Podcasts about afirka

  • 20PODCASTS
  • 336EPISODES
  • 11mAVG DURATION
  • 5WEEKLY NEW EPISODES
  • Jul 28, 2026LATEST

POPULARITY

20192020202120222023202420252026


Best podcasts about afirka

Latest podcast episodes about afirka

hr2 Zuspruch
Der Zuspruch – Insektenkrankenhaus in Afrika

hr2 Zuspruch

Play Episode Listen Later Jul 28, 2026 3:03


Naturforscher und -forscherinnen haben in Afirka ein Ameisenkrankenhaus entdeckt. Gebaut von den Ameisen selbst. Was dort passiert und warum Autorin Susanna Petig davon fasziniert ist, erzählt sie hier.

Bakonmu a Yau
Ibrahim Salissou kan sauyin da aka samu a Nijar bayan juyin mulki

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Jul 27, 2026 3:31


A jamhuriyar Nijar jiya lahadi aka cika shekaru 3 da kifar da Mohamed Bazoum daga kujerar shugancin ƙasar bayan ya share shekaru biyu da watanni uku kan karagar mulki. Sojoji a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahman Tiani, babban kwamandan askarawan kare lafiyar shugaban ne suka sanar da kifar da gwmanatin. Ibrahim Salissou shi ne shugaban ƙungiyar FRSA mai fafutukar ƴantar da Afirka, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal cewa tabbas an samu sauyi cikin shekaru ukun da suka gabata a ƙasar. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...

samu bayan nijar afirka abdoulkarim ibrahim shikal
Mu Zagaya Duniya
Faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran bayan rugujewar yarjejeniya

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Jul 11, 2026 20:36


Shirin a wannan makon zai leka Gabas ta Tsakiya inda rikici ya sake barkewa tsakanin Amurka da Iran abin da ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta watanni uku da suka cimma a tsakaninsu. Bayan nan, shirin zai taɓo wasu mahimman lammuran da suka wakana a sassan yammacin nahiyar Afirka, musamman Najeriya, Nijar da Kamaru.

iran sake shirin bayan kamaru nijar najeriya afirka amurka
Wasanni
Tawagogin ƙasashen Afirka 7da aka yi waje dasu bayan sun tsallaka zagayen ƴan 32

Wasanni

Play Episode Listen Later Jul 6, 2026 10:00


Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........

fifa afrika bayan shiga dasu waje afirka
Lafiya Jari ce
Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya

Lafiya Jari ce

Play Episode Listen Later Jul 6, 2026 10:10


Shirin na Lafiya Jari ce zai  a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

shirin typhoid yadda asiya najeriya afirka
RUMFAR AFRICA | ADPlus Hausa
53 | YAƘI KO SULHU? MAKOMAR RIKICIN IRAN, AMURKA DA ISRA'ILA | DR. RAYA'UDDEEN ZUBAIR MAITAMA

RUMFAR AFRICA | ADPlus Hausa

Play Episode Listen Later Jul 5, 2026 225:56


Shin ana iya warware wannan rikici ta hanyar yaƙi, ko kuwa mafita tana cikin tattaunawa da diflomasiyya?-------------------------------------A yau duniya na ci gaba da sa ido kan rikicin da ke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila. Tashin hankali na ƙaruwa, hare-hare na ci gaba, yayin da duniya ke tambayar kanta: Shin wannan rikici zai tsaya a nan, ko kuwa zai rikide zuwa babban yaƙin yanki? Mene ne mafita? Kuma wane tasiri wannan rikici zai iya yi ga tattalin arzikin duniya, tsaron ƙasashe, har ma da rayuwar al'ummar Afirka?A wannan shirin na Rumfar Africa Podcast Hausa, za mu yi nazari cikin natsuwa tare da baƙo na musamman domin fahimtar tushen rikicin, matsayinsa a siyasar duniya, da hanyoyin da za su iya kai ga zaman lafiya.

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu sauraro kan ci gaba da zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afrika ta Kudu

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Jul 1, 2026 9:30


Bayan cikar wa'adin ranar 30 ga watan jiya da suka bai wa ƴan-ci rani don ficewa daga ƙasar, daga ƙarshe dai masu adawa da zaman baƙi a Afirka ta Kudu sun ƙaddamar da zanga-zangar neman ala dole sai sun fice daga ƙasar. Masu tarzomar dai na kallon ƴan asalin ƙasashen ƙetare a matsayin waɗanda suka mamaye gurabobin aiki, lamarin da ya jefe ɗimbin Ƴan Afirka ta Kudu cikin yanayin zaman kashe wando. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Bakonmu a Yau
Rakiya Sa'idu akan cika wa'adin korar baƙi a Afirka ta Kudu

