Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan wasu dalilai dake haifar da rashin samun isasshen barci a cikin dare. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson, don jin sauran tambayoyin da kwararru suka amsa a wannan mako.
Shirin TAMBAYA DA AMSA na wanan makon tareda Nasiru Sani ya amsa wasu muhimman tambayoyin da suka shige muku dufu. Ku shiga cikin alamar sauti domin jin karin bayani.....
A yau shirin tamabaya da amsa, tare da Nasiru Sani, zai kawo muku bayanai ne akan tasirin tsarin harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙabawa ƙasashen Canada da Mexico da kuma China akan ƙasashe Afirka. Shirin ya kuma zanta da kwararru a fannin lafiya, kan dalilan da ke sanya shan ruwa a kai.Akwai kuma cikakken bayani kan Sultan Makenga, wato jagoran ƙungiyar 'yan tawayen M23 wanda ya hana zaman lafiya a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, musamman ma a gabashin ƙasar.Shiga alamar sauti, domin saurarin cikakken shirin.
Shirin TAMBAYA DA AMSA na wanan rana tareda Nasiru Sani, cigaba ne na tarihin Sarkin Musulmi Muhammed Bello da kuma wasu karin tambayoyi na masu sauraro suka aiko mana. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin....
Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani bisa al'ada kan kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da ku masu sauraro kuka aiko mana. A yau shirin Tambaya da Amsa zai amsa tambaya wani mai sauraro ne wanda ke neman sani ko kuma ƙarin bayanai game da tasirin matakin matatar man Dangote na daina sayar da ɗanyen mai da Naira, ga tattalin arziƙin ƙasar da kuma yadda hakan zai shafi ɗaiɗaikun jama'a.Don jin amsar wannan tambaya da kuma ƙarin wasu da shirin ya amsa a wannan mako, ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Kasancewar Azumin na watan Ramadan ya kunshi ladubba da tarin alkhairi a cikinsa, waɗanda suka haɗa ƙara kusanci ga mahalicci ta hanyar gudanar da ɗumbin ibadu da kyautatawa juna da nisantar dukkanin ayyuka ko lamura da suka saɓawa shari'a. Watan na Ramadan wata ne mai matuƙar daraja wanda dukkanin musulmi ke neman falala daga Allah a cikinsa, wakimmu na jihar Bauchi a Najeriya Ibrahim Malam goje ya zanta da Shehin Malami Imam Muhammad Hadi Abubakar, Na'ibin Babban Limamin Masallacin Juma'a na At-Taqwa, da ke garin Bauchi dangane da muhimmancin watan na Ramadana.
A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne dangane da ra'ayin riƙau a fagen siyasa wanda jama'a da dama ke neman bayani akansa.
Shirin TAMBAYA DA AMSA da wanan mako tareda Nasiru Sani ya kuma amsa tambaya da wasu suka aiko mana kan muhimmanci Garin Goma na Jamhuriya Dimokradiyar Congo ga 'yantawayen M23. Ku latsa alamar sauti domin jin karin bayani
Tambaya da Amsa,bisa al'adar shiri ne da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, Shin kome me ke kawo faduwar gaba? Jin tsoro ne ko kuma wata alama ce ta gazawar zuciya?
Shirin na Tambaya da amsa na baiwa masana damar kawo ƙarin haske a wasu daga ciƙin tambayoyinku daga nan Rfi,shin ko wata kasa a doron duniyar nan, ta taba fusƙantar irin gobarar da ta tashi a birnin Los Angeles na Amurka kuma duk da kasancewarta babbar ƙasa mai isassun kayan aiki,ko mai ya hana ya hana Amurka samun nasarar shawo kan gobarar a cikin ƙanƙanin lokaci
Shirin 'Tambaya Da Amsa na wannan mako zai kawo muku tarihin kafuwar ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch, da kuma tarihin Gadar Jebba da ke tsakiyar Najeriya..
A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan yanayin tattalin arzikin Kasashen duniya da hanyoyin da kan haifar da ci gaban sa da kuma karayarsa a wasu kasashen na duniya.A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan yanayin tattalin arzikin Kasashen duniya da hanyoyin da kan haifar da ci gaban sa da kuma karayarsa a wasu kasashen na duniya.
A yau shirin tamabaya da amsa zai fara ne da kawo muku takaitaccen tarihi ne akan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana wato John Dramani Mahama da tasirin sa ga lamuran ƙasar.
