POPULARITY
Shugabannin ƙasashen Musulmi da na Larabawa, sun kammala taronsu da gabatar da buƙatar korar Isra'ila daga Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan gillar da ta yi a Gaza. Taron ya kuma amince da wasu ƙudurori daban daban da su kai ga tabbatar da ƙasar Falasɗinu. Dangame da matakan da shugabannin suka ɗauka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Chika, tsohon jakadan Najeriya a Iran. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar ta su..........
A kwanan nan ne rikicin masarauta ya ɓarke a jihar Kano da ke Najeriya, bayan da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagoranci gwamna Abba Kabiru Yusuf ta ɗauki aniyar yi wa masarautn ƙasar gyaran fuska, bayan da ta ce an tafka ƙuraƙurai a baya. Zalika, gwamnatin jihar Sokoto ma ta ɗau wannan hanya, inda har ta ɗauki matakin farko na fara zamn sauraron jin ra'ayin jama' a a game da yi wa ikon sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar kwaskwarima, lamarin da masu sharhi su ka bayyana a matsayin hawan ƙawara da ƴan siyasa ke yi wa masarautun gargajiya.Kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Mustapha Salisu Fernandez, wani mai sharhi a kan siyasa da al'amuran yau da kullum.Danna alamar saurare don jin cikakkiyar tattaunawar.
Yau Musulmin duniya ke cika kwanaki 30 da fara azumin watan Ramadana, yayin da ake shirin bukukuwan Sallar Eid el Fitr daga gobe Laraba. Azumin na dauke da darussa da dama da Musulmi ke dauka.Ibrahim Malam Goje ya tambayi Farfesa Mansur Isa Yelwa na Jami'ar Abubakar tafawa Balewa dake jihar Bauchi a arewacin Najeriya, dangane da darussan da ya kamata musulmi ya yi amfani da su.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A doron ƙasa, mallaka Allah an samu wata nahiyar da idan kayi Sallah a fili bainar jama'a, sai ka biya harajin Euro Ɗari Biyu (sama da Naira Dubu Ɗari da Saba'i a yau da 11/12/2023). Ga kuma tubka da warwara a aiwatar tsare-tsare da suka yi na Ƴancin ɗan Adam da suke ikirarin yi. Mu samu damar tattaunawa da Mohammed Moayad al-Rachid da ya zauna a wannan ƙasar don jin yadda ya rayu a matsayin sa na Musulmi. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN CIGABAN MUSULUNCI A NIJAR, DA CIGABAN DA'AWA DA KALUBALEN DA MASU DA'AWA SUKE FUSKANTA DA HANYOYIN WAR-WARE SU, HADARIN KABILANCI, HADARIN SHI'A, TSARIN MAKARATUN ISLAMIYYA DA NA BOKO, TSARIN BADA FATAWA, ABUBUWAN DA AKE KARE MARTABA DA KIMAR MALAMI A CIKIN AL-UMMA, MATSAYIN MIMBARI DA MAI DA'AWA, TSARIN GUDANARWA NA KUNGIYOYIN ADDNIN MUSULUNCI A NIJAR. BAKON SHIRIN: SH. MUH'D ABDURRAHAMAN SADIS, BABBAN LIMAMIN MASALLACIN AMIR SULTAN A NIJAR, MAI GABATARWA: DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI
Shirin 'Kasuwa kai miki dole' na wannan makon ya leka kasar Ghana wadda a yanzu haka ke fama da matsin tattalin arziki irin wanda ta jima ba ta ga irinsa ba. Matsalar tattalin arzikin dai ta yi sandiyar tashin farashin kayayyaki tare da haifar wa al'umma tsadar rayuwa a kasar ta Ghana, a daidai lokacin da Musulmi ke cikin watan Ramadana da aka gudanar da azumi a cikinsa.
Musulmi mun zama mutane da sai abu ya faru sannan muke neman daukar mataki. Haka kuma na nuna rashin wayewa ne da kuma ci baya. Kamata ya yi a ce kafin abu ya faru, mun riga mun tanada abubuwa da za su tinkari abin. In alheri, alheri in kuma sharri, rigakafi. Wannan tattunawar ta kawo fukoki fuda biyu da suka kamata ace muna amfani da su. Allah bamu iko gyarawa, amin. Ayi sauraro lafiya. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Mun tattauna yadda al'amura suke yanzu musamman kasancewar lokaci ne na zabe. Shin wai me ya kamata mu yi a matsayin mu na Musulmi? Ina muka dosa sannan gaba wace irin shiri zamu yi ne? Saurara ku ji hirar ta mu. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/taskar-mallam/message
Musulmi a sassan duniya, na ci gaba da gudanar da bukukuwan Mauludi, don tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah. A irin wannan rana dai, musulmi kan tunatar da juna ne a game da tarihi da kuma halayen manzon Allah annabin Muhammad.
Musulmi da Kirista a Jihar Filaton Najeriya na zaune a unguwani dabam-dabam sabanin yadda a baya al'ummomin biyu ke zaune wuri guda suna cudanya.
An samu wasu mabiya addinin Musulunci da suka taya abokan zamansu mabiya addinin Kirista bikin ranar Kirsimeti a Najeriya, matakin da suka bayyana a matsayin mai muhimmanci wajen karfafa hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu. Dangane da haka ne Nasir sani ya tattauna da Pastor Yohanna Buru, wanda ke cikin shugabannin mabiya addinin Kiristan da ya ga irin wannan ziyara a Mujami'arsa.
Sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Sa'ad Abubakar da kungiyar Jam'atul Nasril Islam tare da kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya sun sake bayyana matukar damuwar su dangane da tabarbarewar tsaro a kasar, wanda ke kaiga ci gaba da hallaka jama'a ba tare da kaukautawa ba. Wannan ya biyo bayan kashe kashen da Yan bindiga suka yi a sassan kasar musamman kona matafiya 42 a Sokoto da kuma harbe Masallata 15 a Neja. Dangane da sanarwar da suka gabatar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren kungiyar Jam'atu Nasril Islam na kasa Dr Khalid Aliyu, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
A duk ranakun 12 ga watan Rabi'ul Auwal na ko wacce shekara, al'ummar Musulmi a fadin duniya kan yi bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAAW). A wannan shirin mun yi nazarin yadda aka gudanar da bukukuwan na bana a jihar Kano da ke Najeriya.
Yau talata 12 ga watan Rabi'u Awwal na shekarar 1443, rana ce da al'ummar Musulmi ke gudanar da bukukuwan Mauludi a sassan duniya. Dangane da wannnan biki, wakilinmu a Bauchi, Ibrahim Malamgoje, ya tattauna da Sheikh Dahiru Usman Bauchi, shugaban mabiya darikar Tijjaniya, kuma ga abinda ya shaida masa dangane da Maulidin.
Masallacin Hagia Sophia kafin ya dawo hannun musulmi, sai da ya shekara sama da 900 a matsayin Babban Coci. Shirinmu na yau zai duba tarihin masallacin kamar yadda wakiliyarmu Ruqayyat Sadauki ta ziyarce shi a Instanbul, da ke Turkiyya
WANENE ZA YA HAU TUDUN UBANGIJI?
WANENE ZA YA HAU TUDUN UBANGIJI?
Yadda matasa suka gudanar da bikin Sallah babba, ko ya aka gudanar da bikin a bana a Najeriya da Nijar da ke fuskantar matsin tattalin arziki?
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan wata manhajar lissafin Zakka wadda wani dan arewacin Najeriya ya samar domin saukake wa al'ummar Musulmi fitar da Zakkar da zarar abin da suka mallaka ya kai nisabi.
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan wata manhajar lissafin Zakka wadda wani dan arewacin Najeriya ya samar domin saukake wa al'ummar Musulmi fitar da Zakkar da zarar abin da suka mallaka ya kai nisabi.
Musulmi ba ya da abin da ya kai Sallah Muhimmanci a rayuwar sa. Tabbatuwa akan yin ta yadda ya kamata, alamar tsira ne. Tozarta ta kuma alamar halaka ne a duniya da lahira. Mai hankali baya wasa da Sallah kuma idan ya ga mutum na wasa da ita, tausayin sa yake ji.
A birnin Yamai na kasar Jamhuriyar Nijar aka fara gudanar da zaman taron ministocin harakokin wajen kungiyar kasashen Musulmi ta duniya OIC karo na 47 bisa taken yaki da ayukan ta’addanci,samar da zaman lafiya da kuma ci gaba a tsakankanin kasashen Musulmi Mahaman Salisou Hamisou ya tattauna da Malam Sabi’u Malam Idi, daya daga cikin 'yan kungiyar addinin Musulunci ta kasar Nijar, kan muhimman batutuwan da zaman taron zai tattauna a kai kamar haka.
Ko kun san cewa a wani gari da ke jihar Katsina a Tarayyar Najeriya, akwai al'ummar Musulmi da Kirista da ke zaune kusan shekaru 100 ba tare da an taba jin kansu ba? Ku biyo mu domin jin dalili.
Dambarwar da ta biyo bayan janye gayyatar da aka yiwa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai domin yiwa taron kungiyar lauyoyin Najeriya jawabi yanzu haka na neman raba kungiyar gida biyu, ganin yadda kungiyar lauyoyi Musulmi suka bukaci daukaci ‘yayan su su kauracewa taron. Dangane da wannan mataki Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barista Lawal Ishaq, lauya mai zaman kan sa, kuma ga bayanin da yayi mana akan wannan mataki.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ne, alumar Musulmi a fadin duniya suka fara shagulgulan babbar Salla ko kuma Sallar layya. To sai dai a bana bikin ya zo ne daidai lokacin da duniya ke ci gaba da fama da annobar corona da ta janyo koma baya a bangarori dabam-dabam na rayuwa.
A yayin da aka fara azumin watan Ramadan a sassa daban daban na duniyar Musulmi ciki har da Najeriya, a karon farko daukacin tafsiri na Alquarni da ake yi ya koma ana yinsa ne kai tsaye ta hanyar sadarawa ta yanar Gizo watau Internet saboda cutar Covid 19 da ta hana cunkoson jama’a.
SAKAMAKON ZUNUBI / GASKANTA GA MAHALICCI
Shirin na wannan mako ya duba yadda al'ummar Musulmi ke shirye-shiryen tarbon azumin watan Ramadana a kasashen Nijar da Najeriya da kuma falalar da ke tattare da wannan wata.