"Radio D" yana magana ne akan wasu wakilan jarida guda biyu tare da al'amuransu masu kayatarwa. Wannan kwas na masu koyo a matakin farko yana da manufa kan auna fahimtarsaurare. Akwai takardu da ayyukan yi da ke hade da fayafayan sautin muryar.
Wannan rana ce ta bakin ciki a ofishin Radio D. Domin kuwa Ayhan yana ban-kwana kuma zai koma kasar Turkiyya. Duk da cewa abokan aikinsa sun shirya masa walima ta ba-zata, wannan bai kwantar masa da hankali ba. Paula ta zo aiki da safe ta samu kowa yana shirye-shiryen zuwa walima. Yanayin bai gamsar da ita ba: Ayhan fa barin Radio D zai yi ya koma kasar Turkiyya don ya taimaka wa babansa. Don yi masa ban-kwana, abokan aikinsa sun shirya yin wani takaitaccen jawabi da kuma wata kyauta domin su tuna masa da abokiyarsa mujiya Eulalia. Don girmamawa ga wannan walima ta ban-kwana, shi ma Farfesa ya ajiye kundinsa na nahawu a gefe. Amma duk da haka ya yi cuku-cuku ya shigo da wadansu 'yan bayanai game da hardaddun sunaye.
'Yan jaridar sun yi kokarin gano ma'anar kalmar "getürkt", don haka suka kai ziyara wata gabar teku, inda kowane jirgi da irin tarbar da ake yi masa.A gabar tekun Willkomm-Höft, ana tarbar kowane jirgi ne da taken kasar da yake dauke da tutarta. A wasansu na rediyo, Paula da Philipp sun duba asalin wannan al'ada, wadda za a iya danganta ta da ma'anar kalmar "getürkt." A daya bangaren, Ayhan yana can a ofis yana karanta littafi a kan mujiyoyi, kafin lokaci ya yi. Tun da Eulalia ba ta iya karatu ba, Ayhan ne yake karanta mata. Wannan kashin ya fi ba da karfi a kan dafa-goshi, da kuma yadda kalmar aikatau ke sauya ma'ana idan aka sauya dafin.
Mujiya Eulalia ta taimaka wajen sa Paula da Philipp kan hanya. Sun gano cewa ashe abokan aikinsu da ke aiki a jaridar Hamburg na da hannu a cikin wannan al'amari. Paula da Philipp da mujiya Eulalia sun gano cewa ashe jaridar Hamburg ce ta shirya wannan abu a gabar teku domin su yi cinikin jaridarsu. Daga baya Philipp da Paula sun samu sabani a kan yadda za a yi amfani da wata kalma ta musamman. Philipp na fatan cewa gayyatar da aka yi masa zuwa tashar jirgin ruwa ta Willkomm-Höft zai kwantar wa da Paula hankali. Da Philipp ya mai da hankalinsa ga yadda yake zabar kalmominsa, da hakan bai bata wa Paula ba. Dafi a goshin kalmar aikatau ba tsawo ke gare shi ba, amma kuma na iya sauya ma'anar kalmar. Don haka yana da kyau a lura da cewa wasu dafe-dafen ana raba su daga tushen aikatau.
Paula da Philipp sun warware matsalar ganin kifin "shark", sannan kuma sun sake gano wata damfara. Amma, har yanzu ba a gano dalilin da ya kawo wannan ba. Yayin da ake neman mai wasan sululun kan ruwa, Paula da Philipp kuma sun hadu da wani mai iyo, sun kuma gano bakin zaren. Mai iyon nan ya razana yawancin mutanen birnin Hamburg saboda ganin kayar kifin "shark" din da ke bayansa. Amma me ya sa? A daya bangaren kuma, Eulalia ta bayyana a birnin Hamburg din don taimakawa. Ita ma ta gano wani abu. Eulalia ta samo wata makama wadda ta yiwu, za ta taimaka wa Paula da Philipp -- wata dama ta yin alfani da shudadden lokaci. A kula da yadda aka hada kalmar da take nuna lokacin aikin da aka yi a baya.
Philipp da Paula sun bi sawun kifin "shark" inda suka gano abubuwan ban-mamaki. Ga allon wasa amma kuma ba mahayinsa a gabar tekun, kuma wani labari a cikin wata jarida ya dauki hankalinsu. Da suka bar wajen hayaniyar da ake ciki, sai 'yan jaridar suka shiga binciken ko za su ga kifin. A yayin da suka ga wani bangare na allon sululun kan ruwa, sai suka razana. Sai kuma suka ga hoton kifin a cikin wata jaridar Hamburg, ga kuma hoton abokan aikinsu, Laura da Paul fuskokinsu cike da fargaba. To, ko ta yaya za a fahimci wannan lamarin? A cikin wannan kashi za a jaddada bayani a kan wakilan suna "sie" da "er", wadanda za a iya amfani da su wajen wakiltar sunayen mace ko namiji, wanda tuni aka yi bayanin haka.
Yayin da yanayin cikin ofishin Radio D ya zama mara dadi, Paula da Philipp sai suka ji dadin aikin da zai kai su bakin teku, inda aka ga wani kifin "shark" a gaba. Paula da Philipp da Ayhan ba su ji ta dadi ba. Zafin cikin ofis din ya tsananta, ga shi kuma ko fanka ba su da ita. Paula tana so ma ta samu dama ta je bakin teku, sai kuma kwamfuta Compu ta bayar da wannan damar. Ya kamata 'yan jaridar su tafi Hamburg saboda an ce an ga wani kifin "shark" a bakin teku. Saboda cunkoson mutanen da suka je don su ga wannan kifi, Paula da Philipp ba su samu isa wajen ba. Haka ma abubuwa suka dagule wa Farfesa, wanda yake ta kokarin shawo kan yadda zai gabatar da yadda kwayar kalmar jinsin namiji take karewa. Kalmar musantawa ta "kein" ma ta wannan hanyar take karewa.
Paula da Philipp na son jin ra'ayoyin masu saurare. Batun da za a tattauna a kai shi ne, "Shin karya laifi ce?". Masu saurare na iya bayyana ra'ayoyinsu kan wannan da'irar ta jabu, da halayyar manoman. Tambayar da Paula da Philipp suka yi wa masu saurare ita ce, "Shin yin karya laifi ne?". Wannan tambaya ta samo asali ne daga irin abubuwan da suka faru a gonar nan ta hatsi, inda 'yan jaridar suka dauko rahotonsu. Shin ko abin da wadannan manoma suke aikatawa daidai ne? Ko kuma laifin 'yan yawon bude ido ne da suka zamo marasa wayo? Masu saurare dai ba su yi wata tambaya ba wajen bayyana ra'ayoyinsu. Sai dai kuma akasin yadda 'yan jaridar suka yi tambayarsu ga masu saurare mai amsar "e" ko "a'a", shi Farfesa ya gabatar da wani darasi a kan jinsi a harshen Jamusanci. Ya nuna cewa kalmomin sunaye a Jamusanci na iya daukar jinsin namiji, da mace, da kuma na hadaka. An yi bayanin wadannan abubuwa a cikin wannan kashi ta amfani da kalmomin "der", da "die", da "das".
Duk da cewa manoma ne suka yi wannan da'irar, har yanzu Eulalia ta yarda akwai aljanun samaniya. Binciken Philipp da Paula suke yi na damfarar nan ya kai su mashaya, suka yi hira da mazauna kauyen. Paula da Philipp sun warware wannan siddabaru na da'irar amfani, amma har yanzu ba su tabbatar da cewa ko akwai aljanun samaniya ba ko babu. Me ake nufin da aljanun samaniya ne? Eulalia dai ta dage a kan ta taba ganinsu. Daga karshe dai sai 'yan jaridar suka tambayi wadansu baki a wata mashaya da ke wani kauye a kan abin da suka fahimta game da wannan da'irar. Ziyara zuwa wannan mashaya wata dama ce ta gabatar da aikin a shudadden lokaci, musamman ta amfani da fandararriyar kalmar aikatau "sein". Haka kuma an sake bayanin kalmar aikatau mai nuna yanayi ta "können" a wannan kashin. A kula da yadda wasalin ya canja yayin hada kalmar da take nuna aikin.
