POPULARITY
Shirin namu na yau zai mayar da hankali ne akan yadda mahukunta a jihar Damagaram ko Zinder ta Jamhuriyar Nijar suka yi hobbasa wajen samar da yanayi mai ƙyau na noman shinkafa ga manoman da suka bada himma a bara, suka kuma ga amfaninta.
Shirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana'o'i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......
Shirin Tambaya da Amsa tare da Michael Kuduson a wannan mako ya amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko, kuma a wannan makon za ku ji ci gaban amsa kan dalilan da ke haddasa girgizar kasa dama dangantaka tsakanin wannan matsala da aman wutar dutse da kasashe da dama ke fama da su. Haka zalika akwai amsa game da tarihin Marigayi Malam Amadou mai wa'azi na jihar Damagaram a Jamhuriyyar Nijar wanda ya koma ga mahaliccinsa a ranar 3 ga watan Satumbar da muke ciki ya na da shekaru 73 a Duniya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...........
a birnin Damagaram na Jamhuriyar Nijar, matasan da suka goge wajen taka leda na kwadayin rungumar buga kwallon kafa a matsayin sana'a a kasashen waje.
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' ya yi tattaki zuwa jihar Damagaram Zendir ta Jamhuriyar Nijar ne, inda jami'ar Damagaram ta yaye daliban farko da suka yi karatun aikin likita. A wannan jami'ar, kuma a wannan rana aka gudanar da bikin karrama malaman sashen koyar da kiwon lafiya da suka samu karin girma, sakamakon nasarar da suka yi ta cin jarabawar kwarewar nan ta hukumar kula da kwarewar malaman jami'o'i a nahiyar Afrika.
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda wasu asibotoci a Jamhuriyyar Nijar ke fama da karancin jini sakamakon rashin masu bayar da gudunmawar jinin don tallafawa marasa lafiya. Bayanai sun bayyana cewa galibi a irin wannan lokaci na watan Ramadana akan fuskanci irin wannan matsala ta karancin hatta a sashen 'yan haihuwa da kuma bangaren da ake kula da masu lalurar koda.Duk da matakin da asibitoci suka dauka na adana jinin don kaucewa fuskantar yankewarsa, sai dai Bankin jini na jihar Damagaram na ganin abu ne mai wuya idan ba a sake fuskantar yankewarsa a bana ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............
Shirin "Al'adunmu na Gado" a wannan makon ya yi duba ne akan yadda wasan gargajiya na Tabastaka ke ta ka rawa wajen abinda ya shafi zaman lafiya a yankunan Damagaram da kuma Zindar.Haka nan kuma, shirin ya duba yadda al'ummar Hausawa suka rungumi abincin al'adar al'ummar kasar Ghana.Shirin bai tsaya nan ba sai da ya leka tarayyar Najeriya, inda ya kawo yadda aka gudanar da bikin nadin sabon Sarkin Kwantagora a jahar Niger da ke tsakiyar kasar.
Shirin na yau ya duba halin da ajizuwan da dalibai ke daukar darasi a Nijar ke ciki, da kuma shirin gwamnati na gina ingantattun ajizuwa a wadannan makarantu. Kamar yadda watakkila aka sani, an sha samun matsaloli na tashin gobara a wasu makarantun yara a Nijar, musamman a jihohin Maradi da Damagaram sabod yadda ake gina aajizuwan kara da ke saurin konewa. Yanzu gwamnati ta yunkuru ddo warware. matsalar.
A yau larabra 3 ga watan Agusta Jamhuriyuar Nijar ta gudanar da bukukuwan cika shekaru 62 da samun ‘yancin-kai, bayan share kusan shekaru 70 na mulkin mallakar Faransa. Kamar dai kowace shekara, daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan, a gefe daya ana amfani da wannan rana ta ‘yancin-kai domin dasa milyoyin itatuwa saboda yaki da gurgusowar hamada a duk fadin kasar. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Sani Roufa'i, mazauni birnin Damagaram da ke sharhi kan lamurran da suka shafi kasar. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya garzaya jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, inda ya yi nazari kan al'adar maita.
Shirin ya duba matsalolin da karatun jami'a ke fuskanta a Jamhuriyar Nijar musamman a jami'ar Damagaram mai dalibai sama da 12,000.
Ko Kun san yadda al'adar tauri take, a Jamhuriyar Nijar musamman a birnin Damagaram? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari.
Karancin wuraren shakatawa a jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar, ya sanya matasan yankin kokawa. Shirin Dandalin Matasa.
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya yi tattaki zuwa jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, inda aka yi hawan daushe a bikin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi wa bangaren shari'a garambawul inda ta saka alkalai kusa da al'umma domin samun shari'a cikin sauki ta yadda talaka ba zai sha wahalar zuwa nesa ba. Har ila yau gwamnatin ta kara yawan kotunan shari'a a cikin kasar. Kalla Hankurau, dan majalisar dokoki ne da suka ziyarci jihohin Dosso da Maradi da Damagaram da kuma Tahowa inda suka gana da alkalai da yan kaso da kungiyoyin fararen hula akan sabon tsarin. Bayan ziyarar ya gana da manema labarai, kuma ga tsokacin da yayi akai.
Al'adar wasan kara a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar wanda matasa ke yi a lokacin kaka bayan girbin amfani gona
Ko kuna da masaniya kan yadda al'adar wasan kara ke gudana a jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar? Shirin Taba Ka Lashe
Al'adar hawan kaho a Jamhuriyar Nijar, dadaddiyar al'ada ce ta ake gudanar wa a karshen watan azumin Ramadana na kowacce shekara. Ku biyo mu domin jin yadda al'adar take.
Shirin na wannan lokaci, ya tattauna ne da matasa masu dogaro da kansu a jihohin Kano da Gombe a Tarayyar Najeriya da kuma Damagaram a Jamhuriyar Nijar.
Shirin Al'adunmu na gado tare da Mahaman Salissou Hamissou ya mayar da hankali kan bikin kalankuwar makafi a masarautar Damagaram, bikin da ke da dadadden tarihi wanda bisa al'ada ke guda a duk karshen damuna bayan zuwan amfanin gona gida.
Wani matashi Mahaman Sabi'u Sa'idu Alhaji Tahir da ake kira Dan Tubawa dalibi da ke matakin digirin-digirgir a jami'ar Damagaram ya rungumi sana'ar kira.
Annobar cornavirus da ta addabi duniya, ta yi mummunan tasiri ga al'amura da dama ciki kuwa har a al'adu. Shun ko ya annobar ta shafi makada da mawakan gargajiya? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari a kai.
Shirin zai leka jihohin Kano da Sokoto a Tarayyar Najeriya da kuma Damagaram a Jamhuriyar Nijar, domin zakulo muku matasan da suka kasance masu dogaro da kawunansu.
Duba shirye-shiryen karamar sallah musamman a garin Katsina da ke Najeriya da kuma Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar.