POPULARITY
Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bukukuwan Easter, waɗanda ke matsayin tunawa da ranar da aka gicciye Yesu Almasihu da kuma tashinsa bayan kwanaki uku. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Reverand Andrew Dayyu, wanda ya yi masa ƙarin bayani a game da abin da ake nufi da Easter da kuma muhimmancinta ga mabiyar addinin Kirista. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawarsu.............
Yanzu haka saura watanni 2 kafin cikar wa'adin shekara guda da ECOWAS ta gindaya domin duk wani mai shirin fita daga cikin ta, sakamakon shelar da Jamhuriyar Nijar da ƙawayenta Mali da Burkina Faso suka yi na janyewa daga cikin ta. Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ke nuna janye matakin, ya yin da aka tabbatar da cewar har yanzu wakilan Nijar na aiki a hukumomin na ECOWAS. Domin duba wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon ministan ayyuka na musamman a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu........
Yanzu haka al'ummar musulmi a sassan duniya na ci gaba da gudanar da bukukuwan Mauludi, domin tunawa da ranar da aka haifi annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah. Shin ko yaya matsayin wannan rana yake a gare ku?Ta wace fuska ku ke gudanar da bikin tunawa da wannan ranar?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Shirin a wannan mako ya duba yadda tsarin jagoranci da bada shawarwari a makarantu, tsarin da ke taimakawa dalibai zabar irin fannin da suke son kwarewa akai, inda sun kai matakin jami'a da sauransu. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara
Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan yadda har yanzu wasu daga cikin al'ummar Najeriya basa amfani da tsarin inshorar lafiya. A shekarar 2022 ne gwamnatin kasar ta sake dawo da dokar inshorar lafiya da aka samar tun 1999, a wani yunƙuri na sauƙaƙawa Jama'a samun kulawar lafiya cikin rahusa, lura da yadda kaso mai yawa na al'ummar ƙasar ke rasa kudaden iya kai kansu ga likitoci ko da suna cikin matsananciyar cuta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......
'Yan Najeriya na ci gaba da tafka mahawara a kan dakatar da auran wasu marayu 100 da ministar kula da harkokin matan kasar ta bukata a Jihar Neja, saboda abinda ta kira sabawa dokar kare hakkokin yara.Yanzu haka kungiyoyi daban daban sun ruga kotu domin kalubalantar ministar.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da lauya kuma tsohon 'dan majalisar tarayya, Hon Samaila Muhammed, wanda yace dokar da ake magana a kai ta sabawa dokokin kasa.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren hirar.
Yanzu haka damina ta fara sauka a wasu sassan arewacin Najeriya, yayin da manoma ke shirin tinkarar aikin gona gadan gadan domin magance matsalar karancin abincin da kuma tsadar shi da aka fuskanta. Dangane da shirye shiryen noman, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara a kan aikin noma. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu..........
Shirin duniyar wasanni na wannan mako ya dubi yadda ake tufka da warwarwa game da tsarin samar da cikakken tsaro yayin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh
Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci. Yanzu haka farashin litar man ya haura naira dubu biyu a wasu sassan Najeriyar, yayin da ake samun dogayen layuka a manyan birane irin su Lagos da Abuja da Kano.Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da farfesa Kelani Muhammed, kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron hirar da suka yi.
A wannan makon shirin Kasuwa akai miki dole, zai yi duba ne game da bakar ukubar da al'ummar kasashen Nahiyar Africa ke fuskanta, a sanadiyar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, musamman kasashen Nijeriya, Nijar da kuma Cameroon. Yanzu haka dai a iya cewa wannan yanayi na hauhawar farashin kayan masarufi tuni ya zame wa kasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da kuma Cameroon Dan zani a kasuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa.....
