POPULARITY
Hukumar kula da jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya ta JAMB ta nemi gafarar jama'ar kasar saboda matsalolin da aka samu wajen jarabaswar bana, wadda ta kai ga dalibai sama da miliyan guda da rabi suka kasa samun makin da ake bukata. Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede cikin hawaye ya nemi gafarar jama'a da kuma daukar alhakin lamarin.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Umar Saleh Gwani masanin harkar sadarwa.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A kasar Gabon, ana ci gaba da yakin neman zabe a yau da ke jajiberin zaɓen Shugaban ƙasar,wanda ya haɗa 'yan takara takwas. Gwamnati ta ayyana ranar zaben gobe a matsayin ranar hutu, domin baiwa masu rajista a larduna damar yin balaguro.Ƴan adawa sun bayyana damuwarsu ganin ta yada shugaban majalisar sojin kasar ke amfani da kadarorin gwamanti a yakin zaben.Abdoulaye Issa ya tattauna da Janjouna Ali Mahaman Sani, masani siyasar kasar ta Gabon da kewaye.Ga kuma yada zantawar tasu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
A Gabon, ana ci gaba da yakin neman zabe a yau da ke jajuburin zaben Shugaban kasar,wanda ya hada 'yan takara takwas. Gwamnati ta ayyana ranar zaben gobe a matsayin ranar hutu, domin baiwa masu rajista a larduna damar yin balaguro. Ƴan adawa sun bayyana damuwarsu ganin ta yada shugaban majalisar sojin kasar ke amfani da kadarorin gwamanti a yakin zaben. A game da zaɓen, Abdoulaye Issa ya tattauna da Janjouna Ali Mahaman Sani, masanin siyasar ƙasar ta Gabon da kewaye.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu
Hukumar EFCC dake yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sanar da kwato kuɗaɗen da suka kai naira Triliyan guda a shekarar da ta gabata, abinda ke nuna irin nasarar da ta samu, baya ga samun nasara a kotu a shari'o'in da suka kai sama da 4,000.Dangane da wannan nasarar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Isa Sanusi, Daraktan Ƙungiyar Amnesty a Najeriya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiya hirar...........
Shugaban Ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya ƙaddamar da wani shirin diflomasiya domin shawo kan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, wadanda suka fice daga cikin ƙungiyar ECOWAS.A ƙarshen makon da ya gabata, shugaban ya ziyarci waɗannan ƙasashe guda uku, inda ya gaba da shugabannin su.Dangane da tasirin wannan ziyarar, Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da Dr Elharun Muhammad na Cibiyar kula da manufofin ci gaban ƙasashe dake Kaduna, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Majalisar Dattawan Najeriya ta kaddamar da bincike domin gano yadda bindigogi dubu 178,459 suka bata daga rumbun aje makaman 'yansanda daga shekarar 2018 zuwa yanzu. Shugaban kwamitin binciken, Sanata Samuel Godwin ya ce daga cikin bindigogin, dubu 88,078 manya ne kirar AK-47, yayin da dubu 3,097 kuma kanana ne.Dangane da wannan labari mai tayar da hankali, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Sule Ammani, Yarin Katsina.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan fitar da amfanin gona da aka noma a damunar bara da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce a ke yi sakamakon karyewar darajar kuɗin ƙasar, lamarin da su ka ce ya sanya su suma su ka tsunduma cikin masu ribibin sayen amfanin gonar, su na adanawa a rumbunansu domin maganin gobe. A farkon makon watan Janairun wannan shekarar, a yayin ziyarar gaisuwar sabuwar shekara da kungiyar gwamnonin Najeriya ta ka kai wa Shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Ƙungiyar gwamnonin, kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi bayani tare da ƙarin haske a kan aniyar gwamnonin.Sai dai kungiyar Manoman ƙasar wato AFAN, ta bakin kakakinta Muhammad Magaji, ta bayyana cewa ba sabon abu bane yadda ake fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje domin neman riba, amma ta ce ƴan kasuwa da ke sayen kayan a hannun manoman ne ke yin hakan ba manoman da kansu ba.Kasancewar matakin da gwamnonin su ka ce sun fara ɗauka na sayen kayan abinci su na adanawa na da buƙatar fashin baƙi daga masana, mun tuntuɓi Malam Abubakar Lawal Kafinsoli na sashen nazarin noma a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina dangane yadda hakan zai taimaka wa manoma da kuma harkar noma a ƙasar, wanda ya ce wannan ba hanya ba ce mai bullewa ba, musamman ga talakawan kasar.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.
