Dandalin Fasahar Fina-finai

Follow Dandalin Fasahar Fina-finai
Share on
Copy link to clipboard

Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya  bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare…

Rfi - Abdoulaye Issa


    • Nov 16, 2024 LATEST EPISODE
    • infrequent NEW EPISODES
    • 20m AVG DURATION
    • 84 EPISODES


    More podcasts from Rfi - Abdoulaye Issa

    Search for episodes from Dandalin Fasahar Fina-finai with a specific topic:

    Latest episodes from Dandalin Fasahar Fina-finai

    Karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar su a Najeriya

    Play Episode Listen Later Nov 16, 2024 20:00


    A cikin shirin na wannan mako a bangaren mu na Kannywood zamu duba yadda karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar fina-finan. Za ku ji mu tafe da dambarwar da ta kunno kai tsakanin fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara, da hukumar tace fina-finai ta jijar Kano.

    Korafe-korafen makallata fina-finan Hausa

    Play Episode Listen Later Jul 13, 2024 20:00


    A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa.Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya.Muna tafe da tattaunawa da Hadiza Gire, guda daga cikin matan da suka yi tashe a jamhuriyar Nijar lokacin da suke fagen rera wakokin ‘yan mata.

    Ko ana 'kan ta waye' a masana'antar Kannywood?

    Play Episode Listen Later Feb 6, 2022 20:01


    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' ya yi nazari ne a kan al'amarin nan da ake kira 'kan-ta-waye'. Shirin ya yi  bayani a kan menene 'kan-ta-waye', sannan ya tattauna da baki, wadanda suka fadada bayanin don fahimtar mai sauraro.

    Rayuwar mata masu shirya fina-finai a Nollywood a Najeriya

    Play Episode Listen Later Jan 30, 2022 20:00


    A cikin wannan shirin na dandalin fasahar Fina-finai,Hawa Kabir ta samun tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar fina-finai dangane da makomar mata musaman a gidajen mazan su,ko wandada ke da niyar yin aure.

    mata nollywood masu najeriya duniyar
    Halin da masana'antar Fim ta shiga a makon da ya kare

    Play Episode Listen Later Jan 9, 2022 20:00


    Kamar yadda aka saba kowane mako shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai tare da Hauwa Kabeer ya tattauna akan wasu daga cikin muhimman al'amuran da ke wakana a masana'antar fina-fina da ke arewaci da kuma kudancin Najeriya.

    kamar shiga najeriya masana
    Abinda ya wakana cikin kungiyar MOPAN a baya bayan nan

    Play Episode Listen Later Dec 19, 2021 20:00


    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer, ya leka kungiyar MOPAN ne domin jin wainar da ake toyawa.

    bayan cikin
    An kamala zaben wakilan kungiyar yan Fim a jihar Kaduna

    Play Episode Listen Later Dec 12, 2021 19:56


    A cikin shirin duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harakar fim yan lokuta bayan kamala zaben wakilan MOPAN a jihar Kaduna. Makomar duniyar Fim,hanyoyin kawo karshen baraka a wannan duniya na daga cikin manyan batutuwa da Hawa ta samu tattaunawa da bakin na ta.

    Fitaccen makawaki ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i

    Play Episode Listen Later Dec 5, 2021 19:42


    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da wani fitaccen mawakin Hausa da ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i.

    An fara daukar shirin 'Gidan Badamasi' zango na 4

    Play Episode Listen Later Nov 21, 2021 20:00


    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai ya leka inda ake daukar shirin barkwancin nan mai dogon zango, wato 'Gidan Badamasi', inda ya gana da jarumai da masu ruwa da tsaki a shirin, cikin su har da babban daraktan shirin, Falalu Dorayi.

    shirin zango
    Rayuwar Alhaji Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi

    Play Episode Listen Later Nov 7, 2021 20:00


    Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna' ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya. Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama. Hawa Kabir a cikin shirin dandalin fasahar fina-fanai ta jiyo ta bakin wasu daga cikin mutanen Danjuma Katsina wanda ke  daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama. Kasagi ya bada gudumawa sosai wajen daga darajar wasan kwaikwayo da ake sawa a wancan lokaci a Gidan Rediyo da talabijin Kaduna, yayin da littafin sa na ‘Kulba Na Barna' ya shiga cikin jerin litattafan adabin da suka dauke hankalin dalibai da masu sha'awar karance karance na wancan lokaci.