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi nazari ne kan komawar dan wasan gaba na kungiyar PSG, Kylian Mbappe kungiyar Real Madrid a karshen kakar bana. Yanzu dai za a iya cewa an yi ta, ta kare bayan da a ranar 13 ga wannan watan ne dan wasan mai shekara 25 ya sanar da kungiyarsa PSG batun sauya shekarar tasa da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kakar watan Yuni. Kungiyar Real Madrid dai tayi suna wajen dauko manyan ‘yan wasan da tauraruwarsu ke haskawa a fagen kwallon kafa a duniya, ba tare da la'akari da tsadarsu ba.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan lokacin yayi nazari ne akan wasannin matakin dab da na kusa da na karshe wato na zagayen Kwata final da aka yi a gasar AFCON. Yanzu haka dai kasashe hudu ne suka rage a gasar ta cin kofin kasashen nahiyar Afirka da kasar Ivory Coast ke karbar bakunci, bayan wasannin da aka fafata a ranakun Juma'a da Asabar.
Kusan watanni biyu kenan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ci gaba da bai wa ‘yan kasuwa da ke shigar da wasu kayayyaki fiye da 40 a cikin kasar damar samun dala cikin sauki daga babban bankin kasar, amma har yanzu bincike na nuni da cewa ba a fara aiwatar da umurnin ba. To sai dai a daya bangare an wayi gari da karin kudaden da ‘yan kasuwa ke biya a matsayin fito ko kuma harajin shigar da kaya a kasar ne saboda an bari kasuwa ta aikinta a fagen canjin Naira zuwa kudaden ketare.Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Zubairu Mele Abba-Ganamma, daya daga cikin shugabannin kungiyar masu aikin fito wato 'Transit Agents', wanda ya yi mana karin bayani a game da hakan.
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne da tsarin karatun 'yayan makiyaya, wato Nomadic Education. Gwamnatin jihar Neja ce ta yi hobbasa don farfado da shirin karatun 'yayan makiyaya a jihar. Shirin zai bai wa makiyaya damar samun ilimi a duk inda suka yi balaguro don inganta makomarsu. Yanzu haka dai shirye-shirye sun yyi nisa a game dfdaa wannan shirin a jihar Neja mai fara da matsalar tsaro sakamakon ayyukan 'yan bindiga da ke kashe mutane da satar su don kudin fansa.
‘Yan bindiga sun sace sama da mutane 100 a wani hari da suka kaddamar kan al'ummar Mutunji da ke Karamar Hukumar Maru a jihar Zamfara ta Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan mazauna yankin sun gaza biyan kudin harajin da ya kai Naira miliyan 50 da ‘yan bindigar suka lafta musu cikin mako guda. Yanzu haka gwamnatin da ta shude da kuma mai ci na zargin juna da gazawa wajen shawo kan matsalar ‘yan bindigar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Yanzu haka wakilan kasashe 175 na Nairobi dake kasar Kenya, inda suke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a kan yadda za'a magance matsalar sharar robobi da suka addabi bil Adama wajen toshe magudanan ruwa da mamaye tafkuna da teku tare da yiwa jama'a da dabbobi illa. Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin manyan kasashen dake sarrafa robobin da wadanda ke shan radadin matsalar. Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar muhalli, Malam Marwan Yakasai, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Yanzu haka wakilan daga kasashen duniya sun fara taro game da yadda za a samar da yarjejeniyar da za ta taimaka wajen rage amfani da ledoji da kuma robobi a duniya. Yanzu haka dai milyoyin tontonnai na ledoji ne ke ci gaba da cunkoshewa a cikin tekuna, kuma suke matsayin barazanar ga halittun da ke rayuwa a teku, da dabbobi da kuma bil'adama. Shin ko kuna da masaniya a game da irin illolin da ledoji ke haifar wa muhalli da kuma sauran halittu? Wadannan irin matakai ku ke fatan ganin kasashen duniya sun dauka domin ragewa ko kuma hana amfani da leda a duniya?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a kan wannan maudu'in.
