POPULARITY
Shirin namu na yau zai mayar da hankali ne akan yadda mahukunta a jihar Damagaram ko Zinder ta Jamhuriyar Nijar suka yi hobbasa wajen samar da yanayi mai ƙyau na noman shinkafa ga manoman da suka bada himma a bara, suka kuma ga amfaninta.
Shirin Muhalllinka Rayuwarka' ya yada zango ne a jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar, inda ɗimbin manoman albasa suka shiga halin ‘ni ƴasu' sakamakon yadda ƙaddara ta sa suka yi kiciɓis da mugun irin albasa, lamarin da ya sa suka tafka asara.
Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta bai wa hafsan sojojin ƙasar umarnin cewar babu wanda zai tafi ritaya a cikin wannan shekarar, sakamakon wasu matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta. Dangane da wannan umarni, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Sani Yahya Janjuna, mai sharhi akan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai.
Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan shaushawar ƙyandar da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka jagoranta sakamakon ɓullar cutar wadda a duk lokacin da aka ga bazuwarta ta ke yiwa ƙananan yara illa matuƙa. Dai dai lokacin da duniya ta gudanar bikin makon rigakafi a ƙarshen watan Mayun da ya gabata, a Jamhuriyyar Nijar annobar ƙyanda ce ke ci gaba da yaɗuwa tare da galabaitar da ɗimbin ƙananan yara, lamarin da ya tilasta mahukunta ɗaukar matakan yiwa jama'a rigakafin wannan cuta mai haɗari.Cutar ta Ƙyanda ko Ado ko kuma Dusa na matsayin babbar matsalar kiwon lafiya ta yadda a duk lokacin da ta ɓulla ta kan haddasa asarar ɗimbin rayuka, kodayake a yanzu tuni ma'aikatar lafiya ta jagoranci aikin rigakafin na ƙasa baki ɗaya da zai shafi dukkanin ƙananan yara tun daga watanni 6 da haihuwa har zuwa shekarun 5 da nufin murƙushe cutar.Tsawon mako guda aka shafe daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Mayu ana gudanar da rigakafin na ƙyanda a sassan Nijar wanda aka yiwa ƙananan yaran da yawansu ya tasamma miliyon 5 a kasar, da nufin daƙile asarar rayukan da ake fuskanta sanadiyyar cutar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Bisa ga dukan alamu Maroko na ƙara samun kusanci da ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da alaƙa ke ƙara yin tsami tsakanin waɗannan kaasashen da Aljeriya. Ministocin Harkokin Wajen ƙasashen uku sun ziyarci Maroko tare da ƙulla yarjejeniyar da ke ba su damar yin amfani da tashoshin ruwa ƙasar, alhali ba ɗaya daga cikinsu da ke da iyaka da Marokon.Ko yaya ku ke kallon wannan alaƙa tsakanin Maroko da AES, yayin da suka juya wa makociyarsu Aljeriya baya?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman, kamar kowannen mako kan yi bitar muhimman labaran da suka faru cikin makon da muke ban kwana da shi, kuma kamar kodayaushe a wannan karon wasu daga cikin labaran da ke ƙunshe a shirin sun ƙunshi ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Najeriya ya kai Jamhuriyar Nijar, wadda a karon farko kenan tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum da sojoji suka yi. A Najeriya shirin ya leƙa Filato aka samu hasarar ɗimbin rayuka, sakamakon hare-haren da aka kai a wasu yankunan jihar, a Najeriyar za a ji yadda wata shu'umar cuta ta janyowa manoman Tumatir hasarar ɗimbin amfanin gonar, sai kuma yadda ‘yan damfara suka yi awon gaba da sama da naira tiriliyan 1 a Najeriyar.A Sudan kuwa ƙungiyar bayar da agaji ta Redcross ce ta aƙalla mutane dubu 8000 suka bace a yakin kasar.Sai kuma Kenya inda aka cafke wasu mutane da ke shirin fasa kaurin dubban tururuwa zuwa ƙasashen ƙetare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya ta fara aiki a Jamhuriyar Nijar, bayan da aka kaddamar da fara aikin ƙudurorin da taron ƙasar na watan Fabarairu ya bayar da shawarar aiwatarwa.A Najeriya hukumar Kwastam ta janaye haraji a kan dukkanin kayayyakin asibiti da magungunan da ake shigar da su ƙasar daga ƙasashen ƙetare.Mummunar girgizar kasa ta rutsa da gwamman mutane a ƙasashen Myanmar da Thailand.
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce an fara samun saukin karancin man fetur da aka fuskanta a kwanakin da suka gabata, abinda ya jefa jama'a da dama cikin halin kunchi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Muhammadu Gamatche, shugaban gamayyar kungiyoyin masu motocin sufuri ta kasa a Nijar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana
Shirin Mu Zagaya Duniya'na wanan makon tareda Micheal Kuduson ya kuma duba batun watsi da wasu kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Nijar suka yi da rahoton taron ƙasa da ta shawarci shugaban mulkin sojin ƙasar ya ci gaba da zama kan karagar mulki har nan da shekaru biyar. Latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin....
Kwanai bayan miƙa rahoton taron ƙasar da aka yi a Jamhuriyar Nijar, mutane na ci gaba da gabatar da ra'ayoyin su akai. Malam Sirajo Issa na ƙungiyar Mojen ya ce basa goyon bayan taron.
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta kafa kwamitin musamman da aka ɗora wa alhakin shirya taro maharawa don sake dawo da ƙasar kan turbar dimokuradiyya. Ana kyautata zaton sakamakon ayyukan kwamitin ne za su fayyace tsawon lokacin da ake buƙata don tafiyar da mulkin riƙnon ƙwarya da kuma irin salon mulin da ya kamata a ɗora Nijar a nan gaba.Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sani Rufa'i ga kuma yadda tattaunawarsu ta gudana.
Shekaru aru-aru maroka da mawakan baka na bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen bunkasa al'adu da martaba kimar al'umma a daular Hausa.
Hukumomin sojin Jamhuriyar Nijar sun gabatar da wata sabuwar dokar da zata hukunta baƙin da ke shiga cikin kasar ba tare da halartattun takardu ba. Wannan ya biyo bayan zarge zargen da ake na samun wasu baki da ke yiwa kasar zagon kasa. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mai sharhi a kan Nijar, Abdoul Naseer, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon, yayi duba ne game da gasar kokuwar gargajiya a Jamhuriyar Nijar, wacce za a faro a ranar 20 ga wannan wata na Disamba nan a jihar Dosso da ke rike da takobi ko kambun gasar, inda ƴan wasa 80 daga Jihohi 8 na Nijar za su fafata har zuwa 29 ga watan, don samun sabon sarkin ƴan kokuwa wanda ke lashe kyautar takobi da kuɗaɗe da sauran kyautuka. Sai dai wani hanzari da ba gudu ba shi ne yadda a bana aka samu wasu sabbin sauye-sauye musamman ɓangaren dokokin wannan gasa.Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh..........
A watan Janairun shekarar da ta gabata Jamhuriyar Nijar da wasu ƙasashen Sahel 3 su ka bayyana aniyar ficewa daga ƙungiyar ECOWAS ta ƙasashen yammacin nahiyar Afrika a hukumance. A halin da ake ciki, watanni 3 ne kacal su ka rage wa'adin ficewar su ta cika, bayan sanar da ECOWAS batun janyewar kamar yadda dokokinta su ka tanada.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Yanzu haka saura watanni 2 kafin cikar wa'adin shekara guda da ECOWAS ta gindaya domin duk wani mai shirin fita daga cikin ta, sakamakon shelar da Jamhuriyar Nijar da ƙawayenta Mali da Burkina Faso suka yi na janyewa daga cikin ta. Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ke nuna janye matakin, ya yin da aka tabbatar da cewar har yanzu wakilan Nijar na aiki a hukumomin na ECOWAS. Domin duba wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon ministan ayyuka na musamman a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu........
A yau shirin al'adun zai je jihar Nassarawa inda muka samu zantawa da mai Martaba Sarkin Nassarawa,daga bisani za mu je Jamhuriyar Nijar inda zamu duba koma bayan wakokin gargajiya a cikin al'umma.
Kusan shekara guda da rabi da juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, har ya zuwa yanzu babu wani shiri daga sojojin na mayar da mulki ga fararen hula. Wannan ya sa wasu daga cikin jama'ar ƙasar gabatar da buƙata ga sojoji da su sake tunani akai domin bai wa jama'a damar zaɓin shugabannin da suke so. Domin tattauna wannan batu, Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Alhaji Adamu Muhammad Madawa, daya daga cikin shugabannin ƴan Nijar mazauna Najeriya. Ku latsa alamar sauti dominjin yadda zantawarsu ta gudana........