Shirin TAMBAYA DA AMSA na wanan makon tareda Nasiru Sani , ya amsa tambaya kwaraarre kan sha'anin siyasar kasa da kasa gameda kungiyar 'yan tawayen HTS wadda ta hambarar da Bachar Al-assad daga karagamar mulki.
A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan alfanun shan lemon tsami da akasin hakan akan lafiyar mutane.
Shirin 'Tambaya da Amsa na wannan makon tare da Nasiru Sani ya amsa wasu daga cikin tambayoyin masu sauraro ciki har da masu neman ƙarin bayani kan wace tafi ƙarfin iko tsakanin Majalisun Najeriya biyu wato Dattawa da ta Wakilai.
Shiri ne da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma a kowane mako yake zuwa muku a daidai wannan lokaci. A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku taƙaitaccen tarihi ne na fitattun jaruman film ɗin India domin sanin inda suka fito da kuma alaƙar dake tsakaninsu, wato Sharuh khan da Salman Khan.
Shiri ne da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma a kowane mako yake zuwa muku a daidai wannan lokaci.A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku ƙarin haske ne akan Salam sashin Hausa na RFI wai ko akwai bambanci tsakanin aikin Kotun ICC da Kotun ICJ idan akwai shi mine ne kuma a wasu kasashe ne kotunan suke sannan a wasu shekaru ne aka samar da su. Sannan akwai tambayar dake neman karin bayani dangaen da tasirin dumamar yanya ga halittu.
A cikin wannan shirin Tambaya da amsa,masu sauraro sun bukaci karin haske a kan wannan kungiya ta 'yan Arewa da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ke shugabanta.Akwai wasu daga cikin amsoshin tambayoyin masu saurare daga nan sashin hausa na Rfi.
A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku takaitaccen tarihi ne akan yankin Bakasi wanda ke kudu maso kudancin Najeriya da kuma tasirin sa wadda yakai ga samun tababa akansa tsakanin Najeriya da Kamaru. Sai a latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
A cikin wannan shirin ,Nasir Sani ya tattaro tambayoyin ku masu sauraren Rfi hausa,wandada a cikin wannan shirin za ku ji amsoshin wasu daga cikin su.Masu saurare sun bukaci samun karin haske dangane da yarjejeniya a bangaren da ya shafi yankinn Neja Delta da Gwamnatin Najeriya.Shirin Tambaya da amsa na zuwa maku ne a duk karshen mako daga sashen hausa na Rfi.
Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani a wannan mako kamar yadda ya saba ya amsa wasu jerin tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki kuwa har da amsar tambaya kan tarihin Marigayi shugaba Ibrahim Ra'isi na Iran da Allah ya yi rasuwa sakamakon haɗarin jirgin sama cikin shekarar nan.
A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan tasirin hotunan mutane ko dabbobi ko na tsirrai da akan sanya a jikin takardun kudi da na kwandaloli.
A cikin shirin tambaya da amsa, a duk karshen mako,Nasiru Sani kan kawo maku wasu daga cikin amshoshin ku masu saurare.A wannan mako za ku ji amsa dangane da siyasar Birtaniya,da wasu daga cikin amsoshin tambayoyin ku masu saurare.
Shiri ne da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, domin samun fahimta kan batutuwa ko abubuwan da suka shige muku duhu wanda ke zuwa muku a kowanne mako kuma a daidai wannan lokaci. Kuma a yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan tasirin da tarzoma ke da ita ne akan tattalin arziki.
Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani a wannan mako ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da aka aika mana, Shirin ya amsa tambaya kan yadda neman ƙarin bayani da wani mai sauraro ya yi kan zubu ko kuma yanayin siyasar Birtaniya dama banbancinta da siyasar da ake gani a ƙasashen da ta mulka.Wannan da sauran tambayoyi na tafe a cikin shirin na wannan mako.
A cikin shirin Tambaya da amsa na wannan mako zaku ji fashin baki kan Ma'askin dare, da kuma duniyar aljanu Danna Alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani
Shirin 'Tambaya da amsa' na wannan mako kamar kullum ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aika, masaman ƙarin bayani gameda yarjejeniyar SAMOA da ya haifar da cece -kuce tsakanin gwamnatin Najeriya da ƴan ƙasar masannan malaman addini.