A Jamhuriyar Nijar, yau 26 ga watan Okotba, watanni 3 kenan da sojoji suka kifar da gwamnatin dimokuradiyyar da ke karkashin jagorancin Mohamed Bazoum, lamarin da ya sa kungiyar ECOWAS da kuma UEMOA suka kakaba wa kasar takunkumai da dama. Yanzu haka dai wannan lamari ya jefa al'ummar kasar a cikin hali na kunci saboda rashin kudi da kuma rashin kayayyakin masarufi. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ambasada Abubakar Cika, domin jin yadda yake kallon wannan rikici da kuma halin da Nijar ke ciki saboda wannan juyin mulki.
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon zai duba tarin nasarorin da Dan wasan Tennis Novak Djokovic ya samu a gasar a fadin Duniya, inda a kwanan nan ya kafa wani gagarumin tarihi a gasar Grand slam. Yanzu haka dai Dan kasar ta Serbia wato Djokovic ya kafa tarihin lashe gasar Grand slam har sau 24, bayan lashe gasar US Open a baya bayan nan. Wannan nasara tasa dai yanzu ya kamo tarihin fitacciyar Yar Tennis din nan wato Magreth Court ta lashe gasar har karo 24. Shirin ya tattauna da masana.
Majalisar Dinkin Duniya ta amince da matakin janye dakarunta dubu 13 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali bayan da gwamnatin sojin kasar ta yi matsin lamba don ganin an kawo karshen ayyunkan rundunar ta MINUSMA da ta shafe shekaru 10 a kasar. Yanzu haka gwamnatin Mali ta kulla alaka da sojojin haya na Wagner daga Rasha domin samar da tsaro a kasar. To ko mece ce makomar tsaro a kasashen yankin Sahel bayan kawo karshen aikin rundunar a Mali? tambayar kenan da Abdurrahman Gambo Ahmad ya fara yi wa Dr. Yahuza Getso, mai sharhi kan lamurran tsaro a Sahel.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu...
Yanzu haka maniyata aikin Hajjin bana daga sassan duniya sun isa Makkah da Madina, inda suke shirin fara aikin Ibadar ta wannan shekara, yayin da rahotanni ken una cewar akalla mutane sama da miliyan 3 ake saran su gudanar da aikin Hajjin bana. Dangane da matsayin aikin Hajjin a addinin Islama, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulkadir Suleiman Muhammed na Jami'ar Abuja, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. A latsa alamar sauti don jin tattaunawar ta su.......
Yanzu haka shugabannin kasashen duniya sama da 50 da shugabannin hukumomin kasa da kasa daban-daban, da kungiyoyi masu zaman kansu, sun hallara a birnin Paris na Faransa, domin tattauna yau Alhamis da ake fara taron duniya don shimfida tsarin da zai bai wa kasashen damar samun tallafi da nufin tunkarar matsalar sauyin yanayi. Wannan taro na zuwa ne a daidai lokacin da kasashe da dama ke fama da zaizaiyar kasa, fari, ambaliya yayin da teku ke yi wa wasu birane barazana. Me ku ke fatan taron ya yi don tunkarar wadannan matsaloli? Me za ku ce a game da rawar da rawar da gwamnatocin kasashenku ke takawa domin tunkarar wannan kalubale? Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Salissou Hamissou.
Yanzu haka sabuwar gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta kaddamar da aikin rusa shaguna, ofisoshi, gidaje da kuma otel-otel, wadanda ta ce tsohuwar gwamnatin Umar Ganduje ce ta sayar wa jama'a su ba a kan ka'ida ba. A cewar sabon gwamna Kano Abba Kabir Yusuf, an yi wadannan gine-gine ne akan filaye mallakin gwamnatin jihar, yayin da su kuma jama'a ke cewa sun saya ne a kan ka'ida daga gwamnatin da ta gabata. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Muhammad Salissou Hamissou ya gabatar.
