POPULARITY
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan gasar lashe kofin duniya da za a fara a wannan makon. Ita dai wannan gasa ta lashe kofin duniya da aka faro a shekarar 1930, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakin yaƙin duniya na biyu. Bayan kammala gasar da ƙasar Qatar ta karɓi baƙunci a shekarar 2022, jumullar ƙsashe 80 ne suka taɓa fafatawa a cikinta, inda aka buga wasan ƙarshe har 22 sai kuma ƙasashe 8 ne kawai suka taɓa lashe ta, inda Brazil ke da 5, Argentina da ke rike da kofin na da 4, Jamus da Italiya na da 3-3 sai Faransa da Uruguay da ta fara karɓar baƙuncin gasar ke da 2-2, yayinda Ingila da Spain kowaccensu ta lashe so guda-guda. Ku latsa alamar sauti don sauaron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............
A wannan Alhamis 21 ga watan Mayu, Sashin Hausa na Radio France International RFI ke cika shekaru 19 da kafuwa, bayan fara yaɗa shirye-shiryensa a shekarar 2007, kuma dangane da wanna rana Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Umar Pate, ɗaya daga cikin masanan da ke bibiyar ayyukan wannan kafa a Najeriya.
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokacin yayi duba ne kan yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai, in banda gasar Firimiyar Ingila. Barcelona ta lashe gasar La liga a Spain, a Inter Milan ta lashe gasar Serie A na Italiya, ita kuwa Bayern Munich ta ɗauke kofin Bundesliga na ƙasar Jamus, yayin da PSG ta lashe gasar League 1 ta Faransa. A yanzu haka dai gasar Firimiyar Ingila ce ake dakon jirar ƙungiyar da za ta lashe tsakanin Arsenal da Manchester City, waɗanda kowaccensu ke da ragowar wasanni biyu-biyu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........
A zantawarsa da Radio France Internationale, da France 24 da kuma TV5 Monde a ƙarshen taron Afrika da Faransa da aka kammala birnin Nairobi na ƙasar Kenya, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana matsayinsa a game da taɓarɓarewar sha'anin tsaro a Mali da kuma alaƙar Faransa da sauran ƙasashen Afirka ta fannin tsaro da aikin soji. To amma da farko shugaban ya fara amsa wata tambaya ce dangane da dalilan da suka sa Faransa ke ci gaba da taka rawa a wajen tafiyar da takardar kuɗin CFA. Ga dai tattaunawar. Latsa alamar sauti domin sauraren zanatawar.
A taron Afirka da Faransa da aka kammala jiya talata a ƙasar Kenya, Faransa ta sanar da shirin saka jarin Euro bilyan 23 don ƙarfafa kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu. Shugaba Emmanuel Macron ne ya sanar da haka, yana mai cewa daga yanzu ɓangarorin biyu za su gudanar da mu'amala ce irin ta ba ni gishiri in ba ka manda a maimakon bai Afirka tallafi kamar yadda ake yi a baya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
A ranar Talata ne ake kammala taron shugabannin ƙasashen Afirka da Faransa da ya gudana a birnin Nairobi ta ƙasar Kenya, wanda ya mayar da hankali kan hanyoyin ci gaban tattalin arziki da noma da samar da abinci ga jama'ar nahiyar. Yaƙin Iran na ɗaya daga cikin abubuwan da ake ganin na maida hannun agogo baya wajen magance ƙarancin abinci, musamman rufe mahsigin Hormuz da ake amfani da ita wajen safarar takin zamani. Kan haka ne Nura Ado Suleiman ya zanta da ministan noman Najeriya Sanata Abubakar Kyari a wurin wannan taro, inda kuma ya ce su na ƙoƙarin magance matsalar. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A jiya ne ake faro taron kwanaki biyu tsakanin Faransa da ƙasashen Afrika a birnin Nairobi, wanda shugaba Emmanuel Macron da takwaransa William Ruto ke jagoranta. Taron ya haɗa shugabannin ƙasashen Afrika, da Hamshaƙan ƴan Kasuwa, da sauran masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan nemawa nahiyar Afrika mafita wajen samun ci gaban Tattalin Arziƙi a fannonin da suka haɗa da, bunƙasa Masana'antu da Kimiyya da Fasaha da inganta Noma da Tsarin Kiwon Lafiya, da kuma samun wadatar makamashi. Danna alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar Nura Ado Suleiman da hadimin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Daniel Bwala.......
