POPULARITY
Hukumar kula da ilimin Firamare a Najeriya ta roƙi gwamnonin ƙasar da su yiwa Alla su je su karɓi naira biliyan 332 waɗanda yanzu haka ke ajje a Banki, domin inganta ilimi a jihohinsu. Shugabar hukumar Aisha Garba ta ce baya ga naira biliyan 65 da aka ware domin kai ɗaukin gaggawa, akwai kuma naira biliyan 267 da ke ajje domin amfanin jihohin. Dangane da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Muhammad Dukku, tsohon shugaban hukumar kula da ilimin Firamare a jihar Gombe ga kuma tattaunawarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.......
Hukumar zaɓen Najeriya ta gabatar da jerin sunayen ƴan takarar zaɓen shekara mai zuwa da takardun shaidar ilimin da suka mallaka. Bisa doka ana buƙatar duk mai sha'awar tsayawa takara ya gabatar da shaidar kammala karatun firamare kafin ya shiga a dama da shi, daga muƙamin Kansila zuwa shugaban ƙasa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barrister El-Zubair Abubakar, ga kuma yadda tattaunawar su ta kasance.
Duk da cewa an samu faɗuwar farashin ɗanyan man fetur a kasuwar duniya sakamakon sulhun tsakanin Amurka da Iran, amma har yanzu ana ci gaba da fama da tsadar wannan makamashi a mafi yawan ƙasashen duniya. A Najeriya tuni Hukumar kare masu amfani da kayan masarufi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa ko dai dillalan mai su karya farashi ko kuma ta ɗauki matakan ladaftarwa a kansu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Hukumar kwallon ƙafar Afrika ta sanar da ƙwace Kambun da Senegal ta lashe a gasar neman kofin nahiyar da aka kammala cikin watan Janairun da gabata tare da miƙa shi ga ƙasar Moroko. Wannan dai mataki ne da ya yi matuƙar girgizar masu shawar harkar ƙwallon ƙafa a sassan duniya, inda tuni Senegal a buƙaci a gudanar da bincike bisa zargin cewa akwai yiyuwar an bayar da rashawa ne don ƙwace wannan galaba. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Yusuf.
Hukumar kwallon ƙafar Afrika ta sanar da ƙwace Kambun da Senegal ta lashe a gasar neman kofin nahiyar da aka kammala cikin watan Janairun da gabata tare da miƙa shi A a hannun ƙasar Moroko. Wannan dai mataki ne da ya yi matuƙar girgizar masu shawar harkar ƙwallon ƙafa ba wai a nahiyar Afrika ba har da sauran sassan duniya. To sai tuni Senegal ta buƙaci a gudanar da bincike bisa zargin cewa akwai yiyuwar an bayar da rashawa ne don ƙwace wannan galaba. A game da wannan mataki ne Michael Kuduson ya zanta da Aliyu Awwal Ibrahim, Sakataren tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ƴan ƙasa da shekaru 20. Ga kuma zantawarsu. A latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar.
Shirin ‘Muhalinka Rayuwarka' a wannan makon ya yaɗa zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan hasashen ruwan sama da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya NIMET ta yi, gabanin kamawar daminar bana, inda ta bayyana cewa damina za ta sauka da wuri a jihohi irin su Kano da Niger da Rivers da wasu jihohi 12 na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..............
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za'a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki tsakanin kasashen biyu. Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi, ya sake jaddada aniyar Hukumar na sauƙaƙe cinikayya a yankin, ta hanyar saukaka jigilar kayayyaki da kuma haɓaka haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka da su, musamman Jamhuriyar Nijar. Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata, yayin wani babban taron haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam ta Najeriya da takwararta ta Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Muhammadu Yaqouba, da aka gudanar da hedikwatan Kwastam da ke Maitama a Abuja. Tawagar Nijar ta kunshi shugabannin cibiyar inganta kasuwanci na Nijar wato Chamber des Commerce. Cikin mahimman abubuwan da aka duba a ganawar akwai saukaka zirga-zirga a kayan a iyakokin kasashen biyu ciki harda jigilar man metur na kamfanin Dangote, hakazalika za'a bada damar wucewar wasu kayayyaki da suka makale a bodar Kamba na jihar Kebbi, tireloli 1,600, da suka kwashe sama da watanni 2. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
A wannan makon shirin zai yi dubi ne kan dokar ta baci a harkan lafiya da gwamnatin Najeriya ta kaddamar inda ta sanar da karuwar cutuka masu alaka da gurbatacciyar iskar da jama'ar ƙasar ke shaka. Hukumar duba gari ta Najeriya ko kuma Environmental Health Council a Turance ita ta sanar da wannan dokar ta baci inda tace munin cutukan dake alaka da numfashi da kuma cutar kansa dake karuwa yasa dole gwamnati da dauki tsauraran matakan, kamar yadda shugaban hukumar Dr Yakubu Muhammad Baba ke cewa. Gurbacewar iska a muhallin ɗan adam kan faru ta hanyoyi da dama kama daga yawaitar hayaƙin da motoci ke fitarwa da kone-konen dazuka ko ƙona itace a gidajen jama'a dama masana'antu da kan fitar da tiriri mai guba, wanda kuma kai tsaye ke cutar da lafiyar ɗan adam tare da haddasa cutuka ko ta'azzarar lalura masu fama da cutukan lumfashi, lamarin da ƙwararren likita Dr Lawal Musa Tahir ke cewa illar gurɓatacciyar iska ta wuce duk inda ake tunani. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........
Hukumar daidaita farashin wutar lantarki a Najeriya ta ce yanzu haka akwai sama da layuka milyan biyar da jama'a ke amfani da wuta ba tare da an ɗora su a kan mita ba. Wannan ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da ɗiga ayar tambaya dangane da dalilan da suka sa aka gaza samar da mitocin a wadace. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Shirin a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ake ƙara samun raguwar kayayyakin masrufi a Najeriya. Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, tace watanni biyar jere kenan, ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, inda tace an samu sauƙar farashin kayyaki a watan Agustan da ya wuce, da kaso 1 da ɗigo 76 cikin 100, wanda hakan ke nuna yadda aka samu sauƙi fiye da kaso 21.88 na watan Yuli, yayin da yanzu kuma ya koma kaso 20.12 cikin 100. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan makon ya na wannan makon tare da Nasiru Sani ya amsa tambayoyi da dama da suka hada da wada ke neman sanin dalilin kafa Hukumar Raya yankin Arewa Maso Yammcin Najeriya.
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce tattalin arzikin ƙasar ya samu ƙarin tagomashi da kashi 3 da ɗigo 13 a rubu'in farko na wannan shekarar ta 2025, saɓanin kashi 2 da ɗigo 27 yake a daidai wannan lokaci a shekarar 2024. Wannan na zuwa ne yayin da talauci ke ci gaba da ta'azzara a tsakanin al'ummar ƙasar, kuma manoma sun gaza yin noma yadda ya kamata saboda matsalar ta'addanci. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Kamar yadda akaji a farkon Shirin, Hukumar kula da ƴansanda a Najeriya ta gurfanar da manyan jami'ai sama da 150 a gaban kwamitin ladabtarwa, bisa zarginsu da wulakanta aikin ɗansanda da kuma take hakkoki fararen hula a wasu lokutan. Bayanai sun ce an baiwa kwamitin kwanaki 10 ya gama binciken ƴansanda masu muƙamin ASP zuwa sama, ya kuma gabatar da rahoto wanda zai baiwa hukumomi damar ɗaukar matakin hukunci a kansu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiya hirar.....
Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta Najeriya ta ce adadin mutanen da ‘yan ta'adda suka kashe a cikin watanni shidan farko na wannan shekara, ya zarce adadin da aka lissafa a shekarar bara. Ƙungiyar direbobin motocin dakon kaya a Senegal ta koka kan matsalolin tsaro da suka fara shafar yankunan kan iyakar ƙasarsu da Mali, inda ta yi barazar dakatar zirga-zirga zuwa Malin muddin mahukunta suka gaza ɗaukar matakan da suka ɗace. Kakakin majalisar dokokin Kenyan ya goyi bayan bai wa ‘yan sandan Umranin harbe duk mai zanga-zangar da aka samu yana satar dukiyar jama'a da lalata kayan gwammnati. A Amurka kuwa Ambaliyar ce ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 119 Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
Hukumar kula da jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya ta JAMB ta nemi gafarar jama'ar kasar saboda matsalolin da aka samu wajen jarabaswar bana, wadda ta kai ga dalibai sama da miliyan guda da rabi suka kasa samun makin da ake bukata. Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede cikin hawaye ya nemi gafarar jama'a da kuma daukar alhakin lamarin.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Umar Saleh Gwani masanin harkar sadarwa.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin TAMBAYA DA AMSA na wanan rana tareda Nasiru Sani, cigaba ne na tarihin Sarkin Musulmi Muhammed Bello da kuma wasu karin tambayoyi na masu sauraro suka aiko mana. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin....
