POPULARITY
An gudanar da ƙwarya-ƙwaryar biki don murnar cika shekaru 18 da buɗe Sashen Hausa na Radio France International, inda aka samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da sarakunan gargaji, ƴan siyasa da kuma masu sauraren rediyon da sauran kafafensa na yaɗa shirye-shirye. Ɗaya daga cikin manyan baƙi a taron shi ne Distinguished Senator Aliyu Ikra Bilbis wanda ya bayyana mahangarsa a game da waɗannan shekaru 18 na RFI Hausa. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal..............
Hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara .Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta kaya a wannan karowandada suka kuma bayyana cewa anfi samun asarar mafi girma akan kayan lambu amma hakan bai tsaya a bangare guda ba domin hatsi ma ba a barshi a baya ba
A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan batun hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara . Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta kaya a wannan karo, Ado Hassan yakasai shine mataimakin sakatare janar na kungiyar manoman shinkafa ta kasa RiFAN, reshen jihar Kano ya kuma bayyana cewa anfi samun hasarar mafi girma akan kayan lambu amma hakan bai tsaya a bangare guda ba domin hatsi ma ba a barshi a baya ba.
A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako;Rukayya Abba Kabara ce za ta jagoranci shirin tare da lalubo amsoshin tambayoyin da kuka aiko zuwa sashen hausa na Rfi.
Ga wannan tambayar da ta fito daga Aminu Adamu Malamadori, Abdulllahi Aliyu Koya Miga da Malam Musa Dan Malam Mai Wankin Hula Garbo Miga a jihar Jigawa dake Najeriya. Suka ce a yi musu bayani a kan matsayin magajin gari musamman a kasashenTurai da ake zaba? Shirin ‘Tambaya Da Amsa' , daga sashen Hausa na Radio France Internationale tare da abokinku Michael Kuduson
Tambayar da muka samu daga, Usman Manika Mai Ruwa Road Funtua a jihar Katsina, ya ce me ake nufi da dokar mallakar makamai a hukumance. Me haka ke nufi, kuma wake da alhakin Sanya wannan dokar mallakar makamai dan kare kai tsakanin gwamna da jami'an tsaro?
Yau shirin 'Mu Zagaya Duniya' shiri ne na musamman a kan ta'aziyyar abokin aiki, kuma mataimakin editan sashen Hausa na RFI, garba Aliyu Zaria, wanda Allah ya wa rasuwa a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairu, 2022.
A cikin wannan mako,ku saurari labarai da dama da suka shafi siyasar kasashen duniya,a daya geffen za ku ji irin wainar da aka tuya a taron sauyin yanayi na COP 26 a Glascow na Scotland.
A cikin shirin fina-finai daga nan sashen hausa na RFI,Hawa Kabir ta mayar da hankali tareda hiri da wasu jarumai a Duniyar Fim a Najeriya. A cikin shirin za ku ji halin da masu shirya Fim suka tsudduma a yanzu haka.
Kamar kowane mako, Sashen Hausa na RFI kan yi dubi game da wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Bashir Ibrahim Idris ya ba mu damar yin waiwaye a game da irin wadannan labarai cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya'.
Kamar kowane mako, Sashen Hausa na RFI kan yi dubi game da wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karo ma, Garba Aliyu Zaria zai ba mu damar yin dubi a game da irin wadannan labarai cikin shirin Mu Zagaya Duniya.
BBC Hausa Shirin Safe (Tue Feb 12th 2019 - 6:30am NG) [1] [2] Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi USA: 'Yan jam'iyyun Democrat da Republican, sun cimmawa matsayar kaucewa sake dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka. Nigeria: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar PDP, ya ce rashin kayan aiki ne ke dawo da hannun agogo baya a yaƙi da ta'addanci a ƙasar."I beleive our military are not getting the best of equipment... Na yi imani sojojin mu basa samun ingantattun kayan yaƙi. Wasu lokuta ma, za ka ga makaman da 'yan ta'adda ke amfani da su, sun fi na sojoji inganci da zamunanci." Election special: Sashen Hausa na BBC sun yi tanadi na musamman a lokacin zaɓen."Saboda idan ka fara shiri, ba za ka tsaya ba, tun ƙarfe shida na safe (6 AM), har zuwa ƙarfe goma sha ɗaya na dare. Ɗanɗanon shirin da sauran shirin zai sauya, kamar yadda muka sauya shi a lokacin da muka yi bakukuwan cika shekaru sittin da kafuwa."
Sashen Hausa na RFI na farin cikin gabatar muku da sabon shirin Dandalin Siyasa da zai rika nazari game da al'amuran da suka shafi siyasar Najeriya, Nijar, Afrika da sauran kasashen duniya. Shirin na makon farko tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari ne game da tasirin na'urar tantance masu kada kuri'u a zaben Najeriya, abin da masana ke cewa, ta na taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar magudi.
Sashen Hausa na Iran 1 na 2017-09-05 • Sashen Hausa na Iran 2 na 2017-09-05 • VOA Hausa Shirin Safe 0500 UTC na 2017-09-05 • VOA Hausa Shirin Hantsi 0700 UTC na 2017-09-05 • VOA60 AFIRKA:Masu Binci...