A ƙoƙarinta na ganin ta bunƙasa harkokin tattalin arzikinta, gwamnatin jihar Katsina ta ce ƙofofinta a buɗe suke ga masu zuba jari na ƙasashen ƙetare. A yayin wani taro na masu zuba jari da ya gudana a birnin Paris na Faransa, gwamnatin jihar Katsina ta ce akwai masu zuba jarin da suka nuna sha'awar zuba jari a ɓangaren noma da ma'adinai da kiwon lafiya a jihar. Domin jin irin matakan da suke ɗauka domin cimma wannan narasa, Khamis Saleh ya tattauna da mataimakin gwamnan jihar Kastina Malam Faruk Lawal Jobe. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Azima Bashir a wannan mako ya yi bita tare da bibiyar manyan labarai mafiya jan hankali a makon da mukayi bankwana da shi daga sassa daban-daban na duniya. Labarai mafiya jan hankali a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi shi ne naɗin sabon ministan tsaro Janar Christopher Musa mai ritaya bayan murabus ɗin bazata da Alhaji Badaru Abubakar ya yi daga kan kujerar bisa dalilai na rashin lafiya dai dai lokacin da matsalolin tsrao ke ci gaba da ta'azzara a wannan ƙasa. Sai kuma batun tantance ƙarin Jakadun da shugaba Tinubu ya miƙawa Majalisar dattijai kana mutuwar ɗan adawa Anicet Ekane can a Kamaru, yayinda aka ga yadda tattaunawa ta yi nisa da fatan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine tsakanin masu shiga tsakani, a gefe guda kuma aka ƙulla yarjejeniya mai cike da tarihi tsakanin Congo da Rwanda bisa jagorancin Amurka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Har yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar Kamaru sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka bayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya samu nasara. Shugaban 'yan adawa Issa Tchiroma Bakary da ya zo na biyu ya ƙi amincewa da sakamakon, inda ya buƙaci jama'a da su sake fitowa zanga zanga a ranakun litinin da Talata da kuma Laraba na makon gobe, yayin da a ɓangare ɗaya gwamnati ke barazanar ladabtar da duk wanda ya saɓa dokokin ƙasar, ciki harda shi Isa Tchiroma. Domin tattauna halin da ake ciki a ƙasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammadu Sani. Ku alatsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...
Shirin a wannan makon ya yi dubi ne kan zare sunan Najeriya da cibiyar da ke sanya idanu kan almundahanar kuɗaɗe da ɗaukar nauyin ta'addanci a duniya ta yi cikin baƙin kundinta. A makon da ya gabata ne, Cibiyar nan ta Yaƙi da Masu Safarar Kuɗi da Ɗaukar Nauyin Ta'addanci ta duniya (FATF), ta sanar da cire sunan Najeriya daga jerin ƙasashen da take ɗaukarsu a matsayin masu wanan ɗabi'a. Wannan mataki ba iya Najeriya ta shafa ba, harma da ƙasashen Burkina Faso da Afrika ta Kudu da ma Mozambique duk a nahiyar Afrika. Cibiyar wadda ke da hedikwata a birnin Paris na ƙasar Faransa, wadda ke gudanar da binciken kwakwaf kan yadda ake hada-hadar kuɗaɗe tsakananin ma'aikatun gwamnati da hukumomi ko kuma cibiyoyin gwamnati ta ce duk da cire waɗannan ƙasahe cikin baƙin littafinta, har yanzu za'a ci gaba da sanya idanu akan waɗannan ƙasashe. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba................
Daga cikin labarun da shirin 'Mu zagaya Duniya' tare da Nura Ado Sulaiman, ya waiwaya a wannan makon akwai halin da ake ciki a Zirin Gaza bayan yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin da aka samu nasarar ƙullawa tsakanin Isra'ila da Hamas.Shirin ya kuma waiwayi zaɓen shugabancin Kamaru wanda masu fashin baƙi ke ci gaba da tofa albarkacin bankinsu a kai. A najeriya kuma akwai waiwayen afuwar da shugaba Bola Tahmed Tinubu ya yi wa wasu mutane fiye da 170 Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...........
A ƙarshen wannan mako ne jama'ar ƙasar Kamaru za su kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, inda ƴan takara 10 ke neman shugabanci, cikin su harda shugaba Paul Biya dake neman wa'adi na 8. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammad Sani game da zaɓen. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawarsu...
