POPULARITY
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya kawo cigaban yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya mafi muhimmanci a ƙasar.
Mahukuntan soji a Burkina Faso sun bayyana mutukar jin ɗaɗinsu tare da mika godiya ga ƙasar Togo, dangane da namijin ƙoƙari na miƙa musu tsohon shugaban riƙon ƙwaryar ƙasar, laftanar kanar Henri Damiba, wanda su ke zargi da yunƙurin juyin mulki a lokuta da dama.Damiba zai fuskanci kotu domin amsa wannan tuhuma.... Abdoulaye Issa ya tattauna da Farfesa Ali Sakola Jika malami a jam'iar Ouagadougou.
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya mafi muhimmanci a ƙasar. Tun a bara ne aka ƙara wa'adin ranakun gudanar da wannan biki wanda ke samun mahalarta daga sassa daban-daban na duniya, inda ko a bara aka ga baƙi fiye da dubu 100 da suka halarci wannan biki. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi duba game da yadda aka gudanar da bikin al'adu na masarautar Jiwa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.......
Shirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya. A baya duk macen da za'a kai gidan miji, akan hadata da Turmin babba da ƙarami kana da kuma na ƙarfe wanda za ta rika daka kayan ƙanshi wasu ma hatta Kwalli fari da ake sanyawa jarirai da shi suke dakawa, baya da kuma na da kan sakwara da kuma babba na surfe da daka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa............
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban. Yayin wannan bikin Kalankuwa dai an duba fannoni daban-daban na al'adu kama daga Kiɗan gargajiya da Waƙa baya ɓangarorin wasanni da dama, bikin da ya samu halartar sarakuna da dama. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa. Shekaru aru-aru, da zarar an yi auren budurwa a ƙasar Hausa akan haɗata da ƙaramar yarinya da za ta yi mata zaman ɗaki, wanda a wasu lokutan anje kenan domin galibi aure ke raba wannan ƙaramar yarinya da gidan, kodayake wasu kan shafe wani wa'adi ne gabanin komawa gaban iyayensu na ainahi. Sai dai a ƴan shekarun nan wannan al'ada da kan yi tasiri wajen ƙarfafa zumunci ta zama tarihi, walau ko saboda yanayi na rayuwa, ko kuma saboda yadda aka tsagaita da auren ƴammata masu ƙarancin shekaru da dai sauran dalilai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
A Cote d'Ivoire, a jajiberin zaɓen shugaban ƙasar, hukumomi sun ɗauki matakan da suka dace na ganin an gudanar da zaɓen ba tare da an fuskanci wata matsala ba. To domin jin ko a ina aka kwana ,Abdoulaye Issa ya tattauna da Usman Ture,wani ɗan ƙasar ta Cote d'ivoire da ya karɓi katinsa na zaɓe. Latsa alamar sauti domin jin yadda tattaunawarsu ta gudana...
Jamhuriyar Nijar a duk kullum za ta kare hakokin ƴan ƙasar mazauna ketare, Wasu daga ciki tarin matsalolli da ƴan Nijar mazauna ƙasashen ketare ke fuskanta sun hada da rashin takardun zama wadanan kasashe. Jakadan Nijar a Jamhuriyar Benin, Kadade Chaibou ya bayyana haka yayin zantawa da Abdoulaye Issa a ofishinsa dake birnin Kwatanu.
