Lafiya Jari ce

Follow Lafiya Jari ce
Share on
Copy link to clipboard

Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.

Rfi - Azima Bashir Aminu


    • Jun 2, 2025 LATEST EPISODE
    • weekly NEW EPISODES
    • 10m AVG DURATION
    • 196 EPISODES


    Search for episodes from Lafiya Jari ce with a specific topic:

    Latest episodes from Lafiya Jari ce

    Matsalolin da yawan shan suga ke haifarwa jikin mutum a lokacin da ya girma

    Play Episode Listen Later Jun 2, 2025 9:25


    Shirin Lafiya Jari Ce a wannan makon shirin ya mayar da hankali kan yadda wani bincike ke gano cewa yawan shan suger ko kuma sikari a lokutan ƙuriciya na taka muhimmiyar rawa wajen haddasawa mutum ciwon suga a lokacin girma. Wannan cuta ta suga ko kuma Diebetes na cikin jerin cutukan da ke barazana ga rayukan ɗimbin mutane musamman a sassan Najeriya da tuni cutar ta fara zama ruwan dare mai gama duniya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............

    Sharhi kan ƙiba fiye da ƙima da ke baraza ga matasan Afirka

    Play Episode Listen Later May 26, 2025 10:12


    Shirin 'Lafiya Jari Ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan hasashen da wata ƙungiya ta yi cewar nan da shekarar 2025 raɓin al'ummar Afirka masamman matasa za su fuskanci cutar ƙibar da ta wuce ƙima ko Obesity a turance.

    obesity baraza najeriya afirka
    Ƙaruwa masu kamuwa da cutar tarin fuka a sassan Jamhuriyar Nijar

    Play Episode Listen Later May 19, 2025 9:59


    Shirin namu na wannan makon zai mayar da hankali ne kan ƙaruwar mutanen da ke kamauwa da cutar  babban tari, ko kuma tarin fuka, ko kuma TB a sassan Jamhuriyar Nijar, lamarin da ke zuwa a lokacin da ake fuskantar ƙarancin agajin magangunan yaƙi da wannan cuta. Wanmnan cuta na sahun daɗaɗɗun cutuka masu yaɗuwa, waɗanda wani kan iya goga wa wani.Abin da ya  sa ya zama wajibi a rika wayar da kan al'umma akan hanyoyin kariya daga ita.

    Yadda aka sake samun ɓullar cutar Polio a Najeriya

    Play Episode Listen Later May 12, 2025 10:04


    Shirin Lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba na musamman game da dawowar cutar Polio a Najeriya, cutar da alamu ke nuna nasarar yaƙarta ke yiwa ƙasar kwan gaba kwan baya, lura da yadda a lokuta da dama ake sake ganin ɓullarta bayan nasarar kawar da ita, kodayake ƙwararru sun ce wadda ta ɓulla a wannan karon ba wadda aka saba gani ba ce kuma bata kai waɗanda suka gabace ta illa ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............

    Annobar ƙyanda ta tilastawa mahukunta Nijar yin rigakafin ƙasa baki ɗaya

    Play Episode Listen Later May 5, 2025 10:06


    Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan shaushawar ƙyandar da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka jagoranta sakamakon ɓullar cutar wadda a duk lokacin da aka ga bazuwarta ta ke yiwa ƙananan yara illa matuƙa. Dai dai lokacin da duniya ta gudanar bikin makon rigakafi a ƙarshen watan Mayun da ya gabata, a Jamhuriyyar Nijar annobar ƙyanda ce ke ci gaba da yaɗuwa tare da galabaitar da ɗimbin ƙananan yara, lamarin da ya tilasta mahukunta ɗaukar matakan yiwa jama'a rigakafin wannan cuta mai haɗari.Cutar ta Ƙyanda ko Ado ko kuma Dusa na matsayin babbar matsalar kiwon lafiya ta yadda a duk lokacin da ta ɓulla ta kan haddasa asarar ɗimbin rayuka, kodayake a yanzu tuni ma'aikatar lafiya ta jagoranci aikin rigakafin na ƙasa baki ɗaya da zai shafi dukkanin ƙananan yara tun daga watanni 6 da haihuwa har zuwa shekarun 5 da nufin murƙushe cutar.Tsawon mako guda aka shafe daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Mayu ana gudanar da rigakafin na ƙyanda a sassan Nijar wanda aka yiwa ƙananan yaran da yawansu ya tasamma miliyon 5 a kasar, da nufin daƙile asarar rayukan da ake fuskanta sanadiyyar cutar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Yadda cuɗanya wajen amfani da moɗa ko cokali ke taimakawa wajen yaɗa cutuka

    Play Episode Listen Later Apr 28, 2025 9:57


    Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon, ya mayar da hankali ne kan nau'ikan cutukan da ke bazuwa sakamakon cuɗanyar da jama'a ke yi wajen amfani da kayayyakin da bisa ƙa'ida yakamata kowanne mutum ya yi amfani da nasa shi kaɗai. Har yanzu ana samun waɗanda ke yin gamayya wajen amfani da moɗar-shan ruwa ko cokali ko kuma kwanon cin abinci dama sauran kayakin da basu cancanci amfanin gamayya ba, lura da yadda cikin sauƙi hakan ke iya yaɗa cutuka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........

    Matakan da ya kamata a ɗauka yayin kai ɗaukin gaggawa a lokacin faruwar haɗari

    Play Episode Listen Later Apr 21, 2025 10:00


    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakan da ya kamata mutane su riƙa ɗauka gabanin kai ɗaukin gaggawa a lokacin afkuwar haɗari ko ibtila'i, waɗanda rashinsu a wasu lokutan ke kaiwa ga asarar rayuka ko kuma haddasa gagarumar illa ga mutanen da haɗarin ya rutsa da su. Shirin ya shawarci jama'a game da samun ilimin iya kai ɗaukin gaggawa don kaucewa haddasa matsala ba tare da sani ba ga mutanen da ake ƙoƙarin ceton rayuwarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Ana samun ƙaruwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki a Ghana

    Play Episode Listen Later Apr 14, 2025 10:04


    Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan ƙaruwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki ko kuma HIV AIDS ko sida tsakanin matasan Ghana a shekarun baya-bayan nan, wadda masana ke ɗora alhakin yawaitarta kan rashin ɗaukar matakai. Wannan ƙaruwar alƙaluma na zuwa a dai dai lokacin da duniya ke ganin ƙarancin magunguna rage kaifin cutar sakamakon matakin Amurka na zaftare tallafin da ta ke bayarwa ƙarƙashin ƙungiyar USAID.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.

    Mutane na ɓoye cutukan ƙwaƙwalwa saboda fargabar alaƙantasu da hauka

    Play Episode Listen Later Mar 24, 2025 10:41


    Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba na musamman kan cutuka ko kuma lalurar ƙwaƙwalwa, dama rabe-rabenta baya ga nazarin yadda mutane ke ɓoye irin wannan lalura saboda kunyar kar a alaƙanta su da ciwon hauka. Alƙaluman hukumar lafiya ta duniya WHO a shekarar 2017 sun nuna cewa kashi 19 na yawan al'ummar duniya na fama da matsalar ƙwaƙwalwa walau a babban mataki ko kuma a mataki na ƙasa, matsalar da kuma bayanan hukumar ke cewa yafi tsananta a ƙasashe masu tasowa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    ku hauka
    An samu ɓullar cutar sankarau a wasu jihohin arewacin Najeriya

    Play Episode Listen Later Mar 17, 2025 10:04


    Shirin 'Lafiya Jari Ce'  na wannan makon ya mayar da hankali ne akan cutar sankarau, wanda ke yin ƙamari a cikin yanayi na zafi da ake ciki, musamma a ƙasashenmu na nahiyar Afrika. Tuni aka samu ɓullar cutar sankarau a sassa daban-daban na Najeriya inda ta kashe gomman mutane a jihohin Kebbi da Sokoto, wadda aka bayyana ta da annoba. Masana a ɓangarorin lafiya da kuma yanayi, na ci gaba da gargaɗi kan yiwuwar ɓullar tarin cutuka sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta a wasu daga cikin jihohin Najeriya, a wani yanayi da ake ci gaba da azumin watan Ramadana,, wannan shi ne maudu'in da shirin lafiya jari ce na wannan mako zai mayar da hankali akai sai ku biyomu.

    Ƙarancin magungunan kuturta da abubuwan da ke haddasa cutar

    Play Episode Listen Later Mar 10, 2025 9:58


    A wannan makon shirin na lafiya jari ce ya mayar da hankali kan cutar kuturta ko kuma Lebrosy ko albaras, cutar da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke ganin sam bai kamata a samu ɓirɓishinta a banƙasa ba.Rayuwar masu wannan lalura ta kuturta rayuwa ce mai cike da ban tausai, musamman waɗanda ke killace a asibitin na Bela wanda Turawan mishan daga Netherlands suka samar tun a shekarar 1928 wato tun gomman shekaru kafin ƴancin Najeriya. Alƙaluma sun nuna cewa, duk shekara Najeriya na ganin fiye da mutum dubu guda sabbin kamuwa da wannan cuta ta kuturta wadda tuni ta zama tarihi a wasu sassa na duniya.Masu lalurar ta kuturta na rayuwa cikin yanayi na tsangwama ko ƙyama wannan dalili ya sanya da dama daga cikinsu tattarewa a  Bela.

    Rashin kulawa ta sanya wasu asibitoci a jihar Kano komawa Kufai

    Play Episode Listen Later Mar 3, 2025 9:49


    Shirin ''Lafiya Jari Ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon, ya kai ziyara wasu asibitocin yankunan karkara a arewacin Najeriya, inda sashen Hausa na RFI ya ganewa idonsa tarin matsalolin da suka dabaibaye irin waɗannan asibitoci da bisa al'ada ke matsayin masu kula da lafiya a matakin farko. Tarin asibitocin yankunan karkarar jihar Kano na fama da matsaloli kama daga rashin malaman jinya da kuma rashin wadatattun kayakin aiki, koma rashin ginin Asibitin ɗungurugum, ta yadda da dama daga cikinsu suka juye daga matsayin cibiyoyin kula da lafiya zuwa dandalin shaƙatawar dabbobi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Tiyatar fitar da jarirai daga cikin Uwa na yawaita a sassan Najeriya

    Play Episode Listen Later Feb 24, 2025 10:15


    Shirin Lafiya jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda fasahar cire ɗa ta hanyar CS ke taimakawa wajen ceto rayukan uwa da ɗa da nufin rage asarar rayukan da ake fuskanta a lokacin haihuwa. Duk da cewa haihuwa 3 cikin 100 ce kaɗai ake yi ta hanyar tiyata ko kuma CS a Najeriya bisa alƙaluman 2019, amma a baya-bayan nan ana ganin yawaitar matan da ake yiwa CS gabanin haihuwa kama daga nau'in matan da basa zuwa asibiti da kuma mata masu shekaru da yawa ko waɗanda suka yi haihuwa da dama, duk dai a ƙoƙarin kange yawaitar mace-macen mata ko kuma asarar jariran da ake gani a sassan ƙasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    Mahukuntan Najeriya sun tsawaita shekarun aiki ga likitoci da jami'an lafiya

    Play Episode Listen Later Feb 17, 2025 9:44


    Shirin ''Lafiya Jari Ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya na tsawaita lokacin ritayar likitoci da malaman jinya a wani yunƙuri na ganin sun ci gaba da bayar da gudunmawa ga al'ummar wannan ƙasa wadda ke fama da ƙarancin ƙwararrun likitoci. Matakin na gwamnatin Najeriya ya nuna cewa Likitocin ko kuma sauran jami'an lafiya na da zaɓin ƙarin shekaru 5 akan ainahin shekarunsu na ritaya, ta yadda za su kai har shekaru 65 na haihuwa a bakin aiki maimakon shekaru 60 a baya, ko da ya ke wannan mataki bai samu maraba daga wasu unguzoma ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....

    Lafiya Jari Ce: Illar rashin zuwa awon ciki ga lafiyar mata da jariransu

    Play Episode Listen Later Feb 10, 2025 10:09


    Shirin ''Lafiya Jari ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matsalar rashin zuwa awo da ke matsayin babban ƙalubalen ga mata masu juna biyu a yayin goyon ciki ko kuma haihuwa, matsalar da aka fi ganin ta'azzararta a yankunan karkara, wadda a lokuta da dama ke kaiwa ga asarar rayukan walau uwa ko jariri. Ƙorafe-ƙorafen jami'an lafiya na ci gaba da yawaita kan matsalolin da suka dabaibaye tsarin renon ciki da kuma haihuwa a yankunan karkara, matsalar da wala'alla ake ganin ta na da alaƙa ta ƙut da ƙut da halin matsi ko kuma tsadar rayuwar da ake fama da ita wadda ta ƙai ƙololuwa a yankin arewacin Najeriya mai fama da durƙushewar ɓangaren kiwon lafiya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    Barazanar da fannin lafiya ke fuskanta kan ficewar likitoci daga Najeriya

    Play Episode Listen Later Jan 27, 2025 10:07


    Shirin lafiya Jari ce na wannan makon ya taɓo batun yadda kwararrun likitoci ke tserewa daga Najeriya, inda wasu alkaluma suka nuna cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, sama da likitoci dubu 16 suka fice daga ƙasar don yin aiki a wasu ƙasashen ketare, lamarin da ke barazana ga tsarin kula da lafiya a ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............

    Ƙoƙarin da ƙungiyoyi ke yi don magance cutar yanar ido tsakanin al'ummar Nijar

    Play Episode Listen Later Jan 20, 2025 10:11


    Shirin Lafiya jari ce bisa al'ada tare da Azima Bashir Aminu na yin duba ne kan wasu batutuwa da suka shafi kiwon lafiya, kuma a wannan makon ya yada zango a Jamhuriyyar Nijar inda wasu ƙungiyoyin agaji suka yiwa tarin mutanen da ke fama da matsalar cutar yanar ido aiki a ƙokarin dawo musu da ganinsu. A cikin shirin za ku ji yadda kusan kashi 2 cikin 100 na al'ummar wannan ƙasa ta yankin Sahel ke fama da matsalar lalurar ta yanar ido a wani yanayi da mahukunta tare da taimakon ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ke fatan magance matsalar zuwa ƙasa da kashi 1 nan yan shekaru masu zuwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Tsarin tazarar Iyali ya fara samun karɓuwa a yankunan karkara

    Play Episode Listen Later Jan 6, 2025 9:59


    Shirin lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu bisa al'ada kan taɓo batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ko kuma a lokuta da dama ya lalubo ƙalubalen da fannin lafiyar ke fuskanta don ankarar da mahukunta da nufin ɗaukar matakan gyara. A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tazara ko kuma tsarin iyali ko Family Planning wanda ke sahun shawarwarin kiwon lafiya da ke ganin kakkausar suka musamman a arewacin Najeriya wala'alla saboda yadda tsarin ya ci karo da al'adun al'ummomin wannan yanki, sai dai a baya-bayan nan alamu na nuna yadda wannan tsari ke samun karɓuwa gadan-gadan.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....

    Cutar sanƙarau ta fara fantsamuwa a sassan jihar Maradi ta Nijar

    Play Episode Listen Later Dec 30, 2024 9:49


    A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda aka samu ɓarkewar cutar sankarau a wata Makaranta da ke jihar Maradin Jamhuriyar Nijar, cutar da tuni ta harbi tarin ɗalibai, a wani yanayi da masana ke gargaɗi kan haɗarin da ke tattare da wannan cuta musamman nau'in wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi. Kafin yanzu akan ga ɓullar cutar sanƙarau ne a lokaci na zafi sai dai a shekarun baya-bayan nan ana ganin yadda wannan cuta kan sauya salo tare da ta'azzara a lokacin sanyi wadda masana ke ganin ta na da haɗari matuƙa a wasu lokutan illarta kan zarta wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi, kasancewarta mai saurin kisa matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............

    Barazanar da hunturu ke yi ga keɓantattu ko kwantattun cutuka

    Play Episode Listen Later Dec 23, 2024 9:54


    Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda lokacin sanyi ko kuma hunturu kan zo da wasu keɓantattu ko kuma tayar da wasu kwantattun cutuka. Nau'ikan cutukan da suke barazana ko kuma tashi a irin wannan lokaci na hunturu sun ƙunshi mura ko tari, ko ciwon hakori baya ga saɓar fata kana yawan fitsari ko cutuka masu alaƙa da zuciya yayinda cutuka irin sikila ko asma kan tashi duk dai a wannan lokaci. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......

    Yadda ƙungiyar ALIMA ta Faransa ke taimakawa wajen yaƙi da cutar yunwa a Najeriya

    Play Episode Listen Later Dec 16, 2024 9:54


    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan ta'azzarar cutar Tamowa ko kuma rashin sinadaran abinci mai gina jiki da ke addabar ƙananan yara a Najeriya, a wani yanayi da asusun UNICEF ke cewa duk yaro 1 cikin 3 na fama da matsalar ƙarancin abinci a ƙasar, wanda ke wakiltar kashi 37 cikin 100 na yawan yaran ƙasar ko kuma adadin yara miliyan 6. Duk da cewa tsawon lokaci wannan cuta ta ɗauka ta na addabar yara a Najeriyar, a wannan karon cutar ta tsananta a jihohin arewacin ƙasar wanda masana suka alaƙanta da matsaloli masu alaƙa da rashin tsaron da ya hana jama'a noma da kuma gushewar damunar bana da wuri, lamarin da ya ƙara yawan yaran da ke fama da cutar ta Tamowa ko kuma yunwa, dalilin da ya ja hankali ƙungiyoyin agaji da dama ciki har da ALIMA wato Alliance for International Medical Action ta Faransa wadda ke bayar da agajin lafiya a ƙasashe 13 ciki har da Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    Irin kulawar da ya kamata iyaye su bai wa ƴaƴansu a yanayi na hunturu

    Play Episode Listen Later Dec 9, 2024 10:01


    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan cutukan da ke barazana a lokacin sanyi, baya ga shawarwari kan yadda iyaye za su kula da lafiyar yaransu a irin wannan lokaci, musamman ganin cewa yaran ne sanyi ya fi yiwa illa fiye da manya. Dai dai lokacin da iskar hunturu ta fara kaɗawa a sassan jamhuriyar Nijar, jihar Difffa na sahun jihohin da wannan matsala ke tsananta matuka ta yadda a kowacce shekara ake ganin tarin waɗanda sanyi kan yiwa lafiyarsu illa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......

    Adadin masu kamuwa Cancer zai ninka sau 10 a Najeriya- Masana

    Play Episode Listen Later Dec 2, 2024 10:00


    Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda cutar Cancer ko kuma Daji ko Najeriya ke ta'azzara a Najeriya a wani yanayi da ake da ƙarancin wayar da kai kan cutar duk kuwa da illar da ta ke ci gaba da yiwa jama'a. Hankulan masana a ɓangaren kiwon lafiya ya tashi ne matuƙa bayan hasashen da ke nuna yiwuwar alƙaluman masu kamuwa da cutar duk shekara a Najeriyar da yawansu ya kai dubu 70 ya iya ruɓanyawa fiye da ninki 10 nan da shekaru ƙalilan masu zuwa a ƙasar, a wani yanayi da har yanzu jama'a ke jahiltar cutar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    cancer ku masu ninka najeriya masana
    Matsalar mace-macen mata masu juna biyu ta sake ta'azzara a Nijar

    Play Episode Listen Later Dec 2, 2024 10:06


    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matsalar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai walau a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki, matsalar da ke tsananin ta'azzara a Jamhuriyyar Nijar bayan da alƙaluma suka nuna yadda matsalar ke kwan-gaba-kwan-baya sakamakon dawowarta a baya-bayan nan bayan daƙileta a shekarun baya. Masana sun alaƙanta matsaloli masu alaƙa da rashin cin abinci mai gina jiki ko kuma rashin kulawar lafiya baya da rashin garkuwa mai ƙwari ga matan a jerin manyan dalilan da kan sabbaba mace-macen matan masu juna.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Yadda ake samun ƙaruwar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju'a

    Play Episode Listen Later Nov 25, 2024 10:13


    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya nazarci yawaitar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju'a da ake ganin ta'azzararsu a wannan lokaci musamman a sassan Najeriya a wani yanayi da matsi ko kuma tsadar rayuwa ke ci gaba da galabaitar da jama'a. Dai dai lokacin da masana ke alaƙanta wannan matsala ta mutuwar far ɗaya da wasu kwantattun cutuka da yanayi kan tayar da su a lokaci guda, wani bincike baya-bayan nan ya danganta tsananin damuwa da yawaitar tunane-tunne halin rayuwa a matsayin ummul aba'isin kamuwa da wasu cutuka da ke kisan jama'a. Tuni dai masana a ɓangaren kiwon lafiya suka tsananta kiraye-kirayen ganin jama'a sun mayar da hankalin wajen sanin halin da lafiyarsu ke ciki don kaucewa mutuwar ta kwaf ɗaya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......

    Lafiya Jari ce: Illar da hayaƙin girki ke yiwa lafiyar idon Mata

    Play Episode Listen Later Nov 11, 2024 10:01


    A wannan makon shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani gargaɗin masana game da illar hayaƙi ga lafiyar jama'a a wani yanayi da masanan ke ganin mazauna garuruwa irin Kano da Sokoto da Kwara baya ga kaso mai yawa na jihohin arewacin Najeriya na cikin haɗarin kamuwa da cutukan masu alaƙa da numfashi sakamakon yadda suka dogara da itace ko kuma gawayi wajen yin girki. A ɓangare guda wasu ƙwararrun na ganin matan da suka shafe lokaci suna girki da itace ka iya fuskantar matsalar ido, tambayar a nan ita ce ko matan na da masaniya kan illar hayakin girki ga lafiyar idonsu? Ku biyo mu a cikin shirin don sauraren mahangar masana da kuma yadda Mata ke kallon illar ta hayaƙin girki ga lafiyarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....

    Yadda cutar kwalara ta addabi wasu jihohin arewacin Najeriya

    Play Episode Listen Later Nov 4, 2024 9:55


    Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar Kwalara ko Amai da Gudawa da ta afkawa wasu jihohin Najeriya, inda ta haifar da asarar ɗumbin rayuwa tun bayan ɓullarta a farkon wannan shekara ta 2024

    Ƙuncin rayuwa na jefa ɗimbin ƴan Najeriya cikin tsananin damuwa - Rahoto

    Play Episode Listen Later Oct 28, 2024 9:54


    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan matsalar damuwa mai dankwafarwa ko tsananin damuwa da ake kira Depression, cutar da ake ganin ta'azzararta a baya-bayan nan tsakanin ƙasashe masu tasowa musamman waɗanda ke fama da matsi ko kuma ƙuncin rayuwa. Wasu bayanan ƙwararru yayin bikin ranar lafiyar ƙwaƙwalwa da ya gudana a farkon watan nan, ya nuna yadda matsi da ƙunchin rayuwa ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya a tsananin damuwar ko kuma damuwa mai dankwafarwa, matsalar da likitoci suka yi gargaɗin cewa ka iya kaiwa ga taɓin ƙwaƙwalwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........

    Yadda mutane ke kauracewa yin gwaje-gwajen lafiya na wajibi

    Play Episode Listen Later Oct 21, 2024 9:49


    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon yayi duba ne kan ƙalubalen da fannin lafiya ke fuskanta na yadda ake gani a halin yanzu jama'a ke tsoro ko kuma kaucewa gwaje-gwajen lafiya ciki kuwa da har da wajibi da suka ƙunshi hawajini da nau'in jini ko kuma rukuninsa duk kuwa da muhimmancin hakan ga lafiyarsu. A baya-bayan nan bincike ya gano yadda jama'a kan kaucewa yin gwaje-gwaje kama daga na wajibi ko kuma a lokacin kamuwa da cutuka, walau ko saboda tsoron gano wasu nau'in cutuka da ke tare da su ko kuma wani dalili na daban.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......

    ku yadda najeriya
    Illar shan magani ba tare da shawarar masana kiwon lafiya ba

    Play Episode Listen Later Oct 14, 2024 9:57


    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar shaye-shayen magunguna ba bisa ka'ida ko kuma shawarwarin masana kiwon kiwon lafiya ba, wadda hakan ke haifar da matsaloli da dama a jikin dan'adam. 14/10/2024

    Illar da hayaƙin taba sigari ke da shi ga lafiyar al'umma

    Play Episode Listen Later Oct 7, 2024 10:00


    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar zuƙar taba sigari a cikin al'umma saɓanin  wasu keɓantattun wurare da doka ta tanada. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a duk shekara sama da mutane miliyan 8 ne ke mutuwa sanadiyar shakar hayakin taba sigari kuma daga cikin wancan adadi, akwai sama da yara dubu 65 waɗanda lamarin ke shafa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    Yadda ake samun ƙaruwar masu fama da cutar amasonin jini

    Play Episode Listen Later Sep 30, 2024 9:53


    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda ake ganin ƙaruwar masu fama da cutar amasonin jini, ko Sickler ko kuma Emasi, batun da ke da alaƙa ta kai tsaye da auratayyar da ake yi tsakanin masu nau'ikan jinin da masana ke gargaɗi kan illar da hakan ke da shi ga ƴaƴan da za su haifa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    Tsanantar cutar ƙoda da abubuwan da ke haddasa ta a tsakanin al'umma

    Play Episode Listen Later Sep 23, 2024 9:44


    A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan abubuwan da ke haddasa cutar koda, la'akari da yadda cutar ke tsananta a wannan lokaci musamman a kasashe irin Najeriya, sabanin a lokutan baya da ba kasafai ake ganinta ba, baya ga karancin wuraren wankin kodar da ake fama dasu wato dialysis centers a turance. Wani bincike na baya-bayan nan na nuni da cewa cutar koda ita ce ta 10 cikin cututtukan da ke kan gaba wajen haddasa mace-mace a fadin duniya, inda binciken ya nuna cewa kuma tana shafar kusan kashi 10 na al'ummar duniya, wanda a halin yanzu sama da mutane miliyan 850 ke fama da ita.

    wani najeriya
    Abubuwan da ke haddasa tsinkewar laka ga ɗan Adam

    Play Episode Listen Later Sep 20, 2024 9:21


    Shirin lafiya jarice na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar katsewar laka wacce ke iya afkuwa a sanadiyar hadarin mota ko makamantansu da rikice-rikice ko fadowa daga wurare masu tudu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin

    Yawaitar masu fama da lallurar laka a sassan Najeriya

    Play Episode Listen Later Sep 16, 2024 9:58


    A wannan mako shirin zai mayar da hankali game da cuta ko kuma ‘‘lalurar katsewar Laka'' wato Spinal cord Injury, lalurar da a baya-bayan nan alƙaluma ke nuna yawaitar masu fama da ita a sassan Najeriya, walau sakamakon haɗarin mota ko rikici dama sauran dalilai. Yayin bikin ranar wayar da kai game da lalurar ta Laka da ke gudana a kowanne wata na Satumba, da a wannan karon aka yiwa take da ‘‘ Kawar da tarzoma a matsayin hanyar kawar da laka'' masana sun ce baya ga haɗurran mota hanyoyi da dama na haddasa wannan lalura ta laka.

    Yadda cutar borin gishiri ke addabar mata masu juna biyu a Jamhuriyar Nijar

    Play Episode Listen Later Sep 9, 2024 10:04


    A wannan makon shirin zai mayar da hankali kan cutar borin gishiri ko kuma kumburin da mata ke fama da ita yayin da suke da dauke da juna biyu, wacce kuma a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka. Wannan cuta a Jamhuriyar Nijar na daga cikin wacce ke ciwa hukumomi tuwo a kwarya ganin yadda mata sama da dari biyar da 30 cikin kowace mace dubu daya ne kamuwa da wannan cuta, kuma sama da 50 ke rasa ransu a sanadiyarta.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    Ƙaruwar ƙananan yara da ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki

    Play Episode Listen Later Sep 2, 2024 10:16


    A wannan makon shirin zai mayar da hankali kan ƙaruwar ƙananan yaran da ke fama da cutar yunwa ko kuma Tamowa a yankunan da ke fama da ƙarancin abinci, cikinsu kuwa har da Nijar, ƙasar da alƙaluman 2021 ke cewa akwai ƙananan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 akalla miliyan 1 da dubu 800 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki. A baya-bayan nan anga ƙaruwar yaran da ke fama da cutar Tamowa ko da ya ke har yanzu akwai ƙaranci sani game da cutar, kan hakan mu ka fara da tuntuɓar Dr Fayuz Mu'azu likitan mai kula da ƙananan yara masu fama da cutar Tamowa a jihar Diffa, ya kuma yi mana bayani kan cutar da dalilan da ke haddasata.

    Hatsarin da ke cikin amfani da maganin ƙwari wajen adana kayan abinci

    Play Episode Listen Later Jul 22, 2024 9:50


    Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai mayar da hankalli ne a kan gargaɗin da hukumar kiyaye ingancin abinci da magunguna a Najeriya, wato NAFDAC ta yi a kan hatsarin da ke tattare da amfani da maganin kashe ƙwari na Sniper a wajen adana kayan abinci domin kare su daga ƙwari. NAFDACdai ta jaddada haramcin da ta yi a kan amfani da wannan magani da ma sshigowa da shi Najeriya, bayan da ce bincikenta ya tabbatar  da cewa maganin yana haddasa cutuka da suka haɗa da cancer.

    Tasirin sabbin abinci da aka ƙirƙira wato Synthetic Foods ga lafiyar jama'a

    Play Episode Listen Later Jul 15, 2024 9:45


    Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan tasarin nau'ukan abinci da akan ƙirkira a ɗakunan bincike wadanda ake kira Synthetic foods a turance, domin nazari kan illolinsu ko kuma akasi ga lafiyar jama'a, duba da yadda nau'ukan abinci da nomansu akayi ba ko kiwo ke samun ƙarbuwa a wasu kasashen duniya.

    Yadda cutar kansar bakin mahaifa ke hallaka mata a tarayyar Najeriya

    Play Episode Listen Later Jul 1, 2024 9:56


    Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi duba ne kan yadda kansar bakin mahaifa ke hallaka Mata, musamman ƴan tsakanin shekaru 15 zuwa 44, a Najeriya. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron shirin...

    mata kuna yadda najeriya tarayyar najeriya
    Yadda mata ke rungumar tiyatar gyaran jinki duk da gargadin da likitoci ke yi

    Play Episode Listen Later Jun 24, 2024 9:47


    Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya duba kan yadda mata ke yin tiyatar gyaran jiki ko sauya sura wato Cosmetics Surgery, wacce a yanzu mata da dama suka runguma, duk kuwa da yadda likitocin ke ganin hakan na da illa ga lafiyarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......

    Tsarin kiwon lafiya da mahukunta ke dauka a Saudiyya

    Play Episode Listen Later Jun 10, 2024 10:02


    Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya duba yanayin lafiyar mahajjata, a dai-dai lokacin da al'ummar Musulmai ke gudanar da ibadar hajji a Saudiyya. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu

    Har yanzu 'yan Najeriya da dama basa cin gajiyar shirin Inshorar lafiya -Bincike

    Play Episode Listen Later Jun 3, 2024 9:56


    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan yadda har yanzu wasu daga cikin al'ummar Najeriya basa amfani da tsarin inshorar lafiya. A shekarar 2022 ne gwamnatin kasar ta sake dawo da dokar inshorar lafiya da aka samar tun 1999, a wani yunƙuri na sauƙaƙawa Jama'a samun kulawar lafiya cikin rahusa, lura da yadda kaso mai yawa na al'ummar ƙasar ke rasa kudaden iya kai kansu ga likitoci ko da suna cikin matsananciyar cuta.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......

    Yara 'yan kasa da shekaru biyar na gaza samun alluran rigakafin da ta dace

    Play Episode Listen Later May 27, 2024 9:51


    Shirin na wannan mako ya duba yadda kananan yara musamman a Najeriya da sauran kasashe masu tasowa ke gaza karbar alluran rigakafin da ya kamata su samu kafin cika shekaru biyar da haihuwa.

    Halin da ake ciki a yaki da cutar yunwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar

    Play Episode Listen Later May 20, 2024 9:58


    A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya yi duba ne a kan halin da ake ciki a yaki da cutar Tamuwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar.

    yaki ciki jamhuriyar nijar
    Bayani a kan cutar ƙyanda da yadda za a kare yara daga kamuwa

    Play Episode Listen Later May 13, 2024 9:58


    A wannan makon shirin zai yi duba kan cutar kyanda ko kuma measles a turance, cutar da galibi akan ga bullarta a irin wannan lokaci da ake fama da matsanancin zafi musamman a yankunan kasashen yammacin Afrika Sahel.  Zuwa karshen watan Fabarairun da ya gabata, fiye da yara 700 suka harbu da cutar kyanda a jihar Borno cikin watan yayinda zuwa yanzu ta kashe kananan yara 42 a jihar Adamawa yayinda wasu fiye da dubu guda suka harbu.Bari mu bude da rahoton wakilinmu Ahmad Alhassan daga jihar Adamawa, jihar da zuwa yanzu tsanantar wannan cuta ta kyanda ta tilasta kulle makarantu.

    Yadda matasa ke rungumar tsarin yin kaho a zamanance

    Play Episode Listen Later May 6, 2024 10:09


    Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan tsarin yin kaho a zamanance Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu

    Karancin ruwa na haddasa tarin cutuka ga al'ummar arewacin Kamaru

    Play Episode Listen Later May 3, 2024 10:07


    Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al'ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu'in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai. Tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha na  matsayin ginshikin lafiyar jama'a wanda kuma rashin ke matsayin babbar barazanar bullar tarin cutuka na cikin wajen jikin bil'ada, sai dai samun ruwan sha ko na amfani ga galibin al'ummomin da ke rayuwa a yankin arewacin Kamaru na matukar wahala.A baya-bayan nan al'ummar yankin na ganin bullar cutuka da dama masu alaka da rashin tsaftataccen ruwan sha ko na amfani, yankin da kashi 43.5 na al'ummarsa ne kadai musamman mazauna karkara kan iya samun wadatacce kuma tsaftataccen ruwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.

    Amfanin Azumi ga lafiyar jikin dan Adam

    Play Episode Listen Later Apr 1, 2024 9:58


    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne game da alfanun Azumi ga lafiyar jikin dan Adam. Masana kiwon lafiyar dai na bayyana cewar Azumi na taimakawa wajen rage kaifin wasu cutuka a jikin dan adam. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    Yadda ya kamata mai Azumi ya kula da kansa a lokacin zafi

    Play Episode Listen Later Mar 25, 2024 9:05


    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan irin cutukan da ke karuwa a lokutan Azumi musamman yadda a wannan karon ake gudanar da ibadar a cikin yanayi na tsananin zafi, wanda masana ke ganin akwai wasu naukan cutukan da ka iya bijorowa. Masana kiwon lafiya dai sun gargadi masu dauke da wasu nau'ukan cutuka kan irin matakan da ya kamata su dauka don kula da lafiyarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    Yadda aka yi wa sama da yara dubu dari 9 rigakafin cutar Polio a Kamaru

    Play Episode Listen Later Mar 18, 2024 10:13


    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gangamin rigakafin cutar shan inna wato Polio a Jamhuriyar Kamaru don dakile bazuwarta. A baya-bayan nan ne dai ake ganin bullatar cutar a wasu sassan kasar, lamarin da ya sanya mahukunta tashi tsaye don yin rigakafin cutar. Sama da yara dubu dari 9 da 48 ne aka yi wa rigakafin a fadin jahohi 10 na Kamaru, a aikin da aka kwashe tsawon kwanaki uku ana yi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    Claim Lafiya Jari ce

    In order to claim this podcast we'll send an email to with a verification link. Simply click the link and you will be able to edit tags, request a refresh, and other features to take control of your podcast page!

    Claim Cancel