Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Cibiyar nazarin da bincike kan ƙasar noma ta jam'iar Bayero a jihar Kano dake Najeriya ce ta shirya taron da ya hada ƙasashe da masana da suka yi duba a kai.Taron karo na biyar ya baiwa masana damar nazari don lalubo hanyoyin magance matsaloli da suka hadabi wannan sashe da ya hada da noma da kiwo a Sahel da wasu ƙasashen.
A wannan makon, shirin zai yi duba ne kan halin da madatsun ruwa da ke jihohin Jigawa da Kano ke ciki, da irin amfanuwa ko akasi da masu cin moriyar su da suka haɗa da manoma da masunta da sauran al'ummmar yankunan ke yi da su.
Shirin namu na yau zai mayar da hankali ne akan yadda mahukunta a jihar Damagaram ko Zinder ta Jamhuriyar Nijar suka yi hobbasa wajen samar da yanayi mai ƙyau na noman shinkafa ga manoman da suka bada himma a bara, suka kuma ga amfaninta.
Shirin Muhalllinka Rayuwarka' ya yada zango ne a jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar, inda ɗimbin manoman albasa suka shiga halin ‘ni ƴasu' sakamakon yadda ƙaddara ta sa suka yi kiciɓis da mugun irin albasa, lamarin da ya sa suka tafka asara.
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan hadin gwiwa da Gwamnatin jihar Jigawa ta yi da wani babban kamfanin samar da dabino na kasar Saudiyya da kuma wani kamfanin ƙwararru da bunkasa harkokin noma na Najeriya. Babbar manufar wannan haɗin gwiwar ita ce bunƙasa noman dabino a jihar, ta hanyar bullo da dabarun noma na zamani, da musayar fasahohi, da kuma samar da jarin noma.
A yau shirin zai yi nazari ne akan yadda karyewar farashin kayan abinci zai yi tasiri akan noman bana, sakamakon zargin da ake cewa gwamnatin ƙasar ta shigar da kayan abinci daga waje, wadanda ke gogayya da waɗanda manoman cikin gida suka noma. A shirin da ya gabata, mun kawo kukan da manoma ke yi akan wanna al'amari, inda suke cewa gwamnati ba ta yi wani abu a game da kayayyakin aikin gona da suke saya da tsada. A yau shirin zai duba irin tasirin da hakan zai yi da noman bana.
Manoma a Najeriya na cigaba da kokawa dangane da matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na karya farashin kayan gona a daidai lokacin da ƙasar ke ƙokarin samar da wadatar abinci.
Shirin ya yi duba kan yadda matsalar ta ƙaracin ruwa ke haifar da tasgaro a fannin noma don samar da wadatar abinci, inda mu ka ji daga manoma musamman na rani a Najeriya kan irin kalubale da su ke fuskanta na rashin samun wadataccen ruwa a gonakinsu, a daidai lokacin da ƙasar ta yi watsi da batun gyara galibin madatsun ruwa da ake da su ballantana ma a kai ga batun gina sabbi.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wanan makon tareda Micheal Kuduson wanda kashi na uku ne ya dora akan kashi na biyu wanda ya gabata a makon jiya. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata shirin ya mayar da hankali ne kacokam akan yadda masu aiki a cikin teku ke rayuwa har ma da yadda za a yi amfani da teku, tafki, rafi ko kogi domin gudanar da harkokin noma da kuma kyautatawar muhalli.
Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon ci gaba ne daga shirin da kuka ji a makon jiya. Idan a wannan kashi na uku wanda shi ne na ƙarshe, ya mayar da hankali ne kan tasirin ruwan Tekuna da Tafkuna da kuma Koguna ga kyautatuwar muhalli ko gurbatarsa, da kuma hanyoyin magance ƙalubalen da muhalli ka iya fuskanta. Masana kimiyyar muhalli sun haƙiƙance cewa tabbas waɗannan nau'ika na ruwa guda uku suna da ɗumbin tasiri akan muhalli. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan bambancin da ke tsakanin teku da tafki da kuma kogi, tare kuma da yin duba game da irin gudunmowar da suke bayarwa ga muhall. Babu shakka masana kimiyyar halittu sun kasa ita wannan duniyar da muke ciki zuwa ɓangarori guda hudu: na farko, wanda ke dauke da duk ragowar ukun shi ne tsandauri, wanda ya hada da duwatsu da tudu da kwari da kasa da kwazazzabai, wadanda ake takawa ake tafiya a ciki da sauran abubuwa da ake yi yau da kullum.
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓataccen sauti ga lafiyar halittu da muhalli wato Sound pollution a turance daga nan RFI.
Shirin ‘Muhalllinka Rayuwarka' ya na dubi ne kan batutuwan da ke da nasaba da muhalli, sauyin yanayi, da kuma noma da kiwo, kuma duk mako ya ke zuwa muku a wannan tasha, kuma a daidai wannan lokaci, tare da abokinku, Michael Kuduson.A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne a kan noman kango ko kuma noman filin bayan gida wato Backyard Farming or Green House Farming a turance.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan fitar da amfanin gona da aka noma a damunar bara da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce a ke yi sakamakon karyewar darajar kuɗin ƙasar, lamarin da su ka ce ya sanya su suma su ka tsunduma cikin masu ribibin sayen amfanin gonar, su na adanawa a rumbunansu domin maganin gobe. A farkon makon watan Janairun wannan shekarar, a yayin ziyarar gaisuwar sabuwar shekara da kungiyar gwamnonin Najeriya ta ka kai wa Shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Ƙungiyar gwamnonin, kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi bayani tare da ƙarin haske a kan aniyar gwamnonin.Sai dai kungiyar Manoman ƙasar wato AFAN, ta bakin kakakinta Muhammad Magaji, ta bayyana cewa ba sabon abu bane yadda ake fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje domin neman riba, amma ta ce ƴan kasuwa da ke sayen kayan a hannun manoman ne ke yin hakan ba manoman da kansu ba.Kasancewar matakin da gwamnonin su ka ce sun fara ɗauka na sayen kayan abinci su na adanawa na da buƙatar fashin baƙi daga masana, mun tuntuɓi Malam Abubakar Lawal Kafinsoli na sashen nazarin noma a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina dangane yadda hakan zai taimaka wa manoma da kuma harkar noma a ƙasar, wanda ya ce wannan ba hanya ba ce mai bullewa ba, musamman ga talakawan kasar.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wanan mako tareda Michael Kuduson ya mayar da hankali ne kan tasirin rashin tsara birane da gine-gine a kan muhalli, da kuma dangantaka tsakanin rashin tsara gari da gurbatar Muhalli.
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon tare da Michael Kuduson ya tattauna ne akan muhimmancin kula da ƙasar noma ta yadda za ta amfanar da al'umma ta fuskar bunƙasar ayyukan noma.
A cikin shirin wannan makon, zamu ji cewa a karon farko, gwamantin tarayya Najeriya ta kaddamar da shirin noman rani da na damina a jihar Cross River a ƙoƙarin da ta ke yi na haɓɓaka noma don samar da isasshen abinci, kuma ministan noma da samar da abinci Abubakar Kyari ne ya kaddamar da shirin noman rani na farko a madadin gwamnatin tarayya a wannan jiha da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Najeriya na cikin kasashen da suka yi fice a noman rani dana damina, inda manoman ke noma shinkafa, tun bayan da tsohuwar gwamnatin kasar ta hana shigo da wasu nau'ukan kayan abinci, ciki har da shinkafa, a wani kokari na bunkasa noman shinkafar a cikin gida.Shirin zai yaɗa zango ne a Jihar Nassarawa da ke tarayyar Najeriya, jihar da ta bayyana shirin shiga harkar noman shinkafa ita da kanta, inda ta ware kadada sama da dubu 10 don noma shinkafar.
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Michael Kuduson kamar kowanne mako a wannan karon ya yi duba ne kan tsarin noma mai ɗorewa da ke nufin magance matsalar ƙarancin abinci da kuma yadda za a baiwa muhalli kariya.
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon ya yi tattaki zuwa Kano, inda hadin gwiwar Bankin Duniya da Gwamnatin jihar, ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki kan kiwon dabbobi, domin inganta fannin ta kyautatawa ko zamanantar da tsarin kiwon dabbobin, samar da abincinsu, da kula da Lafiyarsu, gami da sarrafa madara da naman da suke samarwa.
A yau shirin zai leka Jamhuriyar Nijar don duba matsalar zaizayewar kasar noma da kiwo da ta jawo yaduwar sakaran gari ko tumbin jaki, wata kalar ciyawa dake mamaye filayen noma da kiwo, kuma dabbobi sam ba sa cin ta, haka ba ta da wani amfani da aka sani ga al'umma.
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka' da ke nazari kan abin da ya shafi muhallli, canjin yanayi, noma da kiwo, ya yi tattaki zuwa Kamaru, inda ya duba shirin tallafa wa manoma wajen noman dawa mai jure fari da kasa mara kyau. Hukumar kula da samar da albarkatun gona a arewacin Kamaru IRAD ce ke jagorantar aiwatar da shirin na sake fasalin bunkasa noman dawa 'yar rani, wato moskowari.
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon zai mayar da hankali ne a kan matsalar karancin nama da aka shiga a sassa da dama na Najeriya, inda za mu je jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar don jin yadda ake ciki da kuma inda matsalar ta ke.
A yau Shirin zai mayar da hankali ne kan wani babban Taron karawa juna ilimi kan harkokin samar da abinci da bunkasa noma a Jihar Kano dake arewacin Najeriya Karkashin kulawar bankin Musulunci da Gidaunaiyar Bill and Melinda da Gidaunaiyar sarki Salman Wanda kungiyar harkokin noma ta SASAKAWA Africa ke jagoranta.
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne akan yadda gwamnatin jihar Jigawa ta samar da cibiyoyin tafi da gidanka sama da 300, domin kula da lafiyar dabbobi. Mahukuntan na Jigawa sun kuma samar da wuraren sarrafa nama da kuma madara, matakan da suka sun ɗauka domin bunƙasa harkar kiwo da zummar mayar da shi na zamani.
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali kan yadda wata al'ada da ake kira ''a ci ba'' dadi da ke zama babbar matsala ga manoma yayin girbin albarkar noma, a cikin wannan shiri za ku ji yadda manoman ke kokawa da yadda wannan al'ada ke kassara su, a wani yanayi da matsi baya ga tsadar kayakin noma ke ci gaba da ta'azzara.
Jamhuriyar Nijar inda tsuntsaye irinsu Angulu da Mikiya da ake samu a mayanka da bayan gari, inda ake jefar da gawawwakin dabbobi a yanzu sun zama tarihi. Za mu duba dalilan ɓacewarsu. Masana a faɗin duniya sun yi ittifakin cewa ɓacewar waɗannan tsuntsaye, musamman ungulu ba karamin koma baya ba ne ga lafiyar muhalli. Kafin mu tafi jihar Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, za mu ji ƙarin bayani a game da ungulu da mahimancinsa ga muhalli da lafiyar al'umma, da kuma dalilan da su ka sa su ke ɓacewa daga doron ƙasa, daga bakinmasanin namun daji da abin da ya shafi halayyarsu.
Yau shirin zai yada zango a ne a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda mamakon ruwan sama da aka yi a cikin kwanakin da suka gabata ya haddasa ambaliya, lamarin da ya jefa al'umar yankuna da dama cikin halin kaka-ni-ka yi. A bangaren da ya shafi noma kuwa, ambaliyar ta janyo wa manoma ɗimbin asara, wanda ana iya bayyana a matsayin mara misaltuwa, duba da irin halin da suka shiga.
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon ya mai da hankali ne a kan yadda wani zubin amfani da kayan gona musamman kayan marmari da a kan yi wa feshi ke haddasa matsalolin kamuwa da cututtuka masu lahani ga rayuwar bil'adama, har ma a iya samun rasa rayuka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson....
Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali ne kan irin gudunmawar da sarakunan gargajiya ke bai wa ɓangaren noma a Jamhuriyyar Nijar musamman a wannan lokaci da sauyin yanayi ke barazana ga harkokin na Noma.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan wata hadaka da aka samu tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kuma katafaren kamfanin nan na sarrafa amfanin gona a Najeriya Wato OLAM, domin farfado da tsarin aikin Malaman Gona ta hanyar horar da wadanda jihar ke da su tare da kara yawansu a kokarin da bangarorin biyu ke yi na shirya samun ninkin amfanin gonar da za a rinka nomawa a jihar ta Kwara.
Shirin wanan makon zai yi dubi ne kan yadda yawan sare itatuwa ke mummunan tasiri a kan muhalli, da aikin noma, inda muka ziyarci jihar Adamawa a Tarrayyar Najeriya .
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka' na wannan mako zai yi dubi ne kan shirin gwamnatin Najeriya na ɓullo da tsarin biyan haraji kan masu gurbata muhalli ta wajen ayyukan da suke gudanarwa, wanda a turance ake kira carbon tax. Kuma ana sa ran wannan harajin zai tursasa wa masana'antu da ke gurbata muhalli yin takatsantsan. Wannan sabon haraji dai har yanzu ba'a gama tantance jadawalin yadda za'a aiwatar da shi ba, amma kwararru a fannin na ta kira ga jama'a da su yi shirin rungumar sa, bayan da suka ce gwamnati na yin tsare-tsare ne don fito da kowa zai biya haraji daidai da yawan hayaƙi mai gurɓata muhalli da yake fitarwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Machael Kuduson.......
Allah ya halici wannan duniya tamu da koguna da dazuka wadanda ke taimako ga rayuwar dan Adam ta hanyoyi da dama. A matakin Nigeria, Allah ya albarkace ta da manyan gandun dazuzzuka da suke da fadi da girma, wadanda suka kunshi nau'o'in tsirrai da mabanbantan dabbobi, wadanda ba a samun su a dazuzzukan da ke wasu yankunan duniya.Amma wasu daga cikin irin wadannan dazuzzuka kamar Dajin Sambisa a jihar Borno, Dajin Falgore a jihar Kano, da kuma Dajin Birnin Gwari a jihar Kaduna tare da Dajin Kuyambana a jihar Zamfara sai Dajin Zugurma a jihar Neja da kuma Dajin Lame – Burra a cikin jihar Bauchi, a baya sun kasance maboya ga miyagu.
Shirin wannan zai yi dubi ne kan wani rahoton da ya ce an samu hauhawar amfani da makamashi mai gurɓata muhalli da ma hayaƙin da ke illata muhallai a shekarar 2023. Shirin zai duba tasirin wannan al'amari ga muhalli da ma abin da ake buƙatar ɗan adam ya yi don ci gaba da harkokinsa a cikin wannan sarari na subahana Wani rahoto a kan makamashi da cibiyar makamashi ta duniya ta fitar ya nuna cewa yawan makamashi mai gurɓata muhalli da aka yi amfani da shi, da kuma hayaƙi mai illa da aka fitar a shekarar 2023 ya kai ƙololuwar da ba a taɓa gani ba, duk kuwa da yadda aka rungumi makamashi mai sabantuwa, mara gurbata muhalli a sassa da dama na duniya.
