POPULARITY
Shirin Al'adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la'akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama'ar gari ke tofa albarkacin bakunansu akan karramawar da wata Jami'a mai suna European-American University ta yi wa fitaccen mawaƙin siyasa a Najeriya Dauda Kahutu Rarara, wanda ta bai wa Digirin Girmamawa na Dakta. Reshen Jami'ar da bayanai a yanar gizo suka nuna cewar hedikwatarta na ƙasar Faransa ne ta yi bikin Karrama mawaƙi Raran ne a Abuja, ranar Asabar, 20 ga watan nan na Satumba, taron da ya samu halartar wasu fitattun mutane. Sai dai Kash! ‘yan sa'o'i bayan bikin da aka yi Jami'ar da ake alaƙanta da Turai da Amurka ta ce ba ta fa san zance ba, domin ba da yawunta aka miƙa wa fitaccen mawaƙin siyasar Digirin na Girmamawa ba, zalika dukkanin mutanen da suka yi iƙirarin alaƙanta kansu da ita ta barranta da su, domin sun yaudari mutane ne da sunanta domin samun damar karɓar na goro a huce. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Lafiya jarice ce na wanan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne a kan hanyoyin gagajiya da mata ke bi wajan sanya tazara tsakanin wannan da waccen haihuwa. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin........
Shirin al'adun mu na gado na wannan rana ya mayar da hankali kan gudunmowar marubuta wajen adana gargaji da tsrain al'adu Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako zai mayar da hankali kan yadda ƙarancin asibitoci ko malaman jinya a yankunan karkara, da kuma rashin kyawun hanyoyin zuwa asibiti musamman ga mata masu juna biyu na tilasta wa matan haihuwar gida saɓanin asibiti, ta yadda galibi Ungozomar gargajiya ke matsayin masu ceto a irin wannan yanayi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu..........
Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi. A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al'adu ke kallon al'amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon, yayi duba ne game da gasar kokuwar gargajiya a Jamhuriyar Nijar, wacce za a faro a ranar 20 ga wannan wata na Disamba nan a jihar Dosso da ke rike da takobi ko kambun gasar, inda ƴan wasa 80 daga Jihohi 8 na Nijar za su fafata har zuwa 29 ga watan, don samun sabon sarkin ƴan kokuwa wanda ke lashe kyautar takobi da kuɗaɗe da sauran kyautuka. Sai dai wani hanzari da ba gudu ba shi ne yadda a bana aka samu wasu sabbin sauye-sauye musamman ɓangaren dokokin wannan gasa.Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh..........
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa kamar yadda ya saba a wannan makon ma ya leƙo wasu daga cikin masarautun Hausawa don jin tarihi da kuma tasirinsu ga al'umma. A wannan karon shirin ya yi duba kan tasirin al'adun gargajiya a matsayin jigon tafiyar da shugabanci bayan ficewar turawan Mulkin mallaka a Najeriya.Haka zalika za kuji hira ta musamman da sarkin Keffi a jihar Nassarawa wato Mai martaba Alhaji Shehu Usman Shindo Yamusa.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....
Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali ne kan irin gudunmawar da sarakunan gargajiya ke bai wa ɓangaren noma a Jamhuriyyar Nijar musamman a wannan lokaci da sauyin yanayi ke barazana ga harkokin na Noma.
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan rayuwar fitaccen mawakin gargajiya na jamhuriyar Nijar Alhaji Ali na Maliki Mawakin haifafffen kauyen Sarkin arewa dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar ya kwashe shekaru akalla 80 na rayuwar sa yana taka rawa a fagen na raye-raye da kade-kaden gargajiya.Shirin ya kuma yi waiwaye kan rayuwar mamacin da ya bar yara 23 a duniya, kuma cikin su guda ya gaje shi.Dannna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abduoullaye Issa.
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda Jama'a ke koken game da rikon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi, kamar Makon jiya yau ma shirin ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da shugaban kwamitin raya Al'adun Gargajiya na Majalisar dokokin Jihar, Hon. Sarki Aliyu Daneji.Ku latsa alamar sauti don jin yadda shirin ya kasance....
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne kan irin ci gaban da aka samu a bangaren wasan damben gargajiya a Najeriya.
A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976, aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha'anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari'ah da kuma batun tara haraji a cikin al'ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al'amura. Amma yayinda gwamnatin Nigeria ke tunanin sake damka wa Sarakuna wannan dama, wasu daga cikin su fara bijiro da sabbin matakai da nufin tsare rayuka da dukiyar al'ummarsu daga ‘yan ta'adda.A baya bayan nan, Mai Martaba Sarkin Ningi a jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad ‘Danyaya, ya samar da wata katafariyar kungiyar tsaro ta ‘yan sa-kai, wacce ke karade sako da lungun yankin don yaki da miyagun iri.