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Jun 30, 2026 3:29


An shiga wani yanayi na fargaba da tsananin tashin hankali a Afirka ta Kudu, yayin da yau wa'adin ranar 30 ga watan nan na Yuni ke cika, game da zanga-zangar da wasu ƙungiyoyin ƙyamar baki suka shirya don tilasta wa baƙin da ba su da takardu barin ƙasar.   Ko da yake hukumar 'yansandan ƙasar ta ce ta tura ɗimbin jami'an tsaro zuwa yankunan da ake sa ran za su fuskanci tashin hankali, kamar su Pretoria, Johannesburg, da KwaZulu-Natal. Shamsiyya Haruna ta tattauna da Hajiya Rakiya Sa'idu, wata yar Najeriya da ke aiki a jami'ar Cape Town a Afirka ta Kudun, dangane da halin da suke ciki.

Wasanni
Irin rawar da ƙasashen Afirka suka taka a gasar Kofin Duniya ta 2026

Wasanni

Play Episode Listen Later Jun 29, 2026 10:00


Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya. A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa. Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32 suka yi saura. Nahiyar Afrika da ke da wakilcin ƙasashe 10, 9 daga cikin su sun samu nasarar kaiwa wannan zagaye, waɗanda suka haɗa da Afrika ta kudu da Senegal da Morocco da Ghana Ivory Coast da DR Congo da Algeria da Masar da kuma Cape Varde, inda Tunisia ta yi adabo da gasar.

Ilimi Hasken Rayuwa
Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos

Ilimi Hasken Rayuwa

Play Episode Listen Later Jun 23, 2026 10:00


A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin New York, an dawo da shi gida Afirka domin tattauna ainihin matsaloli da ci gaban nahiyar ke fuskanta, kuma a bana, fiye da rukunonin tattaunawa 340 ne aka shirya, inda aka haɗa masana daga sassan duniya. Shekarar 2026 ta yi daidai da cikar kungiyar LSA shekaru 10 da kafuwa, inda aka gudanar da taron ƙarƙashin taken makomar ilimin nahiyar Afirka a wannan ƙarni. Wani sashe mai muhimmanci a taron shi ne tattaunawa kan littafi na musamman mai suna 'Our Digital Lives and Indigenous Pathways', wanda masana suka duba yadda za a haɗa fasahar zamani da dabarun gargajiya na Afirka don samun ci gaba mai dorewa. Baya ga tattaunawar kimiyya, taron ya haɗa da baje kolin fasaha na musamman mai taken 'Histories on Scissors: The Black Essence on the Map of Being' wanda Dominic James Aboi daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya gabatar. An kuma tattauna makaloli kan addini da rashin addini a Arewacin Najeriya. An dai gudanar da wannan taro ne domin nazarin al'adun zamani da na gargajiya, inda masana suka gabatar da maƙaloli kan tarihin Afirka, al'adu, da kafafen yaɗa labarai haɗi da baje kolin dabarun bincike na zamani. A taron na bana, masana sun gano muhimman abubuwa da suka shafi makomar nahiyar Afirka ta fuskar ilimi, zamantakewa, da fasaha, kuma babban jigon da aka mayar da hankali akai shi ne yadda za a fassara binciken ilimi ya zama abin da zai amfani rayuwar al'umma kai-tsaye. Haka zalika an gano cewa ko da yake yawan binciken da masana da ke zaune a cikin Afirka ke fitarwa ya ƙaru sosai, amma ingancinsa da kuma bayyanarsa a manyan jaridun ilimi na duniya ya ragu sosai.

Wasanni
Dalilan da ya sa ƴan Afirka suka juyawa tawagar Afirka ta Kudu baya

Wasanni

Play Episode Listen Later Jun 15, 2026 9:59


Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan irin wainar da ake toyawa a gasar nema cin kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka ke karbar bakunci. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri........

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu sauraro kan giɓin kuɗaɗe da WHO ke fuskanta

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later May 19, 2026 10:15


Yanzu haka ƙasashe masu tasowa na ci gaba da ƙoƙarin cike giɓin da aka samu bayan da Donald Trump ya janyewa tallafin da Amurka ke bai wa Hukumar Lafiya don yaƙi da wasu curutuka a duniya. A jawabinsa gaban Taron Hukumar Lafiya WHO da ke a birnin Geneva, shugaban Ghana John Dramani Mahama ya ce ya kamata Afirka ta samar da tsarin kula da lafiyar al'ummarta a maimakon barin lamarin a hannun hukumar WHO. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

donald trump masu afirka amurka yanzu
Bakonmu a Yau
Zantawa da Macron a ƙarshen taron ci gaban Afirka

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later May 14, 2026 10:04


A zantawarsa da Radio France Internationale, da France 24 da kuma TV5 Monde a ƙarshen taron Afrika da Faransa da aka kammala birnin Nairobi na ƙasar Kenya, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana matsayinsa a game da taɓarɓarewar sha'anin tsaro a Mali da kuma alaƙar Faransa da sauran ƙasashen Afirka ta fannin tsaro da aikin soji. To amma da farko shugaban ya fara amsa wata tambaya ce dangane da dalilan da suka sa Faransa ke ci gaba da taka rawa a wajen tafiyar da takardar kuɗin CFA. Ga dai tattaunawar. Latsa alamar sauti domin sauraren zanatawar.

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu sauraro kan taron Afrika da Faransa da aka kammala a Kenya

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later May 13, 2026 10:42


A taron Afirka da Faransa da aka kammala jiya talata a ƙasar Kenya, Faransa ta sanar da shirin saka jarin Euro bilyan 23 don ƙarfafa kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu. Shugaba Emmanuel Macron ne ya sanar da haka, yana mai cewa daga yanzu ɓangarorin biyu za su gudanar da mu'amala ce irin ta ba ni gishiri in ba ka manda a maimakon bai Afirka tallafi kamar yadda ake yi a baya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Bakonmu a Yau
Sanata Abubakar Kyari kan makomar noma a Najeriya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later May 13, 2026 3:28


A ranar Talata ne ake kammala taron shugabannin ƙasashen Afirka da Faransa da ya gudana a birnin Nairobi ta ƙasar Kenya, wanda ya mayar da hankali kan hanyoyin ci gaban tattalin arziki da noma da samar da abinci ga jama'ar nahiyar. Yaƙin Iran na ɗaya daga cikin abubuwan da ake ganin na maida hannun agogo baya wajen  magance ƙarancin abinci, musamman rufe mahsigin Hormuz da ake amfani da ita wajen safarar takin zamani. Kan haka ne Nura Ado Suleiman ya zanta da ministan noman Najeriya Sanata Abubakar Kyari a wurin wannan taro, inda kuma ya ce su na ƙoƙarin magance matsalar. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

iran kenya nairobi hormuz noma abubakar shiga talata najeriya afirka faransa kyari
Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle
Taba Ka Lashe 12.05.2026

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle

Play Episode Listen Later May 12, 2026 10:12


Wannan shirin ya dubi yadda wakokin bege na addinin Islama ke kara samun karbuwa tsakanin matasa a kasashen nahiyar Afirka, duk kuwa da yawan sabanin fahimta da ake da su.

taba wannan islama afirka
Bakonmu a Yau
Abubuwan da taron Faransa da ƙasashen Afirka ke son cimma

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later May 12, 2026 3:41


A jiya ne ake faro taron kwanaki biyu tsakanin Faransa da ƙasashen Afrika a birnin Nairobi, wanda shugaba Emmanuel Macron da takwaransa William Ruto ke jagoranta. Taron ya haɗa shugabannin ƙasashen Afrika, da Hamshaƙan ƴan Kasuwa, da sauran masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan nemawa nahiyar Afrika mafita wajen samun ci gaban Tattalin Arziƙi  a fannonin da suka haɗa da, bunƙasa Masana'antu da Kimiyya da Fasaha da inganta Noma da Tsarin Kiwon Lafiya, da kuma samun wadatar makamashi. Danna alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar Nura Ado Suleiman da hadimin  shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Daniel Bwala.......

Bakonmu a Yau
Ambasada Kazaure kan kiran wasu ƴanmajalisar Najeriya na kwace lasisin MTN da DSTV

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later May 7, 2026 3:37


Wasu daga cikin Ƴan Majalisun Dattawan Najeriya sun buƙaci ɗaukar matakai maus tsauri a kan Afirka ta Kudu, ciki harda kwace lasisin kamfanonin su na MTN da DSTV saboda yadda ake kai wa ƴan ƙasar hari ake kuma kashe su. Majalisar ta yanke hukuncin tura tawaga Afirka ta Kudu domin tattaunawa da hukumomin ƙasar, yayin da shi ma bangaren gwamnati ya tura ministan harkokin waje. Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon Jakadan Najeriya a Saudi Arabia ya yi tsokaci a kai, a tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris.

saudi arabia kiran mtn dstv kudu wasu najeriya afirka majalisar bashir ibrahim idris
Bakonmu a Yau
Dr Rakiya Sa'idu kan halin da ƴan Najeriya da ke Afirka ta Kudu ke ciki

