Podcasts about ingila

  • 5PODCASTS
  • 27EPISODES
  • 11mAVG DURATION
  • ?INFREQUENT EPISODES
  • Jan 27, 2025LATEST

POPULARITY

20172018201920202021202220232024


Best podcasts about ingila

Latest podcast episodes about ingila

Wasanni
Salah ya shafe tarihin Thierry Henry na yawan jefa kwallo a gasar Firimiya

Wasanni

Play Episode Listen Later Jan 27, 2025 9:59


Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya ziyarci gasar Firimiyar Ingila ne don duba sabon tarihin da ɗan wasan Liverpool Mohammed Salah ya kafa a gasar. Mohammad Salah dai a yanzu ya shafe tarihin Thierry Henry na zura kwallaye 175 a gasar Firimiyar Ingila, bayan da ya jefa kwallo a karawar da suka yi da Ipswich. A yanzu dai Mohammed Salah ne na 7 a jerin ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a raga a babbar gasar ta Ingila.Ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a gasar dai su ne Alan Sheare mai  kwallaye 260 da Harry Kane  213 da Wayne Rooney 208 da Andrew Cole 187  da Sergio Agüero 184 da Frank Lampard 177 sai shi Mohamed Salah 176 ya yinda a yanzu Thierry Henry  mai kwallaye 175 ya koma mataki na 8 a wannan jeri.Ƙu latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........

Wasanni
Yadda aka faro kakar gasar Firimiyar Ingila ta bana

Wasanni

Play Episode Listen Later Oct 14, 2024 9:55


Shirin a wannan makon ya maida hankali ke kan yadda aka faro gasar Firimiyar Ingila, inda akwa yanzu kowace ƙungiya ta samu nasarar buga wasanni 7-7. Tuni gasar ta soma nisa, inda Liverpool take a saman teburi da maki 18, yayinda Arsenal da Manchester City ke biye mata da maki, 17, kowannen su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

Wasanni
Manchester City ta kafa tarihi bayan lashe kofin Firimiyar Ingila karo 4 a jere

Wasanni

Play Episode Listen Later May 20, 2024 10:00


Shirin duniyar wasanni na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda aka kammala gasar Firimiyar Ingila, musamman yadda kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kafa sabon tarihin lashe gasar karo 4 a jere.

Wasanni
Hasashen yadda za ta kaya a gasar Firimiyar Ingila

Wasanni

Play Episode Listen Later Apr 15, 2024 9:59


Shirin a wannan lokaci ya fi karkata akalar ne kan gasar Firimiyar Ingila, wadda ke ci gaba da jan hankali, duk da shawo gangarar da akayi. Yar manuniyar dai tuni ta fada kan kungiyoyin ukun saman tebur, wato Manchester City, Arsenal da Liverpool, lura da yadda suke kan kan kan a yawan maki, abunda ke kara nunawa duniya yadda gasar ta Firimiya ta ke ci gaba da jan zarenta a fagen tamola.Ko da yake a halin yanzu Manchester City ce ta karbe ragamar teburin wannan gasa, bayan rashin nasarar da Arsenal da kuma Liverpool suka samu a nasu wasannin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamsi Saleh.