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al'ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al'adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa. Masarautar Katsinar Maradi dai yanzu ta zama madubi kuma abin koyi a bangaren hadin kan al'ummar Nijar.
Shirin al'adunmu na gado na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda abinci gargajiya irin na Bahaushe ke bata sannu a hankali Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa
Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Issa ya maida hankali ne kan bacewar sanar gargajiya ta rini a jihar Kano dake arewacin Najeriya, kafin daga bisa shirin ya leka Maradi dake jamhuriyar Nijar.
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako ya yi nazari ne kan hanyoyin gargajiya da ake bi wajen magance cutar sikila da kuma yadda al'umma suka karbi wadannan hanyoyi don samar wa kansu mafita. Shirin ya tattauna da masu maganin gargajiya da ke ikirarin cewa magungunansu na samar da waraka, kana ya gana da liitocin zamani don neman karin haske a kan inda aka kwana wajen neman mafita a game da wannan cuta ta sikila.
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya mayar da hankali game da tasirin da sabuwar fasahar AI ta sanya na'urori basirar dan adam za ta yi ga tsarin al'adun gargajiya. Baya ga gudunmawar da fasahar ta AI ko kuma Artificial Intelligence za ta bayar wajen adana kayakin tarihi ana ganin za kuma ta taimaka matuka wajen dakile tarin al'adu ko kuma harsuna daga bacewa.Bayanai na nuna cewa wannan fasaha da ake sanya na'urori basirar dan adam za ta bunkasa sassan da suka shafi musayar al'adu tsakanin kabilu daban.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin............
Shirin Al'adunmu na Gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne zuwa garin Filinge a jihar Tillaberi, inda ya tattauna masana tarihi kan dokin nan da aka yi wa wakar "Dokin Iska Dan Filinge"
Wani bincike da hukumar kididdigar kasar Ghana ta gudanar, na nuni da cewa mafi yawan al'ummar kasar sun fi amincewa da tsarin shari'a na gargajiya ko addini a maimakon na zamani. Binciken ya ce yayin da wasu ke ganin cewa rashawa ta dabaibaye tsarin shari'a irin na zamani, wasu kuwa na cewa ana kashe makuden kudade a kan lamarin da bai taka kara ya karya ba, sabanin kotunan gargajiya da na addini. Shiga alamar sauti domin sauraron Hauwa Muhammad cikin shirin.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan taron bajekolin fasahohin kere-kere da zane-zanen gargajiya na yammacin Afrika da ya gudana a birnin Lagos na kudu maso yammacin Najeriya wanda aka yiwa lakabi da Art X. Ayi saurare Lafiya.
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya tattauna akan bikin ranar Maulidi da ya gudana a sassan Najeriya.
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh na wannan makon ya tattauna ne game da wasan damben gargajiya a Najeriya da nahiyar Afrika, inda a yanzu matasa suka rungumi harkar gadan-gadan a yanzu domin neman kudi.
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon ya yada zango ne a dutsen Koma da ke jihar Adamawar Najeriya, inda ya tarar da mutanen Kabilar Koma da ke gudanar da tsantsar rayuwar gargajiya irin wadda aka yi ta dubban shekaru da suka gabata. Har yanzu mutanen na Kabilar Koma na amfani da ganye ne wajen rufe tsaraicinsu, sannan kuma suna da irin gishirinsu na girki da suke miya da shi irin nasu. Kazalika suna amfani da wani irin salo wajen kunna wutar kirki ba tare da ashana ta zamani ba. Kuna iya kallon bidiyon yadda wadannan mutane ke rayuwa a shafinmu na Facebook da Youtube.
Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Isa ya tattauna akan bikin al'adun da 'yan kabilar Berom suka gudanar a jihar Filato. Shirin ya nazarci yadda bikin al'adun ya kunshi 'yan kabilu da kuma mabiya addinai daban daban daga ciki da kuma wajen jihar ta Filato a Najeriya.
Shirin ya yi nazari kan kidan kalangu, ku biyo mu domin ku rausaya.
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya duba sana'o'in gargajiya da muka gada kaka da kakanni a kasar Hausa, da kuma yadda aka yi watsi da su a wannan zamani. An fara ne da batun girke girken gargajiya.
A kowacce shekara ne ake wannan biki na Unaru Ja'e ko da ya ke an samu tsaiko tsawon shekaru ba tare da gudanar da shi ba, gabanin dawo da shi a wannan shekara. Bikin wanda al'adun Fulani akan gudanar da shi a garin hawan dawaki a Jamhuriyyar Nijar na kunshe da kowa, dambe da shadi baya ga nuna bajinta ko zaben sarauniyar kyau da sauran muhimman al'adu, Ayi saurare Lafiya tare da Abdoulaye Issa.