A makon da ya gabata ne dai Hukumar Ƙwallonn Kafar Afirka CAF ta gudanar da zaɓenta, inda aka sake zabar Patrick Motsepe a matsayin shugaba a karo na biyu. Bayan haka ne aka gudanar da zaɓen wakilan nahiyar a Hukumar Ƙwalllon Ƙafa ta Duniya, FIFA, inda Afirka ke da wakilai 6, har da shugaban CAF mai kujerar kai-tsaye..
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda ake kara samun saukar farashin kayan masarufi a sassan Najeriya. Bayanai da muka tattaro na nuni da cewa yawancin kayayyakin da farashin su ya sauka na amfanin gona ne da kuma na kamfanonin kasashen waje, amma na kamfanonin cikin gida har yanzu suna nan a yadda suke.A makon jiya Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce an samu sauƙin matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a ƙasar da a ƙalla kashi 10.3.Cikin sanarwar da ta fitar a Talatar wancan makon, hukumar ta NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriyar ya sauka ne zuwa kashi 24.4 a watan Janairun wannan shekara, saɓanin kashi 34.8 da aka gani a watan Disambar shekarar bara ta 2024.
Hukumar Ƙayyade Farashin Wutatar Lantarki a Najeriya, sanar da sabon tsarin biyan tara a kan waɗanda ke satar makamashin lantarki a ƙasar. Tarar ta kama daga Naira dubu 100 zuwa dubu 300 daidai da irin salon da mutum ya yi wajen sada gidansa da wannan makamashi.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa a Najeriya, ta ce farashin kayan abinci ya sauka a cikin watan Janairun da ya gabata da 10% idan aka kwatanta da na wata Disamba. To waɗannan dai bayanai da hukuma ta fitar, saboda haka za mu so jin ra'ayoyinku a game da wannan rahoto.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Abida Shu'abu Baraza...
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce an samu sauƙin matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a ƙasar da a ƙalla kashi 10.3. Cikin sanarwar da ta fitar a jiya Talata, hukumar NBS ɗin ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriyar ya sauka zuwa kashi 24.4 a watan Janairun wannan shekara, saɓanin kashi 34.8 a watan Disambar shekarar bara ta 2024. Domin jin halin da ake ciki....la'akari da wannan rahoto, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Musa Idris daga jihar Jigawa, magidanci kuma ɗan kasuwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..........
SHirin na wannan ya mayar da hankali ne akan ƙarin kuɗin kira da damar shi internet wato Data, da kmafnonin sadarwa suka yi a Nijeriya. Bayan da Hukumar dake kula da kamfanonin sadarwa NCC ya amince. Sai a latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.
Kamar yadda labari ya karaɗe kafafen yada labarai, ƙaasa da mako guda bayan da hukumar kwastan a Najeriya ta sanar da buɗe shafin yanar gizo don aikewa da takardun neman ɗaukar jami'ai kimanin dubu 4, sama da masu neman wannan aiki dubu dari 5 ne suka gabatar da buƙatunsu. Wannan al'amari ne da ke faruwa a kowace ma'aikata a duk lokacin da aka sanar da buƙatar ɗaukar ma'aikata.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza.
Shirin Duniyar Wassani a wannan makon ya yi duba ne game da kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika da aka bayar. A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Hukumar da ke kula da kwallon ƙafar nahiyar Afrika wato CAF, ta bayar da kyautar gwarzon nahiyar Afrika wanda yafi bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita. Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Najeriya Ademola Lookman ne ya samu nasarar lashe wannan kyauta, biyo bayan irin bajintar da ya nuna ga ƙasar da kuma ƙungiyarsa ta Atlanta. Samun nasarar lashe wannan kyauta da ɗan wasan yayi dai ta sanya zamowa cikin jerin ƴan wasa 6 na Najeriya da a tarihi suka taɓa lashe ta.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh........
Hukumar da ke kula da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta UNESCO ta damƙawa Najeriya takaddar shaidar sanya bikin hawan Daba na Kano cikin manyan al'adun duniya masu matukar tasiri. Jim kaɗan bayan kammala miƙa shaidar wakilinmu a Abuja Isma'il Karatu Abdullahi ya tattanna da ministar al'adu ta Najeriya Hajiya Hannatu Musawa kan tasirin da wannan zai yi wa ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar ta su......
