POPULARITY
Shirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsioyya Haruna.
Shirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro. Ku danna alamar Saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.
Shirin na wannan mako ya waiwaya halin da duniya ke ciki a fannin tsaro, rikice-rikice da kuma Diflomasiyya
A Najeriya, jam'iyyun siyasa sun kammala zaɓen fidda ƴantakarar da za su tsaya musu a matakai daban-daban na zaɓukan da za a yi cikin shekara mai zuwa. To sai dai a ɓangaren adawa, mafi yawan jam'iyyun sun gudanar da zaɓukan ne a cikin yanayi na rabuwar kawuna sakamakon rikicin shugabanci. To akwai yiyuwar wannan rikici na cikin gida ya iya shafar ƙima da kwarjinin adawa a zaɓukan na baɗi? Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi wa Farfesa Usman Mohammed, masani siyasa a Najeriya.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka'ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyarsu na sake jifasu cikin damuwa. A cikin 'yan watannin nan, koke-koke sun mamaye kafofin sada zumunta, sakamakon rashin karin bayani kan yawaitan kudaden da bankunan ke cirewa.. Duk da cewa bankuna sun dage cewa hakan tsari ne da kuma sahalewar haka daga babban bankin kasar CBN, kwastomi na diga ayar tambaya kan cirewa fiye sau ɗaya kan, ko kuma daga wanda ya tura da kuma wanda ya ƙarba, yayin da wasu ke kokawa kan rashin maida musu kudinsu nan take idan aka samu masalar sabis kudi bai je ga wanda aka tura ba da dai sauransu... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokacin yayi duba ne kan yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai, in banda gasar Firimiyar Ingila. Barcelona ta lashe gasar La liga a Spain, a Inter Milan ta lashe gasar Serie A na Italiya, ita kuwa Bayern Munich ta ɗauke kofin Bundesliga na ƙasar Jamus, yayin da PSG ta lashe gasar League 1 ta Faransa. A yanzu haka dai gasar Firimiyar Ingila ce ake dakon jirar ƙungiyar da za ta lashe tsakanin Arsenal da Manchester City, waɗanda kowaccensu ke da ragowar wasanni biyu-biyu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana bita ne na mahimman labaran al'amura da suka wakana a makon da ya gabata. a wannan makon shirin ya soma ne daga Najeriya inda a farkon makon da ya wuce wani harin da dakarun Najeriya suka kai ta sama a kasuwar Tumfa ta karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamafara ya hallaka akalla mutum dari 100 tare da jikkata wasu da dama. Wannan harin da ke zaman mafi muni da dakarun kasar su kai kan fararen hula shi ne na uku a cikin kasa da wata guda .
Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsadar sufuri. ‘Yan kasuwa, na kukan samun wagegen gibi tsakanin uwar kudin jarinsu da abinda suke kashewa na safarar kayansu zuwa kasuwanni, saboda tsadar kudin sufuri da kuma rashin ciniki saboda halin rashin kudi da ‘yan kasar ke ciki. Kasancewar kowane sasshen Nigeria na da nau'in kayayyakin da yake da su a wadace, ‘yan kasuwa daga arewacin kasar, kan saro kayayyaki irin su Manja da Man Gyada da Garin Kwaki da makamantan su, daga kudancin kasar, yayinda ‘yan kasuwa daga kudanci, kan sayi hatsi, dabbobi da makamantan su daga arewacin kasar. Bayanan hukumar kididdiga ta Nigeria, sun yi nuni da cewa damar ikon sayen kayayyaki a kasuwanni wato purchasing power a turance, da ‘yan Nigeria ke da ita, ta ragu da kashi 21, a sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kayayyakin suka yi, da koma-bayan kudin shigar masu karamin karfi a kasar.
A Glenfarne executive discusses the specifics of the Alaska Natural Gas Pipeline on a podcast and yadda yadda yadda.
Shirin Al'adunmu Na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata al'ada da ake kira sai kowa ya zo a tsakanin al'ummar Hausawa da ke arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......
