POPULARITY
Ko kun san irin al'ummar da ke zaune a yankin Obalande na jihar Legos da ke Tarayyar Najeriya? Shirinmu na Taba Ka Lashe ya lalubo muku wannan amsa.
Ko kun san cewa akwai wasu tarin kabilu a jihar Kaduna da ke Tarayyar Najeriya, wadanda suka alkinta wasanni da al'adunsu? Shirin Taba Ka Lashe ya tattauna da su.
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi duba ne kan yadda kansar bakin mahaifa ke hallaka Mata, musamman ƴan tsakanin shekaru 15 zuwa 44, a Najeriya. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron shirin...
Bayan ɗaukar wasu matakai da gwamnatin Najeriya ta yi wajen yaki da masu tada kayar baya a shiyar Arewa maso gabashin kasar, a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, ganin yadda aka samu raguwar kai hare-haren kunar bakin wake. To sai dai a baya-bayan nan wasu mata da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai harin ƙunar baƙin wake a yankin Gwoza da ke jihar Borno, har ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18, abinda masana harkokin tsaro ke fassarashi a matsayin komawar hannun agogo baya. Dangane da wannan batu ne Abdoulƙadir Haladou Kiyawa, ya tattauna da Dakta El-Harun Muhammad, masanin harkokin tsaro a Tarayyar Najeriya.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron zantawarsu...
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yada zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya yi dubi kan matsanancin kuncin rayuwar da al'umman kasar suka shiga da har ta kai ana fasa rumbunan abinci ko tare manyan motocin dakon kaya a tituna ana kwasan abinci.
A yayin taron yanayi na 27 wanda Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a shekarar da ta gabata, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tashi ta sanar wa duniya cewa za ta dauki matasa masu jini a jika aikin dashen itatuwa har dubu dari 2 da 50 a duk shekara, a shirin da take na daukar mataki a game da sauyin yanayi. Shekara guda bayan wannan alwashi na gwamnatin Najeriya, bincike ya nuna cewa kusan an jefa wannan shiri a kwandon shara, a yayin da ya rage ‘yan kwanaki a bude taron yanayi na 28 da aka wa lakabi da COP 28.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda 'yan kasuwa a Tarayyar Najeriya musamman arewacin kasar, ke shiga kasuwanni da makudan kudi domin saye kayayyakin abinci, su kuma boye domin jiran lokacin da kayan za su yi tsada a kasuwanni kafin su fara fitowa da su da zummar samun kazamar riba, ba tare da la'akari da matsanancin hali da talakawan kasar ke fama da shi ba. Ku danna alamar sauti don sauraren cikakken shirin wanda ya zanta da masu ruwa da tsaki......
Bayan share kusan shekaru 8 da haramta shigar da tsoffin motoci da ake kira ‘yan tuwarist a iyakoki na kasa a Tarayyar Najeriya, bisa ga dukan alamu gwamnati na duba yiyuwar cire wannan haramci. Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito wani babban jami'i a ma'aikatar sufuri ta kasar mai suna Ibrahim Musa na cewa, tuni gwamnati ta amince a bude iyakar Seme da ke tsakanin Nigeria da Jamhuriyar Benin domin ci gaba da shigar da motocin. Khamis Saleh ya zanta da Alhaji Zubair Mele Abbaganama, daya daga cikin shugabannin kungiyar masu fiton kaya a Seme, domin jin ko watakila suna da masaniya a game da wannan mataki. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawarsu.......
A makon da ya gabata ne gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da tawagar kwallon kwando ta kasar daga shiga wasannin kasa da kasa na tsawon shekaru 2 da zummar daidaita al'amura a hukumar kula da wasan kwallon kwando ta kasar da rikici ya wa dabaibayi. Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako ya duba batun jigine shiga gasar.
Shirin na wannan lokaci, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar da kuma Tarayyar Najeriya domin zakulo matasan da ke yin sana'o'in dogaro da kansu.
Wani matashi a jihar Kano da ke Tarayyar Najeriya, ya rungumi sana'ar harhada turare na Afirka da ma na Larabawa.
Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan mako ya yi karin bayani ne akan tambayoyin da suka shafi manhajar Telegram, da na'urar ATM da kuma tattaunawa da mawakin da ya zama dan majalisar Tarayyar Najeriya.
A ranar Litinin aka bude taron zaman lafiya da tsaro karo na 7 a Dakar, babban birnin kasar Senegal wanda zai maida da hankali kan tasirin cutar Korona a fadin nahiyar da kuma matsalolin tsaron yanar gizo, ta'addanci, da kuma sauyin yanayi. An kafa dandalin zaman lafiyar da tsaro na Dakar dake gudana a duk shekara ne yayin taron Faransa da Afirka da aka yi a birnin Paris a shekara ta 2013, kuma a cikin shekarun da suka shige, ya zama fage ga masu yanke shawara a Afirka. Kan wannan taro ne Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Yahuza Getso masanin tsaro dake Tarayyar Najeriya.