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Nura Ado Sulaiman kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata, ciki kuwa har da batun yadda Hukumar Kula da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta sanya hawan Dabar jihar Kano dake Najeriya cikin manyan Al'adun Duniya masu dimbin Tarihi.Da kuma sauran rahotanni da suka gabata.Sai a latsa alamar sauti domin samun cikakken shirin.
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 3.46 a rubu'i na uku na wannan shekarar ta 2024, wato tsakanin watan Yuli zuwa Satumba. A rahoton da ta fitar ranar Litinin, NBS ta ce yawan masara aikin yi ma ya ragu a Najeriya. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dr Kasum Garba Kurfi.
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Nigeria. Wannan dai wani bangare ne na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon ƙafa a Nigeria, tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles na ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon kafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira Football Academy, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya.Pascal Patrick, tsohon ɗan wasan Super Eagles kuma shugaban Hukumar kwallon kafa ta NFA a jihar Bauchi kana co-odinetan tawagar Super Eagles na Nigeria, na daya daga cikin tsofaffin ƴan wasan ƙasar da suka kafa irin wannan cibiya a jihar Bauchi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka' da ke nazari kan abin da ya shafi muhallli, canjin yanayi, noma da kiwo, ya yi tattaki zuwa Kamaru, inda ya duba shirin tallafa wa manoma wajen noman dawa mai jure fari da kasa mara kyau. Hukumar kula da samar da albarkatun gona a arewacin Kamaru IRAD ce ke jagorantar aiwatar da shirin na sake fasalin bunkasa noman dawa 'yar rani, wato moskowari.
A dai-dai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiyen wasannin sharen fagen samun gurbi a gasar lashe kofin Afrika, Hukumar Kula Ƙwallon kafar Afrika CAF ta ce filayen wasan ƙasar Ghana ba su da ingancin da ya kamata a ce an gudanar da manyan wasanni na kasa da kasa a cikin, matakin da ke kara nuna gazawar ƙasar. Ita dai hukumar CAF ta ce ba komai ya sanyata daukar wannan mataki ba, face yadda ta ce aƙwai rashin wadatatciyar ciyawa da rashin magudanun ruwa da dai sauransu a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi, haka ta ce abin ya ke a sauran filayen wasanni irin na Cape Coast da kuma na Accra.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasashen Afirka ta Yamma, wato GIABA ta shirya wani taron fadakar da 'yan kasuwa da masu masana'antu da kuma lauyoyi a kan hakkin da ya rataya a kansu na kin bada dama ga masu halarta kudaden haramun ko kuma 'yan ta'adad su yi amfani da su wajen boye kudaden sata. Taron na kwanaki 2 na gudana ne a birnin Lagos. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mai magana da yawun GIABA Mr Timothy Melaye, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Shirin namu na wannan mako zai yi dubi ne kan yadda hukumar kula da harkar jarabawan shiga jami'o'i a Najeriya wato JAMB da hadin guiwan kungiyar zabiya na kasa ta shirya taron nahiyar Afrika na farko kan baiwa nakasassu ko masu larura ta musamman dangane da harkar ilimi kamar kowani dan adam. Taron an shirya shi ne dai la'akari da irin kalubalen da masu larura ta musamman ke fama da ita a kasashe masu tasowa kamar Najeriya,kama daga kyama,nuna musu banbanci da dai sauransu.
Hukumar tara kudaden haraji a Najeriya tace masu masana'antu a kasar sun yi asarar kudin da ya kai kusan naira triliyan 2 bara sakamakon faduwar darajar naira. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar kididdiga ta kasar ke cewa ma'aikata dubu 30 ne suka rasa ayyukansu saboda durkushewar ma'aikatun da suke aiki. Dangane da wanan labarai mai tada hankali, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ahaji Ali Madugu, mataimakin shugaban kungiyar masu masana'antu a Najeriya. Kuna iya latsa alamar sauti domin jin yadda zantawar ta su ta gudana...
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana. Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai.Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.
Hukumar Yaƙi da Cututuka Masu Saurin Yaɗuwa a Najeriya, ta ce kawo yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar Amai da gudawa wato Cholera sun kai dubu 1 da 579, kuma tuni 54 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya. Hukumar ta yi gargaɗi ga jama'a da su kiyaye ta hanyar ɗaukar matakan kariya, domin kuwa tuni cutar ta shiga jihohi 32 na ƙasar.Waɗanne irin matakai mahukunta ke ɗauka a yankunanku domin hana yaɗuwar wannan cuta?A naku ɓangare, waɗanne matakai ku ke ɗauka domin kare kanku?Kuri ka aiko mana da ra'ayoyinku a lambarmu ta WhatsApp +234 70 66 35 66 41 da kuma shafinmu na Facebook.