    Masu ruwa da tsaki kan rubutun adabi da fina-finai na alhinin rasa Kasagi

    Play Episode Listen Later Oct 31, 2021 20:00


    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir ya tattauna na masu ruwa da tsaki kan rubutun adabin Hausa da kuma fina finai kan rasuwar marigayi Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa 2/2

    Play Episode Listen Later Oct 24, 2021 20:00


    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai tare da Hauwa Kabir ya cigaba da tattaunawa ne kan taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC da ya gudana a garin Zaria, dake jihar Kaduna.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa

    Play Episode Listen Later Oct 3, 2021 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai, hauwa Kabir ta leka taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC  da ya gudana a Zaria, jihar Kaduna. Shirin ya gana da shehunan malaman da suka halarci taron. 

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Rayuwar yan wasan fina-finai a Tarrayar Najeriya

    Play Episode Listen Later Sep 26, 2021 20:00


    A cikin shirin dandalin Fina-finai,Hawa Kabir ta jiyo ta bakin  masu shirya fim a Nollywood,wanda suka kuma yi mata bayyana dangane da rayuwar su da kuma irin wasannin da suke iya kasancewa a cikin su ga baki daya.

    nollywood najeriya
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Gudunmawar Ahmad Aliyu Tage ga masana'antar Kannywood

    Play Episode Listen Later Sep 19, 2021 20:00


    Shirin dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan rashin da masana'antar Kannywood tayi na wasu manyan jaruman ta, musamman Ahmad Aliyu Tage da ya rasu a makon da ya gabata.

    shirin masana
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Ta'aziyyar mawakin siyasa Isyaku Forest

    Play Episode Listen Later Sep 12, 2021 20:00


    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako tare da Hauwa Kabir ya kawo mana ta'aziyyar mawakin siyasan nan, Isyaku Forest, wanda ya rasu kwanan nan. Hauwa Kabir ta tattauna da makusanta da aminansa, ciki har da shahararren mawakin siyasa, Rarara.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Dalilan da suka haifar da koma baya ga kasuwar fina-finan Hausa

    Play Episode Listen Later Sep 5, 2021 20:00


    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan dalilan da suka janyo faduwar kasuwa fina-finan Hausa.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Mutane na yi wa fim kallon hadarin kaji don ba su ke yi ba - Isa Bello Ja

    Play Episode Listen Later Aug 29, 2021 20:41


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa kabir ta kawo abubuwa da dama a bangaren fina-finai, inda ta duba yadda yanzu masana'antar Kannywood ke gogayya da takwararta tav kudancin Najeriya. Ta kuma tattauna da shugaban jaruman Kannywood, Alhassan Kwale wanda ya ce Umma Shehu da Sadiya Haruna ba 'yan Kannywood bane.

    bello kaji najeriya
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Tattaunawa da Yaya Dankwambo na shirin gidan Badamasi

    Play Episode Listen Later Aug 22, 2021 20:00


    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da Muhammadu Nura Yakubu da a yanzu aka fi sani da sunan Yaya Dankwambo na shirin fim din Gidan Badamasi.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Tattaunawa da Tijjani Asase (Damisa) kan masana'antar Kannywood

    Play Episode Listen Later Aug 15, 2021 20:00


    Shirin Dandalin Fasahar Fina Finai ya tattauna da Tijjani Asase da aka fi sani da Damisa kan lamurran da suka shafi masana'antar Kannywood.

    masana
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Ana shirin ci gaban fim din Hausa na 'Malam Zalimu'

    Play Episode Listen Later Jul 25, 2021 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta duba tattauna da Ado Ahmed Gidan Dabino a game da ci gaban shirin fim din Malam Zalimu. Bayan nan ta leka Nollywood ta kudancin Najeriya, inda ta kawo ta'aziyar rasuwar shahararren mawaki, Sound Sultan.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Masu shirya Fina finan Hausa sun koma cin moriyar Youtube

    Play Episode Listen Later Jul 18, 2021 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta yi dubi da batun kasuwanci a masana'antar Kannywood, tare da duba yadda masu shirya fim din suka koma intanet, ta wajen cin moriyar dandalin Youtube, inda suke dora ayyukansu a kai.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Dandalin Fasahar Fina-Finai: Ta'aziyyar jaruma Zainab Booth

    Play Episode Listen Later Jul 11, 2021 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon, Hauwa Kabir ta kawo ta'aziyyar jarumar Kannywood da Allah ya wa rasuwa a makon da ya gabata,inda ta tattauna da abokan aikinta na Kannywood. Shirin ya kuma leka Nollywood da Bollywood.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Jarumai mata na fuskantar kalubale daga masu kallo a kafafen sada zumunta

    Play Episode Listen Later Jun 27, 2021 20:00


    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan yadda Jarumai musamman mata a musamman a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood ke fuskantar cin zarafi daga masu kallo a kafafen sada zumunta na zamani.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Rayuwar mawaka a Duniyar yan fim a Najeriya

    Play Episode Listen Later Jun 20, 2021 20:00


    Mawaka fina-finai a Najeriya na rayuwa ba tareda sun ci moriyar aikin da suke yi ba,banda haka Hawa ta samu tattaunawa da Haro mawakin hausa a Kaduna dake Najeriya. A cikin shirin Duniyar Fina-finai tareda Hawa Kabir,ta samu tattaunwa da wasu dake ruwa da tsaki a Duniyar Fina-finai a Najeriya.Hawa Kabir ta samu

    haro hawa kaduna najeriya duniyar
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Tattaunawa da Isa Bello Ja da kuma rikicin fitattun mawaka mata a Nollywood

    Play Episode Listen Later Jun 13, 2021 20:00


    Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir, ya tattauna da wasu tsoffin 'yan wasan Kannywood cikinsu har da Isa Bello Ja. Kana shirin ya kuma tattaunawa dangane da cacar baki da fitattun mawakan Kudancin Najeriya mata biyu sukayi da ya karade shafukan sada zumunta.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Sai babba ya watsar da girmansa ake rena shi a Kannywood- Isa Bello Ja

    Play Episode Listen Later Jun 6, 2021 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon, Hauwa Kabir ta tattauna da wasu fitattun jaruman Kannywood, ta kuma leka Nollywood, na kudancin Najeriya don ganin wainar da ake toyawa.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Yadda fim mai dogon zango ke tasiri a Kannywood

    Play Episode Listen Later May 23, 2021 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon, hauwa Kabir ta tattauna da wasu jaruman fim din nan mai dogo zango da ake yi a tashar arewa 24, wato 'Kwana Casa'in', inda suka yi bayani a kan yadda irin nau'in fim din ke samun karbuwa a Kannywood.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Dandalin Fasahar Fina-finai ya yi tattaki zuwa Katsina, Nollywood

    Play Episode Listen Later May 9, 2021 20:00


    Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai ya yi tattaki zuwa Katsina don tattaunawa da mawaki, Boda a kan wakar gamayya ta Ramadan, kana ya leka masana'antar frina-finai ta kudancin Najeriya, Nollywood don jin wainar da ake toyawa danagane da zargin da ake wa wani jarumin masana'antar na cin zarafin wata karamar yarinya.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Mawakan Hausa sun yi hadaka a wakokin azumin Ramadan

    Play Episode Listen Later May 2, 2021 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina - Fiinai, Hausa Kabir ta yi hira da mawakin Hausa, Abba Don , wanda ya jagoranci hadakar mawaka wajen raira wakar azumin wata Ramadan. A yi sauraro lafiya.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Kalubalen da ake fuskanta na rashin fahimta tsakanin taurari da masu shirya fim

