POPULARITY
Gwamnan Kano Abba Yusuf ya rattaba hannu a wata doka mai rusa ga baki daya masarautun Kano inda ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa.Bashir Ibrahim Idris dangane da wannan mataki ya tattauna da Abdoulkarim Ibrahim da Nura Ado Suleiman a cikin shirin Duniyar mu a yau daga nan sashen hausa na Rfi.
Najeriya karkashin mai horar da kungiyar Jose Peseiro za ta nemi kare maratabar ta da kuma neman ganin ta tsallaka mataki na gaba a wanan gangami,yayida a daya wajen ,Kamaru a cewar mai horar da ita ,Rigobert Song za su kasance a kan bakar su na ganin su doke Najeriya. A tarihi,haduwar wadanan kungiyoyi Najeriya da Kamaru a shekaru baya suka kasance gagara badau a fagen tamola, Najeriya da Kamru sun hadu sau 22.,Najeriya ta samu nasara a wasanni 11 da ta buga da Kamaru. Yayin da Kamaru ta samu galaba a kan Najeriya sau hudu Kungiyoyin biyu sun yi canjaras sau bakwai. A tarihin lashe kofin gasar Afirka na kwallon kafa baya ga Masar,da ta lashe Kofin sau 7,Kamaru ta daga wannan kofi sau 5 sai Ghana sau 4. A bangaren Najeriya,kungiyar Super Eagles ta lashe kofin sau uku, shekarar 1980,1994 sai 2013..Khamis Saley a cikin wannan shiri na Duniyar wasanni,ya mayar da hankali a gasar.
yanzu haka dai an shiga rana ta 3 da soma gudanar da gasar wasannin kwallon kafar kasar Ingilia (premier Ligue) tare da Khamis Saleh wanda ya tattauna da masu ruwa da tsaki ta fanin kwallon kafa a Igila da Najeriya.
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya duba tarihin tsohon dan wasan tawagar kasar Jamus da ya yi murabus daga buga kwallon kafa a ‘yan kwanakin nan wato Mesut Ozil.
SHIRIN YA TATTAUNA BATUN ALAKAR MUTUM DA ALJANI, WANENE ALJANI? ABINDA KE SA ALJANI YA SHIGA CIKIN MUTUM YA CUTAR DA SHI, HANYOYIN KARIYA DAGA ALJANI, ABINDA AL-KUR'ANI DA SUNNA SUKA CE GAME DA ALJANI DA MUTUM, SOYAYYA KO KIYAYYA TSAKANIN ALJANI DA MUTUM, MASU AIKIN ILAJI DA ALJANU, LABARAN BAKON SHIRIN DA ALJANU, MUN TATTAUNA WADANNAN BATUTUWA NE TARE DA MASANI AKAN DUNIYAR ALJANU SH, DR. AHMAD MUSA ABDULLAHI, TARE DA DR. SANI MOUSSA MAGAWATA MATANKARI MAI GABATARWA.
A karshen wannan mako ake kawo karshen gasar cin kofin duniyar dake gudana a Qatar, inda Faransa zata kara da Argentina a ranar lahadi, yayin da Morocco zata fafata da Crotia gobe asabar domin neman gurbi na 3. Dangane da yadda gasar ta gudana da kuma nasarorin da aka samu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Sakatare Janar na Hukumar Kwallon kafar Najeriya, Hon Sani Ahmed Toro, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Shirin 'Duniyar Wasanni' tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan koma bayan da wasannin Langa ya samu a wasu jihohin arewacin Najeriya, duk da cewa anyi kokarin farfado da shi amma kuma lamarin ya ci tura.
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna kan gasar sukawar dawaki da aka kammala a jamhuriyar Nijar, sai kuma ci gaban hira da Ahmed Mohammed dan gudun hijarar Najeriya da ya shahara a Birtaniya.
