Madubin Kabara

Follow Madubin Kabara
Share on
Copy link to clipboard

Saurari yadda ni dan jarida Usman Kabara nake tattaunawa da kwararrun 'yan Afirka don jin gwagwarmayar rayuwarsu a gida da kasashen waje. Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

Usman Kabara


    • Aug 6, 2024 LATEST EPISODE
    • infrequent NEW EPISODES
    • 39m AVG DURATION
    • 33 EPISODES


    Search for episodes from Madubin Kabara with a specific topic:

    Latest episodes from Madubin Kabara

    Usman Kabara

    Play Episode Listen Later Aug 6, 2024 2:49


    Shirin da zai dinga yin tsokaci a kan yadda al'amuran yau da kullum da suka shafi rayuwarmu suka samo asali.

    KAMALUDDEEN KABIR: Yadda ya sami karatu a Birtaniya

    Play Episode Listen Later Feb 17, 2023 58:20


    Dakta Kamaluddeen Kabir, dan asalin jigar Katsina ne mai digirin digirgir wanda yayi karatunsa a tsakanin Najeriya da Birtaniya sannan kuma Malami ne yanzu haka a jami'ar Umaru Musa 'YarAdua da ke jihar ta Katsina. --- This episode is sponsored by · Anchor: The easiest way to make a podcast. https://anchor.fm/app --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabara/message

    sami yadda katsina najeriya malami birtaniya
    NA'IMA IDRIS: Ta shiga sahun manyan gobe a Afirka

    Play Episode Listen Later Aug 1, 2022 14:53


    Na'ima Idris Usman, cikakkiyar Likita ce da ke jihar Kanon Najeriya, ta yi karatun a tsakanin Najeriys da China. Ta bamu labarin rayuwarta daga kuruciya zuwa girmanta, da ma yadda aka yi ta fara ilimantar da mata ta kafafen sada zumunta game da lafiyar jikinsu duk da cewa furta kalmomin da ke da alaka da al'aura abu ne mai cike da kalubalen a kasar Hausa. Da kuma yadda karshe ta buge da zuwa shirin horar da shugabanci ga matasan Afirka a Amurka da a turance ake kira da Mandela Washington Fellowship da aka fi sani da Young African Leaders Initiative (YALI) na shekarar 2022. --- This episode is sponsored by · Anchor: The easiest way to make a podcast. https://anchor.fm/app --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarahausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarahausa/support

    china hausa gobe shiga mandela washington fellowship afirka amurka young african leaders initiative yali
    AISHA HASSAN: 'Yar Najeriya da Birtaniya gwanar daurin dan-kwali

    Play Episode Listen Later Aug 1, 2022 31:36


    Aisha Hassan matashiya ce 'yar asalin jihar Neja a Najeriya da ta girma a Ingila, sannan ta yi karatu mai zurfi a fannin hada-hadar kasuwanci. Bugu da kari ba a barta a baya ba wajen shiga fagen kafafen sadarwar zamani inda take koyar da salon sa sutura da daurin dan-kwali a shafukanta na yanar gizo. AISHA HASSAN: 'Yar Najeriya da Birtaniya gwanar daurin dan-kwali --- This episode is sponsored by · Anchor: The easiest way to make a podcast. https://anchor.fm/app --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarahausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarahausa/support

    neja kwali najeriya birtaniya ingila
    SOJABOY: Bahaushen da Amurkawa suka fi sani

    Play Episode Listen Later Jul 25, 2022 36:37


    Usman Umar da aka fi sani da SojaBoy mawaki ne, dan wasan kwaikwayon zahirin rayuwa da ya fito a tauraron wani shirin wasan talbijin a Amurka mai suna 90DayFiance wanda ake bibiyar saurayi da budurwa don ganin yadda alakarsu ta soyayya ke tafiya. --- This episode is sponsored by · Anchor: The easiest way to make a podcast. https://anchor.fm/app --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    suka 90dayfiance sani sojaboy amurka
    Yar Najeriya ta sami lambar yabo a Birtaniya