Shirin Al'adu na wannan makon ya tattauna ne kan bikin baje kolin wasu al'adun gargajiya a garin Agadez na Jamhuriyar Nijar.
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya yi dubi kan rawar da sarakunan gargajiya kan taka cikin al'umma don samar da zaman lafiya mai dorewa, bugu da kari shirin wanda bisa al'ada a farkonsa kan tabo batun girke-girken gargajiya, a wannan karonma akwai zantawa da wata mai abincin siyarwa kamar yadda za ku ji a cikin shirin. Ayi saurare Lafiya.
Ko har yanzu ana amfani da wakokin gargajiya da kayan kidan harshen Hausa a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe.
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoullaye Issa ya mayar da hankali kan abincin gargajiyar da ya fi shahara a yankin Agadez na jamhuriyyar Nijar.
Shirin namu na yau Alhamis 30/12/2021 zai tattauna a kan bikin al'adun gargajiya na masarautar Kaltungo da aka yi a bana. Sannan akwai sharhin labarun Jaridar LEADERSHIP ta Alhamis 30/12/2021. Kana akwai labarun wasanni.
Shirin namu na yau Laraba 29/12/2021 zai yi tsokaci ne a kan taron bikin baje kolin al'adun gargajiya na masarautar Kaltungo. Sannan akwai sharhin muhimman kanun labarai da rahotanni na Jaridar LEADERSHIP ta yau Laraba 29/12/2021. Kana akwai labarun wasanni.
Shirin ya duba yunkurin farfardo da wata sarautar gargajiya ta kabilar Abzinawa a garin Afess na jahar Agadez a Nijar.
Shirin al'adunmu na gado ya mayar da hankali kan kokarin farfado da wakokin gargajiya tsakanin matasan Hausawa. Ayi saurare lafiya.
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya yi tattaki zuwa jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, inda aka yi hawan daushe a bikin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W.
Shirin al'adunmu na gado tare da Rukayya Abba Kabara a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda ake shirya bikin wasannin gargajiya na sukuwar dawaki na shekara-shekara da aka saba gudanarwa a garin Filinge na jihar Tilaberri.
Shirin al'adunmu na gado tare da Garba Aliyu Zaria ya yi duba kan yadda Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ke cika shekara guda cur akan mulkin masarautar ta Zaria.
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Rukayya Abba Kabara ya yada zango ne a Agadez ta Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin Cure Salee ko kuma sallar lasar gishiri bayan dakatar da shi tsawon shekaru biyu a dalilin annobar Korona.
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' tare da Rukayya Abba Kabara ya yi dubi ne da yadda al'adar wanzanci ke neman shudewa a kasar Hausa saboda bullar masu askin zamani.
Shirin Al'adunmu na Gargajiya na wannan makon tare da Rukayya Abba Kabara ya tattauna ne game da sihiri ko kuma siddabaru tsakanin 'yan damben gargajiya.
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon ya tattauna ne kan bikin da aka gudanar kan ranar Hausa ta duniya a kasashen Najeriya da Chadi.
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Rukayya Abba Kabara a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda bayar da sandar girma ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
Shirin Al'adunmu na Gado ya tattauna ne game da bikin ranar Hausa ta duniya wanda kasashen Afrika akalla 50 za su gudanar a cikin wannan wata na Agusta. A cikin shirin za ku ji yadda wannan rana ta samo asali.
Shirin 'A'adunmu Na Gado' a wannan makon ya kawo liyafar karrama wani dan Najeriya, marubuci, Abubakar Adam Ibrahim da ofishin jakadancin Faransa ya yi a birnin Abuja na Najeriya.
Shirin Al'adunmu na gargajiya a wannan makon yayi tattaki zuwa birnin Abuja dake Najeriya inda cibiyar raya Al'adun Faransa da Najeriya ta bude dakin karatu domin inganta musayar Al'adu tsakanin kasashen biyu.
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan lokaci zai yada zango ne a Masarautar Agege, wadda ta kasance Masarautar Hausawa ta farko a birnin Lagos da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya da ta shafe shekaru 168 zuwa 200 da kafuwa
A cikin shirin 'Al'adunmu na Gado', Mohammane salissou Hamissou ya kawo mana yadda wasu masu kishin harshenn Hausa suka shirya bikin gasar rubuta gajeren labari a cikin harshen Hausa, inda wadanda suka yi nasara suka lashe kyautuka.
Anyi taron mawaka da makada a garin Abuja Nigeria da zimmar farfado da al'adun gargajiyan jama'a wanda aka fara wasannin a 1982. A cikin shirin Al'adunmu na Gado Mahamane Salissou Hamissou ya hada mana shiri na musamman.