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da samun wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ake kira Lakurawa a Jihohin Sokoto da Kebbi wadanda aka ce sun fito ne daga kasashen mali da Libya da kuma Jamhuriyar Nijar. Rahotanni sun ce 'yayan wanan kungiya na sanya haraji da kafa dokoki a yankunan da suke.Dangane da wannan sabon al'amari, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A yau shirin zai leka Jamhuriyar Nijar don duba matsalar zaizayewar kasar noma da kiwo da ta jawo yaduwar sakaran gari ko tumbin jaki, wata kalar ciyawa dake mamaye filayen noma da kiwo, kuma dabbobi sam ba sa cin ta, haka ba ta da wani amfani da aka sani ga al'umma.
Daga cikin labarun da shirin ya waiwaya akwai, korafin da kungiyar direbobin motocin haya a Najeriya ta gabatar da korafi kan tashin hankalin da mabobinta ke fuskanta, inda ta gabatar da kididdigar da ke nuna cewar, akalla direbobi 50 ‘yan ta'adda suka halaka suka kuma suka yi awon gaba da wasu mutanen da dama daga kan hanyar Gusau zuwa Funtua.Al'ummar Jamhuriyar Nijar na alhinin rashin da suka yi na tsohon Fira Ministan kasar Hama Amadou, wanda ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.
Ƙungiyar Transparency International da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, reshen Jamhuriyar Nijar ta fitar da wani sabon rahotoda ke zargin sojojin ƙasar da gazawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma hana fararen hula guraben shugabancin hukumomin gwamnati. Dangane da wannan zargi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban Transparency International, reshan Nijar, Mamman Wada.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
Gwamnantin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace wa mutane 9 dukanninsu makusanta ga hamɓararren shugaban kasar Mohamed Bazoum shaidar zama ɗan ƙasa saboda zarginsu da shirya wa ƙasa zagon-ƙasa. Tsohon madugun ƴan tawaye Rissa Ag Boula da kuma Janar-Janar biyu na soji na daga cikin waɗanda wannan mataki ya shafa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
Shirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon yayi duba ne kan yadda ake gudanar da bikin Sallar Gani. ita dai wannan sallar na daga cikin dadadun al'adar mallam Bahaushe, kuma har yanzu ana gudanar da wannan biki a wasu masarautu a Arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Jamhuriyar Nijar inda tsuntsaye irinsu Angulu da Mikiya da ake samu a mayanka da bayan gari, inda ake jefar da gawawwakin dabbobi a yanzu sun zama tarihi. Za mu duba dalilan ɓacewarsu. Masana a faɗin duniya sun yi ittifakin cewa ɓacewar waɗannan tsuntsaye, musamman ungulu ba karamin koma baya ba ne ga lafiyar muhalli. Kafin mu tafi jihar Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, za mu ji ƙarin bayani a game da ungulu da mahimancinsa ga muhalli da lafiyar al'umma, da kuma dalilan da su ka sa su ke ɓacewa daga doron ƙasa, daga bakinmasanin namun daji da abin da ya shafi halayyarsu.
Kwararru game da matsalar sauyin yanayi da kuma wakilan gwamnatoci da na ƙungiyoyi, sun fara gudanar da wani taron kwanaki uku a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, domin tattauna matsalar sauyin yanayi a Yankin Sahel da kuma Yammacin Afirka. To domin jin muhimmancin wannan taro, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Moussa Hassan Ousseini, jagoran ƙungiyar Jeunes volontaires pour l'environnement du Niger mai rajin kare muhalli a Jamhuriyar Nijar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.....
A wannan makon shirin zai mayar da hankali kan cutar borin gishiri ko kuma kumburin da mata ke fama da ita yayin da suke da dauke da juna biyu, wacce kuma a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka. Wannan cuta a Jamhuriyar Nijar na daga cikin wacce ke ciwa hukumomi tuwo a kwarya ganin yadda mata sama da dari biyar da 30 cikin kowace mace dubu daya ne kamuwa da wannan cuta, kuma sama da 50 ke rasa ransu a sanadiyarta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta amince da wata dokar tube rigar ɗan kasa a kan duk wanda aka samu da aikata laifuffukan ta'addanci ko kuma taimakawa masu ta'addanci. Dokar ta kuma shafi masu yiwa kasa zagon kasa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Sani Rufai a kan sabuwar dokar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana
Sha'irai mawakan Manzon Allah da Ahlil baitin gidansa da kuma waliyyai na karuwa a tsakanin matasa a Jamhuriyar Nijar.