A yau shirin tamabaya da amsa zai fara ne da kawo muku takaitaccen tarihi ne akan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana wato John Dramani Mahama da tasirin sa ga lamuran ƙasar.
Daga cikin abubuwan da shirin Mu Zagaya Duniya na wanan makon ya yi waiwaye akai akwai yadda gobarar daji ce ke cigaba da tafka barna a birnin Los Angeles inda ta raba mutane kusan dubu 200 da muhalansu bayan kone fadin kasa da gine-gine masu yawan gaske.
A wannan talatar ce aka rantsar da John Mahama a matsayin shugaban Ghana, cikin yanayi na tarin kalubale da suka hada da na matsin tattalin arziki biyo bayan lashe zaben da aka yi cikin kwanciyan hankali da lumana. Masu bibiyar siyasa a kasar sunyi ittifakin cewa duk da cewa Mahaman ya taba jagorancin kasar, ya dawo ne a lokacin da lamura suka sauya ainun.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.
Ƴan Najeriya na fatan ganin samun sauƙi a wannan shekara ta 2025, bayan da suka shiga wani yanayi na matsalin tattalin arziki a shekarar 2024 da muka yi bankwana da ita, sakamkon wasu matakai da gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauka, masamman janye tallafin man fetur da kuma barin naira ta ceci kanta a kasuwar canjin kuɗaɗe. Shugaban ƙasar Bola Tinubu dai ya ce gwamnatinsa za ta rage hauhawar farashi a shekarar 2025 ta hanyar haɓaka noma da tallafa wa masana'antu, danage da fatan da ƴan Najeriyar ke da shi da kuma hasashen masana dangane da farfadowa tattalin arziki a wannan shekara, Ahmad Abba ya tattauna da Farfesa Kabiru Isa Dandago na jami'ar Bayaro da ke Kano, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
A ranar Laraba ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudin ƙasar na shekarar 2025 na naira Tiriliyan 47.9. Sai dai wani batu da ya haifar da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya dangane da kasafin kuɗin na baɗi, shi ne yadda aƙalla kaso 30 zuwa 32 na yawan kuɗaɗen za su tafi a biyan basuka ko kuma kudin ruwan basukan, kwatankwacin naira tiriliyan 15 da biliyan 800, adadin da ya zarce yawan kudaden da aka warewa tsaro, ilimi, lafiya da manyan ayyuka.Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Kabiru Mohammed Dan Bauchi...
Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani a wannan mako kamar yadda ya saba ya amsa wasu jerin tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki kuwa har da amsar tambaya kan tarihin Marigayi shugaba Ibrahim Ra'isi na Iran da Allah ya yi rasuwa sakamakon haɗarin jirgin sama cikin shekarar nan.
Daga cikin Labarun da suka fi ɗaukar hankali a makon da ya ƙare akwai jerin makamai masu linzamin da Iran ta kai wa Isra'ila hari da su, a yayin da ita kuma Isra'ilar ta karkatar da hare-haren da take kai wa a Gaza zuwa Kudancin Lebanon, h da zummar murkushe mayakan Hezbolla A Najeriya kuwa ɗimbin Iyallai ne suka shiga alhinin rashin da suka yi, biyo bayan nuutsewar da wani jirgin ruwa yayi ɗauki da fasinjoji sama da 300 da ke ƙoƙarin tsallaka kogin Kwara domin zuwa taron Maulidi.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirin gudanar da wani taron matasa na kasa domin basu damar tattauna matsalolin da suka addabe su da zummar share musu hawaye. Ana saran wannan mataki ya kwantar da hankalin fusatattun matasan wadanda ke korafi a kan yadda ake gudanar da mulkin Najeriya.Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Muntaqa Abdulhadi Dabo, daya daga cikin fitattun matasan kasar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Shugaban majalisar gudanarwar Kungiyar tintiba ta arewacin Najeriya wato ACF, Alhaji Bashir Dalhatu ya nemi gafarar 'yan arewacin kasar saboda abinda ya kira gazawar su ta kare yankin daga fadawa rikici mafi muni a tarihinsa. Dalhatu ya ce suna ci gaba da lalubo hanyar shawo kan wadannan matsaloli da suka yiwa yankin kamun kazar kuku. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu tare da Bashir Ibrahim Idris.......