    Play Episode Listen Later Jul 1, 2022 71:52


    HALIMA ALI SHUWA: An karrama ta da lambar yabon gama digirin digirgir a matsayin dalibar da ta yi wa sa'o'inta fintinkau a fanni binciken sojojin garkuwar jikin bil'adama. Bugu da kari kuma sai ga wani babban kamfanin hada magunguna a duniya ya bata aiki sakamakon fahimtar amfanin abin da ta kware a fannin binciken kwayar halitta. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    sami yabo najeriya birtaniya
    MUAWIYA SAIDU: Masanin tsara birane a Koriya ta Kudu

    Play Episode Listen Later Mar 28, 2022 24:19


    Muawiya Saidu Abdullahi, ya yi karatu ne a fannin zanen gidaje da kuma tsara birane. An haifeshi ne a garin Kaduna, sannan iyayensa Lauyoyi ne. Ya fara digirinsa ne daga jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria, ya kuma kammala a daya daga jami'o'in kasar Malaysia. Yayi digirinsa na biyu da na uku a Korea ta Kudu, inda yanzu haka ya ke aiki a matsayin shugaban bangaren kula da bangaren tsara biranen kasashen waje a wani babban kamfani a kasar ta Koriya ta Kudu mai suna WithWorks da ke birnin Seoul. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/support

    I SHARIF: Dan Najeriya matukin jirgi a Afirka ta Kudu

    Play Episode Listen Later Mar 5, 2022 36:47


    Kaftin Ibrahim Sharif bakano ne dan Najeriya da ya bar gida tun yana dan saurayi zuwa Birtaniya domin aikin sa kai. Inda daga baya ya nausa Afirka ta Kudu inda ya cika burinsa na zama matukin jirgin sama, har ma ya buge da tsere keke a can. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/support

    sharif inda kudu najeriya afirka birtaniya
    NURA ABUBAKAR: Koyar da Hausa ya kai shi Amurka

    Play Episode Listen Later Feb 17, 2022 29:43


    Nura Abubakar dalibi ne da yake digirin digirgir a fannin Turanci da fasahar hotunan finafinan majigi. Matashin ya bayyana yadda jin wani shiri a gidan radiyon Muryar Amurka na VOA ya ba shi kaimin neman zuwa karatu a Amurka, har ya buge da koyar da harshen Hausa tun a digirinsa na biyu a wata jami'a ta Amurka. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarahausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarahausa/support

    MARZUQ UNGOGO - Likitan Dabbobi

    Play Episode Listen Later Jan 16, 2022 38:22


    Marzuq Ungogo wani hazikin matashin likitan dabbobi ne da yake digirin-digirgir a birtaniya, tare da yin binciken a fanni kwayoyin cututtukan dabbobin da kuma gano dalilan da ke hana wasu magungunan dabbobin aiki da ya kamata su yi. Ya bayyana mana tarihin rayuwarsa da ma yadda aka yi yayi digiri na biyu a Turai da ma ci gaba da digirinsa na uku. Ya tabo batun yadda yake ganin noma da kiwo a kasashe kamar Najeriya. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarahausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarahausa/support

    turai najeriya
    IMAN AL-HASSAN - 'Yar Amurka mai son dandana rayuwar Najeriya

    Play Episode Listen Later Dec 31, 2021 22:54


    Karatu ne ya kawo iyayenta 'yan asalin jihohin Kano da Jigawa zuwa Amurka daga a Najeriya, amma kuma kaddarar zama ta kama su har suka hayayyafa. Iman ta fada min yadda take da burin zaman Najeriya duk kuwa da cewa a Amurka aka haifeta ta girma. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarahausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarahausa/support

    iman kano najeriya jigawa amurka
    HADIZA ALIYU GABON: Abinda ke kaita kasashen waje

    Play Episode Listen Later Nov 18, 2021 16:00


    Hadiza Aliyu da aka fi sani da Hadiza Gabon, na daya daga cikin fitattun taurarin fina-finan Hausa mafi shahara. Ta shiga Najeriya a lokacin da bata jin Hausa, amma kuma tana son zama tauraruwar fina-finan Hausa na Kannywood. Yanzu kuma sai gashi mun da cewa tana yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya, ciki har da Amurka inda muka yi wannan hirar da ita. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/support

    gabon hausa waje najeriya amurka yanzu
    MAIMUNA ‘YAR BICHI: Ta yi damarar kafa shagon abincin Najeriya a Amurka