A yau shirin za ya kai mu Jamhuriyar Nijar, musaman jihar Maradi.A wannan yankin na Maradi a garin Radi, zamu duba batun kirar gargajiya da ke kan hanyar bacewa, bayan a can baya kira, wanzamci, sun kasance sana'o'i biyu da ake alfahari da su a cikin gari. A dauri, makeri baya noma a irin wannan lokaci na damina, sai dai ya yi ta aikin kera kayan noma da gyaransu idan sun lalace, idan kaka ta yi dukan manoma sai su hada masa dammuna hatsi, irin su dawa ko ma wake da zai kula da iyalinsa.
A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa.Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya.Muna tafe da tattaunawa da Hadiza Gire, guda daga cikin matan da suka yi tashe a jamhuriyar Nijar lokacin da suke fagen rera wakokin ‘yan mata.
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda dalibai a jamhuriyar Nijar suka yi mummunar faduwa a sakamakon jarabawar karshe ta makarantar Sakandare. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadir Haladu kiyawa
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan rayuwar fitaccen mawakin gargajiya na jamhuriyar Nijar Alhaji Ali na Maliki Mawakin haifafffen kauyen Sarkin arewa dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar ya kwashe shekaru akalla 80 na rayuwar sa yana taka rawa a fagen na raye-raye da kade-kaden gargajiya.Shirin ya kuma yi waiwaye kan rayuwar mamacin da ya bar yara 23 a duniya, kuma cikin su guda ya gaje shi.Dannna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abduoullaye Issa.
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali kan yadda gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta fara saidawa talaka shinkafa a farshi mai rahusa, domin saukakawa ƴan kasar radadin matsin tattalin da suke ciki sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi. A ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata gwamnatin Nijar ta hannun ma'aikatar kasuwanci ta kaddamar da wannan shirin, inda ake sayar da buhu mai nauyin kilo 23 kan jaka 13 da rabi maimakon jika 17 zuwa jika 19 da ake sayar da shi a a wasu wurare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......
Akwai lokacin da 'yan bori da matsafa ke haduwa a sassan yammacin Jamhuriyar Nijar.
Amurka ta yi gargadin cewa, bayan ficewar dakarunta daga Jamhuriya Nijar a tsakiya watan Septumbar wannan shekara, akwai yiyuwar za a fuskanci tarin matsaloli a cikin kasashen Yammacin Afirka. Domin jin yadda masana ke kallon wannan gargadi na Amurka, Umar Sani ya tattauna da Malam Sanoussi Mahamane, masani kan lamurran da suka shafi tsaro a Jamhuriyar Nijar.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
Matsalar tsaro a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da ɗaukar sabon salo lura da yadda ake samun ɓullar sabbin ƙungiyoyin tawaye da ke kai hare-hare, inda suke cewa suna yin hakan ne saboda neman a saki hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum. Bayan da ƙungiyar FPL ta kai hari kan bututun mai da ke sada ƙasar da jamhuriyar Benin, a ranar juma'ar da ta gabata kuwa, wata ƙungiyar mai suna FPJ ta kama da kuma yin garkuwa da kantoman mulkin soji na yankin Bilma da muƙarrabansa a jihar Agadez. Don jin dalilan bayyanar waɗannan ƙungiyoyi da kuma manufofinsu, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Mahaman Sani Roufa'i mai sharhi kan lamurran yau da kullum a Damagarm.Latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawarsu.......
Daga cikin Labarun da shirin ya waiwaya a wannan mako akwai matakin mahukuntan sojin Jamhuriyar Nijar na cirewa hamabararren shugaban ƙasar Bazoum Muhd rigar kariyar, abinda ya bude kofar samun damar gurfanar da shi gaban kotu.A Najeriya kuwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zai ci gaba da yi wa tattalin arzikin ƙasar garambawul duk kuwa da yadda hakan ke ta'azzara wahlhalun da al'ummar kasar ke sha. Sai Kuma Senegal inda shugaban kasar Basirou Diomaye Faye ya sassauta farashin kayayyakin masarufi don saukaka wa jama'a tsadar rayuwar da suke ciki.Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ƙaruwar mutanen da rikici ke tilastawa barin matsugunansu a sassan duniya, adadin da zuwa yanzu ya kai mutum miliyan 120.
‘Muhallinka Rayuwarka' shiri ne da zai leka Jamhuriyar Nijar, inda wani rahoton ma'aikatar kididdiga ke cewa a duk shekara kasar na asarar Eka ko kadadar noma dubu dari sakamakon zaizayewar Ƙasa da gusowar hamada. Lamarin da ya zama babban koma baya ga ayyukan wadata kasa abinci. Wata matsalar ita ce ta sallacewar kasa da komawarta hako da ba a iya noma a kai.
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya yi duba ne a kan halin da ake ciki a yaki da cutar Tamuwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar.
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar. Akwai mu dauke da yadda Maroka da kuma Sankira ke fuskantar barazana a sakamakon tsadar rayuwa.Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.
Daga cikin muhimman batutuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon akwai matakin Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar na kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka. A Najeriya kuwa hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar ce ta kawo karshen binciken da take gudanarwa kan zargin da ake yi wa rundunar sojin kasar na tilasta wa mata akalla dubu 10 zubar da juna biyun da suka samu a bisa tilas daga mayakan Boko haram
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka, tare da zargin cewa dakarun Amurka wadanda adadinsu ya zarta dubu daya na zaune a kasar ne ba a kan ka'ida ba. Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da wata babbar tawagar Amurka ta kamma ziyarar da ta kai Nijar ta tsawon kwanaki uku. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Farfesa Dicko Abdourahmane, masani tsaro kuma malami a jami'ar Damagaram Zinder, wanda da farko ya fara yin bayani a game da dalilan da suka sa mahukuntan Nijar suka dauki wannan mataki.Ku latsa alamar sauti don jin zantawarsu.......
Al'ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da jimamin rasuwar Alhaji Mahaman Kanta fitaccen dan Jarida kuma wakilin Deutsche Welle na farko a Jamhuriyar Nijar.
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa kan sanin muhimmancin da ilimi ke da shi. A Nijar kashi 25 na yara ne ke samun zuwa makarantar boko, kuma daga yara 100 da ake sanyawa a makarantun firamare uku kadai ke kaiwa matakin jami'a.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al'ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al'adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa. Masarautar Katsinar Maradi dai yanzu ta zama madubi kuma abin koyi a bangaren hadin kan al'ummar Nijar.
Kungiyar ‘Yan Nijar mazauna Cote d'Ivoire ta bukaci a cirewa Nijar takunkumai da aka kakaba mata sakamkon juyin mulki da sojoji suka yi, saboda halin kunci da hakan ya jefa su ciki. Shugaban kungiyar ta Ho consei de Nijar a Cote d'Ivoire Alhaji Abdou Jibo ya yi wannan kira, yayin zantawa ta musamman da sashin hausa na RFI a Abidjan.Amma ya fara yi wa Ahmad Abba bayani kan zamantakewarsu a kasar da ke mamba a ECOWAS.Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan cutar kazuwa ko kuma Smallpox a turance, cutar da ke sahun cutuka masu matukar hadari da ke haddasa kuraje masu matukar kaikayi da mashasshara da kuma hana barci, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da kawar da ita daga ban kasa tun a shekarar 1980 amma kuma duk da haka ake ganin bullarta lokaci zuwa lokaci. Cutar ta kazuwa wadda ake alakantawa da kazanta a baya-bayan nan ne aka samu barkewarta a wasu kauyukan Jihar Maradi ta Jamhuriyyar Nijar, inda masana ke cewa zuwa yanzu akwai fiye da mutum dubu 3 da suka harbu, kuma kaso mai yawa na Almajirai da magidanta sai kuma kananan yara musamman a kauyukan Surori zuwa Tsibiri da kuma garin Udal, wanda ke matsayin karon farko da aka ga bullar cutar bayan shafe tsawon shekaru ba tare da jin duriyarta ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu....
Sannu a hankali rikicin dake gudana tsakanin ECOWAS da sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar na neman rikidewa zuwa rikici tsakanin Najeriya da Nijar, ganin irin matakan da kasashen ke dauka da kuma zafafan kalaman dake fitowa tsakanin bangarorin biyu. Bayan rufe iyakoki da kuma katse wutar lantarki, yanzu haka kasashen biyu sun katse zirga zirgar jiragen sama a tsakanin su.Dangane da tasiri ko illar da wannan matsala za ta yiwa wadannan kasashen biyu dake da alaka mai dimbin tarihi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Elharun Muhammad, na Cibiyar kula da manufofin ci gaba da dangantakar kasashe dake Kaduna, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin....