Muna tattaunawa kan matsaloli masu muhimmanci da suka shife mu. Matsaloli masu kawo canji cikin al'umar mu, canji na kwarai ko canjin da ake kyama.
Kasancewar yanzu kayan masrufi sun yi tsada. An samu hauhawan farashi a dukkan abubuwan da zasu samar da ingantacciyar rayuwa. Menene sabubba sannan ina mafita. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
A doron ƙasa, mallaka Allah an samu wata nahiyar da idan kayi Sallah a fili bainar jama'a, sai ka biya harajin Euro Ɗari Biyu (sama da Naira Dubu Ɗari da Saba'i a yau da 11/12/2023). Ga kuma tubka da warwara a aiwatar tsare-tsare da suka yi na Ƴancin ɗan Adam da suke ikirarin yi. Mu samu damar tattaunawa da Mohammed Moayad al-Rachid da ya zauna a wannan ƙasar don jin yadda ya rayu a matsayin sa na Musulmi. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Yadda muke da Banki don ayijar kudi, akwai hanya da wasu masu himma suke amfani da ita wajen tanada abinci don taimaka wa mabukata a lokaci da a ke matukar buqata. Mun tattauna da wani kwararre a fannin noma da kiwo wanda ya kwashe shekaru masu yawa yana aikin gona da ta kai hectare 350. Kuma masani ne kwarai wajen harkar bada tallafi da gudanar qungiyoyin agaza wa gajiyayyu da mabuƙata. Mun samu zama da Mal. Muzzammil Abdullahi (Abu Nadia) don ƙarin haske akan taimaka wa mabuƙata a halin da muka tsinci kan a wannan duniyar. BANKIN ABINCI --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
An samu wani da ya ke ganin ya fi Annabi ilimi da iya adalci, don haka ba abin mamaki ba ne ko yaushe kuma a ko ina, a samu wasu da suke ganin ilimin su ya kai matsayin da hatta Malaman su, ba su ganin su da gashi a ido. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Malamai da suka wallafa littafai a baya, sun duba yanayin al'umarsu ne da buqatuwar al'umar tasu ga wannan littafai da suka rubuta, shi ya sa suka wallafa su. Misali idan ka duba irin su Aqida Wasitiyyah, Aqida Hamawiyyah da su Tadmuriyyah, ai duk daga sunayen garuruwa ne aka basu suna, Ibn Taymiyyah ya wallafa su ne musamman ga mutanen wadannan wurare. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Shin laifi ne in kwaikwayi wani? Akwai wasu sinfin mutane da Shari'a ta yadda in kwaikwaya ne? Mun tattauwa akan wannan mas'ala ganin cewa musamman matasan, suna duba zuwa ga wasu mutana ne suna kwaikwayon irin rayuwar su. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Wannan karo, mu taɓo fanni ne da ta shafar ilimi na Addini da irin kutse da katsalandar da za ka ga wasu na yi a cikin ilimi. Ɗanuwa Mal. Abbas Tijjani ya yi magana kan yadda magabata suke bada ƙima da nuna ladabi ga ilimi. Ku sauraa --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Yadda muke ƙoƙari wajen ciyar da mabuƙata a watan azumi, da haka muke huɓɓasa wajen ganin mun ciyar a watannin da ba Ramadan ba, da abin ya yi kyau. Abin da zai fi wannan shi ne a gina al'umma wadda adadin wanda ake ciyarwa kullum raguwa suke yi. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Wannan ne karo na farko da muka tattauna da macce. Ganin cewa wantan Azumi ya kama, mata da yawa suna dukufa wajen aikin neman Aljanna ta hanyar hidima da gida, miji, yara da kuma babban abin, wato Ibada. Shin wai wadannan matan, ya ya suke yi ne ganin cewa kema Allah Ya azurta ta da aure, yarinya kuma tana kasuwancin ta? Ku saurari tattaunawar mu da Fatima Zarah Maitambari --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Yadda watan Ramadan ya gabato, yana da kyau a ce mutum ya gama duk wata shiri da ya ke tunanin ya yi yanzu. A wannan tattaunawar, mu yi magana kan wani muhimmin abu da ya kamata a ce mu sani game da Rayuwar mu da kuma Ramadan --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Yau mutane da yawa suna fifita ra'ayin su abisa abin da Addini ya karantar, yin haka kuma matsalolin da ya ke haifarwa na da yawa. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Musulmi mun zama mutane da sai abu ya faru sannan muke neman daukar mataki. Haka kuma na nuna rashin wayewa ne da kuma ci baya. Kamata ya yi a ce kafin abu ya faru, mun riga mun tanada abubuwa da za su tinkari abin. In alheri, alheri in kuma sharri, rigakafi. Wannan tattunawar ta kawo fukoki fuda biyu da suka kamata ace muna amfani da su. Allah bamu iko gyarawa, amin. Ayi sauraro lafiya. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Mun tattauna yadda al'amura suke yanzu musamman kasancewar lokaci ne na zabe. Shin wai me ya kamata mu yi a matsayin mu na Musulmi? Ina muka dosa sannan gaba wace irin shiri zamu yi ne? Saurara ku ji hirar ta mu. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Yadda Shari'a ya karantar da mu irin sutura da ya kamata mu ringa sa wa
Muhimmancin mahaifaya a musulunci. An tattauna akan irin yadda uwa ta samu fifiko akan kowa I makusanci
Dole iyaye su tashi tsaye wajen ganin sun kare yaran su daga alfasha da ta zama ruwan dare
Yadda ake tarbiyar yara na da tasiri ga ci gaba ko taɓarɓarewar al'umma
Shi ba mu ga yadda Allah ya albarkaci rayuwar iyaye da kakanni ba ne? Ai daga cikin manya dalili, akwai kyautatawa mutane
Mun ko san Muhimmancin wannan ranar da ake ce wa ranar Idi. Zai matuqar amfanarwa idan muka saurari wannan gajeren saqo
Akwai wani abu da mutane da dama yau basu san muhimmanci shi ba yau sai kadan daga ciki. Iyaye da kakanni sun matuqar darajta wannan abu kuma sai Allah Ya albarkaci rayuwar su a dalilin haka. Don sanin wani abu ne, ba mu aron kunnuwar ku.
Yau fa ranar Arafah, ranar da babu kamar ta. Mai wayo shi ke ribatar ta fiye da yadda ya taba ribartar kowace rana a rayuwar sa. Maza mu saurari wannan don samun fahimta akan ta sosai
Ikon Allah, kun ji irin wannan alfanun kuwa. Kar mu bari wannan lada ya wuce mu.
Alhamdulillah da Allah Ya ni'imta mu da irin wannan ni'ima. Saurara ku ji wace ni'ima muke nufi.
Akwai wasu furuci da harasan mu har mun saba da furta su, amma da yawa ba mu hankalta da irin alfanu da suke qumshe da su... To lallai mu hankalta sannan yu ke kawo wannan tunani lokacin da muke furta su.
Allah Ya nuna mana wata siffa na Munafukai, maza mu saurara sannan mu dau darasi don mu bambanta da su
Babu lokaci da bawa zai iya cika dukka shika-shikan musulunci 5 kamar wannan lokaci. Salloli 5, Azuma, Zakka, Hajji da kalmar shahada
Daga cikin abubuwa da kullun muke maimaitawa idan ana kiran Sallah shine nuna gazawar mu sai dai in Allah Ya bamu iko, inda muke cewa lahaula wala quwata illa billah. To yanzu ma sai mun hada da neman agajin Sa.