Et comme chaque vendredi, RFI en français donne la parole à nos rédactions en langues étrangères pour revenir sur plusieurs thématiques d'actualité. Premier sujet, la démonstration de force, cette grande parade militaire organisée en Chine, à Pékin. C'était mercredi 3 septembre, pour commémorer les 80 ans de la fin de la Seconde Guerre mondiale et la capitulation japonaise. C'était aussi l'occasion pour Xi Jinping, le dirigeant chinois, d'impressionner 26 autres chefs d'État qui étaient invités. Parmi eux, le leader nord-coréen Kim Jong-un, mais aussi Vladimir Poutine. Avec : Kseniya Zhornokley de la rédaction de RFI en ukrainien Rodolphe de Oliveira de la rédaction en portugais Abdoulaye Issa de la rédaction de RFI en Hausa Accident mortel du funiculaire de la Gloria à Lisbonne Le traumatisme des Portugais ne s'estompe pas deux jours après le drame du funiculaire de Lisbonne. L'engin avait alors déraillé rue de la Gloria, dans le centre touristique de la capitale, faisant 16 morts et 25 blessés. Les enquêteurs poursuivent toujours leur travail pour tenter de comprendre comment cet accident a pu se produire. Rodolphe de Oliveira de la rédaction de RFI en portugais nous raconte cette « tragédie » comme l'a qualifiée le maire de Lisbonne. Sud-Est du Nigeria : Amnesty International alerte sur une zone de non-droit Le sud-est du Nigeria transformé en véritable zone de non-droit. Dans un rapport présenté à Lagos, Amnesty International décrit une situation alarmante, marquée par les violences. Abdoulaye Issa de la rédaction Hausa, que contient cette étude ? Ukraine : les 18-22 ans autorisés de nouveau à sortir du territoire L'Ukraine autorise les hommes de 18 à 22 ans à quitter le pays, et ce, en pleine loi martiale. Le gouvernement a pris la décision le 26 août dernier. Cela suscite autant d'espoir que de critiques et ça pose aussi des questions sur l'avenir démographique et économique du pays. Pour en parler, Kseniya Zhornokley de la rédaction de RFI en ukrainien.
Et comme chaque vendredi, RFI en français donne la parole à nos rédactions en langues étrangères pour revenir sur plusieurs thématiques d'actualité. Premier sujet, la démonstration de force, cette grande parade militaire organisée en Chine, à Pékin. C'était mercredi 3 septembre, pour commémorer les 80 ans de la fin de la Seconde Guerre mondiale et la capitulation japonaise. C'était aussi l'occasion pour Xi Jinping, le dirigeant chinois, d'impressionner 26 autres chefs d'État qui étaient invités. Parmi eux, le leader nord-coréen Kim Jong-un, mais aussi Vladimir Poutine. Avec : Kseniya Zhornokley de la rédaction de RFI en ukrainien Rodolphe de Oliveira de la rédaction en portugais Abdoulaye Issa de la rédaction de RFI en Hausa Accident mortel du funiculaire de la Gloria à Lisbonne Le traumatisme des Portugais ne s'estompe pas deux jours après le drame du funiculaire de Lisbonne. L'engin avait alors déraillé rue de la Gloria, dans le centre touristique de la capitale, faisant 16 morts et 25 blessés. Les enquêteurs poursuivent toujours leur travail pour tenter de comprendre comment cet accident a pu se produire. Rodolphe de Oliveira de la rédaction de RFI en portugais nous raconte cette « tragédie » comme l'a qualifiée le maire de Lisbonne. Sud-Est du Nigeria : Amnesty International alerte sur une zone de non-droit Le sud-est du Nigeria transformé en véritable zone de non-droit. Dans un rapport présenté à Lagos, Amnesty International décrit une situation alarmante, marquée par les violences. Abdoulaye Issa de la rédaction Hausa, que contient cette étude ? Ukraine : les 18-22 ans autorisés de nouveau à sortir du territoire L'Ukraine autorise les hommes de 18 à 22 ans à quitter le pays, et ce, en pleine loi martiale. Le gouvernement a pris la décision le 26 août dernier. Cela suscite autant d'espoir que de critiques et ça pose aussi des questions sur l'avenir démographique et économique du pays. Pour en parler, Kseniya Zhornokley de la rédaction de RFI en ukrainien.
Shirin al'adun gargajiya na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya yada zango ne a Ghana, inda a ‘yan kwanakin da suka gabata, ‘Yan Ƙabilar Zarma ko kuma Zabarmawa suka yi taron baja kolin al'adunsu karo na huɗu a ƙasar. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan guda cikin al'adun Ƙabilar Kanuri can a kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijar, Al'adar da ake yiwa laƙabi da ''Mai suna'', al'adar da ke da matuƙar tasiri a cikin wannan ƙabila da ke da matuƙar yawa a ƙasashen Najeriya da Nijar da kuma Kamaru. Al'adar ta Mai suna ko kuma takwara, na cikin al'adu masu matuƙar girma a wannan ƙabila da kuma ke da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ƴan uwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya maida hankali a kan bikin al'adun Dukkawa na wanan shekara ta 2025 wanda ya gudana a jihar Neja da ke Tarayya Najeriya. Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shiri.......