A jawabin da ya gabatar ga al'ummar ƙasar biyo bayan soma zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsadar rayuwa, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi buƙaci a jingne zanga-zanga tare da bayyana aniyar tattaunawa da waɗanda suka shirya zanga-zangar. Sai dai an yi ta mayar da martani a game da jawabin nasa, wanda masu sharhi ke cewa bai taɓo inda ake so ya taɓo ba, hasali ma tamkar bai fahimci bukatun al'ummar ƙasar ba.A kan haka ne Aisha Shehu Kabara ta tattauna da Kwamared Bello Basi Fagge, wani mai fafutuka, kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kulluma Kano, Najeriya.
Kamfanin Dangote ya yi watsi da zargin samar da man da bashi da inganci da kuma fara aiki ba tare da lasisis ba da hukumomin Najeriya suka masa, inda ya sake jaddada cewar tabbas wasu mutane na neman yiwa matatar tasa zagon kasa. Shugaban hada hadar kasuwanci na kamfanonin Dangoten Rabiu Umar ya bayyana haka a tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris. Kuna iya latsa alamar sauti domin jin yadda zantawar tasu ta gudana...
Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump, wanda ke takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam'iyyar Republican a zaɓe mai zuwa ya tsallake rijiya da baya, bayan da wani mutum mai shekaru 20 ya ya yi yunƙurin kashe shi ta hanyar harbin bindiga, yayin da ya ke yaƙin neman zaɓe a jihar Pennsylvania a ranar Asabar, al'amari da ya ta'azzara rarrabuwar kawuna mai muni da a ke da ita a fagen siyasar Amurka. Ko wane tasiri ne hakan zai yi ga siyasar wannan ƙasa, wadda ke zama a matsayin abin koyi, kuma ke da'awar kare dimokaradiyya a faɗin duniya. A kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da masanin siyasar ƙasa da ƙasa, Farfesa Kamilu Sani Fagge.
Shugaban gudanarwar kungiyar ECOWAS Omar Alieu Touray yace kungiyar tana fuskantar baraznar rugujewa sakamakon ficewar kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuruyar Nijar, wadanda tuni suka kafa kungiya a tsakanin su. Tourey yace ficewar su zata raunana kungiyar ta fuskar kasuwanci da zirga zirgar jama'a da kuma yaki da ta'addanci. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Cika, masanin harkar diflomasiya, kuma ga yadda hirar su ta gudana. Danna alamar saurare don jin cikakkiyar tatttaunawar
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali da kan kiranda wasu kungiyoyi suka yi wa gwamnatin Najeriya da ta yi wa Allah ta farfado da harkokin noma da sarrafa manja kamar yadda aka san ƙasar a baya. Kungiyar ɗalibai ta ƙasar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya farfado da harkokin sarrafa manja da Allah ya wadata ƙasar da shi, ta yadda hajar zata wadata ƴan Najeriya da ma fitar da shi ƙasashen waje kamar yadda lamarin yake a baya. Kirin ƙungiyar ta NANS na zuwa ne bayan da Shugaban ƙungiyar masu samar da manja ta Najeriya Mista Alphonsus Inyang, ya ce Najeriya na kashe sama da daka miliyan 600 duk shekara wajen shigo da Manja daga katare duk da cewa Allah ya albarkaci ƙasar da kwakwan Manja.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......
Shirin tamabaya da amsa na wannan mako zai kawo muku tarihin shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar 19 ga watan Mayun shekarar 2024, tare da bayani akan ma'askin dare kamar yadda aka aiko mana da tambayoyi akansu, sai a kasance tare da mu a cikin shirin.
A cikin shirin Mu Zagaya Duniya akwai cikar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu shekara guda a kan karagar Mulki.sai kuma yadda asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, yayi A wadai da KARUWAR cin zarafi da take hakkin kananan yara a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar a dalilin ta'azzarar ayyukan kungiyoyin ‘yan ta'adda. da kuma sauran rahotanni da ke biye dasu.