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later May 5, 2026 3:29


Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta fara kwashe ƴan ƙasarta da ke son komawa gida daga Afirka ta Kudu, matakin da ta ce ya zama dole saboda tsananin kyamar baƙi da kuma rahoton mutuwar wasu ƴan Najeriya biyu sakamakon hare-haren da ake kai wa ƴan cirani. Akalla 'yan Najeriya 130 ne suka riga suka yi rajista don neman a kwashe su zuwa gida, sakamakon fargabar makomarsu na rashin tabbas. Dakta Rakiya Sa'idu daga jami'ar Capetown, ta bayyana mana yadda ƴan siyasa ke amfani da lokacin zaɓe wajen rura wutar wannan matsala. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar da Shamsiyya Haruna ta yi da ita............

cape town ku kudu ciki akalla najeriya rakiya afirka
Lafiya Jari ce
Yadda Cutar Sankarau ke barazana ga wasu ƙasashen yammacin Afirka

Lafiya Jari ce

Play Episode Listen Later Apr 13, 2026 9:55


Shirin Lafiya Jari ce a  wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi  duba ne kan cutar ɗan sanƙarau ko kuma meningitis, cutar da a yanzu haka wasu ƙasashe ke cikin haɗarin fuskantar ɓullarta musamman a yammacin Afrika, waɗanda dama ke a tubalin fuskantar wannan cuta lokaci zuwa lokaci.

afrika yadda wasu afirka
Wasanni
Hasashe game da rawar da ƙasashen Afirka za su taka a gasar lashe Kofin Duniya

Wasanni

Play Episode Listen Later Apr 6, 2026 10:00


Shirin a wannan lokaci tare da  Khamis Saleh ya yi duba ne kan yadda aka kammala samun tawagogin ƙasashen da za su fafata a gasar lashe kofin duniya da ke tafe a watan Yuni mai zuwa. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

Bakonmu a Yau
Tattaunawa da Dr Maman Kassou na jami'ar Andre Salifou a Nijar kan cinikin bayi

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Mar 26, 2026 3:34


Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana fataucin bayi da aka share ɗaruruwan shekaru ana yi daga Afirka zuwa Turai da Amurka a matsayin ‘'cin zarafin bil  Adama mafi girma'' da aka taɓa gani a tarihi. Ƙasashen duniya 123 ne suka kaɗa ƙuri'ar goyon bayan wannan ƙuduri, wasu uku wato Amurka, Isra'ila da Argentina suka ƙi amincewa yayin da wasu ƙasashe 52 suka yi ƙememe ta hanyar rowar ƙuri'unsu. To domin tuni a game da lokacin da aka fara ɗibar bayi daga Afirka da kuma yadda hakan ya shafi ci gaban nahiryar, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani tarihi Dr Maman Kassou, malami a jami'ar Andre Salifou da ke Damagaram, ga kuma zantarwarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.

argentina ku isra maman adama bayi duniya nijar turai afirka amurka majalisar damagaram abdoulkarim ibrahim shikal
Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle
Taba Ka Lashe 06.03.2026

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle

Play Episode Listen Later Mar 6, 2026 9:54


Shirin ya duba kabilar Dogon na kasar Mali da ta yi fice a yankin yammacin Afirka musamman a Kudu maso gabashin kasar Mali.

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Yadda yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haifar da tsadar makamashi a duniya

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Mar 4, 2026 9:55


A yayin da yaƙi tsakanin Isra'ila da Amurka da Iran ke daɗa rincaɓewa, an fara gani tasirinsa a kasuwar ɗanyen mai da makamashi ta duniya. Ko a Najeriya, ƙasar da ta fi arziƙin ɗanyen mai a Afirka, farashin litar fetur ya tashi, kuma masana sun ce ana iya ganin cigaba da tashin farashin makamashi. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

iran ko isra duniya yadda shiga najeriya afirka amurka
Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle
Taba Ka Lashe: 25.02.202

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle

Play Episode Listen Later Mar 3, 2026 10:18


Dauri rayuwa ta zamantakewar al'ummar Hausa Fulani da ma wasu kabilun ta kasance cike da alkunya da kuima kamun kai ta yadda matar aure ke kauracewa fadar sunan danta ko mujinta.

taba nijar najeriya afirka
Bakonmu a Yau
Dr Kassum Garba Kurfi kan yarjejeniyar Ɗangote da kamfanonin dillancin Fetur

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Feb 26, 2026 3:37


A Najeriya, Matatar Man Dangote mafi girma a Afirka ta cimma matsaya da wasu manyan kamfanonin dallancin Mai guda 12 domin rarraba man fetir kimanin lita miliyan 60 zuwa 65 a kowace rana. Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana haka cikin wata sanarwar, da ya ce gagarumin mataki ne na wadata kasar da mai da kuma dogaro da kai a bangaren makashi. Domin sanin tasirin matakin, Ahmad Abba ya tattauna da Dr. Kasum Garba Kurfi, masanin tattalin arziki a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

ku domin dangote garba najeriya afirka shugaban
Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle
Taba Ka Lashe 18.02.2026

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle

Play Episode Listen Later Feb 18, 2026 9:41


Shirin ya yi nazari kan suna a tsakanin kabilu da kuma radin suna ko kuma zanen suna a kasashe daban-daban na Afirka.

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle
Taba Ka Lashe: 11.02.2026

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle

Play Episode Listen Later Feb 17, 2026 9:41


Suna dai linzami ne, kuma 'dan adam ya fara amfani da suna tun fil azal domin fayyace asali ko al'ada ko kuma jinsin da mutum ya fito.

suna hausa taba najeriya afirka jamhuriyar nijar hausawa
Bakonmu a Yau
Tattaunawa kan matakin Amurka na tura sojojinta zuwa Najeriya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Feb 5, 2026 3:27


Amurka ta sanar da tura wata tawagar sojinta zuwa Najeriya, abinda a karon farko ke tabbatar da isar dakarun nata ƙasar, tun bayan ƙarfafa yarjejeniyar tsaron da ƙasashen biyu suka yi, biyo bayan zargin da shugaba Donald Trump ya yi a shekarar bara, cewa ana kashe Kiristoci a Najeriyar. Kwamandan rundunar sojin Amurka da ke kula da Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson ya ce sun tura dakarun ne a bisa amincewar Najeriya.  Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Yahuza Ahmed Getso masanin tsaro a Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.......

donald trump tura shiga najeriya afirka amurka
Tambaya da Amsa
Menene yake haifar da sukar ciki ko kuma naɗewar hanji a cikin ɗan Adam

Tambaya da Amsa

Play Episode Listen Later Jan 24, 2026 21:19


Shirin tambaya da amsa na wannan mako zai fara ne da bayani akan abinda ke haifar da sukar ciki ko kuma naɗewar hanji a cikin mutum. Sai kuma tambayar da ke neman ƙarin bayani a kan yaushe aka fara taron duba lamuran tattalin arziki na Duniya da ake kira Davos world economic forum kuma wane tasiri yake da shi ga duniya da kuma yankin mu na Afirka. Sai kuma tambayarmu ta gaba wadda ke buƙatar ƙarin haske kan irin gudunmawar da ake la'akari da su kafin a ba wa mutum kyautar lambar yabon zaman lafiya ta duniya wato Nobel peace price, kamar yadda aka baiwa ƴar ƙasar Venezuela Maria Corina Machado. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin

nobel davos sai shirin kuma duniya shiga yake sukar hanji najeriya cikin afirka
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu sauraro kan kayan aikin soji da Amurka ta bai wa Najeriya

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Jan 14, 2026 10:32


Amurka ta sanar wa bai wa Najeriya wasu muhimman kayan aikin soji domin tunkarar ƙalubale na tsaro da ƙasar ke fama da shi. Rundunar Amurka mai kula da nahiyar Afirka wato Africom ce ta sanar da hakan, sama da makonni biyu da Amurka ta ƙaddamar da farmakin farko kan wasu wurare ta bayyana cewa maɓoyar yan ta'addace. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

soji africom masu kayan najeriya afirka amurka
Bakonmu a Yau
Dr Kabiru Adamu na Beacon Consulting kan tallafin kayan yaƙin Amurka ga Najeriya

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Jan 14, 2026 3:35


Hedikwatar rundunar sojin Amurka mai kula da nahiyar Afirka, AFRICOM, ta sanar da miƙa wa gwamnatin Najeriya taimakon kayayyakin aikin soji, matakin da ke ƙarfafa yarjejeniyar tsaron da ke tsakaninsu don yaƙi da ta'addanci. Sai dai cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, rundunar sojin Amurkan ba ta yi ƙarin bayani kan nau'ika da kuma adadin makaman ba. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Kabiru Adamu  shugaban  kamfanin Beacon Consulting da ke bincike kan tsaro a nahiyar Afrika.

consulting afrika beacon sai africom adamu kayan najeriya afirka amurka
Muhallinka Rayuwarka
Dalilan da masana suka ce su ke ƙara bayyana sauyin yanayi

Muhallinka Rayuwarka

Play Episode Listen Later Jan 11, 2026 20:06


Shirin muhallinka rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne  kan yadda sauyin yanayi ko dai na zafi ko na sanyi ko kuma damina ke bayyana ƙarara, musamman a yankin yammacin Afirka. Ga misali a Najeriya, ɗaya daga cikin sauye-sauyen yanayin da aka shaida shi ne rashin hunturu a shekarar  bana, musamman a Yankin arewacin ƙasar, inda aka saba ganin kankamar Yanayin na sanyin mai tsanani daga ƙarshen watan Nuwamba ko farkon Disamba zuwa ƙarshen watan Janairu ko farkon Fabarairu. Gabanin fuskantar wannan lamari dai hatta yanayin damina da lokacin zuwanta ya sauya daga abinda aka saba da shi, batun da hatta a wasu wuraren da ke yankin Kudu maso yammacin Najeriya ma an shaida hakan. Tuni dai wannan al'amari na sauyin lokutan yanayin zafi da damina ko kuma sanyi ya zama abin tattaunawa a tsakanin jama'a dangane da dalilan da suka janyo hakan, da dai wasu sauran tambayoyi da ake da ƙishirwar neman amsoshinsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman............