Wasanni
Shiri na musamman a kan gasar Olympics

Wasanni

Play Episode Listen Later Dec 18, 2023 9:59


A yayin da wakilan kasashen ke kintsawa don zuwa gasar wasannin motsa jiki na Olympic da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa a shekara mai zuwa, shirin 'Duniyar Wasanni', ya kawo tarihin gasar, inda ya yada zango a Najeriya, wadda tawagar kwallon kafarta ta 'Dream Team' ta kasance ta farko a nahiyaar Afrika da ta lashe kofin kwallon kafa a gasar Olympiic a shekarar1996.Shirin ya samu damar tattaaunawa da wasu 'yan wasa da jami'ai da aaka dama da su a lokacin.   TARIHIN GASAR WASANNI TA OLYMPICGasar motsa jiki ta Olympics an fara gudanar da ita ne a karni na 8 a kasar Girka, sai dai daga bisani aka dakatar da ita.Bayan dakatar da gasar na tsawon lokaci, a shekarar 1940, kwamitin shirya gasar Olympics na Duniya IOC ya zabi babban birnin kasar Finland Helsinki don gudanar da gasar, amma sai dai sanadiyar barkewar Yakin Duniya na 2 aka sake dakatar ita.Bayan kawo karshen yakin, a shekara ta 1946, IOC ya yanke shawarar sake farfado da harkar wasannin Olympics na zamani, inda aka fara gudanar da wasannin gasar a shekarar 1948 a birnin London na kasar Ingila, duk  da cewa itama ta kasance kamar sauran kasashen Turai, ta na cikin yanayi na matsi, amma sai da aka sake gina birnin na London don gudanar da gasar wasannin Olympics.Fiye da 'yan wasa dubu 4 ne suka fafata a wasanni 136, sai dai ba a gayyaci kasashen Japan da Jamus ba, yayin da Tarayyar Soviet da aka gayyata ta kaurace wa gasar.Shekaru hudu bayan waccan gasar, birnin Helsinki na kasar Finland ta karbar bakuncin gasar, da aka yi wa lakabi da “gasa ta zamani”.An fara wasanni ne a ranar 19 ga Yuli zuwa 3 ga Agustan 1952, wannan gasa ta Olympics wacce ita ce karo na 15, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar bayan kammala yakin duniya na biyu.‘Yan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra'ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.Duk da cewar wannan gasar ba a farota da kasashen nahiyar Afrika ba, akwai wakilan nahiyar da suka shigo daga baya kuma suka nuna bajinta, musammanma a bangaren wasan kwallon kafa, inda a shekarar 1996 da kuma 2000 kasashen Najeriya da Kamaru suka taka rawar gani wajen lashe gasar.A shekarar 1996 ce Najeriya ta kafa tarihin samun nasarar lashe lambar zinari a bangaren kwallon kafar gasar, lamarin daya kara karfafawa sauran kasashen nahiyar gwiwa.A biyo mu a kashi na gaba don jin tagomashin da nahiyar  Afrika ta samu  a wannan gasa ta olympic.

Wasanni
Yadda aka kaya a gasar cin kofin duniya ta mata 2023

Wasanni

Play Episode Listen Later Aug 21, 2023 9:59


Shirin a wannan makon na musamman ne wanda ya yi duba gameda gasar lashe kofin duniya ta mata da aka kammala.Wannan ne karo na farko da kasashe biyu suka karbi bakuncin gasar lashe kofin duniya ta mata, kuma aka kara yawan kasashen da ke halartar gasar daga kasashe 24 zuwa 32. Kasashen Spain da Ingila ne suka samu nasarar kaiwa wasan karshe, inda kasar Spain ta samu nasarar lashe gasar, kasar Ingila ta kare a mataki na biyu, ita kuma kasar Sweden tazo ta uku, sai kuma kasar Australia daya daga cikin masu masaukin baki ta kare a mataki na hudu. 

Wasanni
Duniyar wasanni na wannan mako zai duba gasar Kwallon kafar kasar Ingila

Wasanni

Play Episode Listen Later Aug 14, 2023 9:58


yanzu haka dai an shiga rana ta 3 da soma gudanar da gasar wasannin kwallon kafar kasar Ingilia (premier Ligue) tare da Khamis Saleh wanda ya tattauna da masu ruwa da tsaki ta fanin kwallon kafa a Igila da Najeriya.

ligue mako duba wannan najeriya duniyar ingila
Wasanni
Muhawara tsakanin Manchester City da United bayan taddo harihin da ta kafa

Wasanni

Play Episode Listen Later Jun 19, 2023 9:58


Shirin 'Duniyar Wasanni' na wanann makon ya maida hankali ne kan bajintar da Manchester City ta nuna a kakar wasan da ta gabata.  Tawagar ta Pep Guadiola ta taka rawar gani a gasar zakarun Turai, musamman idan aka yi la'akarin da manyan kungiyoyin da ke da gogewa a wannan gasa amma bata yi wata wata ba wajen yin waje da kungiyoyi irin su Real Madrid da ke kare kambin da Bayern Munich da dai sauran su. Toh sai dai bayan lashe gasar zakarun Turai da kofunan Frimiyar Ingila da kuma kofin kalubale na FA, sai mahawara ta kaure tsakanin magoya bayan kungiyar Manchester United da Manchester City, wato Manchester birni data kauye kamar yadda magoya bayan wasanni ke fadi.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Khamis Saleh..... 

Wasanni
An kammala wasannin kakar bana a manyan lig din Turai 5

Wasanni

Play Episode Listen Later Jun 5, 2023 10:01


Shirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya yi duba ne kan yadda aka kammala wasannin lig lig din Turai  A farkon wannan watanne aka kammala manyan wasanni musamman a kasashen Ingila da Spain da Jamus da Italiya da kuma Faransa. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....

Wasanni
Manyan kungiyoyin gasar Firimiyar Ingila na fuskantar kalubale a bana

Wasanni

Play Episode Listen Later Feb 20, 2023 9:44


Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako ya tattauna ne da masu ruwa da tsaki kan wasannin kwallon kafa, dangane da koma bayan da wasu daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa ke fuskanta a gasar Firimiyar bana.