Shirin 'Tambaya Da Amsa' wanda ya ke zuwa duk mako a wannan tasha zai amsa tambayar da ke neman bayanni a kan ayyukan Hukumar Lafiya ta Duniya,,musamma inda take samun kuɗaɗen gudanar da ayyukanta da kuma yadda taa ke ɗaukar ma'ikata.
Daga cikin labarun da shirin karshen makon ya waiwaya akwai neman tsohon gwamnan jihar Kogi yahya Bello da hukumar EFCC ke yi ruwa a jallo, lamarin da ya kai ga daukar matakin dakile duk wani yunkurinsa na ficewa daga Najeriya Shirin ya kuma leƙa gabas ta tsakiya inda Iran ta ƙi fusata kan makamai masu linzamin da na'urorin tsaron sararin samaniyarta suka kakkaɓo a birnin Isfahan, waɗanda wasu majiyoyi suka ce Isra'ila ce ta yi yunkurin kai mata hari da su.
‘Tambaya Da Amsa' shiri ne da ke kawo amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Bayan janye tallafin lantarki a Najeriya, hukumar samar da wutar ta yi bayani game da rukunnai dabam dabam na masu amfani da wuta da abin da za su biya a matsayin kudin wuta. A yi mun ƙarin bayani a kan wadannan rukunnai. Menene ya sa dole sai an kasa al'umma zuwa rukuni -rukuni?
Hukumar alhazai a Najeriya, ta sanar da karin kusan Naira milyan biyu a kan kujerar aikin hajjin bana ga maniyatan da suka riga suka zuba kudadensu. Wannan dai mataki ne da ya yi matukar bai wa jama'a mamaki, tare da kara haifar da fargar cewa dubban maniyata ba za su iya sauke faralin na shekarar bana ba.Abin tambayar shine, wane tasiri wannan mataki zai yi a kan maniyatan Najeriya na shekarar bana?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
A wannan Juma'a ake kammala yakin neman zaben shugaban Senegal, kasar da rikicin siyasa da ya auku a cikinta a baya-bayan nan ya gaza yin mummunan tasiri a kanta duk kuwa da jan hankalin duniya da lamarin ya yi. Hukumar zaben kasar ta ce kimanin mutane miliyan 7 ne suka yi rajistar kada kuri'a a zaben da ‘yan takara 19 suka raba rana.Masu sharhi da dama sun lura da yadda duk da rikice-rikicen siyasa da suka taso ba a samu wani tashin hankali da ya taka wa shirin zaben birki ba.Kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Dakta Mukhtar Bello, malami a bangaren kimiyyar siyasa a jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyarta ta samar da hukumar da zata dinga daidaita farashin kayan masarufi kamar yadda aka saba yi a shekarun baya, wanda ake kira 'Commodity Board', sakamakon kiraye kirayen 'yan kasar ganin yadda 'yan kasuwa ke cin karen su babu babbaka. Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya sanar da haka wajen wani taro a Abuja. Dangane da tasirin wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar noma, Farfesa Mohammed Khalid Othman na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Shirin wannan mako zai yi dubi ne yadda Hukumar da ke kula da harkokin hasashen yanayi ta Nigeria, ta yi hasashen samun wani gagarumin sauyin yanayi a yankunan arewa maso gabas da arewa ta tsakiya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa. Bugu da kari hukumar, ta bayyana cewa shima yankin kudancin Nigeria zai shiga yanayi na zafin rana da wasu alamun hadari, kana yankunan da ke kusa da ruwa, za su shiga yanayi na hazo da ganin alamun hadari. Jihohin kudancin Nigeria irin su Lagos, Delta, Rivers da Bayelsa, ana sa ran samun yanayin hadari da tsawa a wadannan kwanaki.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani ............
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sake bude wani sabon babin bincike a kan wasu tsoffin gwamnoni da ministoci 13 da take zargi da aikata laifukan almundahana na sama da naira biliyan 853 da miliyan 800. Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da gwamnatin kasar ta dakatar da wata minister da aka zarga da karkata akalar wasu makudan kudade, tare da kaddamar da bincike a kanta.A kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Awwal Musa Rafsanjani n kungiyar farar hula ta CISLAC a Najeriya.