A cikin shirin Tambaya da amsa daga Sashen hausa na Rfi,masu sauraro kan aiko da tambayoyin su,wandada muke mika su ga masana da suke yi mana fashin baki a kai.A cikin wannan shirin Nasir Sani ya leko wasu daga cikin tambayoyin masu sauraro.
Shirin tambaya da amsa na wannan makon ya amsa tambayoyi da dama da masu saurare suka aiko mana su. Danna alamar saurare don jin masoshin tambayoyin ta cikin shirin tare da Nasiru Sani
Shirin 'Tambaya Da Amsa' wanda ya ke zuwa duk mako a wannan tasha zai amsa tambayar da ke neman bayanni a kan ayyukan Hukumar Lafiya ta Duniya,,musamma inda take samun kuɗaɗen gudanar da ayyukanta da kuma yadda taa ke ɗaukar ma'ikata.
Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru sani kamar kowanne mako ya na gayyato ƙwararru ne don amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana. A wannan mako, shirin ya amsa tambaya game da tasirin taken ƙasa da ake kira National Anthem a Turance.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..
Shirin tamabaya da amsa na wannan mako zai kawo muku tarihin shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar 19 ga watan Mayun shekarar 2024, tare da bayani akan ma'askin dare kamar yadda aka aiko mana da tambayoyi akansu, sai a kasance tare da mu a cikin shirin.
Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a game da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC da batun sammacin kama firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da wasu shugabannin ƙungiyar Hamas. Ku latsa alamar sautin donjin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.........
Shirin, wanda ke zuwa muku duk mako a lokacin irin wannan, yana kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wasu daga cikin masu bibiyanmu suka aiko mana ne, kuma a yau, za ku ji amsar tambayar da ke neman ƙarin bayani a kan salon mulkin gurguzu, da kuma ko da gaske yana da kamanceceniya da mulkin kama-karya kamar yadda masu kushe shi ke fadi. Sai a kasance tare da mu.
‘Tambaya Da Amsa' shiri ne da ke kawo amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Bayan janye tallafin lantarki a Najeriya, hukumar samar da wutar ta yi bayani game da rukunnai dabam dabam na masu amfani da wuta da abin da za su biya a matsayin kudin wuta. A yi mun ƙarin bayani a kan wadannan rukunnai. Menene ya sa dole sai an kasa al'umma zuwa rukuni -rukuni?
Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a kan yakin duniya da yadda za a kauce wa aukuwar wani yakin duniya.
shirin a wannnan mako zai ba da hankali ne akan abinda ya kai ga katsewar hanyoyin sadarwa na internet a wasu sassa na Nahiyar Afirka.
Shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa mukua wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, za mu ji karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol. Abokinku, Michael Kuduson ne ke muku lale marhabun.
Kamar yadda muka saba, shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware, da kuma tasirin haka a kan kasar da aka maida saniyar ware.
A cikin shirin na wannan mako,Michael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyin,ko wadanan hanyoyi ne ake bi domin samun tikiti kujerar wakili a Kwamity tsaro na MDD.Ya kuma duba wasu tambayoyi da suka jibanci bangaren tsaro da sauren su.
A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako, Michael Kuduson ya mayar da hankali a tambayar da ta shafi yan Tawayen Houthi na kasar Yemen.Sai ku biyo mu.
Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin tarihin Hausawa ‘yan asalin kasar Mali. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.
Shirin ‘Tambaya Da Amsa' yana kawo muku amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana ne, kuma duk mako yake zuwa muku a daidai wanna lokaci, kuma a wannan tasha. Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami'an tsaro? Wannan tambayar na daya daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau. Sai ku kasance tare da abokinku, Michael Kuduson.
Shirin ‘Tambaya Da Amsa' yana zuwa muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wsu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako ya ke zuwa muku a daidai wannan lokaci.Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci. Sai a biyo
Kamar yadda aka saba, shirin yana kawo muku amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana ne, kuma duk mako yake zuwa muu a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa, akwai wadda ke neman bayani a kan ramukan nan da ke sarari, wadanda ake kira ‘black holes.
Shirin ‘Tambaya Da Amsa ‘ yana zuwa muku ne kowane mako a wannan tasha, inda ya ke kawo amsoshin tambayoyin da suka samu shiga daga masu sauraronmu. Daga cikin tambayoyi da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayani a kan dalilin da ya sa kasashe masu tasowa ba iya dogaro da kan su wajen yaki da matsalar tsaro,, musamman ma ta'addanci da sauransu.