    Play Episode Listen Later Apr 4, 2021 20:00


    Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai na wannan makon ya cika da tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan matsalolin dake kunno kai tsakanin masu shirya fina-finai da kuma taurari.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Dandalin Fasahar Fina-Finai: Tattaunawa da Tahir Fagge

    Play Episode Listen Later Mar 28, 2021 20:00


    A cikin wannan shiri na 'Dandalin fasahar Fina-Finai', Hauwa Kabir ta tattauna da babban tauraro a masana'antar Kannywood ta fina-finan Hausa Alhaji Tahir Fagge, inda ya yi bayani a ka gwagwarmayar rayuwa da irin kalubalen da suka addabi sana'arsa. Hauwa ta kuma duba masana'antar fina-finan Yarabawa a kudancin Najeriya.

    tahir najeriya
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Tattaunawa da Zuwaira yar wasan Fim a Najeriya a Duniyar Nollywood

    Play Episode Listen Later Mar 21, 2021 20:00


    A Najeriya,yan wasan Fim da dama ne yanzu ke sa ran ganin sun samu zama tareda kasancewa jarumai a Duniyar Nollywood gida dama wajen kasar. Hawa Kabir ta samu tattaunawa da daya daga cikin yan wasan Fim  mai suna Zuwaira,banda haka ta kuma duba wasu daga cikin matsalollin da yan wasan na Fim ke fuskanta a wannan Duniya.  

    fim nollywood duniya najeriya duniyar
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Shirin fina-finai daga sashen hausa na RFI

    Play Episode Listen Later Mar 14, 2021 20:00


    A cikin shirin fina-finai daga nan sashen hausa na RFI,Hawa Kabir ta mayar da hankali tareda hiri da wasu jarumai a Duniyar Fim a Najeriya. A cikin shirin za ku ji halin da masu shirya Fim suka tsudduma  a yanzu haka.    

    fim rfi shirin daga najeriya sashen hausa
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Samun daukaka a Kannywood lokaci ne - Saratu Abubakar Zazzau

    Play Episode Listen Later Feb 21, 2021 20:00


    Hauwa Kabir ta tattauna da jarumar Kannywood, Saratu Abubakar Zazzau a kan daukakar da ta samu a fagen fina - finai bayan shekaru 21 a cikin masana'antar, da dai sauran abubuwa a cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina- Finai.

    abubakar zazzau
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Masoyan mawaki Nura M. Inuwa sun yi zanga- zangar rashin sakin wakokinsa na tsawon lokaci

    Play Episode Listen Later Feb 7, 2021 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai', Hauwa Kabir ta duba wasu daga cikin abubuwan da suke wakana a fannin fina finai da wakoki, ciki har da zanga - zangar da wasu masoyan mawaki Nura M. Inuwa  suka yi sabili da dadewa da ya yi bai saki waka ba.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - ko yaya ake shirya fim a Najeriya ?

    Play Episode Listen Later Jan 31, 2021 20:00


    A cikin shirin fina-finai,Hawa Kabir ta samu zantawa da masu shirya Fim a Najeriya,domin jin ko a ina aka kwana dangane da batun shirya fim a kasar,yanayin rayuwar yan Fim a Najeriya. Hama Kabir ta dubo wasu daga cikin labaran da suka shafi Duniyar yan Fim a Indiya a cikin wannan shirin na Dandalin fasahar fina-finai.

    fim yaya najeriya duniyar
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Muhimmancin masana'antar shirya fina-finai wajen samar da ayyukan yi (2)

    Play Episode Listen Later Jan 17, 2021 20:01


    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya cigaba da tattaunawa da  shugaban hukumar tace fim na jihar Kano kan wasu muhimman al'amuran da suka danganci masa'antar .

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Muhimmancin masana'antar shirya fina-finai wajen samar da ayyukan yi

    Play Episode Listen Later Jan 10, 2021 20:00


    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna dashugaban hukumar tace fim na jihar Kano kan wasu muhimman al'amuran da suka danganci masa'antar fshirya fina-finai.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Tasirin shirya fina-finai a Najeriya

    Play Episode Listen Later Jan 3, 2021 20:00


    A cikin shirin Dandalin fasahar Fina-finai Hawa Kabir ta samu zantawa da masu shirya fim a Najeriya domin jin halin da suke da kuma jin irin kalubalen da suke fuskanta a Duniyar Fina-finai da muka sani da Nollywood.

    nollywood najeriya
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Aishatu Aliyu Kaduna yar wasan fim a Najeriya

    Play Episode Listen Later Dec 20, 2020 20:00


    A cikin shirin Duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da Aishatu Aliyu Kaduna,wacce ta yi bayyani dangane da rayuwarta a fani fina-finai,banda haka ta kuma yi bayyani dangane da irin kalubalen da ta yi fama da su a wannan mataki.

    kaduna najeriya duniyar
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Rayuwar yan wasan fina-finai a Najeriya

    Play Episode Listen Later Dec 6, 2020 20:00


    A cikin shirin Dandalin fasahar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da jarumi Ismail,daya daga cikin masu shirya fina-finai a Najeriya. Sau dayawa ,jarumin a duniyar fina-finai a Najeriya kan yi fice tareda neman ilimi a fanoni da dama kamar dai yada zaku ji a wannan shiri.

    ismail sau najeriya
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Rayuwar yan wasan Fim a Najeriya musaman bangaren Nollywood

    Play Episode Listen Later Nov 29, 2020 20:00


    A cikin shirin na wannan mako,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da wasu yan Fim a Duniyar Nollywood, wandada suka kuma yi mata bayyana dangane da rayuwar su. Duniya Nollywood na fuskantar  dinbin matsaloli da yan wasan ke fatan hukumomi za su taimaka don kawo karshen su,wanda hakan zai bayar da damar raya sashen fina-finai a Najeriya.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - 'Mai Kwashewa' ya yi karin haske a game da fim dinsa mai taken "Manyan Mata"

    Play Episode Listen Later Nov 21, 2020 20:00


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako, Hauwa Kabir ta duba batutuwa da dama inda har ta kawo fitaccen mai shirya fina finai Abdul Mai kwashewa, wanda ya yi karin haske a kan sabon fim dinsa mai fitowa, 'Manyan Mata'.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Tasirin tufafi a rayuwar dan Fim

    Play Episode Listen Later Nov 15, 2020 20:00


    A cikin shirin Duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta mayar da hanakali tareda duba tasirin tufafi a duniyar yan Fim a Najeriya,ta kuma yi amfani da wannan dama don jin ta bakin wasu daga cikin masu shirya fim a Najeriya. Sai ku biyo mu

    fim sai najeriya duniyar
    Dandalin Fasahar Fina-finai - Rahma Sadau ta nemi afuwa a game da cece - kucen da hotonta ya haddasa

    Play Episode Listen Later Nov 8, 2020 19:58


    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai', Hauwa Kabir ta duba mana batun cece- kucen da hoton Rahma Sadau ya haddasa, da kuma afuwa da ta nema a sakamakon batancin da ya janyo wa Musulunci.

    Dandalin Fasahar Fina-finai - Matsaloli dake janyo koma baya a Duniyar Fina-finai

    Play Episode Listen Later Nov 1, 2020 20:00


    Hawa Kabir ta jiyo ta bakin masu shirya Fim a Najeriya dangane da wannan matsala da ta shafi yan wasa wanda akasari ke janyo mutuwar tauraro a Duniyar Fim. Dandalin fina-finai na daga cikin hanyoyin da sashen hausa na RFI ke baiwa masu shriya Fim damar nuna ci gaba da ake samu a wannan sashe kama daga gida Najeriya zuwa kasashen ketare.

    fim koma rfi baya dake najeriya duniyar

    Claim Dandalin Fasahar Fina-finai

    In order to claim this podcast we'll send an email to with a verification link. Simply click the link and you will be able to edit tags, request a refresh, and other features to take control of your podcast page!

    Claim Cancel