Wasanni
Waiwaye kan rawar da Najeriya ta taka a gasar Commonwealth a Birtaniya

Wasanni

Play Episode Listen Later Oct 17, 2022 9:18


Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya tattauna ne akan irin rawar da tawagar 'yan wasan Najeriya ta taka a lokacin gasar guje-guje da tsalle-tsalle na kungiyar kasashe renon kasar Ingila wato Commonwealth da aka gudanar a birnin Birmingham ta kasar Birtania.

birmingham commonwealth taka najeriya birtaniya ingila
Mu Zagaya Duniya
Bitar labaran makon da ya gabata: Mutuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta 2

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Sep 10, 2022 21:11


Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman bisa al'ada kan bibiyi manyan labaran da suka faru a makon da muke shirin ban kwana da shi, inda a wannan karon ya tabo manyan labarai ciki har da mutuwar sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta 2 wadda ta shafe shekaru 70 ta na mulkin gidan sarautar Birtaniya.

bitar duniya birtaniya ingila
Bakonmu a Yau
Isyaku Ibrahim kan yadda Sarauniyar Ingila ta hana a sato Umaru Dikko daga Landan

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Sep 9, 2022 3:49


Yayin da aka fara zaman makoki a Birtaniya sakamamon rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Biyu, mazauna kasashe renon Ingila na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu akan marigayiyar, musamman wadanda suka yi hulda da ita. Alhaji Isyaku Ibrahim, tsohon dan siyasa kuma daya daga cikin dattawan Najeriya, ya shaida wa Bashir Ibrahim Idris mu'amalarsu da ita da kuma yadda ta taka rawa wajen hana gwamnatin Najeriya dauko Umaru Dikko daga London zuwa gida a cikin akwati. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.

ku sato daga yadda umaru landan yayin najeriya birtaniya bashir ibrahim idris ingila
Wasanni
Kungiyoyin da suka haska a wasan farko na sabuwar kakar Firimiyar Ingila

Wasanni

Play Episode Listen Later Aug 8, 2022 9:36


Shirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali kan yadda aka faro gasar Firimiyar Ingila a makon da ya gabata da kuma irin kungiyoyin da suka faro gasar da kafar dama baya ga rawar da sabbin 'yan wasan gasar suka taka. Ayi saurare Lafiya.

suka ayi ingila
Madubin Kabara
AISHA HASSAN: 'Yar Najeriya da Birtaniya gwanar daurin dan-kwali

Madubin Kabara

Play Episode Listen Later Aug 1, 2022 31:36


Aisha Hassan matashiya ce 'yar asalin jihar Neja a Najeriya da ta girma a Ingila, sannan ta yi karatu mai zurfi a fannin hada-hadar kasuwanci. Bugu da kari ba a barta a baya ba wajen shiga fagen kafafen sadarwar zamani inda take koyar da salon sa sutura da daurin dan-kwali a shafukanta na yanar gizo. AISHA HASSAN: 'Yar Najeriya da Birtaniya gwanar daurin dan-kwali --- This episode is sponsored by · Anchor: The easiest way to make a podcast. https://anchor.fm/app --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarahausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarahausa/support

neja kwali najeriya birtaniya ingila
Wasanni
Duniyar Wasanni: Abubuwan mamaki da aka gani a gasar Firimiyar Ingila

Wasanni

Play Episode Listen Later May 23, 2022 10:21


Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattaune ne kan gasar Firimiyar Ingila da aka karkare a karshen mako, inda Manchester City ta lashe kambin wannan kaka.

manchester city gani duniyar ingila
Wasanni
Zakarun Turai: Liverpool da Real Madrid sun kai wasan karshe

Wasanni

Play Episode Listen Later May 9, 2022 10:00


Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako ya duba batun gasar kwallon kafa ta  zakarun nahiyar Turai, wadda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta Spain da Liverpool ta Ingila suka kai matakin wasan karshe, abin da nufin cewa kungiyoyin biyun za su barje gumi a wasan karshe na gasar. Shirin ya tattauna yadda wasannin kusa da karshe suka kaya  tare da sharhi a kan karon battan da za a yi a wasan karshe.

Wasanni
Wasanni - Tasirin sauyin shekar Ronaldo zuwa Manchester United a gasar Firimiyar Ingila

Wasanni

Play Episode Listen Later Sep 3, 2021 10:04


Shirin Duniyar Wasanni tare da Abdullahi Isa ya tattauna ne akan tasirin sauyin shekar Cristiano Ronaldo yayi zuwa Manchester United akan kungiyar da kuma gasar Firimiyar Ingila.