A cikin wannan shirin da ke waiwaye kan mahimman labaran wannan makon, za ku ji cewa: Faransa ta jagoranci ƙarin gwamman ƙasashe wajen amincewa da Yankin Falasɗinu a mamtsayin ƙasa ‘Yantacciya a wani yunƙuri na Diflomasiya da ke zama ɗaya daga cikin mafiya girma da aka gani cikin shekaru da dama. Shirin zai kuma waiwayi jawaban wasu daga cikin shugabannin Nahiyar Afrika a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya. Najeriya ta yi fatali da rahoton Amurka da ya zargi mahukuntan ƙasar da gazawa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na aiwatar da ayyukan raya ƙasa da akw warewa maƙudan kuɗaɗe a kasafi duk shekara. Da dai sauran mahimman labarai.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasar Rasha ta yi rauni sosai a yaƙin da take gwabzawa da Ukraine. Macron ya bayyana haka ne a zantawa ta musamman da ya yi tashar talabijin ta France24 da Kuma RFI a gefen Babban Taron Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York, inda ya taɓo batutuwa da dama ciki har da amincewa da Palesdinu a matsayin ƙasa da daidai sauransu. Da farko dai Emmanuel Macron ya jinjina wa shugaba Amurka Donald Trump ne a game da ƙoƙarinsa don kawo ƙarshen rikicin Ukraine. Ku latsa alamar sauti don sauraron fassarar kalamansa...............
Shirin Al'adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la'akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama'ar gari ke tofa albarkacin bakunansu akan karramawar da wata Jami'a mai suna European-American University ta yi wa fitaccen mawaƙin siyasa a Najeriya Dauda Kahutu Rarara, wanda ta bai wa Digirin Girmamawa na Dakta. Reshen Jami'ar da bayanai a yanar gizo suka nuna cewar hedikwatarta na ƙasar Faransa ne ta yi bikin Karrama mawaƙi Raran ne a Abuja, ranar Asabar, 20 ga watan nan na Satumba, taron da ya samu halartar wasu fitattun mutane. Sai dai Kash! ‘yan sa'o'i bayan bikin da aka yi Jami'ar da ake alaƙanta da Turai da Amurka ta ce ba ta fa san zance ba, domin ba da yawunta aka miƙa wa fitaccen mawaƙin siyasar Digirin na Girmamawa ba, zalika dukkanin mutanen da suka yi iƙirarin alaƙanta kansu da ita ta barranta da su, domin sun yaudari mutane ne da sunanta domin samun damar karɓar na goro a huce. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Sabon firaministan Faransa Sebastien Lecornu ya karɓi ragamar tafiyar da mulkin daga hannun Francois Bayrou, wanda ƴan Majalisar dokokin ƙasar suka tsige a ranar Litinin ta gabata.Wannan dai shi ne Firaminista na 5 bayan da Emmanuel Macron ya karɓi ragamar mulki domin yin wa'adi na biyu, lamarin da ke nuni da cewa ƙasar na fama da rikici a fagen siyasa. Dr Mubarak Muhammad, mazauni Faransa kuma masani a game da salon siyasar ƙasar, ya bayyana wa Nura Ado Sulaiman mahangarsa a game da wannan batu. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu..................
Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya mayar da hankali ne a kan yadda aka fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a bana a manyan Lig-Lig na sassan nahiyar Turai. Manyan wasannin dai sun haɗa da na Firimiyar Ingila, La Ligar Spain, da kuma gasar Ligue 1 na ƙasar Faransa. Kamar yadda za a ji cikin shirin tare da Khamis Saleh, Liverpool ce ta fara buɗe sabuwar kakar wasa a Firimiyar Ingila inda ta lallasa Bournemouth da ƙwallaye 4-2.
A cikin shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon tare da Rukayya Abba Kabara ya waiwayi yadda gwamnatin jihar Katsina ta Najeriya, ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Radda ta tabbatar da mutuwar jami'an tsrao 130 a hannun yan ta'adda. Shirin ya kuma waiwayi yadda ƙasashen duniya ciki har da Faransa suka nuna gamsuwarsu da samar da ƴantacciyar ƙasar Falaɗinu, don tabbatuwar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.............
Shugaban Kamaru Paul Biya ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a karo na 8 yana mai shekaru 92 da haihuwa, inda ya yi iƙirarin cewa matasa da mata ne zai fi bai wa fifiko idan ya samu ya zarce. Wani saƙo da Biya mai shekaru 92 ya wallafa a shafinsa na Twitter ne ke sanar da wannan mataki wanda ya kawar da jita-jitar da ke nuna cewa shugaban a wannan karon bashi da sha'awar tsayawa takara don neman wa'adi na gaba. Fiye da shekaru 40 kenan Paul Biya ke jagorancin Kamaru kasancewarsa shugaba na biyu da ya jagoranci ƙasar tun bayan samun ƴancinta daga Faransa wato bayan murabus ɗin shugaba Amadou Ahidjo. Idan har Paul Biya ya yi nasarar lashe zaɓen da zai bashi damar sake yin shekaru 7 a karagar mulki, kenan shugaban mafi daɗewa kan mulki, zai tasamma shekaru 100 na rayuwarsa a karagar mulki karon farko da ake ganin irin hakan a tarihi. Shiga alamar sauti, domin sauraro cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.
Yayin da aka buɗe babban taro kan alkinta tekunan duniya a birnin Nice na Faransa, Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a sake rattaba hannu kan sabbin yarjejeniyoyi da za su mayar da hankali kan alkinta tekuna da kuma kare hallittun ƙarƙashin ruwa. To sai dai duk da kasancewar Nahiyar Africa yankin da yafi fama da matsalolin muhalli ciki har da gurgusowar tekun, da alama taron bai yiwa yankin tanadin komai ba. Kan haka muka tattauna da Dr Mustapha Zakari Karkarna. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Rukayya Abba Kabara................
Karon farko a tarihi, ƙungiyar Paris Saint Germain ta Farnasa ta yi nasarar lashe kofin gasar Zakarun Turai ta wannan kaka bayan da ta doke Inter Milan ta Italiya, inda ta zama ta biyu da ta taɓa cin wannan kofidaga Faransa. Wani abin lura a game da wannan wasa, shi yadda PSG ta lallasa abokiyar karawarta da ci 5 da banza.Me za ku ce a game da wannan nasara da PSG ta samu?Ko meye ra'ayoyinku a game da yadda gasar ta Zakarun Turai ta wannan kaka ta gudana?
Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya yi duba ne kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da aka yi a ƙarshen mako tsakanin PSG ta Faransa da kuma Inter Milan, inda PSG ta samu nasarar lashe gasar bayan da ta zazzaga wa Inter Milan ƙwallaye biyar. Wannan ne dai karon farko da PSG ta lashe wannan kofi, kuma karo na farko da wata ƙungiya daga Faransa ta lashe shi tun bayan Marseille a shekarar 1993.Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Khamis Saleh............
Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman, kamar kowannen mako kan yi bitar muhimman labaran da suka faru cikin makon da muke ban kwana da shi, kuma kamar kodayaushe a wannan karon wasu daga cikin labaran da ke ƙunshe a shirin sun ƙunshi ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Najeriya ya kai Jamhuriyar Nijar, wadda a karon farko kenan tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum da sojoji suka yi. A Najeriya shirin ya leƙa Filato aka samu hasarar ɗimbin rayuka, sakamakon hare-haren da aka kai a wasu yankunan jihar, a Najeriyar za a ji yadda wata shu'umar cuta ta janyowa manoman Tumatir hasarar ɗimbin amfanin gonar, sai kuma yadda ‘yan damfara suka yi awon gaba da sama da naira tiriliyan 1 a Najeriyar.A Sudan kuwa ƙungiyar bayar da agaji ta Redcross ce ta aƙalla mutane dubu 8000 suka bace a yakin kasar.Sai kuma Kenya inda aka cafke wasu mutane da ke shirin fasa kaurin dubban tururuwa zuwa ƙasashen ƙetare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tsoffin shugabannin Najeriya guda 2 wato Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari sun gurfana a wata kotun sasanta rikicin kwangilla domin bada ba'asi a kan soke kwangilar gina tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ministan Obasanjo ya bayar bada saninsa ba, da kuma kin biyan kudin sasanta matsalar da gwamnatin Buhari ta ki. Dangane da wannan dambarwa Bashir Ibrahim Idris ya tatauna da daya daga cikin dattawan kasar Alhaji Sule Ammani, Yarin Katsina.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyartattaunawar.
