi yi dubi ne kan bikin wasannin na ƙasa da ke gudana a jihar Ogun da ke Najeriya.

    ogun yadda najeriya
    Dalilan durkushewar ƙungiyoyin Arewacin Najeriya da suka bada gudunmuwa a baya - Kashi na 3

    Play Episode Listen Later May 19, 2025 9:59


    A wannan makon shirin zai ɗora ne akan wanda muka kawo a baya, wanda ya yi bita a game da wasu shahararun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na arewacin Najeriya da suka taimaka wajen ƙyanƙyasar fitattun ƴan wasa da suka yi shura a fagen ƙwallon ƙafa a ƙasar. Shirin ya yaɗa zango ne a Kano, inda ya gana da wasu tsaffin fitattun ƴan wasa, musamman na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Racca Rovers.

    Dalilan durkushewar ƙungiyoyin Arewacin Najeriya da suka bada gudunmuwa a baya - Kashi na 2

    Play Episode Listen Later May 12, 2025 10:00


    A wannan makon, shirin Duniyar Wasanni ya ɗora ne kan shirin mu daya gabata, wanda yayi duba kan yadda manyan ƙungiyoyin da suka taimakawa Najeriya wajen ƙyanƙyansar shahararrun ƴan wasa daga yankin Arewacin ƙasar suka durkushe. A wannan makon shirin zai yada zango ne a garin Jos na jihar Filato, wanda ke zama gida ga ƙungiyar Mighty Jets FC. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........

    Dalilan durkushewar manyan ƙungiyoyin Arewacin Najeriya da suka bada gudunmuwa a baya

    Play Episode Listen Later May 5, 2025 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda manyan ƙungiyoyin da suka taimaka wa Najeriya wajen ƙyanƙyansar shahararrun ƴan wasa daga yankin Arewacin ƙasar suka durkushe. A baya yankin Arewacin Najeriya ne ke kan gaba wajen samar da manyan ƴan wasan da ake ji dasu a ƙasar, kuma mafi yawancin ƴan wasan sun fito ne daga ƙungiyoyi na cikin gida irinsu DIC Bees da ke Kaduna wacce ta koma Ranchers Bees da Racca Rovers da ke Kano da Mighty Jets da ke garin Jos da dai sauransu. Sai dai shirin a wannan lokacin zai yada zango ne a jihar Kaduna, don yin duba a kan ƙungiyar DIC Bees, wacce Sanata Muktar Muhammad Aruwa ya saya a shekarun 1980, kuma ya sauya mata suna zuwa Ranchers Bees.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...........

    Barcelona ta lashe kofin Copa del Rey karo na 32

    Play Episode Listen Later Apr 28, 2025 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon, ya yi duba ne kan wasan ƙarshe da aka yi na gasar Copa del Rey tsakanin Barcelona da Real Madrid, inda Barca ta samu nasarar lashe kofin karo na 32 a tarihi. Haka nan shirin ya duba nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Liverpool ta yi a wannan kaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........

    Tasirin masu horarwa na cikin gida wajen ɗaga likafar tawagogin ƙasashen Afirka

    Play Episode Listen Later Mar 24, 2025 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya mayar da hankali kan tasirin masu horarwa na cikin gida a ci gaban ƙwallon ƙafar nahiyar Afirka. A baya-bayan nan ƙasashen na nahiyar Afirka sun mayar da hankali wajen ɗaukar masu horarwa na cikin gida tun bayan rawar da Morocco ta taka a gasar cin kofin Duniya ta 2022 karon farko da aka ga irin hakan daga wata ƙasa a nahiyar ta Afrika.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Yadda zaɓen shugabannin Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afirka ya gudana

    Play Episode Listen Later Mar 17, 2025 9:59


    A makon da ya gabata ne dai Hukumar Ƙwallonn Kafar Afirka CAF ta gudanar da zaɓenta, inda aka sake zabar Patrick Motsepe a matsayin shugaba a  karo na biyu. Bayan haka ne aka gudanar da zaɓen wakilan nahiyar a Hukumar Ƙwalllon Ƙafa ta Duniya, FIFA, inda Afirka ke da wakilai 6, har da shugaban CAF mai kujerar kai-tsaye..