A ranar Talata ne aka rantsar da sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, wanda ya lashe zaben kasar a makon da ya gabata da kaso sama da 54 cikin 100 na yawan kuri'u sama da miliyan 7 da aka kada. Faye shine shugaba mafi kankantar shekaru a Afrika, kuma ya lashe zaben ne a wani yanayi da kasar ke cikin chukumurdar siyasa.Matashin ya zama shugaban kasa ne kasa da makonni biyu bayan fitowar sa daga gidan yari.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Kungiyar ‘Yan Nijar mazauna Cote d'Ivoire ta bukaci a cirewa Nijar takunkumai da aka kakaba mata sakamkon juyin mulki da sojoji suka yi, saboda halin kunci da hakan ya jefa su ciki. Shugaban kungiyar ta Ho consei de Nijar a Cote d'Ivoire Alhaji Abdou Jibo ya yi wannan kira, yayin zantawa ta musamman da sashin hausa na RFI a Abidjan.Amma ya fara yi wa Ahmad Abba bayani kan zamantakewarsu a kasar da ke mamba a ECOWAS.Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar
Sabon Babban Daraktan RFI, Mr Jean-Marc Four yanzu haka yana ziyarar aiki a Najeriya dokin ganin yadda RFI Hausa ke gudanar da ayyukansa tare da ganawa da ma'aikatan sashen. Yayin ziyarar Mr Four ya bayyana gamsuwa da kwararrun ma'aikatan dake aiki da RFI Hausa tare da gabatar da sabon albishir a kan shirin da yake da shi ga sashen da kuma sauran sassan da ake amfani da karsunan Afirka. Ga yadda zantawarsu ta gudana da Bashir Ibrahim Idris.
Maudu'in na wannan rana ya mayar da hankali ne, kan rahoton da kwamitin shugaban Najeriya ya fitar game da badakalar da aka samu tsohon shugaban babban bankin kasar, Godwin Emefile, da aikatawa na bude asusun bankuna sama da 500 a kasashen waje. Sai dai, Godwin Emefiele, ya yi watsi da rahoton binciken da ya bayyana cewar ya bude asusun bankuna har guda 593, wadanda yayi amfani da su wajen boye makudaden kudaden gwamnati da niyyar yin kwanciyar magirbi akansu.Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Emefiele, wanda aka bayar da belinsa a ranar Juma'a, ya ce tuni ya bai wa lauyoyinsa umarnin shigar da kara kan rahoton da yace babu abinda ya kunsa sai karairayi domin bata masa suna.SHiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Nasiruddeen Muhammad ya gabatar.
A Najeriya, Kungiyar CISLAC da ke bin diddigir ayyukan Majalisar da yaki da rashawa ta gudanar da wani taron karawa juna sani a birnin Legas dangane da kokarin samar da sauye sauye a harkokin zaben Najeriya da kuma kyautata nagarta a bangaren shari'un bayan zabe. Shugaban kungiyar Auwal Musa Rafsanjani ya bayyana mana muhimammancin taron a zantawarsa da Ahmed Abba
Bayan share tsawon watanni ana zaman tankiya, daga karshe dai shugaban Senegal Macky Sall ya sanar da cewa ba zai tsaya takarar neman shugabancin kasar karo na uku a zaben da za a yi cikin watan fabarairun shekaru mai zuwa ba. Shugaba Sall, ya ce ya yanke shawarar kin tsaya takarar ce duk da cewa Kundin Tsarin Mulki ya ba shi dama, sannan kuma akwai masoyansa da dama da ke fatan ganin ya tsaya a zaben mai zuwa. Shin me za ku ce a game da mataki da shugaban na Senegal na ya dauka? Shin anya ya yi hakan ne saboda nuna kishin kasa ko kuma saboda jajircewar masu adawa da tsayawarsa a zaben? Ku latsa alamar ssauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Al'amurran yau da kullum sun fara daidaita a birnin Moscow fadar gwamnatin kasar Rasha, bayan da jagoran kamfanin Wagner Yevgeny Prigozhin ya sanar da dakatar da boren da yake yi wa gwamnatin Vladimir Putin. Shugaban kasar Belarusse Alexander Loukochanko ne ya yi nasarar shawo kan shugaban Wagner domin jingine yunkurinsa na afka wa birnin Moscow, tare da amince wa ya bar Rasha zuwa Belarusse. Domin jin dalilin da suka haddasa tsamin dangantaka tsakanin Putin da Prigozhin, da kuma yadda hakan zai shafi makomar yakin Rasha da Ukraine? Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Janar Idris Bello Dambazau mai ritaya. A latsa alamar sauti don jin tattaunawar ta su.......