A ranar Asabar ce Faransa ta mika sansanin sojinta na biyu a kasar Chadi ga mahukuntan kasar a wani bangare na janye sojojinta a karshen watan Janairu.Kimanin sojoji Faransa 100 ne suka bar sansanin Abéché a ranar Asabar, kafin janye na Djamena su kusan 1000.A tattaunawarsa da Ibrahima Timbi Bah, Editan sashin Fulatanci na RFI, kwamandan dakarun Faransa a Afrika Janar Pascal Lanni ya yi karin haske kan ficewarsu daga Afirka.
Rundunar Tsaron Najeriya ta mayar da martani kan kalaman shugaban soji na Nijar, bisa zarge-zargen da ya yi kan ƙasar na cewa tana haɗa kai da Faransa domin yi mata maƙarƙashiya. Latsa alamar sauti domin sauraren ƙarin bayanin da kakakin rundunar tsaron Najeriya Birgediya Janar Tukur Gusau ya yi wa wakilinmu na Abuja Mohd.Sani Abubakar...
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleimaza ya mayar da hankali ne kan mayan labarai da suka fi ɗaukar hanhali a makon da muka yi bankwana da shi, masamman halin da ake ciki a Najeriya bayan da shugaban ƙasar ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.
Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan ta'azzarar cutar Tamowa ko kuma rashin sinadaran abinci mai gina jiki da ke addabar ƙananan yara a Najeriya, a wani yanayi da asusun UNICEF ke cewa duk yaro 1 cikin 3 na fama da matsalar ƙarancin abinci a ƙasar, wanda ke wakiltar kashi 37 cikin 100 na yawan yaran ƙasar ko kuma adadin yara miliyan 6. Duk da cewa tsawon lokaci wannan cuta ta ɗauka ta na addabar yara a Najeriyar, a wannan karon cutar ta tsananta a jihohin arewacin ƙasar wanda masana suka alaƙanta da matsaloli masu alaƙa da rashin tsaron da ya hana jama'a noma da kuma gushewar damunar bana da wuri, lamarin da ya ƙara yawan yaran da ke fama da cutar ta Tamowa ko kuma yunwa, dalilin da ya ja hankali ƙungiyoyin agaji da dama ciki har da ALIMA wato Alliance for International Medical Action ta Faransa wadda ke bayar da agajin lafiya a ƙasashe 13 ciki har da Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi dubi ne akan yadda aka gudanar da bikin bada kyautar Ballon d'Or ta shekarar 2024.
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami'o'i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.......
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Rukayya Abba Kabara ya taɓo halin da aka shiga a Najeriya bayan da mahukunta suka kara farashin man fetur, sai kuma taron Afirka da China da kuma sabon fraministan Faransa.
Wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da ke gudana a nan birnin Paris na tafiya yadda aka tsara, inda kawo yanzu an kammala wasu wasanni da dama wasu kuma ana daf da kammala su. 'Yan wasan tawagar kwallon kwando ta Mata ta Najeriya na ci gaba da fatan ganin a wannan karon ta samu nasarar tsallake matakin rukuni, ganin yadda suka dage wajen lashe wasansu na farko da Austrelia amma sai dai sunsha kashi a hannun Faransa a wasa na biyu inda a yanzu fatansu shine samun nasara a wasan da zasu yi da Kanada don tsallakawa matakin dab da na kusa da na karshe a wannan gasa.
Shirin duniya kamar yadda aka saba na duba manyan labaran da suka faru a sassan duniya A cikin shirin zaku ji cewa..............Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin janye biyan kudaden haraji kan wasu muhimman kayayyakin abinci da ta dage haramcin shigar da su kasar, don saƙaƙawa jama'a raɗaɗin tsadar raywar da suke ciki.Matakin sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar, Mali da kuma Burkina Faso na tabbatar da ballaewarsu daga ECOWAS ya tayar da hankalin kungiyar kasashen ta yammacin Afirka, a yayin da kwararru ke cigaba da bajakolin ra'ayoyinsu kan matakin.A Kenya kuwa, shugaban ƙasar William Ruto ne ya kori rankatakaf din ministocinsa sai fa ƙwaya biyu rak da ya bari, ‘yan kwanaki bayan zanga-zanga kan tsadar rayuwa da dubban matsasan kasar suka gudanar.Danna alamar saurare don jin gundarin shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
Nasarar lashe zagayen farko na zaɓen ‘yan majalisar Faransa da jam'iyyar RN ta masu ra'ayin riƙau ta samu da kashi 33 cikin 100 a ranar Lahadi, ya tayar da hankalin sauran jam'iyyu masu ra'ayoyin sassauci da na tsaka-tsaki bazama, waɗanda a yanzu haka suke laluben hanyar da za su bi domin hana jagorar masu zafin kishin ƙasar wato Marine Le Pen lashe zaɓen ‘yan majalisar zagaye na biyu da ke tafe a mako mai zuwa. Ko yaya masana ke kallon yanayin da siyasar Faransa ta samu kanta ciki? Da kuma dalilan da suka janyo hakan? Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya. Kuna iya latsa alamar sauti domin jin tattaunawar...