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida da hankali ne kan karancin tsabar kudi a hannun ‘yan Najeriya sakamakon wa'adin daina amfani da wasu takardun kudin kasar Naira da babban bankin kasar CBN ya sauyawa fasali, lamarin da yasa wasu yankunan kan iyakokin kasar suka fara amfani da takardun kudin CFA. Yanzu haka wasu yankunan Najeriya da sukayi iyaka da jamhuriyar Nijar da Kamaru da Benin sun karfafa amfani da takardun kudin CFA, saboda karancin Naira.Mazauna wadanan yankuna irin Sokoto da Zamfara da Lagos da Kwara da Adamawa da Taraba da Cross River da dai sauransu suka ce suna hada-hada da kudin CFA ne saboda rashin tabbas da Naira ya shiga.Yayin da a wasu yankuna ma aka fara amfani da tsarin bani gishiri in baka manda.
Kusan makonni biyu da fara amfani da sabbin kudade a Najeriya, amma yanzu haka tsoffin kudade ne ke ci gaba da yawo a hannayen jama'a hatta a cikin bankuna da kuma wuraren cire kudi da ake kira ATM. Wannan dai na faruwa ne duk da cewa tuni babban bankin kasar wato CBN ya kayyade lokacin da za a daina amfani da tsoffin kudin. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Kasimu Garba Kurfi na kamfanin APT Securities and Funds Limited da ke hada-hadar kudade a birnin Lagos. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Yanzu haka ana iya cewa manyan kasashen duniya da suka hada da Amurka, China da kuma Rasha na ci gaba da gogayya da juna domin samun karin karbuwa a nahiyar Afirka. Yayin da Amurka ke kokarin tallata manufofinta na kasuwanci, tsaro, dimokuradiyya da kuma kare hakkokin bil'adam, Rasha da China kuwa na batun fadada kasuwanci ne ko kuma taimaka wa Afirka a fannin tsaro. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Hauwa Muhammad.
Shirin na yau ya duba halin da ajizuwan da dalibai ke daukar darasi a Nijar ke ciki, da kuma shirin gwamnati na gina ingantattun ajizuwa a wadannan makarantu. Kamar yadda watakkila aka sani, an sha samun matsaloli na tashin gobara a wasu makarantun yara a Nijar, musamman a jihohin Maradi da Damagaram sabod yadda ake gina aajizuwan kara da ke saurin konewa. Yanzu gwamnati ta yunkuru ddo warware. matsalar.
Kakakin majalisar dokokin jihar Borno da ke Najeriya Hon Abdulkarim Lawan, ya ce har mayakan Boko Haram ne ke iko da kananan hukumomi biyu na jihar Guzamala da kuma Kukawa. A zantarwarsa da wakilinmu a Maiduguri Bilyamin Yusuf, Hon Abdulkarim Lawan ya roki gwamnati da kuma rundunar sojin kasar, da su dauki matakan da suka wajaba don samar da tsaro a wadannan yankuna, wanda a cewar sa ta haka ne kawai jama'a za su iya komawa garuruwansu.
Har yanzu shirin 'Duniyar Wasannin' na kasar Qatar, inda ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya. Gasar taa bada mamaki ainun, duba da yadda akasarin kasashen da ake ganin za su kai baanteensu a gasar suka gaza taka rawar gaban hantsi. Yanzu haka gasar ta shiga mako na karshe, bayan da aka samu kasashen da za su fafata a matakin kusa da karshe. A ranar Lahadi ce za a buga wasan karshe na wannan gasa a tsakanin wadanda suka yi nasara a matakin kusa da karshe.
Morocco ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin wasan daf da kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar, bayan doke doke Spain da ci 3-1 a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan da suka tashi caanjaras. Yanzu haka Morocco ce kasa daya tilo da ta rage a cikin kasashen Afrika 5 da suka wakilci nahiyar. A kan wanna ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da coach Garba Lawal, tsohon dan wasan Najeriya.
Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da gasar kwallon kafan neman kofin duniya a Qatarm, inda ake samun sakamako da ke bayar da mamaki. Duk da cewa wasu kasashen duniya sun yi suka a game da bai wa Qatar damar daukar nauyin shirya wannan gasa, amma kwo yanzu ana ci gaba da buga wasanni ba tare da wata tangarda ba. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
Yanzu haka darajar takardar kudin Najeriya wato Naira na ci gaba da faduwar warwas a kasuwannin canji, matsalar da ta kara ta'azzara daga lokacin da babban bankin kasar ya sanar da shirin samar da sabbin kudade daga ranar 15 ga watan disamba mai zuwa. Wasu dai na ganin cewa takaitaccen lokacin da CBN ta sanar domin maye gurbin tsoffin kudaden da sabbin da za a buge, shi ne ya kara haifarwa Naira rashin kima a kasuwa. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
Yanzu haka matsalar karancin man fetur da kuma dangoginsa ta same dawowa a Najeriya, inda ake ci gaba da samun dogayen layuka a kalilan daga cikin gidajen da suka mallaki makamashin. Yayin da a Lagos farashin lita daya ta man fetur ta kai naira 200, a wasu yankuna kuwa ana sayar da ita ne fiye da hakan. Shiga alamar sauti domin sauraron Hauwa Muhammad cikin shirin.
Yanzu haka dai baraka tsakanin kamfanin Dangote da gwamnatin jihar Kogi da ke tarayyar Najeriya na ci gaba da kamari sakamakon umarnin da gwamnan jihar Yahaya Bello na rufe kamfanin siminti na Obajana a cikin sa'o'i 48. Dangane da wannan dambarwa ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ahmed Umar Bolori, mashawarcin gwamnan na jihar Kogi. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Masana a duniya sun danganta yawan ruwan saman da ake samu wanda ke haifar da ambaliya ga sauyin yanayin da ake fuskanta. Yanzu haka kasashen duniya da dama na fama da matsalar ambaliya saboda yawan ruwan saman da ake samu, cikin su harda kasashen dake Afirka ta Yamma. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin sauyin yanayi, Malam Nazifi Alaramma dake Jami'ar Jihar Kano. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
YANZU NE LOKOCINDA YA KAMAT MU FALKA DAGA BARCITHE TIME TO BELIEVE IN THE SAVING GRACE OF GOD IS NOW. LOKOCIN BA DA GASKIYA AKAN CETON YESU YANZU NE
YANZU NE LOKOCINDA YA KAMAT MU FALKA DAGA BARCITHE TIME TO BELIEVE IN THE SAVING GRACE OF GOD IS NOW. LOKOCIN BA DA GASKIYA AKAN CETON YESU YANZU NE
Yanzu haka lauyoyin Najeriya na gudanar da taron su na shekara shekara a birnin Lagos, inda su ke tattauna batutuwan da suka shafi ayyukan su da kuma halin da kasa ke ciki, domin bada shawarwari akan matakan da ya dace a dauka, taron da ke zuwa a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar zabe mai zuwa. Dangane da taron, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barr Solomon Dalung, tsohon ministan wasannin kasar, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Yanzu haka ministocin kula da lafiya na kasashen Afirka 55 na halartar wani taro a Lome dake kasar Togo, domin tattauna batutuwan da suka shafi kula da lafiya a kasashen su. Daga cikin masu halartar taron, harda ministocin kasashen Nijar da Najeriya. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ministan lafiyar Jamhuriyar Nijar, Drakta Ilyasu Idi Mainasara. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh na wannan makon ya tattauna ne game da wasan damben gargajiya a Najeriya da nahiyar Afrika, inda a yanzu matasa suka rungumi harkar gadan-gadan a yanzu domin neman kudi.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saleh ya tattauna ne kan koma-bayan da Kano Pillars da Katsina United suka samu a gasar firimiyar Najeriya. Yanzu haka kungiyoyin na Kano Pillars da Katsina United suka koma ajin gajiyayyu.