A ranar juma'ar data gabata ne dai aka kammala gasar gasar Super 4, wacce aka fafata tsakacin ƙungiyoyi 4 da suka haɗa da Sporting Lagos da Inter Lagos da Ranchers Bees ta Kaduna sai kuma Doma United, da suka zama zagaru a rukunoninsu na gasar NNL, gasa ta biyu mafi daraja a Najeriya. An gudanar da gasar ne a yanayin yadda ake gudanar da gasar lik-lik, inda kowa ya kara da kowa ganin cewa kowaccensu za ta haska a gasar Firimiyar Najeriya a kakar baɗi. A wasannin ƙarshe da aka aka yi, Sporting Lagos ta sha kashi da ci ɗaya mai banshi a hannun Inter Lagos, amma sai dai hakan bai hanata lashi gasar ba da ban-bancin ƙwallaye, domin kowaccensu ta ƙare ne da maki 6. Wannan ne karo na farko da Sporting Lagos ta taɓa lashe kofin tun bayan samar da ita a shekarar 2022.
Shirin lafiya jari Ce a wannan makon zai nazarci yadda ake gudanar aikin yaki da cutar polio tsakanin ƙasashen makwabtan juna wato Najeriya da Nijar a wani yunƙuri na kakkaɓe ɓurɓushin wannan cuta musamman a yankunan kan iyaka na ƙasashen biyu duk kuwa da saɓanin diflomasiyyar da ke tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu.
A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda Ruwan sama na farko da aka samu a baya-bayan nan ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani da fargaba, yayin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasa, NiMet, da masana ke gargaɗi game da tsagaitawar ruwan saman da wuri wanda zai iya lalata duk wani amfani da aka yi a wannan lokaci.
A wannan makon shirin na Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi nazari kan wani bincike can a Ghana da ke ƙiyasta cewa kusan kashi 13.3 na yawan jama'ar ƙasar na rayuwa da cutukan ƙoda, galibi ba tare da masaniyar suna ɗauke da ita ba, lura da yadda cutar bata nuna alamu a farko har sai ta kai ga ta'azzara. Wannan na nuna yadda cutar ta ƙoda ke matsayin babban ƙalubale a Ghana. Binciken ma'aikatar lafiyar Ghana ya nuna cewa matasa ne kan gaba wajen kamuwa da cutar ta ƙoda lamarin da ƙwararru a fannin cimaka ke cewa hakan na da nasaba da rashin daidaita cimaka da kuma yanayin rayuwar da jama'ar ƙasar suka runguma a yanzu wanda kai tsaye ke ƙara yawan masu kamuwa da cutar ta ƙoda. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin ya soma daga ƙasar Mali inda a ranar 25 ga watan Afrilun da mu kayi ban kwana haɗakar mayakan Abzinawa na FLA da na ƙungiya masu ikirarin jihadi ta JNIM suka ƙaddamar da mugayen hare-hare a garuruwa huɗu na ƙasar da suka haɗa da Sevare, Kidal, Gao da kuma Kati. A garin Kati da ke zaman babban sansanin sojin ƙasar ƴan bindigar sun yi amfani da motoci shake da bama-bamai da manyan bindigogi inda suka kai hari kan gidan ministan tsaron kasar Sadio Camara tare da hallaka shi. A kasar Chadi kuwa aƙalla mutum 42 ne suka mutu bayan ɓarkewar wani rikicin ƙabilanci da ya faro sanadiyyar taƙaddama tsakanin wasu mata biyu yayin da suke ɗiban ruwa a wata rijiyar bayan gari. A Najeriya kuwa, ranar Alhamis ne kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci kan rikicin cikin gida na jam'iyyun ADC da PDP. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Oumarou Sani.