Babbar kwalejin horar da likitoci ta duniya, wato ‘International College of Surgeons' reshen Najeriya, ta ce likitoci dubu 6 da 221 ne suka koma aiki Birtaniya daga Najeriya a cikin shekaru 6 da suka gabata, saboda neman rayuwa mai inganci. Cibiyar horar da ma'aikatan lafiyar ta ce wannan rige rigen da likitoci ke yi na barin Najeriya, ya dada haifar da matsala da kuma sanya mutane sama da miliyan 40 basa iya ganin likita guda da zai duba halin lafiyarsu. Shugaban kwalejin, Farfesa Akanimo Essiet ya gabatar da wadannan alkaluma bayan kammala taron masanan kwalejin karo na 56, inda ya bayyana cewar matsalar ta yi matukar illa wajen rage yawan ma'aikatan lafiya a Najeriya. Essiet ya ce kafin shekarar 2022, likita guda ne ya ke kula da marasa lafiya dubu 4 a Najeriya, sabanin ka'idar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gindaya wadda ta ce ana bukatar likita guda domin ya kula da marasa lafiya 600. Essiet ya ce an samu gibi sosai wajen jami'an da ke aikin kula da lafiya a Najeriya, yayin da adadin likitocin da ke aiki a Birtaniya ya tashi daga 4,765 a shekarar 2017, zuwa 10,986 a wannan shekarar. Dangane da dalilan da suka sa ma'aikatar lafiyar ke barin Najeriya zuwa Turai, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Kamaluddeen Garba, ‘dan Najeriya da ke aiki a Birtaniya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Hukumar kula da afuwa a Najeriya ta bukaci rundunar ‘yan sandar kasar ta dauki tubabbun ‘yan tsagerun yankin Neja Delta aikin dan sanda, don taimakawa wajen samar da tsaron kasa. Shugaban hukumar, Janar barry Ndiomu ne ya mika wannan bukata, wanda ke zuwa a daidai lokacin da sufeto janar na ‘yan sandan kasar, Usman Baba Alkali ke korafin cewa kan yadda matasa daga yankin Neja Delta ba sa iya cika gurbin da aka ware musu a lokacin dibar sabbin ‘yan sanda. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauanwa da Muhammad Wakili tsohon kwamishinan 'yan sanda.
Gwamnatin Nijar ta kammala taron kwanaki biyu da ta shirya domin gabatar da shirin raya kasar da take da shi ga manyan ‘yan kasuwa da zuba jari daga kasashen duniya. Shugaban kasar Bazoum Muhammad da manyan jami'an gwamnati ne suka halarci taron na kwanaki biyu a birnin Paris na kasar Faransa Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ministan lafiya na kasar, Dakta Ilyasu Idi Mai-Nasara wanda ya kasance daga cikin tawagar da suka yiwa shugaban rakiya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shugaban kwamitin zaman lafiya a Najeriya, Janar Abdusalami Abubakar ya bayyana matukar damuwa dangane da irin zafafan kalamun da 'yan siyasa ke amfani da su a dai dai lokacin da ake shirin zaben shekara mai zuwa. Tsohon shugaban kasar ya bukaci Yan takarar shugaban kasar da su ja kunnen masu magana da yawunsu domin kaucewa kalaman da zasu tinzira tashin hankalin da zai kaiga rasa rayukan jama'a. Abdusalami ya bukaci yan siyasar da su mutunta alkawarin da suka dauka lokacin da suka rattaba hannu akan yarjejeniyar da aka gabatar musu. Dangane da wannan gargadi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Usman Muhammed, na Cibiyar bunkasa dimokiradiya dake Abuja kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya ci gaba da kawo muku tarihin fiitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a shekarar 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi na 2 daga 1981 zuwa 2001.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya ci gaba da kawo muku tarihin fiitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a shekarar 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi na 2 daga 1981 zuwa 2001. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya ci gaba da kawo muku tarihin fiitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a shekarar 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi na 2 daga 1981 zuwa 2001.
Lauyan dake kare shugaban haramcaciyar kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra a Najeriya, Nnamdi Kanu, wato Mike Ozekome, ya rubutawa shugaban kasar Muhammadu Buhari wasika, inda yake bukatar gagaguta sakin Kanu ta hanyar siyasa. Lauyan yace sakin Kanu zai kawo karshen durkushewar tattalin arzikin Yankin Kudu maso Gabas, saboda tilasta zaman gida kowacce litinin da magoya bayan sa suka yi. Dangane da wannan bukata, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barista Abdullahi Jalo, lauya mai zaman kansa a Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin ya maida hankali ne kan zaben sabbin shugabannin gudanarwar hukumar kwallon kafar Najeriya wato NFF, da ya gudana makon jiya a birnin Benin na jihar Edo da ke kudancin kasar, inda aka zabi Alhaji Ibrahim Musa Gusau a matsayin sabon shugaba, bayan karewar wa'adin Mr Amaju Pinnick wanda ya kwashe tsahon zango biyu yana shugabancin hukumar.