Paula da Philipp suna so su kai ga karshen al'amarin na rikidar amfanin gona, don haka za su bi dare su yi bincike. Mai gonar da wannan da'irar amfani mai ban mamaki take, yakan caji masu yawon bude ido har Euro 5 don ya ba su damar daukar hotuna a gonar. Can ga Philipp da Paula sun yi sansani a cikin daji cikin dare suna jiran aljanun samaniyar nan su fito. A maimakon haka sai suka ga wadansu mutane biyu da wani inji. Ko su ne suke yi wa amfanin gonar da'ira don su jawo hankalin 'yan yawon bude ido? A karshe dai, babu wasu aljanun samaniya da suka fito, wanda hakan ya dada rikita al'amarin. Wannan kalmar aikatau ta "machen" ba ta da rikitarwa kamar abubuwan da suke faruwa a wannan gonar hatsi. A wannan kashi, Farfesa zai nuna muku hanyoyin da za ku yi amfani da wannan kalma.
Yayin da aka gano wata da'ira a gonar, sai Paula da Philipp suka shiga bincike. Shin aljanun samaniya ne suka sauka a wajen ko wani ne yake wasa da hankalin mutane? Yayin da Ayhan ya isa ofishin Radio D, Paula da Philipp sun yiwo waje. An gano wadansu irin da'irori a gonar hatsi, kuma ba wanda ya san wanda ya yi su. Ba 'yan jaridar ne kawai suke son ganin wannan abin mamaki ba, har 'yan yawon bude ido sun taru a wajen. Wannan hayaniyar ta hada mutane dabam-dabam a wajen. 'Yan yawon bude ido suna so su gane wa idonsu, su kuma 'yan jarida suna so su warware matsala, su kuma manoma suna so su sami kudi. A lura da yadda ake amfani da kalmomin aikatau masu nuna yanayi a wannan kashin.
Labarin jarumin nan na tarihin Girkawa, wato Icarus, ya burge 'yan jaridar. Amma ko masu saurare sun san wane ne Icarus? Ga Paula da Philipp nan za su ba ku labarinsa. A yayin da Paula da Philipp suka ga wani yaro ya yi shiga irin ta jarumin nan na Girkiwa, Icarus, sai wata dabara ta fado musu: ya kamata su gabatar da tarihin Girkawa a daya daga cikin shirye-shiryensu na rediyo. Labarin dai na wani matashi ne da ya ki daukar shawarar babansa mai suna Dädalus, har ta kai ga ya fado a lokacin da yake kokarin tashi sama. Shi bukatarsa kawai ya kai ga inda rana take, amma da ya tashi ya nufi kusa da ita, sai dankon da ke jikin fikafikinsa ya narke. Mahaifinsa ya fada masa cewa "Kar ka tashi can sama, kar kuma ka yi kasa-kasa." A wannan kashi an nuna yadda ake iya amfani da kalmar aikatau da ke nuna umarni don bayar da umarni ko neman wani abu. Da Icarus ya saurari gargadin da mahaifinsa ya yi masa, watakila da bai fado kasa ba.
Paula da Philipp sun sake kawo rahoto a kan bikin gargajiya daga cikin gari. Sun ga shiga iri-iri har ma suka koyi wadansu kare-karen Jamusanci a hanya. Da aka koma ofis kuma, Paula ta dauki fansa a kan Ayhan, kuma abin mamaki ta hanyar bikin gargajiyar. Ana tsaka da biki a can cikin gari, sai Philipp da Paula suka kawo rahoto a kan shiga iri-iri da suka gani. Sun kuma hadu da Papageno na cikin wasan sarewar nan na Mozart "The Magic Flute", da Icarus, jarumin nan na tatsuniyoyin Girkawa.