ga ku suka shirin kudu tuni najeriya masana afirka nuwamba
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙasashe 8 da za su fafata a Quarter Finals na AFCON

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Jan 8, 2026 9:41


A gasar neman kofin Afirka da ke gudana a Morocco, a yanzu dai an tantance ƙasashe 8 da za su fafata da juna a matakin da ake kira Quarter Finals, inda Mali-Sénégal, Masar ta haɗu da Côte d'Ivoire, Kamaru ita da Morocco sai kuma Nigeria da za ta kece reni da Algéria. Waɗannan ƙasashe 8, tun farko su ne ake hasashen cewa za su iya taka gagarumar rawa a gasar. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Madubin Kabara
Adamu Garba II | MUK Na 28

Madubin Kabara

Play Episode Listen Later Dec 20, 2025 30:26


Adamu Garba II matashi ne mai kwarin gwiwa sannan wanda ya ke dan kasuwar da yayi iliminsa a tsakanin Najeriya har zuwa Amurka. Yana daga cikin 'yan takarar Shugaban Kasar Najeriya a shekarar 2023 mafi karancin shekaru a tsakanin masu neman wannan kujera a kasar da ta fi kowa ce kasar Afirka yawan al'umma da kuma karfin arzikin man fetur. Shine kuma wanda 'yan uwa da abokan arziki suka tara wa sama da naira miliyan 80 don yin takara a jam'iyyar APC amma kwatsam sai ya canja sheka zuwa YPP.

shine yana apc garba adamu ypp najeriya afirka amurka
Madubin Kabara
Na'ima Idris Usman | MUK Na 32

Madubin Kabara

Play Episode Listen Later Dec 20, 2025 14:14


Na'ima Idris Usman, cikakkiyar Likita ce da ke jihar Kanon Najeriya, ta yi karatun a tsakanin Najeriys da China. Ta bamu labarin rayuwarta daga kuruciya zuwa girmanta, da ma yadda aka yi ta fara ilimantar da mata ta kafafen sada zumunta game da lafiyar jikinsu duk da cewa furta kalmomin da ke da alaka da al'aura abu ne mai cike da kalubalen a kasar Hausa. Da kuma yadda karshe ta buge da zuwa shirin horar da shugabanci ga matasan Afirka a Amurka da a turance ake kira da Mandela Washington Fellowship da aka fi sani da Young African Leaders Initiative (YALI) na shekarar 2022.

china usman hausa mandela washington fellowship afirka amurka young african leaders initiative yali
Madubin Kabara
Ibrahim Sherif | MUK Na 26

Madubin Kabara

Play Episode Listen Later Dec 20, 2025 36:47


Ibrahim Sherif bakano ne dan Najeriya da ya bar gida tun yana dan saurayi zuwa Birtaniya domin aikin sa kai. Inda daga baya ya nausa Afirka ta Kudu inda ya cika burinsa na zama matukin jirgin sama, har ma ya buge da tsere keke a can.

sherif inda kudu najeriya afirka birtaniya
Wasanni
Taƙaitaccen tarihi kan yadda aka faro gasar AFCON a shekarar 1957

Wasanni

Play Episode Listen Later Dec 15, 2025 9:57


Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci tare da Khamis Saleh ya yi duba ne kan tarihin gasar lashe kofin Afrika AFCON da hukumar CAF ke shiryawa. An faro buga gasar lashe kofin nahiyar Afirka, wacce ke zaman gasar kwallon ƙafa mafi girma da daraja a nahiyar a shekarar 1957, da hukumar kula da kwallon ƙafar Afrika CAF ce ta jagoranci. An fara gudanar da gasar ne a watan Fabrairun shekarar 1957 a birnin Khartoum na ƙasar Sudan da ƙasashe 3, kafin a shekarar 2019 aka faɗaɗata zuwa tawogogun ƙasashe 24, kuma Masar ce ta fara lasheta bayan lallasa Sudan da ta karbi baƙunci a wasan karshe, inda ta lashe kofin da aka sanya masa sunan Abdel Aziz Abdallah Salem, ɗan ƙasar Masar da ya fara shugabantar hukumar CAF. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Kasuwanci
Yan Najeriya na yawaba Hasetins kan kafa kamfanin ma'adanai mafi girma a Afirka

Kasuwanci

Play Episode Listen Later Dec 3, 2025 10:06


Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan gina katafaren kamfanin tono da kuma sarrafa ƙarafu da duwatsu masu daraja da wani matashi ya ƙaddamar a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, irinsa mafi girma a Afirka, wanda zai laƙume dalar Amurka miliyan 400.

mafi kafa girma nasarawa najeriya afirka amurka ahmed abba
Bakonmu a Yau
Yadda aka tarawa Najeriya dala miliyan 30 domin samar da tsaro a makarantu

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Dec 3, 2025 3:37


Ƴan Najeriya na ci gaba da neman bayani a kan yadda wasu kuɗaɗen da aka tara, da yawan su ya kai dala miliyan 30 domin samar da tsaro a makarantu suka shiga, sakamakon sake dawowar satar ɗalibai a yankin arewacin ƙasar. A ƙarƙashin wannan shirin da ya fara a shekarar 2014, kasashe da dama suka tallafawa Najeriya, cikin su har da ƙasar Norway da ta bada dala miliyan guda, da wata dala miliyan guda daga Bankin Raya ƙasashen Afirka na AfDB, sai kuma Fam miliyan guda daga gwamnatin Birtaniya. Gwamnatin Switzerland ta bada taimakon dala miliyan takwas, yayin da Amurka ta bada dala miliyan biyu, sai kuma Qatar da ta bada dala miliyan biyu, yayin da ƴan kasuwan Najeriya su kuma suka bada taimakon dala miliyan 10. Ganin yadda aka kasa samar da tsaron a makarantu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abubakar sadiq Umar Gombe.  Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

norway qatar fam domin dala samar yadda tarawa shiga najeriya afirka amurka birtaniya bashir ibrahim idris
Bakonmu a Yau
Farfesa Tukur Abdulƙadir akan juyin mulkin Guinea Bissau

Bakonmu a Yau

Play Episode Listen Later Nov 27, 2025 3:34


 A jiya ne sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Umaro Sissiko Embalo, sakamakon rikicin zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a ƙarshen mako, a daidai lokacin da ake shirin gabatar da sakamako yau Alhamis. Shugaban da madugun yan adawa duk sun yi iƙrarin nasara, a kasar da ta yi ƙaurin suna wajen juyin mulki. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir dangane da juyin mulkin, wanda shi ne na biyar a kasashen Afirka ta Yamma, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai. 

abdul akan guinea bissau adir yamma afirka alhamis shugaban bashir ibrahim idris
Wasanni
Yadda Ashraf Hakimi ya lashe gwarzon shekara na Afrika karon farko

Wasanni

Play Episode Listen Later Nov 24, 2025 9:59


Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafan Afirka da Achraf Hakimi na Morocco ya lashe. A makon daya gabata ne Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF, ta bayar da kyautuka ga zaratan ƴan wasan nahiyar da suka nuna bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita. A yayin bikin da ya gudana a birnin Rabat na ƙasar Morocco, hukumar ta CAF ta sanar da ɗan wasan baya na tawagar ƙasar ta Morocco wanda kuma ya ke yi wa ƙungiyar PSG wasa Achraf Hakimi,  a matsayin wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka a wannan shekarar. Hakimi ya samu nasarar ce bayan doke shahararrun ƴan wasan nahiyar da suka taɓa lashe kyautar irinsu Mohamed Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool,  da kuma Victor Osimhen na Nigeria da ke wasa a Galatasaray. Wannan ne dai karo na farko da ɗan wasan ya taɓa lashe ƙyautar, bayan da a karo biyu a jere ya na ƙarewa a mataki na biyu, a shekarar 2023 da Victor Osimhen ya lashe da kuma 2024 da Ademola Lookman ya lashe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

Madubin Kabara
Murtala Mai | Madubin Usman Kabara #11

Madubin Kabara

Play Episode Listen Later Nov 20, 2025 56:11


Dr. Murtala likitan yara ne dan asalin jihar Adamawar Najeriya da ya rikide ya zama kwararren masanin lafiyar al'umma musamman mata da yara, wanda a yanzu haka ma'aikaci ne a wata kungiya mai zaman kanta da ta ke tallafawa harkokin lafiyar iyali a duniya ciki har da kasashen Afirka mai suna Pathfinder International da ke kasar Amurka.Murtala Mai | Madubin Usman Kabara #11

usman afirka amurka kabara
Madubin Kabara
Sarki Abba Abdulkadir | Madubin Usman Kabara #9

Madubin Kabara

Play Episode Listen Later Nov 18, 2025 61:07


A shekarar 1984 a Najeriya an sami wani saurayi dan jihar Kano da ya fi kowane dalibi a Najeriya cin makin jarrabawar gama sakandaren kasashen Afirka ta WAEC a takaice. Yanzu haka dai wannan dalibin mai suna Farfesa Sarki Abba Abdulkadir farfesa ne a bangaren haddasuwar cututtuka a Jami'ar Northwestern University da ke Chicago a Amurka.