Cikunan ƴan siyasa sun ɗuri ruwa a Faransa, bayan da masu tsattsauran ra'ayi suka lashe sama da 33% na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shiga Majalisar Dokokin Ƙasar, tare da yiyuwar samun gagarumar nasara a zagaye na biyu na zaɓen da za a yi ranar Lahadi mai zuwa. Ana matuƙar nuna fargaba dangane da abin da zai faru matuƙar masu wannan ra'ayi suka samu rinjaye a majalisar, saboda tsauraran manufofinsu da suka haɗa da ƙyamar baƙi da kuma neman rage duk wani taimako da ake bai wa ƙasashe masu tasowa.Shin ko yaya kuke kallon wannan lamari da ke faruwa a fagen siyasar ƙasar ta Faransa?Wannan shi ne abin da shirin Ra'ayoyin Masu Saurare na wannan rana ya tattauna a kai.Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Gabanin taron da za a gudanar ranar Alhamis a birnin Paris don taimaka wa Afirka dangane da yadda za ta samar wa kanta da alluran rigakafin kariya daga wasu cututuka a wadace, tuni aka samu alƙawurran sama da Euro biliyan ɗaya daga ƙasashe da da kuma ƙungiyoyi daban daban a cewar fadar gwamnatin Faransa. Wadannan kuɗade za a yi amfani da su ne don tabbatar da cewa kamfanonin sarrafa magunguna sun samar da alluran rigakafin cututuka kamar Korona, Cholera da kuma zazzaɓin cizon sauro a cikin nahiyar.Shin me za ku ce a game da wannan tallafi na ƙasashen duniya zuwa ga nahiryar Afirka?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
Daga cikin labarun da shirin wannan makon ya ƙunsa akwai harin da wani matashi a Kano ya kaiwa Masallaci ta hanyar cinna masa wuta, wadda zuwa lokacin gabatar da wannan shiri aka tabbatar da salwantar rayukan mutane 15 daga cikin akalla 30 da ke cikin Masalacin. Shirin na kuma ɗauke da tattauna wa da tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, kan tuntubar junan da jiga-jigan jam'iyyun dawa suka fara yi a Najeriya, don kafa sabon ƙawancen da zai tunkari jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya. Fira Ministan Senegal ya bayyana rashin gamsuwarsa kan wanzuwar sansanin sojojin Faransa a Ƙasar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
Ƙasashen duniya da kuma ƙungiyoyi kaƙƙin aikin jarida da kuma ‘yancin bayyan ra'ayi, sun yi tir a game da matakin rufe wasu kafafen yaɗa labarai da gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta dauka. Baya ga kafafen yada labaran Faransa ciki har da RFI da kuma France24, matakin rufe kafafen yaɗa labaran ya shafi na Amurka, Birtaniya Faransa da dai sauransu domin kawai wallafa rahoton kungiyar HRW da ke zargin dakarun gwamnati da yi wa fararen hula kisan gilla.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkeen shirin.
A wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar. Shire-shiryen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci a watan Yuli mai zuwa sunyi nisa, domin dai rahotanni na nuna cewar an kammala tanadin kusan dukkanin inda za a gudanar da wadannan wasanni.Sai dai wani hanzari ba guda ba, duk da matakan da kasar ta Faransa ta dauka na tabbatar da tsaron ‘yan wasa da kuma na ‘yan kallo, bayanai na nuna cewar akwai alamun fuskantar barazanar tsaro a lokacin gasar.Wannan lamari dai ya biyo bayan harin ta'addancin da aka kai birnin Moscow wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 140.A lokacin wata zantawa da aka yi shugaban Faransa Emmanuel Macron a makon da ya gabata, ya ce babu shakka, akwai yuwuwar Rasha za ta kai hari a lokacin gasar da ke tafe.Kai hari a lokacin gasar OlympicsKai hari a yayi gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics a iya cewa ba sabon abu bane, domin a baya an sha samun irin hakan, wanda aka kai a shekarar 1972 a Munich da kuma a shekarar 1996 a Atlanta.Duk da cewa a cikin watan da ya gabata ministar Wasannin Faransa Amelie Oudea-Castera, ta ce a yanzu babu wata barazanar hare-haren ta'addanci da gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics ke fuskanta, sai dai wasu da dama na cewa barazanar abu ne da ke da alaka da rikicin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine da ya kwashe sama da shekaru biyu anayi, wanda kasashen duniya ciki harda Faransa ke goyonma Ukraine baya domin fafatawa da Rasha.Yadda gasar Olympics ke samar da hadin kaiIta dai wannan gasa ana ganinta a matsayin wata farfajiya ta samar da hadin kai, ganin yadda take hada dukkanin bangarorin duniya waje guda.Domin idan aka koma baya cikin tarihi, bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, gasar da aka gudanar ta shekarar 1952, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar.Ƴan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra'ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.To sai dai ana ganin cewa a wannan karon siyasa ta shiga cikin lamarin wanda ke kokarin kawo rarrabuwar kai.Martanin Rasha game da zargin kai hariTo sai dai a wani martani da Rasha ta maida game da kalaman Macron ta bakin mai magana da yawun fadar shugaban kasar Dmitry Peskov, ta ce zargin na Macron babu tushe a cikinsa kuma wani matakine na yada labaran kanzon kurege da kasashen yammaci ke yiwa Rasha.
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........
Daya daga cikin matsalolin da suka addabi nahiyar Turai a wannan lokaci, shine batun bakin haure, ganin yadda matasa daga nahiyar Afirka ke tafiya mai hadari cikin kwale kwale da zummar zuwa nahiyar, abinda ke kai ga rasa rayuka da dama. Dangane da wannan matsala da kuma matakan da magabata ke dauka wajen fadakar da al'umma illar irin wannan tafiya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sarkin Hausawa Turai Alhaji Sirajo Jankado a fadarsa da ke kasar Faransa, kuma ga yadda zantawar su ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu......
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a taron da ya gudana a ranar Asabar a Abuja sun yanke shawarar dage wani kaso mai yawa na takunkumin da aka kakabawa Nijar. Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, wadanda musamman suka juya wa Faransa baya, kuma suka matsa kusa da Rasha, sun hade a cikin kawancen kasashen Sahel (AES).Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
Rikicin siyasa ya barke a Senegal sakamakon dage zaben kasar da shugaba Macky Sall ya yi a karshen mako. Matakin ya haifar da zanga zanga da kuma arangama da 'yan sanda, yayin da kungiyoyi da manyan kasashen duniya irin su ECOWAS da AU da EU da kuma kasashen Faransa da Amurka suka bukaci daukar matakin gudanar da zaben kamar yadda dokar kasa ta tanada. Dangane da wannan rudanin siyasa da ya mamaye kasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Moussa Tchangari na kungiyar Alternative a Nijar
Kasar Rasha ta sanar da kulla sabuwar yarjejeniyar soji da Jamhuriyar Nijar, sakamakon ziyarar da tawagar gwamnatin sojin Nijar ta kai Moscow a karkashin jagorancin Firaminista Ali Mahamane Lamine Zein. Dangane da tasirin wannan yarjejeniyar da kuma yadda zai taimakawa Nijar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Dicko Abderrahmane na Jami'ar Zinder, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.....
Daga cikin labarun da Shirin ya kunsa akwai batun yadda yan ta'adda a Najeriya ke gina ramu suna boyewa, saboda barin wutar da suke sha daga sojojin kasar, sai kuma batun kammala ficewar sojojin Faransa a Nijer da dai sauran manyan labaran da suka hada da Burkina Faso, jamhuriyar Benin, yakin Isra'ila da Hamas, tare da dokar yan ci rani da Faransa ta amince da ita.