Duk da tsananin wahalar da Philipp ya fuskanta, sai da ya kokarta ya dauko rahoto daga dajin, kuma ya shiga cikin shagalin da ake yi. Ita kuwa Paula matsala ta samu da jami'an kwastam. A yayin da Philipp yake holewarsa a bikin gargajiyar, ita kuwa Paula ganin abin take kawai hayaniya. Bayan ta sha wahalar neman Philpp, sai da ta sha wahalar neman motarsa da aka sace. Wannan bikin tsafe-tsafe da ake yi ya ba ta wahala. Ayhan sai da ya zolayi Paula. Aikin aikatau ta "sein" na da yawa kamar yawan irin shigar da aka yi barkatai a lokacin bikin gargajiyar da kuka gani. A wannan kashin, za ku ga yadda cikamakon kalmomin aikatau suke.
Ba kowa ne yake murna da wannan bikin ba a Radio D. Aikin da aka ba wa Compus shi ne ya kai wadannan 'yan jaridar dajin nan mai suna "Black Forest", inda nan ne bikin ya fi armashi. A wadansu bangarori na Jamus, ana yin bikin gargajiya ne cike da nishadi. A Radio D kuwa, wannan biki ya jawo hatsaniya. Paula ba ta ga dalilin zumudin da Phillip yake yi ba, saboda shigar da ya yi ba ta burge ta ba. Abin da ya faranta wa Philipp rai shi ne, bincikensu ya kai su wannan dajin, inda mutane cikin shigar mayu ke sace motoci ana tsaka da shagalin bikin. 'Yan jaridar sun so su gudanar da wani shiri na kai tsaye, amma abin bai yiwu ba. A nan mayu suka jawo Philipp daga mota suka kuma sace shi. Tsarin kalmomi a Jamusanci bai kai jidalin bikin nan ba. Wannan kashin ya mayar da hankali ne a kan bigiren aikau da aikatau.
In akwai abin da ba ku fahimta ba, yana da kyau ku dinga tambaya. Farfesa zai amsa tambayoyin da masu sauraren Radio D suka aiko a kan shirye-shiryen da suka gabata. Masu saurare na aiko da tambayoyinsu, shi kuma Farfesa na amsawa, yana bayani a kan kowace tambaya. Wannan wata dama ce ga masu saurare su yi bitar bayanin da suka samu, ko su fadada iliminsu, ko kuma su yi tambaya a kan wani abu da suke son sani. Sai ku saurari wadannan tambayoyi daga masu saurarenmu da yadda Farfesa zai amsa kowacce. Wace hanyar gaisuwa ce ta fi dacewa da wani yanayi na musamman?
Daga ina wannan suna, wato Eulalia, ya fito ne? Su Compu da Ayhan da Josefine sun nazarin ma'anar sunan kuma sun fitar da amsoshi da dama. Akwai wani abokin aikinsu mutumin kasar Spain da ya taimaka musu. Mujiya Eulalia tana so ta san ma'anar sunanta. Wakilan Radio D sun dukufa inda suka gano sunan ya fito ne daga kasar Girka. Carlos da yake aiki a bangaren Sifaniyanci ya bayar da bayani mai ma'ana a kan al'amarin. Ya san wani waliyyi mai wannan sunan. Amma kuma duk da haka, wadannan wakilai suna da dimbin tambayoyi da za su amsa. A wannan kashin za ku ji an yi tambayoyi ba tare da an yi amfani da kalmomin tambaya ba. Muhimman abu kawai shi ne karin murya.
Philipp ya sami wanda ya fito a Sarki Ludwig a wasan kwaikwayon, ya nemi su yi hira. Nan take sai ya gano muryarsa. Can kuma, wani bako ya bulla ofishin Radio D. A can fadar Neuschwantein, Philipp gano wannan bakuwar fuskar ba tare ma da taimakon Paula ba: ashe wannan jarumin ne cikin wasan kwaikwayon da aka yi na Sarki Ludwig. Phillip ya yi amfani da wannan damar ya yi hira da mutumin. Yayin da ya dawo ofishin Radio D a Berlin, sai ya yi mamakin samun wata mujiya mai magana. Wannan kashin cike yake da abin mamaki ga Philipp. Za ku ji yana ta cewa "Das glaube ich nicht" (wato: ban yarda ba) da kuma "Das weiß ich nicht" (wato: ban sani ba). Wannan wata dama ce ta ku kula da kalmar musantawa ta "nicht".