    Play Episode Listen Later Aug 29, 2021 40:50


    Maimuna Sulaiman Bichi da aka fi sani da ‘yar Bichi ko Lolo's Kitchen ‘yar asalin Najeriya ce ta suka dawo Amurka da zama tun tana shekaru 15 da haihuwa. Ta kuduri aniyar bude gidan abincin da zai kware a girke-girke musamman ma irin na gargajiyar Hausawa. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    kitchen lolo kafa najeriya amurka hausawa
    GANAWA: Binta Aliyu Zurmi (Elbynt)

    Play Episode Listen Later Jul 25, 2021 47:54


    Yar jarida ce daga Najeriya mazauniyar kasar Jamus kuma ma'aikaciya a daya daga fitattun gidajen radiyon Hausa da ke kasashen waje. Ku biyo mu don kallo ko sauraron tattaunawar da muka yi da ita game da tarihin rayuwarta a gida da kasahen waje. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/support

    Dakta Ladan

    Play Episode Listen Later Jun 9, 2021 33:46


    Mohammed Ladan, wanda aka fi sani da Dakta Ladan sakamakon wani fitaccen shirin lafiyar wani gidan radiyon Amurka. Masanin kimiyyar hada magunguna ne kuma dan asalin jihar Neja ne da ke Arewacin Najeriya sannan mazaunin Amurka fiye da shekara 40 tun bayan zuwansa karatu. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/kabarashowhausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/kabarashowhausa/support

    Bello Sisqo

    Play Episode Listen Later Jun 4, 2021 40:00


    Bello haifaffen birnin Maiduguri ne amma girman Kano a tarayyar Najeriya wanda ya ci karo da kalubalen rayuwa a dalilin basirarsa ta waka wanda har korarsa daga gidansu aka yi don ya saduda amma maimakon haka sai ma ya tsalleke zuwa Jamus inda a yanzu haka yake da zama a matsayin mai koyar da rawa kuma mawaki. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Aisha Rimi

    Play Episode Listen Later May 13, 2021 18:25


    Aisha Rimi ‘yar kasar Birtaniya ce wacce iyaiyenta ‘yan asalin Arewacin Najeriya ne. Duk da fadawa hatsarin da ya yi sanadiyyar rabata da kafarta daya, to amma hakan bai canza komai a samun nasararta a rayuwa ba. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    duk rimi birtaniya
    Yuauf Al-Hassan

    Play Episode Listen Later May 13, 2021 59:48


    Farfesa Yusuf Al-Hassan dan asalin cikin birnin Kano ne da ya kwashe shekaru yana koyo da koyarwa a tsakanin Najeriya da Amurka game da ilimin fasahar sana’o’in hannu inda har ya taba zama zakaran gasar malaman koyar da sana’o’i ta Amurka. Malamin ya fada mana tarihin rayuwarsa da yadda zai taimaki ‘yan Najeriya ta hanyar kai Kanawa 100 zuwa Amurka. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    kano kanawa najeriya amurka
    Aliyu Mustapha Lawal

    Play Episode Listen Later May 13, 2021 26:17


    Aliyu Mustapha Lawan bahaushe ne dan jihar Kanon Najeriya da ya ke neman lashe gasar kasidar larabci ta duniya mai taken Yariman Sha’irai, wadda ke gudana a birnin Abu Dhabi ta hadaddiyar daular larabawa. Ya tattauna da Madubin Kabara game da rayuwarsa tsakanin Najeriya da Misira da kuma yadda yadda ya shiga gasa ta larabawa. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Abba Zubair Chedi