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan al'adar nan ta dalilin aure, guda cikin al'adun Hausawa da aka shafe tsawon lokaci ana amfani da ita da nufin haɗin aure walau tsakanin ƴammata da Samari ko kuma Zawara. Kamar yadda kusan kowanne lamari ke tafiya da zamani itama al'adar ta juye, ta yadda ta koma cikakkiyar sana'a da wasu ɗaiɗaikun mutane ke da gogewa akanta, har ta kai ga ake buɗe ofisoshi don gudanar da ita.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
A kasar Gabon, ana ci gaba da yakin neman zabe a yau da ke jajiberin zaɓen Shugaban ƙasar,wanda ya haɗa 'yan takara takwas. Gwamnati ta ayyana ranar zaben gobe a matsayin ranar hutu, domin baiwa masu rajista a larduna damar yin balaguro.Ƴan adawa sun bayyana damuwarsu ganin ta yada shugaban majalisar sojin kasar ke amfani da kadarorin gwamanti a yakin zaben.Abdoulaye Issa ya tattauna da Janjouna Ali Mahaman Sani, masani siyasar kasar ta Gabon da kewaye.Ga kuma yada zantawar tasu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
A Gabon, ana ci gaba da yakin neman zabe a yau da ke jajuburin zaben Shugaban kasar,wanda ya hada 'yan takara takwas. Gwamnati ta ayyana ranar zaben gobe a matsayin ranar hutu, domin baiwa masu rajista a larduna damar yin balaguro. Ƴan adawa sun bayyana damuwarsu ganin ta yada shugaban majalisar sojin kasar ke amfani da kadarorin gwamanti a yakin zaben. A game da zaɓen, Abdoulaye Issa ya tattauna da Janjouna Ali Mahaman Sani, masanin siyasar ƙasar ta Gabon da kewaye.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu
shirin Al'adun Mu na Gado na wanan makon tareda Abdoulaye Issa ya leka Jihar Maradin Jamhuriyar Nijar inda al'adar aikin kwado da lizzami da aka share shekaru ana yin sa da hannu ke fuskantar barazanar samun babban koma baya sakamakon wasu sabbin na'urori ko teloli na zamani da aka samu masu aiki da Computer wadanda ke zuba wannan aiki ga riguna cikin gaggawa. Ku shiga cikin alamar sauti domin sauraron shirin....
Shirin Al'adun Mu na Gado a wannan makon ya kawo muku ci gaban tattaunawa da Dakta Tahir da ake kira da Babba Impossible, wanda a makon daya gabata ya fara fashin baƙi a lamarin da yashafi tsafe-tsafe. Haka nan shirin ya leka Jamhuriyar Benin, inda gwamnatin ƙasar ta sanar da rusa wasu masarautu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa............
Shirin ''al'adunmu na gado'' tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya leƙa jihar Adamawa ta yankin arewa maso gabashin Najeriya don duba yadda gwamnatin Jihar ta ƙara yawan Masarautu a wannan jiha tun cikin shekarar da ta gabata. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan al'adar nan ta naɗin sarauta da wasu masarautun gargajiya ke yi ga ƙabilun da ba su ke da masarautar ba, wanda hakan ya biyo bayan sabbin naɗe-naɗe da ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙabilar gwari a arewacin Najeriya ta yi wa wasu manyan shuwagabannin al'ummar fulani a jihar Neja. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun masarautun Hausa da Fulani da ma wasu masarautun a yankin kudanci da kuma arewacin Najeriya ke baiwa ƙabilun da ke zaune a masarautar sarauta ba, abin da shirin Al'adu na wannan mako ya yi nazari akai tare da jin inda hakan ya samo asali da kuma alaƙar da ke tsakanin al'adun ƙabilar gwari da fulani daga masana al'adu da masarautu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi. A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al'adu ke kallon al'amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Al'adun mu na gado na wannan makon ya mayar da hankali ne ga bukuwan sabuwwar shekara na ƴan ƙasar China, bukukuwan da aka gudanar a sassa daban daban na duniyar. A Najeriya, ƴan China ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da wannan biki a biranen Abuja da kuma Lagas, wanda ya samu halarta jama'a baki daga ciki da waje. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ke kan al'adar shaɗi ko kuma Charo na sahun manyan al'adun ƙabilar fulani a ƙasashen Afrika ta yadda har sai wanda ya iya karɓaɓɓen shaɗi ke iya samun matar aure, yayinda a wasu lokutan ake gudanar da wannan al'adu a shagulgula don nishaɗi kuma jajirtacce shi ne jarumi.