Daya ga watan gobe na disamba ita ce ranar da gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bai wa ma'aikatanta domin su yi allurar kariya daga cutar covid-19, to sai dai alkalumma na nuni da cewa adadin wadanda suka karbi allurar sau biyu bai wuce 3% ba. To domin jin dalilan da suka sa mafi yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya suka ki karbar allurar, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Comrade Nasiru Kabir, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin kwadagon kasar, ga kuma zantawarsu.
Shirin 'Duniyar Wasanni' tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi leka jihar Katsina a Tarayyar Najeriya, inda mahukuntan jihar suka maida hankali don bunkasa harkokin wasannin kwallon kafa domin jan hankalin matasa da zummar kawar da hankalinsu daga fadawa miyagun laifuka da yanzu haka ke addabar jihar da wasu sassan Najeriya.
Shirin na wannan lokaci ya tsakulo matasa masu sana'o'in dogaro da kai, a jihohin Kaduna da Kano da ke Tarayyar Najeriya.
Wani matashi a jihar Kano da ke Tarayyar Najeriya, ya kirkiri radiyo bayan da ya kammala karatunsa na diploma.
Shirin Kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba wanda ya yi duba kan dambarwar da ta kunno kai tsakanin jihohin Lagos da Rivers da kuma gwamnatin Tarayyar Najeriya, bayan da jihohin suka bukaci basu damar cin gajiyar kudaden harajin VAT maimakon aikasu asusun ajiyar Tarayya.
Shirin na yau, ya yi nazari ne kan kalubale da alfanun amfani da kafafen sada zumunta na zamani.
A cikin shirin kamar yadda muka saba, mun zakulo muku matasa a Jamhuriyar Nijar da makwabciyarta Najeriya da suka tashi tsaye domin neman abin dogaro da kansu.
Shirin na waannan lokaci dai baki dayansa ya yasar da zango ne a jihohin Adamawa da Kaduna da kuma Katsina duk a Tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da matasan da ke dogaro da kansu.
Shirin na wannan lokaci ya leka jihar Kaduna a Tarayyar Najeriya da kuma jihar Dosso a Jamhuriyar Nijar da kuma Yamai fadar gwamnatin ta Nijar, domin zakulo muku matasa masu neman na kansu.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba batun musabbabin tsadar Siminti da kuma karuwar bukatarsa a Tarayyar Najeriya duk kuwa da matsin tattalin arziki da ake fama da shi, saboda matsalolin tsaro da annobar korona. Kamfanin Simintin Dangote dai shine ke kan gaba wajen samar da Simintin a Najeriyar kuma wanda ke juya akalar farashin sa a kasuwa, kuma ya musanta batun karin farashin daga garesu kamar yadda Babban daraktan kasuwanci na Kamfanin Alhaji Rabi’u Umar ya tabbatar mana, inda ya jadda shirin samar da karin simintin ga 'yan Najeriyar don saukaka farashinsa a kasuwa ta hanyar farfado da tsoffin kamfanonin sarrafa simintin da kuma sabbi da ake shirin kaddamarwa.
Shirin na wannan lokaci, ya tattauna ne da matasa masu dogaro da kansu a jihohin Kano da Gombe a Tarayyar Najeriya da kuma Damagaram a Jamhuriyar Nijar.
Sarakunan gargajiya da kungiyoyin manoma da makiyaya a Jamhuriyar Nijar, na fadakar da mutane kan muhimmancin zaman lafiya domin kaucewa rigingimu duba da irin abubuwan da suke faruwa a Tarayyar Najeriya da sauran kasashe da ke makwabtaka da Nijar din.
Shirin na wannan lokaci ya leka garin Barebari wato jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya, domin jin yadda al'adar yi wa yara kaciya ko kuma shayi take a ga Kanuri.
Shirin Himma dai Matasa na wannan lokaci ya leka Tarayyar Najeriya, inda ya kai ziyara jihohin Kano da Kaduna da kuma Katsina.
Shirin ya leka jihohin Adamawa da Kano da kuma Kebbi a Tarayyar Najeriya, inda ya zakulo matasan da suka tashi tsaye suka kama san'o'in dogaro da kai.
Shirin ya yi nazari ne kan tasirin shafukan sada zumunta na zamani wajen tunzura matasa, a zanga-zangar da ke ci gaba da gudana a yanzu haka a Tarayyar Najeriya.
Ko kun san cewa a wani gari da ke jihar Katsina a Tarayyar Najeriya, akwai al'ummar Musulmi da Kirista da ke zaune kusan shekaru 100 ba tare da an taba jin kansu ba? Ku biyo mu domin jin dalili.
Wata matashiya a jihar Kaduna da ke Tarayyar Najeriya 'yar shekaru 22 da haihuwa, mai suna Sandra Dalladi Bah ta rungumi sana'ar gyaran mota wato kanikanci.
Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun maka shugaban kasar Muhammadu Buhari a kotun kolin, sakamakon wata dokar da ya sanya wa hannu a watan Mayun wannan shekarar, da ta tura ilahirin nauyin da ya ke kan gwamnatin tarayyar na gudanar da manya da kananan ayyukan manyan kotunan jihohi da kotunan daukaka kara na Shari’ar Musulunci, da na al’adu zuwa kan jihohi. Dangane da wannan batu ne muka tuntubi Farfesa Abdullahi Zuru wanda ya yi mana fashin baki kan dambarwar tsakanin jihohin da gwamnatin Tarayyar Najeriya.
Yau shirin zai ya da zango ne a jihohin Borno da Sokoto da kuma Kaduna duk a Tarayyar Najeriya, domin jin yadda wasu matasa suka tashi tsaye domin neman na kansu. Za mu ji irin sana'ar da suka runguma.
Shirin na wannan lokaci ya tattauna da wasua matasa daga Tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, inda suka bayyana dalilansu na kama sana'o'i domin su dogara da kanasu.
Shirin zai leka Tarayyar Najeriya, inda zai yi nazarin wani abu guda da ya hada manyan kabilun kasar wato Hausawa da Igbo da kuma Yarabawa, wannan abu kuwa shi ne: "Goro."
Shirin Kasuwa Akai miki Dole na wannan makon ya duba kasuwar musayar kudin kasa da kasa ne a Tarayyar Najeriya, inda kudin kasar na Naira ke cigaba da faduwa, yayin da kimar kudaden kasashe ketare ke tashin gwaron-zabi. Wannan faduwar na darajar kudin Naira a cewar masana, na cigaba da haddasa mummunan tasiri a tattalin arzikin kasar, tare da haifar hauhawan farashin kayayyakin masarufi.
Shin ko kun san matashin nan da wakarsa ke tashe a kasar Hausa wato Hamisu Breaker Dorayi? Shirin Dandalin Matasa na wannan makon ya tattauna da shi da ma wasu mutane a Tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Nijar dangane da wakarsa ta Jarumar Mata.
Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmad Abba, ya duba hada-hadar kasuwannin dabbobin Layya a jamhuriyar Nijar da Tarayyar Najeriya, gabanin babbar salla ko sallar Layya dake tafe cikin yanayin koma bayan tattalin arziki da annobar korona ta haifar.
Karancin hasken wutar lantarki da ake fama da shi a Tarayyar Najeriya, ya sanya wani matashi a jihar Bauci da ke yankin arewa maso Gabashin kasar ya kirkiri injin janareto da ba ya bukatar man fetur.
Shirin zai leka jihohin Kano da Sokoto a Tarayyar Najeriya da kuma Damagaram a Jamhuriyar Nijar, domin zakulo muku matasan da suka kasance masu dogaro da kawunansu.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida hankali kan yadda jama’a da dama ke fadawa tarkon ‘yan damfara da sunan tallafi ko agajin gwamnati don rage radadin dokar kulle don hana yaduwar cutar korona masamman a Tarayyar Najeriya.
Wani matashi a jihar Adamawa da ke Tarayyar Najeriya, ya rungumi sana'ar sarrafa alli ko kuma chalk da Turancin Ingilishi, da ake yin rubutu da shi a wajen koyo da koyarwa.
Shirin "Kasuwa a kai miki Dole" na wannan makon ya daura ne kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan halin yadda batun tsarin kudin Fansho yake a tarayyar Najeriya, la'akari da irin matsalolin da masu karbar fansho ko iyalansu suke fuskanta a kasar.
Shirin "Kasuwa a kai miki Dole" na wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin nazarin yadda batun tsarin kudin Fansho yake a tarayyar Najeriya, la'akari da irin matsalolin da masu karbar fansho ko iyalansu suke fuskanta a kasar.
Nazarin hanyoyin inganta harkar ilimi musamman na firamare da sakandare a Jihar Yobe da ke a shiyyar Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya.
Ko kun san rashin ilimi tsakanin yara da matasa na ci gaba da zama babbar matsala a Tarayyar Najeriya shekaru 68 bayan samun 'yancin kai daga Turawan Birtaniya? Ku saurari Shirinmu na Dandalin Matasa na wannan makon.
Shirin ya duba tarihin rayuwar Sharif Rabi'u Usman Baba shahararren mawakin begen Manzon Allah wanda Allah ya yi wa rassuwa a wannan wata na Mayu a birnin Kano na Tarayyar Najeriya.