Yanzu haka takaddama ta kaure tsakanin babban bankin Najeriya da Kamfanin man NNPC dangane da ajiyar sama da Dala biliyan 2 da rabi da kamfanin man yace yayi a lalitar sa dake bankin, yayin da bankin yace babu wadannan kudade. Tuni wannan dambarwa ta haifar da cece kuce a ciki da wajen Najeriya. A kan wannan Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Injiniya Kelaini Mohammed akan yadda wannan dambarwa ke iya shafar bangarorin biyu, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Yanzu haka mahawara ta kaure a Najeriya dangane da dokar zabe wadda ta ce ana iya sauya ‘Yan takarar da aka gabatarwa Hukuma idan bukatar haka ta taso. Yayin da masana shari'a ke cewa akwai wannan tanadi a kundin zaben, kwamishinan zabe Festus Okoye ya ce babu wani hurumi na gabatar da suna da niyyar sauya shi a ka'idodin su. Dangane da wannan matsayi Bashir Ibrahim Idris ya tintibi masanin shari'a Barr Abdullahi Jalo, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Yanzu haka dai shugaban kasar Senegal Macky Sall, wanda kuma shine shugaban kungiyar tarayyar Afrika na ziyara a kasar Rasha, inda a Juma'a ya gana da shugaba Vladimir Putin, a wannan yanayi da duniya ke fuskantar barazanar karancin abinci, sanadiyar yakin na Ukraine, don ya shawo kan Putin ya taimakawa Afrika da Alkama. Toh domin sanin ko ziyarar za ta yi tasiri, Farfesa Usman Muhamad na jami'ar Baze dake Abujan Najeriya ya yi mana tsokaci
YANZU NE LOKOCINDA YA KAMAT MU FALKA DAGA BARCITHE TIME TO BELIEVE IN THE SAVING GRACE OF GOD IS NOW. LOKOCIN BA DA GASKIYA AKAN CETON YESU YANZU NE
YANZU NE LOKOCINDA YA KAMAT MU FALKA DAGA BARCITHE TIME TO BELIEVE IN THE SAVING GRACE OF GOD IS NOW. LOKOCIN BA DA GASKIYA AKAN CETON YESU YANZU NE
Shirin na yau zai tattauna da Dakta Yusuf Ibrahim daga Belgium, kan har yanzu da sauran 'Yan Nijeriya a Ukraine. Haka nan akwai sharhin manyan labarun da Jaridar LEADERSHIP ta yau Litinin 28/3/2022 ta wallafa. Akwai Kuma Labarun Wasanni da ɗimi-ɗiminsu.
Yanzu haka kasashen yammacin duniya sun kaddamar da shirin takaita amfani da Man fetur da kuma gawayi domin rage gurbata muhalli yayin da suke rungumar sabbin dabarun samar da makashi domin dogaro da kai. Wannan ya sa wasu kasashe dake da wannan albarkantun kasa suka kira wani taro a jamhuriyar Nijar domin daukar matakan baidayya kan wannan mataki.
A cikin shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako, Adurrahman Gambo Ahmad ya duba batun kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa ta duniya ta Balon d'Or da dan wasan PSG Lionel Messi ya lashe kwanan nan, inda wasu masu sharhi ke ganin ta rasa tagomashinta.
Yanzu haka ana ci gaba da shiryes-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 24 ga wannan wata na disamba a Libya. To sai dai masu lura da lamurran da ke faruwa a kasar, na ganin cewa abu ne mai wuya a iya gudanar da wannan zabe a cikin kyakkyawan yanayi, lura da cewa har yanzu akwai dubban sojin haya da ke ci gaba da rike makamai a kasar. Kan hakan Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Hammi Souleyman, wani tsohon jami'in diflomasiyyar Nijar a birnin Tripoli, ga kuma zantawarsu.