Wasanni
Wasanni - Sharhin masana kan wasannin karshe na gasar kofin Turai da na Amruka

Wasanni

Play Episode Listen Later Jul 12, 2021 10:04


Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya maida da hankali ne kan wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai da kuma nasarar tawagar Italiya kan Ingila, yayin da shirin ya tattauna kan burin Lionel Messi na lashe kofin Copa America na kasar sa Argentina.

Wasanni
Wasanni - Kasashen 4 na shirin fafata wasannin Semi Finals na gasar Euro 2020

Wasanni

Play Episode Listen Later Jul 5, 2021 9:16


Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya tattauna ne kan wasan neman cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020, wadda ta kai matakin kusa da na karshe wato Semi- Finals tsakanin kasashe 4, da suka hada da Ingila, Denmak, Spain da kuma Italiya.

Wasanni
Wasanni - Ahmed Musa ya daga darajar Kano Pillars

Wasanni

Play Episode Listen Later Apr 19, 2021 10:17


Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne kan komawar Ahmed Musa Kano Pillars domin ci gaba da taka leda bayan ya raba gari da Al-Nesry ta Saudiya a cikin watan Oktoban bara. Yau Litinin ne sabon dan wasan ke fara atisaye da Kano Pillars a barikin Bukabu da ke birnin Kano, yayin da masharhanta ke cewa, ya daga darajar kungiyar ta "Masu Gida".  Dan wasan ya shaida wa RFI Hausa cewa, akwai yiwuwar nan kusa ya koma Ingila da taka leda. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

pillars ku kano daga ahmed musa ingila
Mu Zagaya Duniya
Mu Zagaya Duniya - Mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya mutu yana da shekaru 99

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Apr 10, 2021 19:44


A cikin shirin mu zagaya Duniya ,Garba Aliyu Zaria ya mayar da hankali ga fadar Ingila,yan lokuta bayan da sanar da mutuwar Yarima Philip ya na mai shekaru 99 a Duniya. Mutuwarsa  na zuwa ne a yayin da ya rage watanni kalilan a gudanar da bikin cikarsa  shekaru 100 da haihuwa a cikin watan Yuni mai zuwa. Yariman ya auri Sarauniya Elizabeth a shekarar 1947, wato shekaru biyar kafin ta dare kan gadon sarautar Ingila, yayin da  ma’auratan biyu suka kafa tarihin zama masu mulki mafi dadewa kan karaga a tarihin Birtaniya. Ma’auratan biyu na da yara hudu da jikoki takwas da kuma tattaba-kunni 10.

yana duniya mutu yuni birtaniya ingila garba aliyu zaria
Wasanni
Wasanni - Manyan kungiyoyi na fuskantar kalubale a firimiyar bana

Wasanni

Play Episode Listen Later Sep 21, 2020 9:54


Shirin Duniyar Wasanni na makon nan tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne kan kalubalen da manyan kungiyoyin da ke buga gasar firimiyar Ingila ke fuskanta a daidai lokacin da aka fara sabuwar kaka.

bana ingila
Wasanni
Wasanni - Muhimman abubuwan da suka faru a firimiyar bana

Wasanni

Play Episode Listen Later Aug 3, 2020 10:01


Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari kan wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a gasar firimiyar Ingila da aka kammala. Sannan za ku ji fashin bakin masana game da nasarar da Arsenal ta samu ta lashe kofin FA a karo na 14.

Wasanni
Wasanni - Me yasa Dangote ke son sayen Arsenal a maimakon Kano Pillars?

Wasanni

Play Episode Listen Later Jan 27, 2020 9:58


Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi nazari ne game da kudirin Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote na sayen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila. Wasu masharhanta na ganin cewa, bai kamata Attajirin ya karkata hankalinsa kan Arsenal ba, lura da cewa akwai dimbin kungiyoyin kwallon kafa irinsu Kano Pillars a Najeriya da ya kamata ya fara saya. Kuna iya latsa kan hoton labarin domin sauraren cikakken shirin da kuma tsokacin da Dangote ya yi mana.

Al'adun Gargajiya
Al'adun Gargajiya - Mulkin Turawa ya yi tasiri kan al'adun Najeriya

Al'adun Gargajiya

Play Episode Listen Later Oct 1, 2019 10:29


Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Salissou Hamissou da Ibrahim Malam Goje, ya yi nazari ne kan yadda al'ummar Najeriya ta yi watsi da wasu al'adunta bayan zuwan Turawan mulkin mallaka daga kasar Ingila. Wannan shirin na zuwa muku ne a daidai lokacin da Najeriya ke bikin cika shekaru 59 da samun 'yancin kai. Kuna iya latsa hoton labarin domin sauraren cikakken shirin.

gado kuna wannan najeriya gargajiya ingila