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al'ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al'ada tana neman gushewa a tsakanin al'ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al'adar daga baya. Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana'ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al'adun duniya.Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al'adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa. Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
Shirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna dangene da gushewar a'adar tatsuniya wadda ke zama hanyar da al'ummar Hausawa ke amfani da ita wajen ilmantarwa, fadakarwa da kuma tarbiyantar da yara ta hanyar shirya kagaggun labarai masu kunshe da darussa.
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa kamar yadda ya saba a wannan makon ma ya leƙo wasu daga cikin masarautun Hausawa don jin tarihi da kuma tasirinsu ga al'umma. A wannan karon shirin ya yi duba kan tasirin al'adun gargajiya a matsayin jigon tafiyar da shugabanci bayan ficewar turawan Mulkin mallaka a Najeriya.Haka zalika za kuji hira ta musamman da sarkin Keffi a jihar Nassarawa wato Mai martaba Alhaji Shehu Usman Shindo Yamusa.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....
Shirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon yayi duba ne kan yadda ake gudanar da bikin Sallar Gani. ita dai wannan sallar na daga cikin dadadun al'adar mallam Bahaushe, kuma har yanzu ana gudanar da wannan biki a wasu masarautu a Arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ci gaba ne game da jerin shirye-shiryen da muka faro kan zuwan Turawan mulkin mallaka zuwa ƙasar Hausa. Turawan sha mamakin abinda suka tarar, kasancewar sun samu al'ummar Hausawa da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauran harkoki na rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare ta Abdoulaye Issa.......
Shirin a wannan makon ya maida hankali ne yadda tsarin shugabanci ya ke a kasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ci gaba ne akan na makon daya gabata wanda ya duba muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. inda shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon na musamman ne, wanda ya yi duba akan irin gudunmuwar da marigayi Salissou Hamissou ya bayar a bangaren al'adu, musamman a lokacin da ya ke gabatar da wannan shiri na Al'adunmu na gado. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.....
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda auren Zaga tsakanin al'ummar Sayawa ke komawa tarihi, salon al'adar da ke bayar da damar gadon mace ko kuma bayar da kyautar ta da sunan aure. Duk da tarin kabilun da ake da su a cikin jihohin Najeriya, kowace kabila na da irin nau'o'in al'adunta na gargajiya a fannonin rayuwa dabam dabam.Al'adun kan bambanta ne ta fuskar tsarin zamantakewa, ko ta fuskar auratayya da makamantarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....
Yan majalisun dokokin Faransa sun bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta aiwatar da sauye sauye domin inganta dangantakar ta da kasashen Afirka, lura da yadda kasashen Rasha da China ke fadada karfin fada aji a yankin. Dangane da haka Abdoulaye Issa ya tattauna da Abba Seidick masanin siyasa,zamantakewar kasar Faransa.
Shirin Al'adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya maida hankali ne kan cika shekara daya da sabon sarkin Katsinar Maradi,Mai Martaba Ahmad Ali Zaki Maremawa yayi kan karagar mulki. A dai ranar Asabar 5 ga watan Nuwambar shekarar da ta gaba ne aka nada Mai Martaba Ali Zaki a matsayin Sultan na 2 na Katsinar Maradi. Shirin ya tabo batun nasarorin da sarkin ya samu a wannan lokaci da yayi yana jagoranci.Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa....