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya reshen shiyar Arewa maso yamma, ta ce mutane 85 ne suka rasa ransu a harin bom din da sojoji suka kai, sannan akwai wasu 66 da ke samun kulawa a asibiti. Mafi yawan wadanda lamarin ya shafa dai mata ne da kananan yara da kuma dattijai a lokacin da suke gudanar da Mauludi, a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi da ke Jahar Kaduna.'Yan Najeriya na ci gaba da cece-kuce kan wannan ibtila'i da ba wannan ne karon farko da yake faruwa akan fararen hula ba.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa a kan yadda kotuna ke karbe hurumin da kundin tsarin mulki ya bai wa Hukumar zabe na bayyana wadanda suka samu nasarar zabubbukan da jama'a suka yi, wajen bayyana wasu daban a matsayin halartattun wadanda suka yi nasara. Wannan ya biyo bayan yadda kotunan suka sauya sunayen wadanda hukumar zabe ta sanar sun samu nasara a zabbubukan gwamnoni da kuma ‘yan majalisun kasar. Ko a wannan mako, kotuna sun soke zabubbukan gwamnonin Zamfara da Kano, yayin suka tabbatar da na jihohin Lagos da Bauchi. Dangane da wannan korafi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Naja'atu Muhammad, ‘yar siyasa, kuma mai sharhi akan harkokin Najeriya.Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Hukumar Kula da Gidajen Gyara Halinka a Najeriya, ta ce akalla fursunoni dubu 5 ne aka yanke wa hukuncin kisa, abin da suke jira kawai shi ne zartarwa. Hukumar ta ce an gaza zartar da hukuncin ne saboda rashin samun sahlaewar gwamnonin jihohi ko kuma wasu hukumomi da ke da alhakin rattaba hannu kafin zartarwar. Shin yaya kuke fatan ganin an bullo wa wannan lamari domin rage cunkoson gidajen yari a Najeriya? Shin ko kuna goyon bayan aiwatar da hukuncin kisa a kasashenku ko kuma sauya irin wannan hukunci zuwa na dauri? Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayiyin jama'a a kan wannan maudu'in.
Hukumar da ke kula da kwallon kafa a Najeriya ta NFF ta dakatar da wasu alkalan wasan da ke busa gasar firimiya league su 14 daga aiki, saboda abinda ta kira kura kuran da suka tafka wajen gudanar da alkalancin wasannin da ke gudana a wannan kaka. Irin wadannan kura kurai na daga cikin dalilan da suka saka hukumar kwallon kafa ta Afirka wato CAF kan tsallake alkalan wasan Najeriya lokacin zabo wadanda za su busa wasannin Afirka. Ko gasar da za a gudanar a Abidjan shekara mai zuwa, babu alkalin wasa koda guda daga Najeriya. A kan wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban alkalan wasan Najeriya, Malam Zubairu Sani.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu....
Hukumar kula da hasashen yanayi ta tarayyar Nigeria NIMET, ta ankarar da mazauna wasu jihohin arewacin kasar dangane da mamakon ruwan saman da ake sa-ran zubawa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa. A cewar hukumar, wacce kan yi hasashen yadda yanayi zai kasance a kasar, tuni na'urorinta suka hango alamomin tsawa da walkiya a yankunan jihohin Borno, Taraba, Gombe, Bauchi da kuma Kano.Wannan hasashe na zuwa ne yayinda har yanzu, wasu al'ummomin kasar, ba su gama farfadowa daga barnar da ambaliya ta yi musu a daminar bara ba.
Kamar yadda aka saba, shirin 'Tambaya Da Amsa' tare da Michael Kuduson na zuwa muku ne duk mako da amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Daga cikin taambayoyin da aka amsa a shirin wannan makon, har da karin bayani kan yadda hukumar kididdiga ke aikinta masamman na tattara farashi.
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce sun fara tattaunawa da mahukuntan kasar Masar a birnin Alkahira, kan yadda za a kwaso daliban kasar daga Sudan, yayin da bangarori biyu ke ci gaba da gwabza yaki a kasar da ke Gabashin Afirka. Wannan ya zo ne, bayan da dubban dalibai 'yan Najeriyar da ke karatu a Sudan suka mika koken su ga gwamnatin kasar, game da mummunan yanayin da suke ciki, saboda tashe-tashen hankula a Khartoum, babban birnin ƙasar.Sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF sun shafe sama da mako guda suna rikici da juna, lamarin da ya jefa fararen hula da dama cikin mummunan yanayi.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Shamsiyya Haruna ta gabatar.