    Play Episode Listen Later May 13, 2021 41:16


    Farfesa Abba Zubair Chedi na asibitin Mayo Clinic da ke Amurka, dan asalin jihar Kano ne a Najeriya da ya yi kaurin suna a Amurka musamman lokacin da ya shiga binciken yadda za a yi amfani da kwayar halitta ta stem cell a Turance wajen kirkirar maganin da zai iya sabunta halittar sassan jikin bil adama kamar zuciya da huhu ko bargo da makamantansu. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Hauwa Mustapha Babura

    Play Episode Listen Later Feb 25, 2021 30:53


    Hauwa ‘yar asalin garin Babura ce ta jihar Jigawar Najeriya da ta zo Amurka fiye da shekara talatin da suka wuce. Ta fada mana yadda daga daga renon yara don neman na kai ta buge da karatun sanin bunkasar karatu da halayyar kananan yara har ma tana gan da samun digirin-digirgir. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    mustapha amurka
    Saratu Garba Abdullahi

    Play Episode Listen Later Jan 22, 2021 30:00


    Saratu da aka fi sani da Saratityn Baba, ‘yar jihar Jigawa ce da ke Najeriya amma yanzu haka tana digirin-digirgir a wata jami’a da ke Amurka bayan ta gama digirin farko da na biyu a kasar Indiya a fannin aikin jinya da ungozoma da ma bangaren lafiyar mutanen karkara. Shiga cikin hirar don jin irin gwaggwarmayar rayuwarta a kokarin neman ilimi mai zurfi don cika burin mahaifinta. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    abdullahi garba shiga najeriya jigawa amurka
    Murtala Mai

    Play Episode Listen Later Dec 28, 2020 56:11


    Wani likitan yara ne kuma dan Najeriya da ya rikide ya zama kwararren masanin lafiyar al’umma musamman mata da yara, wanda a yanzu haka ma’aikaci ne a wata kungiya mai zaman kanta da ta ke tallafawa harkokin lafiyar iyali a duniya ciki har da kasashen Afirka mai suna Pathfinder International da ke kasar Amurka da kuma rassa a kasashen waje. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    wani najeriya afirka amurka
    Fadji Maina

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 45:45


    Masaniyar kimiyyar kasa da ruwa da doron kasa da ke dauke da digiri tun daga na daya har zuwa na uku, wacce kuma mujallar Forbes ta wallafa sunanta a cikin matasan duniya guda 30 kuma ‘yan kasa da shekaru 30 da suka sami nasara a rayuwa. ‘Yar asalin Jamhuriyar Nijar ce mai tushe daga kabilar Barebarin Najeriya. Yanzu haka ma’aikaciya ce a hukumar sama jannatin Amurka mai suna NASA a takaice. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    forbes nasa yar maina jamhuriyar nijar amurka fadji yanzu
    Sarki Abba Abdulkadir

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 61:07


    A shekarar 1984 a Najeriya an sami wani saurayi dan jihar Kano da a shekarar ya fi kowane dalibi a Najeriya yawan makin cin jarrabawar gama makarantar sakandare ta kasashen Afirka da ake kira da WAEC a takaice. A lokacin gwamnatin jihar Kano ta yi masa alkawarin daukar nauyin karatunsa har ya gama digirin digirgir. Shin yana ina yanzu, sannan an cika masa alkawarin ko a’a? Ku biyomu a cikin shirin Madubin Kabara don jin tattaunawarmu da shi. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    abba ku shin kano sarki najeriya afirka
    Munira Sulaiman Tanimu

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 45:00


    @meemaestee1 Tana daya daga cikin zaratan matasan mata a Arewacin Najeriya da ta ciri tuta a bangaren ilimi, sana’o’i, siyasa, tallafawa ilimin ‘ya’ya mata ‘yan talla. Mun tattauna da ita don jin tarihin rayuwarta da kalubalen da ta fuskanta. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Adamu Hamza Bamalli

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 120:07


    Dan sarautar Zazzau da ya zama kwararren Injiniya a Amurka. Kafin ya kai ga nasara, Adamu ya sha gwagwarmaya a Najeriya a kokarin samun kyakkyawar rayuwa. To sai dai hakan ya zo masa da kalubalen rashin mahaifi tun yana dan karami wanda hakan ce sanadin kakarsu ya raine ahi tare da ‘yan uwansa. Bayan gama sakandare bai sami zuwa jami’a ba saboda wasu dalilai. Daga bisani kuma ya sami sanadin da ya fitar da shi daga Najeriya zuwa Amurka inda a halin yanzu yake zaune a matsayin kwararren Injiniya. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    bayan daga adamu najeriya zazzau amurka
    Imrana Alhaji Buba