BUKATA NA YANZU YANZU TA JEFA MUTANE DA YAWA CIKIN HALLAKA
BUKATA NA YANZU YANZU TA JEFA MUTANE DA YAWA CIKIN HALLAKA
Hadiza Aliyu da aka fi sani da Hadiza Gabon, na daya daga cikin fitattun taurarin fina-finan Hausa mafi shahara. Ta shiga Najeriya a lokacin da bata jin Hausa, amma kuma tana son zama tauraruwar fina-finan Hausa na Kannywood. Yanzu kuma sai gashi mun da cewa tana yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya, ciki har da Amurka inda muka yi wannan hirar da ita. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/message Support this podcast: https://anchor.fm/usmankabarashowhausa/support
Yanzu haka dimbin motocin sufuri da dama ne dauke da kaya suka tsaya cak a kan titunan Jamhuriyar Nijar, yayin da wasu suka makale a tashar jiragen ruwan Cotonou, sakamakon wani sabani da ya kunno kai tsakanin masu motocin sufuri na kasar da kuma wadanda aka bai wa kwangilar sufurin bututun man fetur da China ke shirin shimfidawa daga Nijar zuwa Jamhuriyar Benin. A kan wannan batu ne, AbdoulKarim Ibrahim Shikal ya tattauna da Alhaji Hima Barkire, daya daga cikin shugannin kungiyar masu motocin dakon kaya a jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sautin domin sauraren cikakkiyar hirar
Hukumar UNICEF ta yi gargadi kan karuwar hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a Najeriya suna kwashe dalibai a makarantu suna garkuwa da su. Yanzu haka dalibai 386 ke hannun 'yan bindiga daban daban suna garkuwa da su domin neman diyya. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar tsaro Dr. Yahuza Getso. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
Dan takar kujerar shugaban kasa a zaben daya gudana a Jamhuriyar Nijar Mahamane Ousmane na jam'iyyar RDR-Canji, ya shigar da kara gaban kotun ECOWAS bisa rashin amincewa da sakamakon zaben da aka sanar da Mohamed Bazoum na jam'iyyar PNDS -Tarayya a matsayin wanda ya lashe. Wakilinmu a Abuja Muhd Sani Abubakar ya samu tattaunawa da Lauyan Mahamane Ousmane, Maitre Lirwana Abdourahamane jim kadan bayan shigar da karar da suka yi.
A yau Laraba 20 ga watan Mayu ne al’ummar kasar Kamar uke bukukuwan cika shekaru 49 da hadewar yankin dake Magana da harshen Turancin Ingilishi da bangaren Faransanci. Yanzu haka shekaru 3 kenan yankin da ake Magana da Turancin Ingilishi ke fafutukan ballewa daga wancan hadewa. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Uba Ali dake Younde mai sharhi dangane da siyasar Kamaru ko yaya yake kallon wannan yunkuri.
Yanzu haka hanya ta bude wa tsohuwar ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo Iweala na zama mace ta farko, kuma ‘yar Afirka ta farko da za ta zama shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya wato WTO, bayan da sabon shugaban Amurka Joe Biden ya mara mata baya, yayin da kuma a gefe guda ministar kasuwancin Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee da ke fafatawa da ita, ta janye takarar ta. MICHAEL KUDUSON tattauna da masanin tattalin arziki daga jami’ar jihar Bauchi ta Kashere, Dokta Isa Abdullahi, ga kuma tattaunawarsu.
Yanzu haka tawagar Sheikh Dr Ahmad Gumi ta kammala ziyarar jihar Zamfara dake Najeriya, inda ta gana da shugabannin Fulanin dake dauke da makamai, da zummar ganin sun aje makaman nasu tare da rungumar zaman lafiya. Bayan kamala ziyarar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Usman Yusuf, tsohon shugaban Hukumar Inshoran Lafiya ta kasa dake cikin tawagar.
Sana'o'in dpgaro da kai na da matukar muhimmanci a tsakanin al'umma musamman ma matasa. Yanzu a nahiyar Afirka, matasan kan rungumi sana'o'in domin su dogara da kansu.