chicago abba northwestern university usman kano sarki abdulkadir najeriya afirka amurka yanzu kabara
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu saurare kan ranar Malamai ta Duniya

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Oct 6, 2025 9:50


A jiya ne aka gudanar da bikin ranar malamai ta duniya cikin yanayin ƙuncin rayuwa da ƙarancin albashi, musamman a wasu ƙasashen Afirka da malaman ke ɗanɗana kuɗarsu. An ware wannan rana ne, domin nuna goyon baya ga irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban rayuwar al'umma a fannoni da dama. Wanne hali malamai ke ciki a yankunanku? Shin kun gamsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a yankunanku. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

Mu Zagaya Duniya
Shirin ƙarin albashin masu riƙe da muƙaman siyasa a Najeriya ya bar baya da ƙura

Mu Zagaya Duniya

Play Episode Listen Later Sep 13, 2025 20:00


A karon farko gwamnatin Najeriya ta hannun hukumarta da ke kula da sufurin jiragen ruwa a koguna ko kuma cikin gida, ta shelanta haramta jigilar duk wani jirgi ko kwale-kwale da ba a yi wa rijista da gwamnati ba, Ghana ta karɓi baƙi ‘yan Afirka ta yamma, waɗanda gwamnatin Amurka ta taso ƙeyarsu a ƙarƙashin shirin shugaba Donald Trump na korar baƙin-haure, wasu kenan daga cikin manyan labarun makon jiya da Nura Ado Suleiman zai kawo muku a cikin shirin Mu zagaya Duniya.. Latsa alamar sauti don sauraron shirin..........

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Ra'ayoyin masu saurare kan taron manyan hafsoshin tsaron Afrika

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Play Episode Listen Later Aug 27, 2025 9:40


Hafsoshin tsaro na ƙasashen Afirka a taron da suka yi a birinin Abujan Najeriya, sun ƙuduri aniyar haɗa gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta. Wannan taro dai ya samu halartar wakilan ƙasashe sama da 50, waɗanda suka yi imani da cewa la'akari da girman matsalar, akwai buƙatar ƙasashen su yi aiki a tare don tunkarar ta. Shin ko meye ra'ayoyinku a game da wannan yunƙuri na ƙasashen Afirka? Waɗannan shawarwari za ku bayar domin samun nasarar wannan fata? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle
Taba Ka Lashe: 30.07.2025

Taɓa Ka Lashe | Deutsche Welle

Play Episode Listen Later Aug 5, 2025 10:00


Shan shayi al'ada ce mai tushe da ta yadu a tsakanin al'umomi mabanbanta a fadin duniya.

shan taba turai najeriya afirka
Lafiya Jari ce
Matakin Amurka ka iya haifar da koma baya ga shirin yaki da cutar HIV a Najeriya

Lafiya Jari ce

Play Episode Listen Later Aug 4, 2025 10:11


Shirin ya mayar da hankali ne kan yadda matakin Amurka na janye tallafin da take ba wa ɓangaren kula da masu fama da cuta mai karya garkuwa jiki ta HIV da ake fargabar zai iya haifar da koma baya ga shirin yaƙi da cutar. Tuni hukumomi a duniya suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan mataki da shugaban Amurka, Donald Trump ya ɗauka, wanda ake ganin zai fi yin tasiri ne ga nahiyar Afirka. Tuni mujallar Lancet ta Biritaniya ta yi hasashen cewa matakin na Donald Trump na iya haifar da mutuwar mutane sama da miliyan 14 nan da shekarar 2030, ciki har da yara sama da miliyan 4.5 'yan kasa da shekaru biyar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashi Aminu.

Afropop Worldwide
Planet Afropop - Syli D'Or Winners And Artists For Aid

Afropop Worldwide

Play Episode Listen Later Feb 6, 2024 52:15


Every winter, starting in February, the organizers of the annual Nuits D'Afrique festival put on a battle of the Afropop bands. Bands face off, three a night at Club Balatou, and the audience votes a winner for the night. Eventually, the field comes down to nine finalists, and that's when we at Afropop are asked to pick the winner of the Afropop prize from those nine acts. So as the festival is about to kick off again this year,we thought it would be great to honor the 2023 winners. The big winner of the entire contest was an awesome Afro-Latin band called Team Salsa Quintet. We'll also feature a visit with a group of young Algerian immigrants in Montreal - the band is called Afirka. And we'll wrap up with a report from correspondent Harrison Malkin on the recent Artist for Aid event in Newark, New Jersey. It was a star-studded evening aimed at raising awareness and funds for the victims of violence in Gaza and Sudan.