Ɗaruruwan ‘yan Afrika ta Kudu masu ƙyamar baƙi, sun gudanar da zanga-zanga jiya Talata a birnin Pretoria, bayan da suka bjirewa kiran da shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa ya yi musu na dakatar da kai wa baƙi hare-hare gami da cin zarafinsu, inda a baya bayan wasu ‘yan Najeriya biyu suka rasa rayukansu. Cin zarafin baƙin da tsagerun ‘yan Afrika ta Kudun na baya bayan nan dai ya fara ne da shafar ‘yan ƙasashen Ghana, da Habasha da Zimbabwe kafin kai wa ga ‘yan Najeriya. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Kabiru Inuwa Dukawa, masanin siyasar ƙasa da ƙasa da ke Najeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakkiyar Hirar.
Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
A wannan makon, shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tsananin zafin da ake fuskanta a wasu jihohi na yankin Arewacin Najeriya, wanda masana suka yi ittifaƙin ya kai matakin da ka iya haddasa wasu cutuka ko kuma tayar da kwantattu. Zafin na bana ya sha bamban da wanda aka saba gani a kowace shekara, domin jama'a na bayyana cewa ya daɗe bai lafa ba kamar yadda aka saba gani a shekarun baya, sai dai ko waɗanne cutuka ne ke haɗari ɓulla ko kuma waɗanda ke iya tashi koma nau'ikan mutanen da ya kamata su yi tsaka-tsan-tsan da lafiyarsu? Tambaya kenan ga ƙwararren jami'in lafiya Abdullahi Isma'ila ƙwalwa.
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..............
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..............
A ƙoƙarinta na ganin ta bunƙasa harkokin tattalin arzikinta, gwamnatin jihar Katsina ta ce ƙofofinta a buɗe suke ga masu zuba jari na ƙasashen ƙetare. A yayin wani taro na masu zuba jari da ya gudana a birnin Paris na Faransa, gwamnatin jihar Katsina ta ce akwai masu zuba jarin da suka nuna sha'awar zuba jari a ɓangaren noma da ma'adinai da kiwon lafiya a jihar. Domin jin irin matakan da suke ɗauka domin cimma wannan narasa, Khamis Saleh ya tattauna da mataimakin gwamnan jihar Kastina Malam Faruk Lawal Jobe. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Ɗan takarar ƙawancen jam'iyyun da ke mara wa gwamnati baya a Jamhuriyar Benin ya yi nasarar lashe 94% na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugabancin ƙasar da aka hana fitattun ƴan adawa tsayawa takara. Romuald Wadagni mai shekaru 49 a duniya, shi ne ministan kuɗi tsawon shekaru 10 kafin shugaba mai barin gado Patrice Talon ya gabatar da shi a matsayin wanda yake son gaje shi. Don jin yadda masu sharhi kan siyasar ƙasa da ƙasa musamman a Nahiyar Afrika ke kallon zaɓen na Jamhuriyar Benin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Janjouna Ali Mahamane Sani.
A arewacin Najeriya, shigar mata makarantun yaki da jahilci ya fara ne a matsayin wani yunkuri na inganta rayuwar iyali da kuma tarbiyyar yara, inda mata da dama sun fahimci cewa rashin ilimi na hana su taimaka wa yaransu wajen karatunsu na zamani da kuma kulawa da lafiyarsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan cutar ɗan sanƙarau ko kuma meningitis, cutar da a yanzu haka wasu ƙasashe ke cikin haɗarin fuskantar ɓullarta musamman a yammacin Afrika, waɗanda dama ke a tubalin fuskantar wannan cuta lokaci zuwa lokaci.
Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka. Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka. To sai dai Kuma irin wannan tsarin na fuskantar cikas ko koma baya, alal misali ga yan kasuwa a jihar filato dake arewacin Najeriya, sakamakon munanan halaye na wasu bata gari marasa tausayin rayuwar Dan Adam, dake tare Yan tireda ko Kuma matafiya inda suke Kai musu farmaki, tare da yi musu kisan gilla. A kwanakin baya wasu Bata gari sun tare wasu Yan kasuwa da ke fatauci daga garin Jos zuwa yankin kudancin Jihar, inda suka kashe biyar daga cikinsu, Wannan al'amari ya Sanya Yan Kasuwar da sauran matafiya shiga hali na fargaba a kowane yanki dake jihar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a yankunan arewacin Najeriya musamman a makarantu ko ɗalibai da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman...........
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon, ya yi dubi ne kan yadda wani matashi a jihar Kanon Najeriya ya ja hankalin jama'a, bayan ƙirƙirar jirgi maras matuƙi, daidai lokacin da matasan wannan ƙasa ke faɗi tashin yadda za su samo masu ɗaukar nauyin ayyukan fasahar da suke son cimmawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruwa...........
Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ake samu canjin yanayi ta hanyar saran icen "Gawo" barkatai daga Makiyaya da su kansu Manoman, wanda ake ganin ke haifar da koma baya wajen samun yalawar abinci kamar, bakamar yadda aka saba ba a shekarun baya a cikin gonaki na Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........
Matasa a Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar na cike da fatan cin moriyar sabuwar dangatakar da aka kyautata tsakanin kasar da makwabciyarsu Aljeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
Reviewing some of the World's Top Independent Talent Every Tuesday night via YouTube. Hosted By Dj Laylo Lex Lu Tre KuL via @SpeakerLeakers Submit music to speakerleakers@gmail.com 1st come. 1st Serve, Tune In via YouTube, Facebook Live 8-9 p.m. EST. Search Speaker Leakers Worldwide Giving it to you Real, Raw, and Right Every Tuesday Night! Honest Opinions & Honest Reviews! 3/10/26 Featured Artist: Jay Ali x A1Krashn, Moe Man, Flames Oh God, Mr. & Mrs. T. Vicks, Zay the Beast, Juss Pieree, Paylo Peff, Swagg, Yadda x Rome. Slap Of The Night - A1Krashn x Jay Ali "Weight On Your Shoulders"
Shirimmu na ilimi hasken rayuwa na wannan mako yayi karin bayani akan wasannin na'ura kwamfuta masu kama da gaske da aka fi sani da virtual reality a turance. Danna alamar sauti domin sauraron karin bayani........
Farashin hajoji da sauran muhimman abubuwa na ci gaba da hauhawa a kasuwannin duniya sakamakon yadda yaƙin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya ya hana fitar da mafi yawan man fetur da kamfanoni da masana'antu suka yi oda ya maƙale a Mashigin Ruwan Hormuz. To domin fahintar girman wannan matsala da kuma ɓangarorin da suka fi fama da ƙarancin makamashi a duniya saboda wannan rikici, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya tuntuɓi masani tattalin arziki Dr Isa Abdullahi, malami a jami'ar Tarayya da ke Kashere a jihar Gomben Najeriya, ga kuma zantawarsu. A latsa alamar sauti domin sauraron tattaunawar
An shiga mako na huɗu da barkewar rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya, inda ɓangarorin da ke hannu a rikicin ke ci gaba da kai wa juna hare-hare tare da kashe mutane da kuma lalata cibiyoyin makamashi. Tuni dai hakan ya haifar da tashin goron zabi ga farshin abubuwa da dama sanadiyar hauhawar farashin mai a kasuwar duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Yusuf
Yanzu haka farashin ɗanyen man fetur na ci gaba da hauhawa sakamakon yaƙin da Amurka da Isra'il suka ƙaddamar kan Iran, inda yanzu haka ake sayar da gangar mai fiye da dala 92 a kasuwar duniya. A wannan yanayi dai ko shakka babu, ƙasashe masu arzikin mai ne irinsu na Najeriya za su ci moriyar wannan rikici. Shiga alamar sauti, domin suararon cikakken shirin.
A yau shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne a kan yadda Yaƙin da kawancen Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran, da hare-haren mayar da martini na jamhuriyar musuluncin kan yahudun Isra'ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo gagarumar koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin duniya masamman a bangaren makamashi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
A Wanan makon shirin zai karkata alakarsa ne yankin Gabas ta Tsakiya inda sabon rikici ya barke tsakanin hadakar Amurka da Isra'ila da kuma Iran. A cikin shirin zamu yi duba dangane da yadda rikicin ke cigaba da faɗaɗa zuwa sauran kasashen yankin da ma tasirinsa kan bangarori daban-daban a wanan duniyar sai a gyara zama domin sauraron cikakakken shirin.
Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan taron taron tattalin arziki da ya gudana a farkon watan Fabarairun da ya gabata a jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
A yayin da yaƙi tsakanin Isra'ila da Amurka da Iran ke daɗa rincaɓewa, an fara gani tasirinsa a kasuwar ɗanyen mai da makamashi ta duniya. Ko a Najeriya, ƙasar da ta fi arziƙin ɗanyen mai a Afirka, farashin litar fetur ya tashi, kuma masana sun ce ana iya ganin cigaba da tashin farashin makamashi. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali ne kan gasar tseren dawaki da aka gudanar a garin Daura da ke jihar Katsina da ke a arewacin Najeriya. A farkon watan Faburairun wannan shekarar ne aka kammala babbar gasar tseren dawaki ta ƙasa da ƙasa da ƙungiyar sukuwar dawaki ta Najeriya ke shiryawa. Wannan ne dai karo na uku da ake gudanar da irin wannan sukuwa a cikin wannan shekarar, bayan da aka yi ta farko a birnin Katsina sai garin Hadeja na jihar Jigawa ya karbi bakunci sannan aka kamma sukuwan zangon farko na wannan shekarar a Daura. Mahaya daga Jihohin Kano da Sokoto da Neja da Bauchi da Kebbi da Katsina, waɗansu daga Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Mali da Chadi da kuma Burkina Faso, suka halarci gasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako zai mayar da hankali kan cimaka a lokacin azumin watan Ramadana, dama yadda wasu ke fuskantar matsaloli masu alaƙa ɓacin ciki sakamakon yanayin ciye-ciyen da akan yi ko dai a lokacin buɗa baki ko kuma sahur. Kamar yadda ya ke bisa al'ada a irin wannan lokaci na azumin watan Ramadan, musulmi kan ƙauracewa abinci da abin sha tun gabanin ketowar alfijir har zuwa bayan faduwar rana, wanda hakan kan jefa masu azumin cikin yanayi na yunwa da kishirwa, sai dai da zarar an buɗi baki mutane kan ci duk abin da suke shawa lamarin da a wasu lokuta kan haddasa ɓacin ciki. A lokuta da dama masana kan gargaɗi jama'a game da cin duk abin da ransu yake so a lokacin da suka buɗi baki, da nufin baiwa lafiyarsu kariya daga cutuka ko lalacewar ciki, dangane da wannan muka nemi ji daga bakin ƙwararru a fannin abinci da amfaninsa a jikin dan-adam. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar. Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa wasu daga cikin jami'an hukumomin da ke kula da shirya jarabawa a matakai daban-daban na taimakawa wannan mummunar ɗabi'a ta satar jarabawa ta hanyar fallasa amsoshin tambayoyin da ake shirin fitarwa ga ɗalibai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za'a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki tsakanin kasashen biyu. Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi, ya sake jaddada aniyar Hukumar na sauƙaƙe cinikayya a yankin, ta hanyar saukaka jigilar kayayyaki da kuma haɓaka haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka da su, musamman Jamhuriyar Nijar. Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata, yayin wani babban taron haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam ta Najeriya da takwararta ta Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Muhammadu Yaqouba, da aka gudanar da hedikwatan Kwastam da ke Maitama a Abuja. Tawagar Nijar ta kunshi shugabannin cibiyar inganta kasuwanci na Nijar wato Chamber des Commerce. Cikin mahimman abubuwan da aka duba a ganawar akwai saukaka zirga-zirga a kayan a iyakokin kasashen biyu ciki harda jigilar man metur na kamfanin Dangote, hakazalika za'a bada damar wucewar wasu kayayyaki da suka makale a bodar Kamba na jihar Kebbi, tireloli 1,600, da suka kwashe sama da watanni 2. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin na wannan mako ya ba da hankali ne akan yadda masu fama da larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a wasu sassan Najeriya.