Yayainda da ake cigaba da dakon ceto tarin daliban da 'yan bindiga suka sace a makarantar Sakandaren Kankara da ke Jihar Katsina, wasu mutane na bayyana tababa dangane da yaran da suka bata, duk da ya ke Gwamnan Jihar ya ce suna neman dalibai 333. Yanzu haka wasu iyayen yara na can sun yi dafifi a makarantar suna jiran alkawarin da ministan tsaro ya yi cewar nan bada dadewa ba za’a kubutar da su. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani da aka sace kaninsa, kuma yanzu haka suna can suna zaman dirshe a Kankara Malam Mustapha Masaudu, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Masaniyar kimiyyar kasa da ruwa da doron kasa da ke dauke da digiri tun daga na daya har zuwa na uku, wacce kuma mujallar Forbes ta wallafa sunanta a cikin matasan duniya guda 30 kuma ‘yan kasa da shekaru 30 da suka sami nasara a rayuwa. ‘Yar asalin Jamhuriyar Nijar ce mai tushe daga kabilar Barebarin Najeriya. Yanzu haka ma’aikaciya ce a hukumar sama jannatin Amurka mai suna NASA a takaice. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/madubinkabara/message Support this podcast: https://anchor.fm/madubinkabara/support
Yanzu haka Amurkawa na dokon sakamakon zaben shugaban kasa da aka kammala kada kuri’u, inda rahotanni ke nuna cewa yanzu haka shugaban kasa mai ci Donald Trump da abokin Hamayyarsa Joe Biden na tafiya kankankan. Dangane da wannan sakamako Ahmad Abba ya tattauna da Adamu Mohammed, wani mazaunin North Carolina na kasar, ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.
Yanzu haka 'yan bindiga a Jihar Nasarawa da ke Najeriya sun yi garkuwa da wasu mutane 17 da suka kama a cikin wani Masallachi da ke kauyen Kwambe a kusa da Gadabuke lokacin da suke Sallar Isha. 'Yan bindigar na neman biyansu diyyar naira miliyan 17 diyya kafin sakin mutanen wadanda suka kwashe kwanaki 9 a hannun su. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mazaunin yankin Malam Iro Danfulani, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
A karon farko cikin shekaru 25, PSG ta Faransa ta samu gurbi a matakin wasan dab da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai bayan ta doke Atalanta da kwallaye 2-1a karawar da suka yi jiya a Lisbon. Yanzu haka PSG za ta hadu da RB Leipzig a ranar Talata mai zuwa a matakin wasan dab da na karshe na gasar. A cikin shirin za mu duba halin da ake cikin dangane da dambarwar da ta kuno kai a Jihar Maradi.
Bayani kan yadda korona ke yaduwa a wannan lokaci
Yanzu haka wata takaddama ta kaure tsakanin Hukumar raba wasiku a Najeriya da Hukumar tara kudaden haraji kan wanda yake da hurumin karbar harajin kan Sarki ko kuma ‘Stamp Duty’ da ake kira a turance. Hukumar tara kudaden haraji tace ita take da hurumi, yayin da Hukumar tara haraji tace ita doka ya baiwa hurumi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Dauda Muhammad Kontagora masanin tattalin arziki, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Yunkurin Sasanta rikicin Libya na cigaba da fuskantar zagon kasa daga kasashen dake goyan bayan bangarorin dake rikicin wanda ya kwashe dogon lokaci ana cigab da zubda jini akai. Janar Khalifa Haftar da ya sha alwashin kifar da gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ke goyawa baya na samun taimakon wasu kasashe, yayin da ita ma gwamnatin ke samun nata taimako. Yanzu haka Masar da Rasha na jagorancin wani sabon yunkurin samun tsagaita wuta a kasar. Dangane da wannan rikici, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Elharun Muhammed na Babbar Kwalejin Fasaha ta Kaduna, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora ne kan na makon jiya, inda ya tattauna da matashin nan da aka yanke masa hannaye a India bayan malaminsa na makarantar allo ya daure hannayen har sai da suka rube.Yanzu haka mashin mai suna Zubairu Yusha'u na amfani da hannun batir.