    Matsalar wariyar launin fata da wasu 'yan wasa ke fuskanta

    Play Episode Listen Later Mar 10, 2025 9:59


    Shirin a wannan makon zai yi duba ne kan matsalar nan ta nuna wariyar launin fata da wasu ƴan wasa ke fuskanta. Nuna wariyar launin fata a wasannin motsa jiki musamman ma kwallon ƙafa na ɗaya daga cikin ƙalubalen da ƴan wasa baƙaƙe ke fuskanta, matsala da ta shafe shekaru aru-aru ana fama da ita.Wani lokaci ƴan wasa baƙar fata dai na fuskantar cin zarafin daga magoya baya ko masu horaswa, ta hanyar zagi kai tsaye ko wata alama ta nuna kaskanci ko kuma cin fuska, duk da cewa hukumomi na ɗaukar kwararar matakai don magance matsalar.

    Najeriya ta samu alƙalan 30 da za su busa wasannin ƙasa da ƙasa

    Play Episode Listen Later Mar 3, 2025 9:59


    Shirin ''Duniyar Wasanni'' tare da Khamis Saleh, a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda Hukumar Kula da Kwallon Ƙafa ta Najeriya NFF ta naɗa alkalan wasa 30, waɗanda hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ke bai wa bajo, don jagorantar manyan wasanni a duniya. A baya, Najeriyar na da irin waɗannan alkalai 27 ne, sai dai a bana an samu ƙarin guda uku, lamarin da ya sanya adadinsu ya kai 30, wannan adadi kuwa ya ƙunshi 22 maza sai kuma mata guda 8.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Abin da ya kamata ku sani kan wasannin zagayen ƴan 16 na gasar zakarun Turai

    Play Episode Listen Later Feb 24, 2025 9:59


    A makon da ya gabata ne Hukumar Kula da Kwallon Ƙafar Turai UEFA, ta fitar da jadawabin yadda wasannin zagayen ƴan 16, na gasar zakarun Turai zai gudana.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........

    Matsalar alƙalanci na barazana ga ƙimar gasar La liga a Spain

    Play Episode Listen Later Feb 17, 2025 10:00


    Shirin ''Duniyar Wasanni'' tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matsalolin alƙalanci ke ƙoƙarin yin illa ga gasar La liga guda cikin manyan lig-lig biyar da aka fi ji da su a nahiyar Turai, la'akari da irin zaratan ƙungiyoyi da kuma ƴan wasa dama masu horaswar da ke fafatawa a cikinta tsawon lokaci. A bana, salon alƙalanci a gasar ta La Liga na ɗaukar hankali, musamman ganin yadda alkalai ke bayar da katin gargaɗi da kuma na kora babu ƙaƙƙautawa, alal misali anga yadda a wasanni 23 zuwa 24 da ƙungiyoyin da ke fafatawa a gasar  suka yi a wannan kaka, an bada kafin gargadi sama da dubu daya da 136, sai kuma na kora.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

    Ƴan kasuwa a Najeriya sun fara zuba jari don gina filayen wasanni

    Play Episode Listen Later Feb 10, 2025 9:59


    Shirin ''Duniyar Wasanni'' tare da Khamis Saleh a wannan makon zai yi duba ne kan yadda ƴan kasuwa suka fara zuba jari a ɓangaren gina filayen wasanni, matakin da masana ke cewa zai ƙara ƙarfafa ɓangaren na wasanni musamman ga yara masu tasowa. Rashin kyauwun filiyen wasanni a nahiyar Afrika, na ɗaya daga cikin abubuwan da ke mayar da harkar wasan kwallon ƙafa baya, a matakin kwararru ko masu koyo ko kuma ga masu motsa jiki a faɗin nahiyar.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    Yadda aka kammala wasannin rukuni a gasar cin kofin zakarun Turai

    Play Episode Listen Later Feb 3, 2025 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya yi duba kan gasar zakarun Turai da aka kammala wasannin rukuni. A ranar larabar makon da ya gabata ne dai aka kallama wasanni rukuni na gasar zakarun Turai, wacce ita ce karo na 70 tun bayan faro gasar kuma karo na 33 bayan sauyawa gasar suna, sannan kuma wannan ne karo na farko da aka faro sabuwar gasar da aka sauya mata fasali.Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

    Salah ya shafe tarihin Thierry Henry na yawan jefa kwallo a gasar Firimiya

    Play Episode Listen Later Jan 27, 2025 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya ziyarci gasar Firimiyar Ingila ne don duba sabon tarihin da ɗan wasan Liverpool Mohammed Salah ya kafa a gasar. Mohammad Salah dai a yanzu ya shafe tarihin Thierry Henry na zura kwallaye 175 a gasar Firimiyar Ingila, bayan da ya jefa kwallo a karawar da suka yi da Ipswich. A yanzu dai Mohammed Salah ne na 7 a jerin ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a raga a babbar gasar ta Ingila.Ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a gasar dai su ne Alan Sheare mai  kwallaye 260 da Harry Kane  213 da Wayne Rooney 208 da Andrew Cole 187  da Sergio Agüero 184 da Frank Lampard 177 sai shi Mohamed Salah 176 ya yinda a yanzu Thierry Henry  mai kwallaye 175 ya koma mataki na 8 a wannan jeri.Ƙu latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........

