Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Wannan shiri zai mayar da hankali ne kan yadda zamani ke tasiri akan salon magana ko gagara gwari a tsakanin al'umar hausawa, musamman ma matasa masana da dattawa da suka jiya suka ga yau sun bayyana dalilai da suka sanya irin wannan salo na zance, wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa a tsakanin al'uma da gudummawar da kowanne ɓangare ke bayarwa wajen disashewar wannan fiƙira ta harshe.
Shirin al'adun mu na Gado na wannan mako zai Dora kan ci gaban Muhawara a tsakanin Masana kan kwarewar waƙa a tsakanin mawaki Shata da kuma Rarara Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare a Nasiru Sani
Shirin al'adu na wannan makon ya waiwayi al'adar waƙoƙin Hausa ne da kuma tasirin Mawaƙan da suke rera su waƙoƙin a fannonin rayuwa daban daban. A baya bayan nan aka tafka muhawara tsakanin wasu masana guda biyu na Adabin Hausa wato Dakta Abdul-Shakur Yusuf Ishaq na Jami'ar Jihar Kaduna da kuma Dakta Mu'azu Sa'adu Kudan na Jami'ar Sule Lamiɗo da ke Kafin Hausa a jihar Jigawa, waɗanda suka baje iliminsu a kan matakin shahara, da kamance-ceniya da kuma banbanci a tsakanin Marigayi Mamman Ibrahim Yero da aka fi sani da Mamman Shata ko kuma Shata mai Ganga da kuma Dauda Adamu Kahutu Rarara da a halin yanzu zamani ke tafiya da shi.
Shirin a wannan makon zai tattauna ne a kan Camfi, da kuma yadda ya kasance a zamanin kaka da kakanni, da rawar da ya taka a waccan lokaci da kuma yadda yake shafar rayuwar jama'a a lokacin da muke.Duk da ƙarancin lokaci, shirin Al'adunmu na gado zai yi ƙoƙarin zayyana rabe-raben al'adar ta Camfi ko kuma wasu daga ciki.
Shirin al'adunmu na gado tare da Oumarou Sani a wannan mako ya mayar da hankali ne kan al'adun ƙabilar Dagomba a ƙasar Ghana, ƙabilar da ke ci gaba da mamaya a wannan ƙasa ta yammacin Afirka suk da kasancewarta wadda a baya tafi ƙarfi a yankin arewacin ƙasar. Yanayin suturun wannan ƙabila na daga cikin abin da ke jan hankalin jama'a, musamman yanayin hularsu wadda ke da nufin ko kuma ma'anar zaman lafiya.Suturun wannan ƙabila dai akan saƙa su da hannu ne.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
A yau shirin zai mayar da hankali ne akan al'adar 'Dalilin Aure' a ƙasar Hausa da yadda aka zamanantar da ita.A baya masu 'Dalilin Aure' a boye suke a cikin al'umma, sai dai yanzu a iya cewa zamani riga, domin kuwa za ka iske sun bude ofisoshi tare da sanya alamar cewa anan fa Dalilin aure ake.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan al'adar nan ta dalilin aure, guda cikin al'adun Hausawa da aka shafe tsawon lokaci ana amfani da ita da nufin haɗin aure walau tsakanin ƴammata da Samari ko kuma Zawara. Kamar yadda kusan kowanne lamari ke tafiya da zamani itama al'adar ta juye, ta yadda ta koma cikakkiyar sana'a da wasu ɗaiɗaikun mutane ke da gogewa akanta, har ta kai ga ake buɗe ofisoshi don gudanar da ita.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Kamar yadda aka saba, shirin yakan yi dduba ne akan al'adun al'ummar Hausawa da sauran su, waɗanda suka gushe ko kuma ake ganin wanzuwan su a yanzu.Al'adar tashe dai na daga cikin al'adun da aka fara ganin yaɗuwarsu a ƙasar Hausa tun a ƙarni na 16, al'ada ce da ta ƙunshi wasannin barkwanci, waɗanda ake gudanar da su da zarar a kammala azumin goman farko na watan Ramadana. Sai dai wannan al'ada ta fara gushewa. Ko menene dalilin haka? Abin da shirin wannan makon zai yi nazari a kai kenan.
shirin Al'adun Mu na Gado na wanan makon tareda Abdoulaye Issa ya leka Jihar Maradin Jamhuriyar Nijar inda al'adar aikin kwado da lizzami da aka share shekaru ana yin sa da hannu ke fuskantar barazanar samun babban koma baya sakamakon wasu sabbin na'urori ko teloli na zamani da aka samu masu aiki da Computer wadanda ke zuba wannan aiki ga riguna cikin gaggawa. Ku shiga cikin alamar sauti domin sauraron shirin....
Shirin Al'adun Mu na Gado a wannan makon ya kawo muku ci gaban tattaunawa da Dakta Tahir da ake kira da Babba Impossible, wanda a makon daya gabata ya fara fashin baƙi a lamarin da yashafi tsafe-tsafe. Haka nan shirin ya leka Jamhuriyar Benin, inda gwamnatin ƙasar ta sanar da rusa wasu masarautu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa............
Shirin Al'adun Mu na Gado na wanan makon tareda Abdullaye Issa ya maida hankali kan dawowa tsafe-tsafe a cikin al'amurran al'umma na yau da kullum.
Shirin ''al'adunmu na gado'' tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya leƙa jihar Adamawa ta yankin arewa maso gabashin Najeriya don duba yadda gwamnatin Jihar ta ƙara yawan Masarautu a wannan jiha tun cikin shekarar da ta gabata. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan al'adar nan ta naɗin sarauta da wasu masarautun gargajiya ke yi ga ƙabilun da ba su ke da masarautar ba, wanda hakan ya biyo bayan sabbin naɗe-naɗe da ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙabilar gwari a arewacin Najeriya ta yi wa wasu manyan shuwagabannin al'ummar fulani a jihar Neja. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun masarautun Hausa da Fulani da ma wasu masarautun a yankin kudanci da kuma arewacin Najeriya ke baiwa ƙabilun da ke zaune a masarautar sarauta ba, abin da shirin Al'adu na wannan mako ya yi nazari akai tare da jin inda hakan ya samo asali da kuma alaƙar da ke tsakanin al'adun ƙabilar gwari da fulani daga masana al'adu da masarautu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi. A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al'adu ke kallon al'amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Al'adunmu na gado na yau, ya yi duba ne kan al'adar shaƙe a ƙasar hausa da wasu kan yi a matsayin al'ada da kuma magani. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
Shirin Al'adun mu na gado na wannan makon ya mayar da hankali ne ga bukuwan sabuwwar shekara na ƴan ƙasar China, bukukuwan da aka gudanar a sassa daban daban na duniyar. A Najeriya, ƴan China ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da wannan biki a biranen Abuja da kuma Lagas, wanda ya samu halarta jama'a baki daga ciki da waje. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ke kan al'adar shaɗi ko kuma Charo na sahun manyan al'adun ƙabilar fulani a ƙasashen Afrika ta yadda har sai wanda ya iya karɓaɓɓen shaɗi ke iya samun matar aure, yayinda a wasu lokutan ake gudanar da wannan al'adu a shagulgula don nishaɗi kuma jajirtacce shi ne jarumi.
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al'ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al'ada tana neman gushewa a tsakanin al'ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al'adar daga baya. Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana'ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al'adun duniya.Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al'adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa. Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
Shirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna dangene da gushewar a'adar tatsuniya wadda ke zama hanyar da al'ummar Hausawa ke amfani da ita wajen ilmantarwa, fadakarwa da kuma tarbiyantar da yara ta hanyar shirya kagaggun labarai masu kunshe da darussa.
A yau shirin al'adun zai je jihar Nassarawa inda muka samu zantawa da mai Martaba Sarkin Nassarawa,daga bisani za mu je Jamhuriyar Nijar inda zamu duba koma bayan wakokin gargajiya a cikin al'umma.
Yau shekaru tara kenan da zama Sarkin masarautar keffi da mai martaba Dr alhaji shehu usman chindo yamusa,bayan rasuwar mahaifinsa mai martaba alhaji Chindo Yamusa na uku 3.A cikin shirin al'adu za ku ji tarihin Sarkin na Keffi.
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa kamar yadda ya saba a wannan makon ma ya leƙo wasu daga cikin masarautun Hausawa don jin tarihi da kuma tasirinsu ga al'umma. A wannan karon shirin ya yi duba kan tasirin al'adun gargajiya a matsayin jigon tafiyar da shugabanci bayan ficewar turawan Mulkin mallaka a Najeriya.Haka zalika za kuji hira ta musamman da sarkin Keffi a jihar Nassarawa wato Mai martaba Alhaji Shehu Usman Shindo Yamusa.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....
Shirin al'adunmu na gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gagarumin biki baje kolin al'adu a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya. An gudanar da bikin ne a fitacciyar cibiyar al'adu ta Nike Art Gallery, wanda ya shahara a duniya, bikin ya tattaro mutane da dama daga sassan fasaha, kasuwanci, siyasa da diflomasiyya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aboulaye Issa........
Shirin al'adunmu na gado tare da Aboulaye Issa, ya mayar da hankali ne kan al'adar gaɗa da ke ƙoƙarin gushewa tsakanin al'ummar Hausawa duk da tasirinta a shekarun baya musamman tsakanin matasa.
Shirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon yayi duba ne kan yadda ake gudanar da bikin Sallar Gani. ita dai wannan sallar na daga cikin dadadun al'adar mallam Bahaushe, kuma har yanzu ana gudanar da wannan biki a wasu masarautu a Arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ci gaba ne game da jerin shirye-shiryen da muka faro kan zuwan Turawan mulkin mallaka zuwa ƙasar Hausa. Turawan sha mamakin abinda suka tarar, kasancewar sun samu al'ummar Hausawa da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauran harkoki na rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare ta Abdoulaye Issa.......
Shirin a wannan makon ya maida hankali ne yadda tsarin shugabanci ya ke a kasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Shirin na wannan mako ya duba irin tasirin masu mulki a ƙasar Hausa kafin zuwan turawan Mulkin mallaka Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani
A yau shirin za ya kai mu Jamhuriyar Nijar, musaman jihar Maradi.A wannan yankin na Maradi a garin Radi, zamu duba batun kirar gargajiya da ke kan hanyar bacewa, bayan a can baya kira, wanzamci, sun kasance sana'o'i biyu da ake alfahari da su a cikin gari. A dauri, makeri baya noma a irin wannan lokaci na damina, sai dai ya yi ta aikin kera kayan noma da gyaransu idan sun lalace, idan kaka ta yi dukan manoma sai su hada masa dammuna hatsi, irin su dawa ko ma wake da zai kula da iyalinsa.
A wanan makon shirin ya mayer da hankali ne kan yadda kabilar Berum da ke jihar Plateau ta tarayyar Najeriya ke gudanar da bukukuwan su na al'ada. Kuna iya latsa alamar sautin domin sauraren cikakken shirin.....
Shirin na wannan mako zai yi duba ne kan Kabilar Gwari da ake samun su a tsakiyar Najeriya. Kabilar Gwari da bahaushe ke kira da "Gwarawa" na da al'adu daban-daban masu ban mamaki da suka sha banban da sauran kabilun mutanen da ke kewaye da su.Domin jin cikakken shirin dannan alamar saurare tare da Abdullahi Isa
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan rayuwar fitaccen mawakin gargajiya na jamhuriyar Nijar Alhaji Ali na Maliki Mawakin haifafffen kauyen Sarkin arewa dake jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar ya kwashe shekaru akalla 80 na rayuwar sa yana taka rawa a fagen na raye-raye da kade-kaden gargajiya.Shirin ya kuma yi waiwaye kan rayuwar mamacin da ya bar yara 23 a duniya, kuma cikin su guda ya gaje shi.Dannna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abduoullaye Issa.
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako, ya je jamhuriyar Benin musaman yankin Wemewe, inda ƙabilar yankin ke shirya wani ƙasaitaccen bikin nuna al'adunsu a duk shekara, wadda ke ƙarfafa danƙon zumunci tsakaninsu da sauren ƙabilu. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ci gaba ne akan na makon daya gabata wanda ya duba muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. inda shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda Jama'a ke koken game da rikon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi, kamar Makon jiya yau ma shirin ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da shugaban kwamitin raya Al'adun Gargajiya na Majalisar dokokin Jihar, Hon. Sarki Aliyu Daneji.Ku latsa alamar sauti don jin yadda shirin ya kasance....
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi.Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata.
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar. Akwai mu dauke da yadda Maroka da kuma Sankira ke fuskantar barazana a sakamakon tsadar rayuwa.Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976, aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha'anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari'ah da kuma batun tara haraji a cikin al'ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al'amura. Amma yayinda gwamnatin Nigeria ke tunanin sake damka wa Sarakuna wannan dama, wasu daga cikin su fara bijiro da sabbin matakai da nufin tsare rayuka da dukiyar al'ummarsu daga ‘yan ta'adda.A baya bayan nan, Mai Martaba Sarkin Ningi a jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad ‘Danyaya, ya samar da wata katafariyar kungiyar tsaro ta ‘yan sa-kai, wacce ke karade sako da lungun yankin don yaki da miyagun iri.
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al'ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al'adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa. Masarautar Katsinar Maradi dai yanzu ta zama madubi kuma abin koyi a bangaren hadin kan al'ummar Nijar.
Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon na musamman ne, wanda ya yi duba akan irin gudunmuwar da marigayi Salissou Hamissou ya bayar a bangaren al'adu, musamman a lokacin da ya ke gabatar da wannan shiri na Al'adunmu na gado. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.....
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda auren Zaga tsakanin al'ummar Sayawa ke komawa tarihi, salon al'adar da ke bayar da damar gadon mace ko kuma bayar da kyautar ta da sunan aure. Duk da tarin kabilun da ake da su a cikin jihohin Najeriya, kowace kabila na da irin nau'o'in al'adunta na gargajiya a fannonin rayuwa dabam dabam.Al'adun kan bambanta ne ta fuskar tsarin zamantakewa, ko ta fuskar auratayya da makamantarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....
Shirin al'adunmu na gado na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda abinci gargajiya irin na Bahaushe ke bata sannu a hankali Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa
Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Issa ya maida hankali ne kan bacewar sanar gargajiya ta rini a jihar Kano dake arewacin Najeriya, kafin daga bisa shirin ya leka Maradi dake jamhuriyar Nijar.
Shirin Al'adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya maida hankali ne kan cika shekara daya da sabon sarkin Katsinar Maradi,Mai Martaba Ahmad Ali Zaki Maremawa yayi kan karagar mulki. A dai ranar Asabar 5 ga watan Nuwambar shekarar da ta gaba ne aka nada Mai Martaba Ali Zaki a matsayin Sultan na 2 na Katsinar Maradi. Shirin ya tabo batun nasarorin da sarkin ya samu a wannan lokaci da yayi yana jagoranci.Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa....
Shirin Al'adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya tabo batun kyautar da matashiya 'yan Farsans ta lashe, inda ta zamo ta daya a duniya a wannan shekarar wajen iya gasa biridi. Tarihi dai ya nuna wannan ne karo na faro da mace ta taba lashe wannan kyauta. Haka nan, shirin ya kuma tattauna da masu ruwa da tsaki a bangaren kan wannan al'amari.Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin al'adunmu na gado na wannan mako ya duba wani babban taron kasa da kasa da aka gudanar kan habbaka harshen Kanuri da al'adunsa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa
Shirin Al'adunmu na wannan mako ya yada zango ne Masarautar Zazzau Suleja ta jihar Neja dake Najeriya domin shaida bikin murnar cika shekaru 30 na Sarkin Masarautar mai dimbin tarihi, Mallam Muhammadu Auwal Ibrahim, wanda ya kasance gwamnan jihar na farko na farar hula a jamhuriya ta biyu daga shekarar alif 979 zuwa alif 983.