‘Muhallinka Rayuwarka, shiri ne da ke kawo batutuwan da suka suka shafi muhalli, noma da kiwo, matsalolinsu da kuma masalaha. Duk mako ya ke zuwa muku a wannan tashaa a kuma daidai wannan lokaci, abokinku ne, Michael Kuduson ke muku maraba lale da sauraro.Yau Shirin namu zai mayar da hankali ne a kan noman koko a tarayyan najeriya.
‘Muhallinka Rayuwarka' shiri ne da zai leka Jamhuriyar Nijar, inda wani rahoton ma'aikatar kididdiga ke cewa a duk shekara kasar na asarar Eka ko kadadar noma dubu dari sakamakon zaizayewar Ƙasa da gusowar hamada. Lamarin da ya zama babban koma baya ga ayyukan wadata kasa abinci. Wata matsalar ita ce ta sallacewar kasa da komawarta hako da ba a iya noma a kai.
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan noman auduga,a shekarun baya, Nigeria ta kasance daya daga cikin kasashe masu tinkaho da noman auguda a nahiyar Afrika da duniya baki daya.Sai dai hankalin mahukuntan kasar ya koma ga bangaren man petur bayanda Allah ya albarkaci kasar da mai.Jihohin da suka yi fice a noman auduga a kasar, sun hada da Zamfara, Katsina, Kano, Adamawa, Bauchi da kuma Gombe.
Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023 wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa har zuwa wannan lokaci.
Shirin 'Muhalli' na wannan makon tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan tu'annatin da wasu nau'in tsuntsaye da ake kira jan-baki ke yi wa gonaki a Najeriya tare da kokarin da gwamnati ke yi domin shawo kan lamarin.
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka, a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali.Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na yawan saukar Ruwan sama.Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin.
Shirin na wanna makon zai yi dubi ne akan katafaren shirin zamanantar da aikin noma da gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta kaddamar. Masana na ganin Jihar a matsayin wadda idan aka tattala kasar noma da take da ita, a cikinta kadai za a iya noma abincin da zai iya ciyar da kasar har ma a iya fitarwa zuwa kasashen ketare. A wannan aikin da aka kaddamar, gwamnatin jihar ta ce ta samar da kayan aikin fasahar noma na zamani tare da tanadar da dabarun noma daga kwararru.Ku latsa alamar sauti dn sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.......
Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin.Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Taraba da kuma wasu ‘yan kalilan din jihohin kudu maso yammacin kasar.
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" a wannan mako na musamman ne, domin kuwa ya yi dubi ne a kan matsaloli da dama suka addabi bangaren noma a Najeriya, wanda ake ganin su suka hana kasar samarwa kanta abincin da zai wadata jama'arta musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tsadar sa a kasuwanni. Shirin na dauke da rahotanni da kuma hirarraki daga sassa dagan daban na kasar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiruddeen Muhammad.....
Shirin mu na wannan mako zai yi duba ne a kan batun yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta da ke tarayyar Najeriya musamman a jahar Cross River.Wakilin mu dake yankin MURTALA ADAMU ya kai ziyara a wa ta Gona da ake wannan kiwon kuma ya zanta da wadanda suke sana'ar, wa ta da ta rungumi sana'ar ta yi bayani dalla dalla yadda ake fara tsara kiwon da kuma abubuwa da suka dace a tanada.
Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan batun halin da yankunan da suka gamu da iftila'in ambaliya ke ciki a Najeriya, tare da duba matakan da suke dauka na kare kai anan gaba.Idan ba a manta ba dai Shekara guda kenan da faruwa mummunar ambiyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, kuma jihar jigawa dake arewacin kasar na cikin jihohin da ambaliyar tayiwa barna
A wannan mako shirin zai yi dubi ne akan shirin gwamnatin Najeriya na bunkasa noman alkama domin yaki da talauci da kuma wadata kasar da abinci.A wani mataki na kawar da matsalar zaman kashe wando da magance rashin aikin yi musamman tsakanin matasa, gwamnatin Nigeria ta kuduri aniyar amfani da noma wajen samar da guraben aikin yi wa dubban matasan da basa da abin yi a fadin kasar.