Philipp ma ya gano wane ne wannan bakuwar fuskar. Ya ga wani talla a jarida a kan shagalin kade-kaden Sarki Ludwig. A hanyarsa ta zuwa can, ya yi hira da 'yan yawon bude ido da suka zo daga ko' ina cikin duniya. Yayin da Paula ke zaune a ofis dinta a Berlin, Philipp kuma na can na sintiri a Munich. Bai san komai game da abin da Paula ta gano ba, sai dai shi ma a kan hanya yake. Wani talla a jarida a kan shagalin kade-kaden Sarki Ludwig ya ja hankalinsa. Kuma da ya hau bas, ya gana da 'yan yawon bude ido a kan tunaninsu game da shagalin bikin. Ku yi ta yin bitar fahimtarku ta saurare a wannan kashin. A cikin bas din, za ku ji ana magana da harsuna dabam-dabam. Ku yi kokarin gano kalmomin Jamusanci. Za a gabatar muku da kalmar musantawa ta "nichts" da kuma inda take fitowa a bayan kalmar aikatau.
A can fadar Neuschwanstein, Paula da Philipp sun yi wa sarki mai jiran gado Ludwig tambayoyi. A nan Paula ta yi dace ta gano wata makama ta fahimtar wane ne wannan shu'umar bakuwar fuska. 'Yan jaridar sun nemi yin hira da Sarki Ludwig a zahiri, wanda ake ganin ya farfado. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko wane ne shi ba. Yayin da Paula ta dawo ofis, sai ta ga wani talla a talabijin da ya ankarar da ita. Ta dan san muryar cikin tallan. Ba za ka fadi abin da ka fi so ba tare da bayyana me ko wanda kake so ba. Kalmar aikatau ta "lieben" ta zo ne a sigar aikau. A wannan kashin, za a fara gabatar muku da yadda sigar aikau take.
Paula da Philip sun gabatar da Sarki Ludwig ga masu saurarensu ta rediyo. Yanayin shigowar dare, da hayaniyar shagulgula da wadansu sababbin kirkire-kirkire, su ne abubuwan da suke nuni da yanayin Ludwig da zamaninsa. 'Yan jaridar sun ja hankalin masu saurarensu zuwa karni na 19. Sai suka hasko Sarki Ludwig mai son nishadi, da irin soyayyar da yake yi wa yanayi mai bishiyoyi da furanni, da kuma son da yake yi wa wakokin Richard Wagner, da dangantakarsa da 'yar'uwansa, Sarauniya Sissi. Kowa ya yi mamakin wani teburi da Ludwig ya kirkiro da kansa. Wannan kashin yana magana ne a kan abubuwan da Sarki Ludwig ya fi so, wanda ya yi nuni ga koyon kalmar da take nuna "lieben" (so). Haka ma abin yake ga wannan kalmar ta "kommen" (zo), ita ma za ku ji ta.
A can fadar Neuschwanstein, Paula da Philipp sun hadu da wata bakuwar fuska sanye da alkyabbar Sarki Ludwig. Sai suka yi wani dan bincike game da sanadin mutuwar Sarki Ludwig. Wannan mutumin da ke sanye da alkyabbar Sarki Ludwig ta alfarma, na son su Paula da Philipp su dauka cewa shi ne ainihin sarkin. Ta yaya Ludwig ya mutu? Sai 'yan jaridar suka shirya wani wasa na rediyo don su haska wa masu saurare zargin mutuwar da Sarki Ludwig ya yi a tafkin Starnberg. Ba wanda zai iya tabbatarwa cewa kashe shi aka yi ko kuma shi ya kashe kansa. Wannan ganawa da suka yi da wannan shu'umin mutumin wata dama ce ta jin bambance-bambance wajen magana tsakanin 'yan gida da kuma baki. Ku saurari yadda ake fadar taken ban-girma na "Sie" da na wanda ka saba da shi na "du." Lura da tushen kalmar aikatau "sein".