Majalisar dokokin Faransa ta amince da kudirin dokar da ke neman tsaurara dokokin bakin hauren da ke shiga kasar ciki har da masu neman mafaka, kudirin da bai samu tsallakewa Majalisa ba har sai da aka yi hadaka tsakanin Jam'iyyar shugaba Macron da ta masu tsattsauran ra'ayi karkashin jagorancin Marine Le Pen. Ita dai wannan doka za ta saukaka wa bakin-hauren da suke aiki a fannoni ko ma'aikatun da suke da karancin ‘yan kwadago, samun takardar izinin zama a Faransa, ko da ya ke a hannu guda kudurin zai kuma saukaka damar korar bakin a duk sanda aka so yin hakan, batun da ya sha bamban da ra'ayin jam'iyya mai shugabancin kasar.Tuni dai wasu ministocin gwamnatin ta Macron da daidaikun ‘yan jam'iyyarsa suka fara juya baya ga shugaban, kuma kan hakan ne muka tattauna da Dr Abba Sadiq mazaunin birnin Paris wanda ya yi mana karin haske kan dokar.
A yayin da wakilan kasashen ke kintsawa don zuwa gasar wasannin motsa jiki na Olympic da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa a shekara mai zuwa, shirin 'Duniyar Wasanni', ya kawo tarihin gasar, inda ya yada zango a Najeriya, wadda tawagar kwallon kafarta ta 'Dream Team' ta kasance ta farko a nahiyaar Afrika da ta lashe kofin kwallon kafa a gasar Olympiic a shekarar1996.Shirin ya samu damar tattaaunawa da wasu 'yan wasa da jami'ai da aaka dama da su a lokacin. TARIHIN GASAR WASANNI TA OLYMPICGasar motsa jiki ta Olympics an fara gudanar da ita ne a karni na 8 a kasar Girka, sai dai daga bisani aka dakatar da ita.Bayan dakatar da gasar na tsawon lokaci, a shekarar 1940, kwamitin shirya gasar Olympics na Duniya IOC ya zabi babban birnin kasar Finland Helsinki don gudanar da gasar, amma sai dai sanadiyar barkewar Yakin Duniya na 2 aka sake dakatar ita.Bayan kawo karshen yakin, a shekara ta 1946, IOC ya yanke shawarar sake farfado da harkar wasannin Olympics na zamani, inda aka fara gudanar da wasannin gasar a shekarar 1948 a birnin London na kasar Ingila, duk da cewa itama ta kasance kamar sauran kasashen Turai, ta na cikin yanayi na matsi, amma sai da aka sake gina birnin na London don gudanar da gasar wasannin Olympics.Fiye da 'yan wasa dubu 4 ne suka fafata a wasanni 136, sai dai ba a gayyaci kasashen Japan da Jamus ba, yayin da Tarayyar Soviet da aka gayyata ta kaurace wa gasar.Shekaru hudu bayan waccan gasar, birnin Helsinki na kasar Finland ta karbar bakuncin gasar, da aka yi wa lakabi da “gasa ta zamani”.An fara wasanni ne a ranar 19 ga Yuli zuwa 3 ga Agustan 1952, wannan gasa ta Olympics wacce ita ce karo na 15, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar bayan kammala yakin duniya na biyu.‘Yan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra'ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.Duk da cewar wannan gasar ba a farota da kasashen nahiyar Afrika ba, akwai wakilan nahiyar da suka shigo daga baya kuma suka nuna bajinta, musammanma a bangaren wasan kwallon kafa, inda a shekarar 1996 da kuma 2000 kasashen Najeriya da Kamaru suka taka rawar gani wajen lashe gasar.A shekarar 1996 ce Najeriya ta kafa tarihin samun nasarar lashe lambar zinari a bangaren kwallon kafar gasar, lamarin daya kara karfafawa sauran kasashen nahiyar gwiwa.A biyo mu a kashi na gaba don jin tagomashin da nahiyar Afrika ta samu a wannan gasa ta olympic.
Ministan kasuwancin Faransa, Olivier Brecht ya ziyarci Najeriya a makon jiya, domin tattauna yadda za'a bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu. Brecht shine ministan Faransa na 3 da ya ziyarci Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu. Shugabar Sashen Hausa ta Radio France International, Sophie Bouillon ta tattauna da ministan a kan dalilin zuwansa Najeriya da kuma yanayin dangantaka tsakanin kasashen biyu.Ku danna alamar sauti don sauraron fassarar zantawarsu.....
Yan majalisun dokokin Faransa sun bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta aiwatar da sauye sauye domin inganta dangantakar ta da kasashen Afirka, lura da yadda kasashen Rasha da China ke fadada karfin fada aji a yankin. Dangane da haka Abdoulaye Issa ya tattauna da Abba Seidick masanin siyasa,zamantakewar kasar Faransa.