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan gina kasuwanni na zamani da Gwamnatin Jihar Yobe ta sake ginawa a wasu sassan jihar domin karfafa harkokin kasuwanci da suka fuskanci koma baya, saboda matsaloli na Boko Haram. Shiga alamar sauti domin sauraron karin bayani.......
in August of 1991 the old guard from the Soviet Union attempted a Coupe to over thrown the burgeoning 'democracy' that was to be a westernized version of Russa. This failed due to lack of military support, general public interest , and the sheer energy of the Russian youth To reward these efforts, the country 'gifted' the largest heavy metal concert in recorded history where an audience of 1.6 MILLION (in Dr. Evil voice) fans watched Pantera, The Black Crows, METALLICA, and AC/DC perform. Not only were these career defining performances for Pantera and Metallica, but it also was the bookend to the last days of the Soviet Union. Yadda yadda yadda and happily ever after....or so you think....stay tuned to learn more As always follow us on the stuff Merch Store- http://tee.pub/lic/doEoXMI_oPI Patreon- https://www.patreon.com/Artandjacobdoamerica Website- https://artandjacobdoamerica.com/ Instagram- https://www.instagram.com/artandjacobdoamerica Facebook- https://www.facebook.com/artandjacobdoamerica/
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka' tare da Michael Kuduson a wanan mako ya yi duba kan wata mummunar cutar tumatiri da ake kira Tuta Absoluta ko kuma cuta mai karya garkuwar tumatir. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane gagarumar yarjejeniyar cinikayya mafi girma da ba'a taba ganin irinta ba, da aka cimma tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turain ƙasar India. Yarjejeniyar da aka cimma yayin ziyarar da shugabannin Turai suka kai New Delhi na ƙasar India, za ta bada damar kasuwanci mara shinge tsakanin ƙasashe mambobin EU 27 da kuma ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya, waɗanda suka kaɗai suka mamaye kusan kashi 25% na jimillar hada-hadar kasuwancin cikin gida na duniya da kuma cinkayyar mutane biliyan biyu. Domin ko a shekarar 2024 kaɗai, an yi cinikin sama da Euro biliyan 120 a tsakanin ɓangarorin biyu. Masu sharhi na ganin cewa kalaman wannan yarjejeniya da ɓangarorin biyu suka cimma, alaƙa da manufofin Shugaban Amurka, Donald Trump, musamman duba da yadda Tarayyar Turai ke ƙoƙarin faɗaɗa abokan hulɗar kasuwancinta, ba tare da dogaro da Amurka kaɗai ba. Yarjejeniyar dai na nufin cewa daga yanzu, India za ta soke ko kuma zaftare haraji kan hajoji da dama da take shigarwa yankin Turai, da suka haɗa da motoci daga kaso 110% zuwa 10% kachal, matakin da zai shafi kayan abinci da barasa da tufafi da kayan ado da dai sauransu. An dai ƙulla yarjejeniyar ce a daidai lokacin da mafi yawan ƙasashen duniya ke takun-saka da Amurka sakamakon haraji babu ƙaƙƙautawa da Donald Trump ke amfani da shi don tursasawa abokan hulɗa. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
The Yadda Yadda is back for episode 118, and with some big news in the music world. They discuss the possible fallout with Jess Hilarious & Loren Lorosa, Playboi Carti selling 300k and Kanye's sad fall from grace.
For episode 119, the Yadda Yadda crew takes on a heavy topic today, as the crew discusses the new single from YG, "2004". Playboi Carti also continues his dominance on the charts and we also discuss the new albums from MyNameIsntJMack and Saba & No I.D.