Paula da Ayhan sun yi wa sabon abokin aikinsu maraba da shiga Radio D. Da ma suna da wani aiki na gaggawa: Ana rade-radin marigayi Sarki Ludwig na Bavaria yana da rai, don haka suna son su bincika. Pilipp ya hadu da sababbin abokan aikinsa, da Paula da Ayhan, ya kuma hadu da miskilar maikula ofis dinsu, Josefine. Lokaci ya kure musu, tun da tuni Philipp da Ayhan sun samo aikinsu na farko. Ana rade-radin cewa shahararren Sarkin nan na Bavaria, Sarki Ludwig II, na nan da ransa, duk da zaton da ake masa ya mutu, ta wani yanayi mai ban mamaki a 1886. 'Yan jaridar sun tafi Fadar Neuschwanstein don su bincika labarin, su kuma gane wa idonsu.
Jami'an Radio D suna ta jiran Philipp. Wadanda zai yi aiki da su, Paula da Ayhan, suna zaman jira. Sai dai ba Philipp ba alamarsa, ga shi waya ba ta shiga. A sakamakon rashin kyan yanayi, sai da Philipp ya makara. Ya yi kokarin kiran Paula ta waya don ta san halin da yake ciki, amma bai same ta ba. A karshe, sai Paula da Ayhan suka bar ofis. Wayar da mahaifiyar Philipp ta bugo sai ta dada rikita al'amura. Philipp ya nemi afuwar makarar da ya yi. A wannan kashi, za ku ji hanyoyin neman afuwa dabam-dabam.
Ga Philipp can ya nufi Berlin. Sai dai saboda rashin kyawun yanayi, tafiyar ba ta sauri. Har abokai Philipp ya yi a hanya. Philipp dai ya tafi filin jirgin sama na Munich a mota, inda ya yi niyyar shiga jirgin sama zuwa birnin Berlin. A saboda ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya, sai tafiyar tasa ta tsawaita. A wannan kashin, za mu ji yadda ma'aikacin shirin Radio D, wato Philipp da mahaifiyarsa, za su gabatar da kansu kamar yadda ya kamata. Za ku ji yadda ake gabatarwar tsakanin 'yan gida da baki.
Philipp har yanzu bai samu hutun da yake so ba. Bayan gama fafatawa da kwaron da ya dame shi, sai ya fuskanci hayaniyar makwabta. Yayin da kwatsam aka yi masa waya daga Berlin, sai ya baro kauyen a gaggauce. Bayan fafatawar da Philipp ya yi da kwari a can, sai ga karar zarto, da hayaniyar wani da yake koyon busa. Duk abubuwa dai sun taru sun dame shi. Don haka, yayin da Paula ta Radio D ta kira shi daga Berlin, sai Philipp ya sami dalilin katse ziyararsa ta kauye. Philipp dai ya yi ban-kwana da mahaifiyarsa wadda ba ta ji dadin tafiyarsa ba, daga nan sai ya garzaya babban birnin kasar Jamus. Idan ma Jamusancinku bai nuna ba, za ku iya fahimtar abin da yake faruwa a wannan kashin. Kalmomin da ake amfani da su na yau da kullum, da kuma karin muryar da ake amfani da shi, za su taimaka muku wajen fahimtar shirin da kuma iya saurarensa.
Philipp wani matashi ne, ga shi can yana tuka mota zai ziyarci mahaifiyarsa mai suna Hanne a kauye. Ya yi shirin shakatawa a can, amma kuma sai ya tarar da yanayin zaman kauye na da irin nasa matsalolin. "Kauye da dadi yake!" in ji Philipp, a yayin da ya isa kauyen da mahaifiyarsa take, inda kuma yake son ya huta daga hayaniyar birni. Sai dai ba shanu da maguna kawai ya tarar ba, har ma da wasu halittun. Yana cikin shan kofi a lambu, sai wani kwaro ya bata masa lissafi. Daga nan sai abubuwa suka fara dagule wa Philipp. Ko masu sauraro ba su iya Jamusanci sosai ba a yanzu, za su iya fahimtar abin da ke kunshe a wannan kashin. Don kuwa hayaniyar da ake ji a bayan fage, ta isa ta bayyana inda Philipp yake. A wannan kashin, za ku koyi yadda ake yin gaisuwa da ban-kwana.