Ko kun san cewa babu kwanaki da Allah Ya fi so a a shekara fiyebda kwanakin da muke ciki yanzu? Aikin alheri da za muyi sun fi nauyin lada? Maza ba da kunnuwan ka aro don jin muhimmancin wadannan kwanaki.
Ga garabasa nan, kar mu bari wannan alfanu su wuce mu. Maza mu samu bibiyi wannan jerin gwanon podcast da za su biyo baya. Wannan gabatarwa ne da zai shajja'a mu don bibiya da qoqarin aiki.
Yana da kyau mu san illar cin hanci da rashawa.
Sanadiyar yawaitar da sauqin kafofin Sadarwa, yau yaɗa jita-jita ya yawaita inda zai yi wuya a kwana biyu baka gani ba. Mafi yawanci mutane basu bin diddigin sahihanci saqo suke yaɗawa. Mu kiyaye, idan an turo mana saqo, kada mu watsa sai mun tabbatar da gaskiya sannan muna da tabbacin akwai buqatar watsa shi.
Duk falala da muke da ita, duk ni'ima da Allah Ya mana, babu daya a ciki ya ya kai imani.
Akwai rashin fahimtar Munin da zalunci kan tafi da shi Qiyamah ban da illata rayuwa a nan duniya. Ranan gobe Qiyamah duhu zalunci kan zama don haka mu guje wa yin zalunci
Ta irin abokai da mutum ke alaqa da su, irin ɗabi'ar da yake siffantuwa da su kenan, don haka mu kula, mu kiyaye wa muke abota da su.
Idan ka samu Allah Ya azurta ka da wannan a zuciyar ka, to lallai ka samu babbar jari.
Saurara don sanin wasu manyan haƙƙoƙin da Allah Ya wajabtawa akan bayi na Maƙwabtaka.
Qofar tuba na bude har sai wasu alamomi sun bayyana. Lokacin da zaka tuba, Shaidan na jin kunya da takaici
Musamman Kyawon hali abu ne wanda ko makaho yana gani. Musulunci kaf na karantar da Kyawon Hali
Shi Allah jiran bawa ya ke yi don ya roqe Shi. Rashin roqon ma na fusata Allah. Roqon kuma Ibadane don haka banyan samun biyan buqata, bawa kan samu lada don ya roqi Allah. Ya kai mumini, maza yi amfani da takobin ka babba kamar yadda Annabi ya bayyana.
Shi musulmi, mumini wanda Allah da Manzon Sa ke gaban shi, yana amfani da wani madubi don tafiyar da rayuwarsa. Ya na da yaqinin cewa idan yayi amfani da wannan madubi, to ya tsira a duniya sannan ya rabauta a lahira. Maza, bada aron kunnen ka don sanin wannan madubi
Ya kai mai son Al-Jannah, akwai madakata da Allah Ya sanya maka kuma wuce wannan madakata, kamar zagin Annabin Allah ne, nuni da cewa Manzon Allah ya ha'inci al'umarsa ne. Maza ka guje ma wannan mummunar abu. Saurara don qarin bayani
Ko kun san sakayyar da Ummu Salma ta samu? Rayuwa dole akwai jarrabawa kuma idan ba a hada da haquri ba, sai tayi daci. Dalilin haka Allah Ya yi kira ga bayi su zama masu haquri. Don haka, mu rika yin haquri idan abun da muke qi ya same mu, sai mu samu lada, sannan Allah Ya azurta ta mu hanyar sakayya fiye tunanin mu.
Duk aiki na da buqatuwa zuwa ga tsarkin niya. Wannan shi ne sanadin samun karbuwar aikin, rashin sa kuma asara ce babba
Akwai wata mummunar tabi'a da yau mutane ba a dauke ta a matsayin komi. https://youtu.be/ZThLOaLSRqM
Shin kana da masaniyar cewa abin da mutane suka gani domin ka sannan su ka yi aiki da shi na iya sama maka lada ko alhaki? Mu kiyaye abin da muke sanya wa a statuses namu.