Sabon Shugaban Kasar Kenya, William Ruto yayi gargadi dangane da matsalar sauyin yanayi da farin da Kenya ke fama da shi, wanda ya shafi wasu kasashen Afirka ta Gabas, inda miliyoyin mutane ke fuskantar barazanar yunwa. Shugaban ya kuma tabo batun tashin hankalin da ake samu a Habasha da kuma dalilin da ya sa ya nada tsohon mai gidan sa Uhuru Kenyatta a matsayin mai shiga Tsakani domin sasanta rikicin. Latsa alamar sauti domin sauraron fassarar kalaman nasa.
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya ci gaba da kawo muku tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.
Shirin Ra'ayoyin Masu Saurare na wannan rana ya tattauna ne kan matakin gwamnonin arewacin Najeriya na bayyana goyan bayansu ga shirin kafa rundunar ‘Yan Sandan Jihohi domin tinkarar matsalar tsaron da ta addabi yankinsu. Shugaban gwamnonin arewacin kasar Simon Lalong ya sanar da amincewar bayan taron da gwamnonin suka yi da Sarakunan gargajiyan da ke yankin, bayan da aka share tsawon lokaci gwamnoni daga sauran yankunan kasar na yin kira da a bai wa jihohi damar kafa wannan runduna.
Gwamnonin arewacin Najeriya sun bayyana goyan bayansu na shirin kafa rundunar 'Yan Sandan Jihohi domin tinkarar matsalar tsaron da ta addabi yankinsu. Shugaban gwamnonin arewacin kasar Simon Lalong ya sanar da amincewar bayan taron da gwamnonin suka yi da Sarakunan gargajiyan da ke yankin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Naja'atu Muhammad, kwamishiniya a hukumar 'Yan Sanda ta kasa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
Shugaban kungiyar likitocin dake kula da mahaukata a Najeriya, yace yan kasar sama da miliyan 60 ke fama da matsalar wani nau'i na tabin hankali, abinda ke nuna kusan kashi daya bisa uku na jama'ar kasar na fama da wannan matsalar. Shehin malamin yace kashi 10 kacal na masu fama da wannan matsalar ce ke samun kula a asibiti. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin da Hauwa Muhammad ta shirya.
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya ci gaba da kawo muku tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.
Shirin Tambaya da Amsa tare da Michael Kuduson a wannan mako ya sake amsa muhimman tambayoyin da masu sauraro suka aiko, ciki har da amsar tambaya kan tasirin tsohon shugaban tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev da ya mutu a farkon makon da muke bankwana da shi, mutumin da ya yi rawar gani wajen kawo karshen yakin cacar baka a Duniya da kuma baiwa kasashen da ke karkashin tarayyar ta soviet damar cin gashin kansu.
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya ci gaba da kawo muku tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yayi gargadin cewar dimokiradiyar kasar na samun koma baya, saboda yadda ake samun shugabannin kama karya musamman a matakan jihohi. Jonathan yace tabbas sha'anin mulki a matakan jihohi na kauce hanya, sabanin yadda aka saba, saboda yadda gwamnoni suka samu karfin da ya wuce kima, da kuma yadda majalisu ke shakkar taka musu birki idan sun kauce hanya. Dangane da wannan gargadi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Jafar Lawal Dabai, na Babbar Kwalejin Fasaha dake Kaduna, a Najeriyar. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da aikewa da sakon ta'aziyar rasuwar tsohon shugaban Rasha, Mikhail Gorbachev, wanda ya rasu yana da shekaru 91 a duniya. Gorbachev ne shugaban tarayyar Soviet na karshe, kafin rushewar ta yadda ta zama kasashe da dama, abinda ya kawo sauyi a siyasar duniya. Domin sanin koshi waye da irin gudumawar da ya bayar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Usman Muhammad, na Cibiyar Bunkasa Dimokiradiya dake Abuja. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya ci gaba da kawo muku tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.