Shirin Al'adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya tabo batun kyautar da matashiya 'yan Farsans ta lashe, inda ta zamo ta daya a duniya a wannan shekarar wajen iya gasa biridi. Tarihi dai ya nuna wannan ne karo na faro da mace ta taba lashe wannan kyauta. Haka nan, shirin ya kuma tattauna da masu ruwa da tsaki a bangaren kan wannan al'amari.Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin Al'adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya yi duba ne kan sana'ar wanzanci, wacce ke cikin sana'oin gargajiya na Hausawa da ke cike da abubuwa na al'ajabi. Mafi yawancin wanzamai gadon sana'ar suke yi daga iyayensu, amma wani lokacin, ana samun wasu daga waje da suke sha'awar koyon sana'ar don su samu hanyar cin abici. Duk kuwa da yadda bincike ya nuna cewa sana'ar ba abar da mutum zai koya cikin sauki da sauri ba ce. Sakamakon yanda ake samun sauyin zamani, yanzu wanzamai sun fara fuskantar kalubale na rashin tabbas a sana'arsu saboda fara bacewar sana'arsu. Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin kidan Duma, guda cikin al'adun jihar Maradi da ke kokarin gushewa. A wani kokari na dakile gushewar al'adu, gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta kaddamar da wani gangamin horar da matasa kidan Duma, salon kidan da ke da shahara a tsakanin garuruwan Hausawa.Akwai dai salo kala kala na kidin Duma da yanzu ke zama inda mata sun fi son gargajiya yayin bukukuwansu abin da ake kira Partyn kauyawa Tasi'u Bakwai ya mana filla filla ma'anar kidi irinsu adamulmula, yar sahabi da sauransu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............
Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da bikin masarautar Hausawar Afrika a jahar Kano da ke tarayyar Najeriya, kuma a lokacin taron an gudanar da nade-nade da bama da akayi da zummar hada kan al'ummar Hausawa da ke kasashe daban daban. Toh domin jin yadda taron ya gudana sai ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin......
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya mayar da hankali game da tasirin da sabuwar fasahar AI ta sanya na'urori basirar dan adam za ta yi ga tsarin al'adun gargajiya. Baya ga gudunmawar da fasahar ta AI ko kuma Artificial Intelligence za ta bayar wajen adana kayakin tarihi ana ganin za kuma ta taimaka matuka wajen dakile tarin al'adu ko kuma harsuna daga bacewa.Bayanai na nuna cewa wannan fasaha da ake sanya na'urori basirar dan adam za ta bunkasa sassan da suka shafi musayar al'adu tsakanin kabilu daban.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin............
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan al'adar auren Bugaje a Jamhuriyyar Nijar guda cikin al'adun da ke mutunta bukukuwan gargajiya da kuma dokokin hada zuriya. A cikin shirin za ku ji yadda Auratayya ta ke a cikin kabilar ta Bugaje, wadanda aurensu ke da matukar tsada musamman idan za su hada zuriya da wani yare daban.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya mayar da hankali ne kan al'adun al'ummar yankin Kumasi da ke kasar Ghana, yankin da ke kunshe da tarin al'ummar Hausawa a kasar ta yammacin Afrika. A cikin shirin na wannan mako za kuma kuji yadda cefane ke wakana a tsari na al'adun Hausa wanda a wasu lokutan ke cin karo da matsalar al'mubazzaranci wato rashin tattali daga Mata a dai dai lokacin da ake fama da matsin rayuwa.Wadannan dama muhimman batutuwan da suka shafi al'adun Malam Bahaushe na kunshe a cikin wannan shiri.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shiri..........
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba ne kan yadda kananan kabilu ke dunkulewa a sassan Najeriya a wani yunkuri na habaka al'adunsu, wannan mataki na zuwa a dai dai lokacin da kananun kabilun ke fuskantar mamaya daga manya. A baya-bayan nan wasu kabilu 8 daga arewacin Najeriya suka sanar da dunkulewa waje guda don habaka al'adunsu na gargajiya da kuma dakile barazanar shudewa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon ya yi nazari kan mabanbantan nau'ukan abinci da ake ci a wasu kasashen Afrika ta yamma kamar Ghana, Najeriya da Nijar. Kasashen Afrika na da ire-iren abincin da suka gada daga iyaye da kakanni wanda watakila har duniya ta nade ba za su iya yin watsi da su ba.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya mayar da hankali kan gasar da masoya tashar radiyon Faransa RFI da aka fi sani da ''Club RFI'' suka shirya a birnin Lagos na Najeriya, wadda ke da nufin musayar al'adu da yaruka tsakanin mabanbantan masu sauraron tashar. Gasar wadda ita ce karon farko da aka taba gudanar da makamanciyarta na da nufin fadada fahimtar yaruka tsakanin al'ummomi, tare da bayar da kyautukan kara kwarin gwiwa ga wadanda suka yi nasara.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gidan sarautar, Sarkin Fulani a jihar Lagos ta Najeriya, Alhaji Abubakar Muhammad Banbado. Ayi saurare Lafiya.