Shirin Duniyar wasanni na wannan mako tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan nasarar da kungiyar Real Madrid na kasar Spain ta yi na lashe gasar zakarun Turai ta kakar bana, sai kuma hira da wani tsahon dan gudun hijar Ahmed Mohammed dan asalin jihar Barno a Najeriya da yaje Birtaniya yana karami kuma yake nuna bajinta a harkar kwallon kafa a manyan kungiyoyi da kuma kokarisa na bada agaji.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattaune ne kan gasar Firimiyar Ingila da aka karkare a karshen mako, inda Manchester City ta lashe kambin wannan kaka.
Hukumar kwallon kafar Afrika ta sanar da dage haramci da ta yi na soke wasanni a filin wasa na Olembe biyo bayan mutuwar mutane 8 da aka samu ranar litinin 24 ga watan janairu 2022. Masar ta yi waje da kungiyar Morrocco da ci 2 da 1, wasar da aka bayyana cewa an baiwa hammuta iska tsakanin yan wasan na Masar da Morrocco jim kadan da kammala ta ,bayan da yan wasan suka fice daga fili. Kungiyar kwallon kafar Sanegal ta samu tsallakawa mataki na ga ba ,bayan doke kungiyar kwallon kafar Equatorial Guinee da ci 3 da 1,Sadio Mane da abokanin tafiyar sa za su kara da kungiyar kwallon kafar Burkina Faso ranar laraba. A bangaren kungiyar kwallon kafar Burkia Faso,mai horar da wannan kungiya mai suna Kamou Malo,da samun nasara a faffatawa da kungiyar Tunisia,ya na mai cewa al'amari ne yan kasar ga baki, jajircewa da juriya suka yan wasan ga samun wannan nasara,abin farin ciki ne ga Burkina Faso. Abdurahamane Gambo daga Yaounde ya hada mana shirin Duniyar wasanni.
A cikin wannan shirin na dandalin fasahar Fina-finai,Hawa Kabir ta samun tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar fina-finai dangane da makomar mata musaman a gidajen mazan su,ko wandada ke da niyar yin aure.
Hulumar kwallon kafar Najeriya NFF ta sallami Gernot Rhor mai horar da kungiyar kwallon kafar Super Eagles. Sallamar dake zuwa a wani lokaci da ya kasa kawo sauyi a tafiyar kungiyar ga baki daya. a cikin shirin Abdurahaman Gambo Ahmad ya ji ta bakin ma'abuta kwallon kafa da kuma irin fatan su bayan nadin sabon mai horar da Super Eagles a cikin shirin Duniyar wasanni.
Kungiyar PSG ta sanar da cewar Lionel Messi ya sanya hannu a kwangilar shekaru biyu bayan barin kungiyar Barcelona inda ya kwashe shekaru 21 yana mata wasa.PSG za ta dinga biyan sa Euro milyan 40,Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni ya duba alfanun zuwa Messi PSG da ma irin kalubalen dake gaban sa.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan rana tare da AbduRahman Gambo Ahmad ya tattauna kan rabuwar Barcelona da gwarzon dan wasanta Lionel Messi, bayan shafe shekaru fiye da 20 suna tare.
Mawaka fina-finai a Najeriya na rayuwa ba tareda sun ci moriyar aikin da suke yi ba,banda haka Hawa ta samu tattaunawa da Haro mawakin hausa a Kaduna dake Najeriya. A cikin shirin Duniyar Fina-finai tareda Hawa Kabir,ta samu tattaunwa da wasu dake ruwa da tsaki a Duniyar Fina-finai a Najeriya.Hawa Kabir ta samu
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako ya yi dubi ne da wasannin kwallon kafa na neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da ke gudana a halin yanzu. ya kuma yi nazari a kan babbar tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles da kalubalen da ke gabanta duk da cewa ta samu tikitin zuwa AFCON. Abdurrahman Gambo Ahmad ne ya shirya ya gabatar.
Daga cikin tikitin 24 ko mu ce 23 bayan da Kamaru mai masaukin baki, kasashe 13 ne aka tabbatar da sun samu na su tikiti ga zaman da ake yanzu. Daga cikin bakin da ake da su a wannan ganggami ,za mu iya zana tsibirin Comoros, Gambia, Gabon , Guinee Equatorial, Masar, Tunisia, Senegal ,Zimbabwe ,Ghana ,Burkina Faso , Mali ,Guinee Conakry. A cikin shirin Duniyar wasanni,Abdurahamane Gambo yayi tattaki zuwa Eko Otel,wurin da aka sauke yan wasan Najeriya yan lokuta kafin sun fice zuwa Jamhuriyar Benin,inda za su kara da kungiyar Ecureuils a birnin Porto Novo ranar asabar. A cikin shirin zaku ji ko a ina aka kwana dangane da shirin da yan Najeriya keyi na ganin sun samu nasara a wannan wasa.
A Najeriya,yan wasan Fim da dama ne yanzu ke sa ran ganin sun samu zama tareda kasancewa jarumai a Duniyar Nollywood gida dama wajen kasar. Hawa Kabir ta samu tattaunawa da daya daga cikin yan wasan Fim mai suna Zuwaira,banda haka ta kuma duba wasu daga cikin matsalollin da yan wasan na Fim ke fuskanta a wannan Duniya.
A cikin shirin fina-finai,Hawa Kabir ta samu zantawa da masu shirya Fim a Najeriya,domin jin ko a ina aka kwana dangane da batun shirya fim a kasar,yanayin rayuwar yan Fim a Najeriya. Hama Kabir ta dubo wasu daga cikin labaran da suka shafi Duniyar yan Fim a Indiya a cikin wannan shirin na Dandalin fasahar fina-finai.
A cikin shirin Duniyar wasanni daga nan sashen hausa na Rfi za mu yi tattaki zuwa kasar Kamaru, inda kasashe 16 da suka hada da Kamaru mai masaukin baki, Zimbabwe, Mali ,Burkina Faso, Libya,Nijar, Jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, Morroco, Togo, Rwanda, Uganda, Zambia, Tanzania, Guinea sai Namibia za su fafata a tsakanin su a gasar cin kofin kasashe Afrika na Confederation. Abdoulaye Issa ke farin cikin gabatar muku da shirin na wannan lokaci. Sai ku biyo mu.
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako ya cigaba da yin waiwaye kan muhimman abubuwan da suka faru a duniyar wasanni cikin shekarar 2020.
A cikin shirin Duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da Aishatu Aliyu Kaduna,wacce ta yi bayyani dangane da rayuwarta a fani fina-finai,banda haka ta kuma yi bayyani dangane da irin kalubalen da ta yi fama da su a wannan mataki.
A cikin shirin Duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta mayar da hanakali tareda duba tasirin tufafi a duniyar yan Fim a Najeriya,ta kuma yi amfani da wannan dama don jin ta bakin wasu daga cikin masu shirya fim a Najeriya. Sai ku biyo mu
Hawa Kabir ta jiyo ta bakin masu shirya Fim a Najeriya dangane da wannan matsala da ta shafi yan wasa wanda akasari ke janyo mutuwar tauraro a Duniyar Fim. Dandalin fina-finai na daga cikin hanyoyin da sashen hausa na RFI ke baiwa masu shriya Fim damar nuna ci gaba da ake samu a wannan sashe kama daga gida Najeriya zuwa kasashen ketare.
A cikin shirin Duniyar fina-finai,za ku ji halin da yan fim suka samu kan su bayan mutuwar Sarkin Zazzau kamar yada Hawa Kabir ta samun zantawa da wasu dake ruwa da tsaki a wannan fani. Sai ku biyo mu..
A duk shekara dai ana hada daliban makarantu a Nijar don su fafata a wasannin shekara na dalibai don a fitar da zakaru tsakanin jahohin kasar ta Nijar. Ana shirya wannan kwambala dai ne mafi yawa a watan Maris a dai dai lokacin da dalibai ke zuwa karamin hutu ista ko paques. Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni ya duba halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.
A Jamhuriyar Nijar ,ma'abuta kwallon kafa na ci gaba da kokawa biyo bayan matsalolli da suka dabai-baye Duniyar kwallon kafa musaman a jihar Maradi. A cikin wannan shirin mu samu tattaunawa da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a Duniyar kwallon kafa. Sai ku biyo mu.
Tun bayan shelanta bullar cutar COVID 19 a duniya, hukumomi a Nigeria suka yi ta bijiro da matakai don dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma. Daga cikin matakan da aka dauka har da rufe dukkan makarantun kasar daga matakin firamari zuwa manyan makarantu, matakin da ya yi tasiri kan harakokin wasannin motsa jiki na dalibai a wadanan makarantu. Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni ya duba halin da ake ciki a kasar ta Najeriya.
Bayan share shekaru bakwai,kasar Japan na shirin karbar bakucin wasannin Olympics na shekarar bana,hukumar CIO dake da nauyin shirya wasannin ta sanar da dage gasar zuwa shekara ta 2021 sabili da cutar Coronavirus. Matakin da wasu yan kasar ta Japan suka soma bayyana damuwa,yayinda wasau ke ganin cewa ya dace a dage wannan gangami Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni,ya ji ta baki wasu daga cikin masu ruwa tsaki a Duniyar wasanni kamar dai yada zaku ji.
A Jamhuriyar Nijar ana fuskanatar koma baya a Duniyar sukuwar dawakai a dai dai lokacin da Najeriya ke ta kokarin ganin an samu ci gaba a wannan sashe. Wasu daga cikin jihohin Jamhuriyar Nijar da aka samu koma baya dangane da sukuwar dawakai sun hada da birnin Yameh, Maradi, Zinder. Abdoulaye Issa ya duba mana halin da ake ciki yanzu haka a cikin shirin Duniyar wasanni.
A taron birnin Rabat na kasar Morocco da ya hada hukumar Fifa da ta Caf,Gianni Infantino Shugaban hukumar Fifa ya bukaci hukumar Caf da ta yi nazari tareda dage gasar cin kofin nahiyar Afrika kama daga shekaru biyu zuwa hudu. Shawarar shugaban ta Fifa na zuwa ne a wani lokaci da kwallon kafa a Afrika ke fama da matsalolli. Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni ya duba halin da ake ciki kamar dai yadda za a ji.
A cikin shirin rayuwarka muhalinka ,Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali zuwa rahoto dake nuna cewa nan da yan shekaru mudin ba a dau matakan magance matsalar abinci a Najeriya. A cikin shirin ya samu tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki a Duniyar noma.
Comenzamos con los tres discos favoritos del mes de febrero, a cargo de los polacos de la Janusz Prusinowski Kompania, los franceses de L'Attirail y el escocés con inspiraciones indias Simon Thacker's Svara-Kanti. Continuamos la estela bengalí que nos deja este músico para escuchar más músicas de aquellas tierras y de Vietnam, para terminar con la música y el anuncio de los próximos conciertos de la colombiana Marta Gómez y, dentro del programa del Tradicionàrius barcelonés, de los griegos Mode Plagal. We start with the three monthly favorite albums, by the Polish Janusz Prusinowski Kompania, the French band L'Attirail and the Scottish with Indian inspirations Simon Thacker's Svara-Kanti. we continue in Asia, in Bengal and Vietnam, to end up with the music and the announcement of the upcoming concerts of the Colombian artist Marta Gómez and the Greek band Mode Plagal, this last one in the Tradicionàrius series in Barcelona. Reproductor de audio Favoritos de febrero / February favorites · Janusz Prusinowski Kompania – Dobrzelin / Kujon from Dobrzelin – Po ?ladach / In the footsteps · L'Attirail featuring Sidi Bemol – Aral crawl – How to swim in the desert · Simon Thacker's Svara-Kanti – Bhromor koio giya – Trikala Viaje asiático y conciertos que vienen / Asian trip and upcoming concerts · Arijit Chakraborty [et al.] – Duniyar jamidari [+ Chhote Golam] – Folks of Bengal: Neelaj · Arijit Chakraborty [et al.] – Akasher taraguli [+ Babu Fakir] – Folks of Bengal: Neelaj · Tri Nguyen – Golden skies – The art of the Vietnamese zither · Marta Gómez – El loro y la lora – Coloreando dos · Mode Plagal – Funky vergina – [directo / live] · (L'Attirail featuring Sidi Bemol – Swimming Kazak Association – How to swim in the desert) Imagen: / Image: Janusz Prusinowski Kompania