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 45:01


    Matashi ne danye daga jihar Yobe wanda har yanzu bai shekara talatin da haihuwa ba sannan ba dan masu kudi ko mulki ba ne, amma ya sami nasararorin rayuwar da har Sarauniyar Ingila sai da ta karrama shi saboda wasu dalilan da matashin ya bayyana a wannan tattaunawa da na yi dashi. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Halima Djimrao

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 60:55


    Tsohuwar ma’aikaciya Muryar Amurka ta yi doguwar hira game da rayuwarta tun daga haihuwa har zuwa girmanta da karatunta da ma yadda aka yi ta sami aiki a Muryar Amurka a birnin Washington DC. Ta fada mana matsayinta game da rayuwar matasa da maganar siyasa da kuma yadda ta ke kallon ‘yan rajin kare ‘yancin mata musamman a kasashen Afirka. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Abubakar Malami

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 30:22


    Ministan shari’a na Najeriya ya ba wa Madubin Kabara tarihin rayuwarsa tun daga kuruciya har zuwa girmansa da yadda aka yi ya zama masanin shari’a har zuwa zama alkali da ma yadda aka yi ya koma cin gashin kansa a matsayinsa na lauya. Har da yadda aka yi ya taka matsayin daraja magi girma a aikin lauya a Najeriya lokacin da yake da karancin shekaru ba kamar yadda aka saba gani tsofaffin lauyoyi na samu ba. Bugu da kari mahaifinsa ma ya babban alkali ne. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    abubakar najeriya
    Sabo Tanimu

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 28:27


    Na ziyarci daya daga cikin kwararrun likitoci a Amurka dan asalin Najeriya da ya kware a fanni hanji da matsarmama da ma cutar daji da ka iya kama cikin bil’adama. Likita Sabo Tanimu kuma ya kai matsayin mataimakin Farfesa a Jami’ar Wisconsin, sannan daya daga daraktocin wani babban asibiti a jihar da yake zaune. Ya bani labarin yadda ya taso a garin Makurdi, har zuwa dawowarsa Amurka. Abin sha’awa kuma a rayuwarsa shine, yadda daukaka bata sa ya manta asalinsa ba wanda hakan ce ta sa ya kafa wata cibiyar inganta rayuwar matasa mai suna Sabo Tanimu Foundation a jihar Benue ta Najeriya. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Haruna Chizo1

    Play Episode Listen Later Dec 7, 2020 44:15


    Matsalar kwarara da kasashen Afirka zuwa Turai ta dade da shiga zuciyar matasan nahiyar, inda wasu ke kai labari wasu kuma ke jikkata har ma da salwantar rayuwa. Matashi Haruna Chizo ya fada mana irin gwagwarmayar da ya sha kafin ya shiga kasar Jamus da a yanzu haka ya ke can tare da matarsa Bajamushiya. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Madubin Kabara

    Play Episode Listen Later Jul 17, 2020 3:01


    Ni Usman Kabara na kirkiro shirin nan ne don in dinga zakulo fitattun mutane musamman ‘yan Arewacin Najeriya da suka yi fice ko nasara a fannoni daban-daban a fadin duniya domin jin irin gwagwarmayar da suke sha kafin kai wa ga gaci, don hakan ya zama jagorar tinkarar rayuwa ga matasanmu. Ku kasance da Madubin Kabara a radiyon tafi da gidanka na ‘podcast’ akan manhajar Apple Podcast da Google Podcast da Spotify da ma duk inda kuke samun podcasts dinku. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support

    Claim Madubin Kabara

    In order to claim this podcast we'll send an email to with a verification link. Simply click the link and you will be able to edit tags, request a refresh, and other features to take control of your podcast page!

    Claim Cancel