    Sharhi kan kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika da Ademola Lookman ya lashe

    Play Episode Listen Later Dec 23, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wassani a wannan makon ya yi duba ne game da kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika da aka bayar. A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Hukumar da ke kula da kwallon ƙafar nahiyar Afrika wato CAF, ta bayar da kyautar gwarzon nahiyar Afrika wanda yafi bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita. Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Najeriya Ademola Lookman ne ya samu nasarar lashe wannan kyauta, biyo bayan irin bajintar da ya nuna ga ƙasar da kuma ƙungiyarsa ta Atlanta. Samun nasarar lashe wannan kyauta da ɗan wasan yayi dai ta sanya zamowa cikin jerin ƴan wasa 6 na Najeriya da a tarihi suka taɓa lashe ta.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh........

    Sauye-sauyen da aka samu a bana a gasar wasan kokuwar gargajiya ta Nijar

    Play Episode Listen Later Dec 16, 2024 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon, yayi duba ne game da gasar kokuwar gargajiya a Jamhuriyar Nijar, wacce za a faro a ranar 20 ga wannan wata na Disamba nan a jihar Dosso da ke rike da takobi ko kambun gasar, inda ƴan wasa 80 daga Jihohi 8 na Nijar za su fafata har zuwa 29 ga watan, don samun sabon sarkin ƴan kokuwa wanda ke lashe kyautar takobi da kuɗaɗe da sauran kyautuka. Sai dai wani hanzari da ba gudu ba shi ne yadda a bana aka samu wasu sabbin sauye-sauye musamman ɓangaren dokokin wannan gasa.Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh..........

    ku sai samu bana nijar jamhuriyar nijar gargajiya
    Ƴan wasan lik ɗin Najeriya na fuskantar barazana sakamakon tafiye tafiye ta mota

    Play Episode Listen Later Dec 9, 2024 9:58


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ƴan wasa a Lik din Najeriya ke fuskantar barazana a tafiye tafiye ta mota da suke yi don yin wasa. Yin amfani da motoci wajen jigilar ƴan wasan da ake fafatawa a gasar Lik ɗin Najeriya ba sabon abu bane, ganin yadda mafi yawancin ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa sun fi amfani da motoci wajen kai ƴan wasansu jihohin ko garuruwan da za su fafata wasa. Irin waɗan nan tafiye tafiye dai na haifar da barazana ga rayuwar ƴan wasan musamman idan aka yi la'akari da rashin ƙyaun hanyoyi ko kuma da kuma matsalar tsaro.Ƙungiyar El-Kenemi Warriors ce ta baya-bayan nan da ƴan wasanta suka fuskanci wannan barazana, a hanyar su ta koma birnin Maiduguri bayan buga wasan mako na 14 da suka yi Ikorodu City a birnin Lagos.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Najeriya ce zakara a wasannin sojoji na Afrika karo na biyu da aka gudanar

    Play Episode Listen Later Dec 2, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako yayi duba ne kan yadda aka kammala wasanni sojoji na nahiyar Afrika. Wannan ne dai karo na biyu da tawogogin ƙasashe 20 suka fafata a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda kuma tawagar ƴan wasan sojoji ta Najeriya ta zamo zakara, bayan da ta samu nasarar lashe lambar zinari 114 da azurfa 65 sai kuma tagulla 55 a jumlace ke nan ta samu lambobin yabo 234. Ƙasar Aljeriya ke bi mata a matsayin na 2 da lambar zinari 53 da azurfa 22 sai kuma agulla 21, a jumlace ita kuma ta samu lambobin yabo 96, Kenya ce tazo ta 3 bayan da ta lashe lambobin yabo 50.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

    Sharhi kan yadda aka kammala wasannin zuwa gasar AFCON da za a yi a Morocco

    Play Episode Listen Later Nov 25, 2024 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda aka kammala wasannin neman gurbin shiga gasar lashe kofin Afrika. Kuma a tsakiyar makon daya gabata ne aka kammala wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin AFCON da ke gudana tsakanin ƙasashen Afrika, gasar da Morocco za ta karɓi baƙunci a watan Disamban shekarar 2025. A yanzu dai dukkanin ƙasashe sun san makomarsu kuma ƙasashen 24 da za a ga haskawarsu a gasar ta baɗi sun ƙunshi ita mai masaukin baƙi Morocco da Burkina Faso da Kamaru da Algeria da Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo da Senegal da Masar da Equatorial Guinea da Cote d'Ivoire da Uganda da Afrika ta Kudu da Gabon da Tunisia da Najeriya.Sauran sun ƙunshi Zambia da Mali da Zimbabwe da Tsibirin Comoros da Sudan da Benin da Tanzania da Botswana da kuma Mozambique, a wani yanayi da Bostwana ke samun tikitin gasar karon farko bayan dakon shekaru 12.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh........

    Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa a Najeriya

    Play Episode Listen Later Nov 18, 2024 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Nigeria. Wannan dai wani bangare ne na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon ƙafa a Nigeria, tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles na ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon kafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira Football Academy, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya.Pascal Patrick, tsohon ɗan wasan Super Eagles kuma shugaban Hukumar kwallon kafa ta NFA a jihar Bauchi kana co-odinetan tawagar Super Eagles na Nigeria, na daya daga cikin tsofaffin ƴan wasan ƙasar da suka kafa irin wannan cibiya a jihar Bauchi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

    Yadda cece-kuce ya mamaye kyautar Ballon d'Or ta 2024

    Play Episode Listen Later Nov 4, 2024 9:58


    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi dubi ne akan yadda aka gudanar da bikin bada kyautar Ballon d'Or ta shekarar 2024.

    Hukuncin da CAF ta yi kan danbarwar Najeriya da Libya da kuma wasan El-Clasico

    Play Episode Listen Later Oct 28, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon yayi duba ne kan yadda wasan El-Clasico ya gudana da kuma hukuncin da Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF tayi kan danbarwar Najeriya da Libya. A ƙarshen mako ne dai kwamin ladaftarwa na hukumar CAF, ya zartar da hukuncin cewa Najeriya ce tayi nasara da ci 3 da nema kan Libya, tare da tarar dala dubu 50. Haka nan shirin ya duba yadda wasan El-Clasico ya gudana tsakanin Real Madrid da Barcelona da aka yi a ƙarshen mako.

    Danbarwar da ta ɓarke kan wasa tsakanin Najeriya da Libya

    Play Episode Listen Later Oct 21, 2024 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan danbarwar da aka samu tsakanin Najeriya da Libya. A makon daya gaba ne dai aka fara kai ruwa rana tsakanin bayan da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi tattaki zuwa Libya don karawa da takwaransu ta ƙasar a wasa na biyu na neman gurbin zuwa gasar lashe kofin Afrika da za ayi a Morocco a shekara mai zuwa. Wannan al'amari dai ya haifar da cece-kuce a duniyar kwallon ƙafar, ganin yadda Super Eagles ta zargi hukumomin kwallon ƙafar Libya da yin watsi da su a filin jirgin sama ba tare da ance kuci kanku ba.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

    Yadda aka faro kakar gasar Firimiyar Ingila ta bana

    Play Episode Listen Later Oct 14, 2024 9:55


    Shirin a wannan makon ya maida hankali ke kan yadda aka faro gasar Firimiyar Ingila, inda akwa yanzu kowace ƙungiya ta samu nasarar buga wasanni 7-7. Tuni gasar ta soma nisa, inda Liverpool take a saman teburi da maki 18, yayinda Arsenal da Manchester City ke biye mata da maki, 17, kowannen su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Ko komen da Ahmed Musa yayi Kano Pillars zai haifar da ɗa mai ido?

    Play Episode Listen Later Oct 7, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi duba ne kan komen da Kyaftin din tawagar Najeriya Ahmed Musa ya yi wa tsohon ƙungiyarsa Kano Pillars tare da abokin wasansa Shehu Abdullahi. A karshen makon da muka yi bankwana da shi ne dai ƙungiyar kwallo ƙafa ta Kano Pillars a hukumance ta sanar da kulla yarjejeniyar shekara guda da ƴan wasan. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Matakin da Hukumar CAF ta ɗauka kan Ghana ya bar baya da ƙura

    Play Episode Listen Later Sep 30, 2024 9:59


    A dai-dai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiyen wasannin sharen fagen samun gurbi a gasar lashe kofin Afrika, Hukumar Kula Ƙwallon kafar Afrika CAF ta ce filayen wasan ƙasar Ghana ba su da ingancin da ya kamata a ce an gudanar da manyan wasanni na kasa da kasa a cikin, matakin da ke kara nuna gazawar ƙasar. Ita dai hukumar CAF ta ce ba komai ya sanyata daukar wannan mataki ba, face yadda ta ce aƙwai rashin wadatatciyar ciyawa da rashin magudanun ruwa da dai sauransu a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi, haka ta ce abin ya ke a sauran filayen wasanni irin na Cape Coast da kuma na Accra.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    An shiga mako na uku a gasar firmiyar Najeriya

    Play Episode Listen Later Sep 23, 2024 9:59


    Shirin a wannan lokaci zai leka gasar Firimirar Najeriya wato NPFL Wanda aka shiga mako na uku da somawa.Gasar Firimiyar Najeriya na daga cikin manyan gasannin Lik-lik da ake ji da su a nahiyar Afrika, musamman idan akayi la'akari da yadda ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa ke taka rawar gani a gasar zakarun Ƙungiyoyin Afrika.

    Koma bayan da harkokin wasanni ke fuskanta a Najeriya

    Play Episode Listen Later Sep 16, 2024 10:00


    Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan koma bayan da harkar wasannin ke fuskanta a Najeriya.Najeriya daya ce daga cikin kasashen da suka yi suna a fagen wasanni a duniya, inda ake ganinta a sahun gaba wajen wakiltar nahiyar Afrika.To sai dai a baya-bayan nan kasar na fuskantar koma baya a bangare, musamman idan aka yi la'akari da rashin katabus din da ta yi a lokacin gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris.

    Yadda aka kammala gasar Paralympics da birnin Paris ya karbi bakunci

    Play Episode Listen Later Sep 9, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi duba ne kan yadda aka kammala gasar gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta nakasassu wato Paralympics da birnin Paris ya karbi bakunci, bayan kwashe tsawon kwanaki 11 ƴan wasa dubu 4 da dari 4 su na fafatawa a wasanni 22 da aka lashe lambobin 549. Kasar China ce dai ta jagoranci teburin lashe lambobin yabo na wannan gasa, bayan da ta lashe lambar zinari 94 da azurfa 76 sai kuma tagulla 50, a jumlace tana da lambobin yabo 220. Ku latsa alamar Sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Sauye-sauyen da aka samu a sabuwar gasar zakarun nahiyar Turai

    Play Episode Listen Later Sep 2, 2024 9:57


    Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan sauye-sauyen da a Ka samu a gasar cin kofin zakarun turai.A makon da ya gabata ne dai hukumar kula wasannin kwallon kafar Turai UEFA ta gudanar da hadin yadda wasanin rukuni na gasar zakarun Turai karo na 70 zai gudana, ganin cewa a wannan karon an samu sauye-saye da dama a gasar. Kadan daga cikin sauye-sauyen da aka samu sun hada da kara yawan kungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa daga 32 zuwa 36.Har illa yau, a wannan sabon tsarin hukumar ta sauya tsarin rukuni da a baya ake amfani da shi, in da a yanzu tazo da tsarin da ke kama da na lik-lik, inda kungiyoyi za su buga wasanni takwas maimakon 6 a matakin farko Kuma dukkanin kungiyoyin zasu kasance a teburi daya, sannan kungiyoyi 8 da suka fi yawan maki ne zasu wuce mataki na 16, wadanda suka kare daga mataki na 9 zuwa na 24 zasu sake neman gurbin ci gaba da zama a gasar sai Kuma daga 25 zuwa na 36 zasu koma gida ma'ana an yi waje rod da su.

    Yadda ake ci gaba da gasar wasannin motsa jiki na Olymmpics 2024 a Paris

    Play Episode Listen Later Aug 5, 2024 9:58


    Wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da ke gudana a nan birnin Paris na tafiya yadda aka tsara, inda kawo yanzu an kammala wasu wasanni da dama wasu kuma ana daf da kammala su. 'Yan wasan  tawagar kwallon kwando ta Mata ta Najeriya na ci gaba da fatan ganin a wannan karon ta samu nasarar tsallake matakin rukuni, ganin yadda suka dage wajen lashe wasansu na farko da Austrelia amma sai dai sunsha kashi a hannun Faransa a wasa na biyu inda a yanzu fatansu shine samun nasara a wasan da zasu yi da Kanada don tsallakawa matakin dab da na kusa da na karshe a wannan gasa.

    Shirye-shiryen gudanar da gasar olympics 2024 a Paris sun kammala

    Play Episode Listen Later Jul 22, 2024 9:59


    Yau shirin zai yi, duba ne kan yaddata kaya a game da sshirye-shiryen gudanar da gasar olympics da za a fara a cikin wannan watann a birnin Paris. shirye-shirye dai sun yi nisa a game da wannan gasa, duba da cewa ilahirin tawagogin kasashe sama da ɗari 2  da za su fafata a wasanni dabam-dabam sun sauka a wannan birni, haka ma mabobin kwamitin shirya wannan gasa. Wani sabon al'amri kuwa shine yadda za a gudanar da bikin fara wannan gasa a cikin kogin Seine daya ratsa birnin Paris.

    Yadda El-Kanemi ta lashe kofin ƙalubale na Najeriya na farko cikin shekaru 32

    Play Episode Listen Later Jul 15, 2024 10:00


    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan nasarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta El-Kanemi Warriors ta lashe kofin kalubale na Najeriya na shekarar 2024. A karshen watan da ya gabata ne dai ƙungiyar ta Jihar Borno ta samu nasarar lashe kofin kalubale na Najeriya, bayan da doke Abia Warriors da ci 2 - 0 a filin wasa na Mobolaji Johnson da ke Lagos.

    lagos yadda najeriya cikin
    An kammala gasar firimiyar Najeriya ta kakar 2023/2024

    Play Episode Listen Later Jul 8, 2024 10:00


    Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan gasar Firimiyar Najeriya ta NPFL da aka kamala, ta kakar 2023 2024, gasar da Enugu Rangers ta lashe.To kamar yadda kuka ji tuni kungiyar Enungu Rangers ta lashe gasar Firimiyar Najeriya ta bana da aka kammala, yayin da kungiyar Remo da Enyimba suka kasance a matakin na biyu dana uku To tun bayan kammala gasar masu sharhi ke faman tabka muhawara game da yadda gasar ta gudana, Isma'ila Abba Tangalash mai sharhin ne kan lamuran wasanni, ya mana bayanin yadda gasar ta gudana a dunkule.

    Yadda sakamakon wasannin gasar kasashen Turai ke ba da mamaki

    Play Episode Listen Later Jul 1, 2024 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda gasar cin kofin Nahiyar Turai ci gaba gaba da bada mamaki, ganin yadda kananan kasashe ke doke manyan da suka yi suna a bangaren kwallon kafa a duniya. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Tarihin gasar Euro da kuma wainar da ake toya wa a gasar da ke gudana a Jamus

    Play Episode Listen Later Jun 24, 2024 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda gasar Turai wato Euro 2024 ke gudana a kasar Jamus. gasar Euro, wacce hukumar kula da kwallon kafar Turai ke shiryawa duk bayan shekaru 4. Shirin ya yayi waiwaye kan tarihin ita wannan gasa da kuma irin wainar da ake toyawa a gasar da yanzu haka ke gudana. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Fatanmu wasan Damben gargariya ya shiga wasannin Olympics - Dambe Warriors

    Play Episode Listen Later Jun 10, 2024 10:00


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan ci gaban da wasan Damben Gargajiya ke samu a kasar Hausa. Akwai kungiyoyi da dama da a yanzu suka shiga cikin sabgar wasan dambe wanda kuma hakan ke kara mata tagomashi dama jawo ra'ayin wadanda da basa ciki shiga cikinta gadan-gaban. Dambe Warriors na daga cikin kungiyoyi da ke suka jima suna shirya wasan inda 'yan wasan ke samun albashi mai tsoka a mataki daban-daban. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Mahawara kan yadda kungiyar Madrid ta lashe kofin zakarun Turai

    Play Episode Listen Later Jun 3, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon, ya maida hankali ne kan wasan karshe na gasar zakarun Turai wanda kungiyar Real Madrid ta lashe karo na 15 a tarihi, bayan doke Brussia Dortmund, abunda ya maida ita kungiyar data fi kowwacce nasarar dauke wannan kofi mafi girman dearaja a Turai. Gabanin wasan dai ana ganin da wahala Madrid din ta iya samun nasara lura da yadda Dortmund ta zo matakin wasannan na karshe, duk kuwa da cewar tarihin Madrid din na nuna tafi iya lashe kofin data sha wahalar zuwa wasan karshe.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

    Bitar yadda aka kammala kakar wasanni ta bana

    Play Episode Listen Later May 27, 2024 10:00


    Shirin a wannan mako shirin ya yi sharhi ne kan yadda aka kammala gasar La liga da wasan karshe na kofin FA da sauran abubuwan da suka faru a karshen wannan mako. Haka nan shirin ya yi tsokaci game da babban wasan da za a iya cewa ya rage a nahiyar Turai a wannan kaka wato wasan karshe na gasar Zakarun nahiyar da za ayi tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikken shirin tare da Khamis Saleh.....

    Manchester City ta kafa tarihi bayan lashe kofin Firimiyar Ingila karo 4 a jere

    Play Episode Listen Later May 20, 2024 10:00


    Shirin duniyar wasanni na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda aka kammala gasar Firimiyar Ingila, musamman yadda kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kafa sabon tarihin lashe gasar karo 4 a jere.

    Har yanzu akwai rashin tabbas game samar da ingantaccen tsaro yayin gasar Olymics mai zuwa

    Play Episode Listen Later May 6, 2024 9:59


    Shirin duniyar wasanni na wannan mako ya dubi yadda ake tufka da warwarwa game da tsarin samar da cikakken tsaro yayin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh

    Nazari kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana

    Play Episode Listen Later Apr 22, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana. A makon da ya gabata ne dai aka kammala wasannin zagayen, inda aka fafata a wasanni 4. Dortmund da aris Saint-Germain da Bayern Munich da Real Madrid ne suka kaiga wasan kusa da na karshe a gasar ta bana. A yanzu Bayern Munich zata fafata da Real Madrid ita kuwa Borussia Dortmund ta kara Paris Saint-Germain.Ku letsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

    Hasashen yadda za ta kaya a gasar Firimiyar Ingila

    Play Episode Listen Later Apr 15, 2024 9:59


    Shirin a wannan lokaci ya fi karkata akalar ne kan gasar Firimiyar Ingila, wadda ke ci gaba da jan hankali, duk da shawo gangarar da akayi. Yar manuniyar dai tuni ta fada kan kungiyoyin ukun saman tebur, wato Manchester City, Arsenal da Liverpool, lura da yadda suke kan kan kan a yawan maki, abunda ke kara nunawa duniya yadda gasar ta Firimiya ta ke ci gaba da jan zarenta a fagen tamola.Ko da yake a halin yanzu Manchester City ce ta karbe ragamar teburin wannan gasa, bayan rashin nasarar da Arsenal da kuma Liverpool suka samu a nasu wasannin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamsi Saleh.

    Shiri na musamman kan shirye-shiryen gasar Olympics kashi na 2

    Play Episode Listen Later Apr 8, 2024 9:59


    A wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar. Shire-shiryen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci a watan Yuli mai zuwa sunyi nisa, domin dai rahotanni na nuna cewar an kammala tanadin kusan dukkanin inda za a gudanar da wadannan wasanni.Sai dai wani hanzari ba guda ba, duk da matakan da kasar ta Faransa ta dauka na tabbatar da tsaron ‘yan wasa da kuma na ‘yan kallo, bayanai na nuna cewar akwai alamun fuskantar barazanar tsaro a lokacin gasar.Wannan lamari dai ya biyo bayan harin ta'addancin da aka kai birnin Moscow wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 140.A lokacin wata zantawa da aka yi shugaban Faransa Emmanuel Macron a makon da ya gabata, ya ce babu shakka, akwai yuwuwar Rasha za ta kai hari a lokacin gasar da ke tafe.Kai hari a lokacin gasar OlympicsKai hari a yayi gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics a iya cewa ba sabon abu bane, domin a baya an sha samun irin hakan, wanda aka kai a shekarar 1972 a Munich da kuma a shekarar 1996 a Atlanta.Duk da cewa a cikin watan da ya gabata ministar Wasannin Faransa Amelie Oudea-Castera, ta ce a yanzu babu wata barazanar hare-haren ta'addanci da gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics ke fuskanta, sai dai wasu da dama na cewa barazanar abu ne da ke da alaka da rikicin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine da ya kwashe sama da shekaru biyu anayi, wanda kasashen duniya ciki harda Faransa ke goyonma Ukraine baya domin fafatawa da Rasha.Yadda gasar Olympics ke samar da hadin kaiIta dai wannan gasa ana ganinta a matsayin wata farfajiya ta samar da hadin kai, ganin yadda take hada dukkanin bangarorin duniya waje guda.Domin idan aka koma baya cikin tarihi, bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, gasar da aka gudanar ta shekarar 1952, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar.Ƴan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra'ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.To sai dai ana ganin cewa a wannan karon siyasa ta shiga cikin lamarin wanda ke kokarin kawo rarrabuwar kai.Martanin Rasha game da zargin kai hariTo sai dai a wani martani da Rasha ta maida game da kalaman Macron ta bakin mai magana da yawun fadar shugaban kasar Dmitry Peskov, ta ce zargin na Macron babu tushe a cikinsa kuma wani matakine na yada labaran kanzon kurege da kasashen yammaci ke yiwa Rasha.

    Sharhi game da kamun ludayin Finidi George a tawagar Super Eagles

    Play Episode Listen Later Apr 1, 2024 9:58


    Shirin a wannan mako shirin ya yi sharhi ne kan kamun ludayin mai rikon kwaryar tawagar Super Eagles ta Najeriya Finidi George, bayan da tawagar ta buga wasannin sada zumunci biyu a makon daya gabata karkashin kulawar Finidi George da aka damkawa tawagar a hannunsa a matsain mai horaswa na rikon kwarya. Tawagar ta yi nasara kan takwararta ta Ghana a wasan farko da tayi, sai dai kuma ta sha kashi a hannun Mali karo na farko cikin gwamman shekaru da hakan ta faru.Ku latsa alamar sauti donjin cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Masar ce ta daya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Afrika da aka yi a Ghana

    Play Episode Listen Later Mar 25, 2024 9:58


    Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako yayi duba ne kan yadda gasar guje-guje da tsalle -tsalle ta nahiyar Afrika ta gudana a kasar Ghana. Kasar Masar ce ta zamo zakarar lashe lambobin yabo har 189, sai Najeriya da ke bi mata da lambobn yabo 120, yayinda Janhuriyar Nijar ta lashe lambobin yabo 11, lamarin da ya bata damar zama amatsayi na 16 a teburin kasashe 53 da suka halarci gasar bayan da Cape Verde ta janye daga fafatawa a wannan karon. Wannan ne kuma  karo na 13 da ake gudanar da wannan gasa a tarihi, inda aka gudanar da wasanni kusan 30.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

    Sharhi kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai za su gudana

    Play Episode Listen Later Mar 18, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai za su gudana. A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai hukumar kula da wasan kwallon kafar Turai UEFA ta hada yadda kungiyoyi 8 da suka yi saura a gasar zakarun Turai z asu kara da junanansu. Tsohon kyaftin din Najeriya wanda kuma ya taba lashe gasar da kungiyar Chelsea Mikel John Obi ne ya jagoranci hada yadda kungiyoyin za su kara da juna. Arsenal za ta fafata da Bayern Munich, Atletico Madrid za ta kece raini da Borussia Dortmund, Real Madrid ta kara da Manchester City ya yin da Paris Saint-Germain za ta kara da Barcelona.Ku letsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

    Ci gaban da aka samu a wasan damben gargajiya a Najeriya

    Play Episode Listen Later Mar 11, 2024 9:59


    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne kan irin ci gaban da aka samu a bangaren wasan damben gargajiya a Najeriya.

    samu najeriya gargajiya
    Yadda aka kammala zangon farko na gasar kwallon kafa ta Firimiyar Najeriya

    Play Episode Listen Later Mar 4, 2024 10:00


    Shirin awanan lokaci zai nazari game da yadda zangon farko na gasar Firimiyar Najeriya ya kammala, inda tuni aka juya zagaye na biyu na gasar ta kwararru.Shirin ya kuma duba batun soma gasar a kan lokaci da kuma batun daukar nauyi, sai kuma batun rashin ingancin filaye, baya ga kuma karanchin samun bayanan ‘yan wasan da ke taka leda a gasar.Latsa alamar sauti don sauraron shirin: 

    Nazari kan komawar Kylian Mbappe kungiyar Real Madrid a kaka mai zuwa

    Play Episode Listen Later Feb 26, 2024 9:59


    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi nazari ne kan komawar dan wasan gaba na kungiyar PSG, Kylian Mbappe  kungiyar Real Madrid a karshen kakar bana. Yanzu dai za a iya cewa an yi ta, ta kare bayan da a ranar 13 ga wannan watan ne dan wasan mai shekara 25 ya sanar da kungiyarsa PSG batun sauya shekarar tasa da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kakar watan Yuni. Kungiyar Real Madrid dai tayi suna wajen dauko manyan ‘yan wasan da tauraruwarsu ke haskawa a fagen kwallon kafa a duniya, ba tare da la'akari da tsadarsu ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

    Claim Wasanni

    In order to claim this podcast we'll send an email to with a verification link. Simply click the link and you will be able to edit tags, request a refresh, and other features to take control of your podcast page!

    Claim Cancel