POPULARITY
Shiri ne da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma a kowane mako yake zuwa muku a daidai wannan lokaci.A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku ƙarin haske ne akan Salam sashin Hausa na RFI wai ko akwai bambanci tsakanin aikin Kotun ICC da Kotun ICJ idan akwai shi mine ne kuma a wasu kasashe ne kotunan suke sannan a wasu shekaru ne aka samar da su. Sannan akwai tambayar dake neman karin bayani dangaen da tasirin dumamar yanya ga halittu.
A babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya kuwa, shugaban Senegal ne ya ɓare kwamitin tsaron majalisar, a bisa yadda yake gaza ɗaukar matakan warware matsalolin tsaron da ke haddasa hasarar rayukan da ɗimbin duniya a yankin Sahel.
Kamar yadda wata kila kuka ji a cikin labaran duniya, Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambassada Yusuf Tuggar ya bayyana manyan dalilan da ya kamata a yi dubi da su domin sanya kasar a matsayin mambar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. Shugaban Sashen Hausa na RFI, Mr Joseph Penney ya tattauna da ministan a zauren Majalisar dake ci gaba da gudanar da taronta a New York ta kasar Amurka, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Kasashen duniya sun fara mayar da martani dangane da kazamin hare haren da Isra'ila ke kai wa a yankin kudancin Lebanon wanda a jiya kawai ya kai ga hallaka mutane kusan 300. Cikin wadanda suka bayyana damuwa da yadda yakin Isra'ilar ke fadada har da Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres. Dangane da wannan yaki Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulhakeem Garba Funtua na Babbar Kwalejin Fasaha dake Kaduna, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Yau ake fara taron babban zauren Majalisar dinkin duniya karo na 79, wanda ake saran ya gudanar da mahawara a kan batutuwa da dama cikin su harda sabon daftarin majalisar wanda ya kunshi sauyin yanayi da rikice rikice da matsalar sauyin yanayi da rashin shugabanci na gari tare da matsalar yunwa. Dangane da wannan taro Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Abubakar Chika, tsohon jakadan Najeriya a kasar Iran, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Wani binciken haɗin gwuiwa da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a Najeriya tare da Cibiyar MacArthur Foundation da kuma Ofishin Ma'aikatar Harkokin Wajen Denmark ya daɗa fito da matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar tare da gabatar da likitoci da nas-nas da kuma unguwarzoma a matsayin waɗanda ke sahun gaba a karbar cin hanci, kafin ma'aikatan wutar lantarki da kuma ƴan sanda tare da malaman jami'oi A kan wannan batu ne, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan MacArthur Foundation, daya daga cikin waɗanda suka gudanar da binciken.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawarsu.
Shirin Mu zagaya duniya bisa al'ada kan yi bitar muhimman labaran da suka gudana a makon jiya, a wannan makon shirin tare da Nasrudden Muhammad, ya duba kan dambarwar yajin aikin NLC a Najeriya sai kuma yadda Jam'iyyar ANC a Afrika ta kudu ke laluben kafa gwamnatin haɗaka. Duk dai a cikin shirin za kuma kuji yadda ta ke ci gaba da kayawa a Gaza, bayan da Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare sassan Rafah ciki har da makarantar da ke ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya.Waɗannan da ma sauran muhimman labarai na ƙunshe a cikin shirin.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin..
Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a game da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC da batun sammacin kama firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da wasu shugabannin ƙungiyar Hamas. Ku latsa alamar sautin donjin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.........
Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma'aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin. Sakamakon wannan biki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Umar Pate, shugaban Jami'ar Kashere, kuma shehun malami a bangaren horar da ‘yan jarida a Najeriya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
A wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar. Shire-shiryen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci a watan Yuli mai zuwa sunyi nisa, domin dai rahotanni na nuna cewar an kammala tanadin kusan dukkanin inda za a gudanar da wadannan wasanni.Sai dai wani hanzari ba guda ba, duk da matakan da kasar ta Faransa ta dauka na tabbatar da tsaron ‘yan wasa da kuma na ‘yan kallo, bayanai na nuna cewar akwai alamun fuskantar barazanar tsaro a lokacin gasar.Wannan lamari dai ya biyo bayan harin ta'addancin da aka kai birnin Moscow wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 140.A lokacin wata zantawa da aka yi shugaban Faransa Emmanuel Macron a makon da ya gabata, ya ce babu shakka, akwai yuwuwar Rasha za ta kai hari a lokacin gasar da ke tafe.Kai hari a lokacin gasar OlympicsKai hari a yayi gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics a iya cewa ba sabon abu bane, domin a baya an sha samun irin hakan, wanda aka kai a shekarar 1972 a Munich da kuma a shekarar 1996 a Atlanta.Duk da cewa a cikin watan da ya gabata ministar Wasannin Faransa Amelie Oudea-Castera, ta ce a yanzu babu wata barazanar hare-haren ta'addanci da gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics ke fuskanta, sai dai wasu da dama na cewa barazanar abu ne da ke da alaka da rikicin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine da ya kwashe sama da shekaru biyu anayi, wanda kasashen duniya ciki harda Faransa ke goyonma Ukraine baya domin fafatawa da Rasha.Yadda gasar Olympics ke samar da hadin kaiIta dai wannan gasa ana ganinta a matsayin wata farfajiya ta samar da hadin kai, ganin yadda take hada dukkanin bangarorin duniya waje guda.Domin idan aka koma baya cikin tarihi, bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, gasar da aka gudanar ta shekarar 1952, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar.Ƴan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra'ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.To sai dai ana ganin cewa a wannan karon siyasa ta shiga cikin lamarin wanda ke kokarin kawo rarrabuwar kai.Martanin Rasha game da zargin kai hariTo sai dai a wani martani da Rasha ta maida game da kalaman Macron ta bakin mai magana da yawun fadar shugaban kasar Dmitry Peskov, ta ce zargin na Macron babu tushe a cikinsa kuma wani matakine na yada labaran kanzon kurege da kasashen yammaci ke yiwa Rasha.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce shekarar da ta gabata ita ce mafi zafi da duniya ta gani, sai dai ta yi gargadin cewa 2024 za ta fi bara muni. A wani rahoton shekara-shekara da Majalisar ta fitar, ta ce dukannin binciken da ta gudanar ya nuna cewa 2023 itace mafi zafi a tarihin duniya.Rahoton binciken ya kuma ce shekaru biyun da suka gabata, sune mafi tsananin zafi cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da ake fargabar zafin zai ci gaba da tsananta a bana.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasirudden Muhammad.
Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar mata da ke da aniyar lalubo matsalolin da mata ke fuskanta da kuma duba hanyoyin warware su. Bikin ranar na bana dai ya zo ne a dai-dai lokacin da mata ke fuskantar matsin rayuwa sanadin tashe-tashen hankula da kuma tsananin talauci.Kan bikin wannan rana, Michael Kuduson ya tattauna da Saudatu Abubakar Kabir, shugabar mujallar Muryar Matan Afirka.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A yayin da wakilan kasashen ke kintsawa don zuwa gasar wasannin motsa jiki na Olympic da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa a shekara mai zuwa, shirin 'Duniyar Wasanni', ya kawo tarihin gasar, inda ya yada zango a Najeriya, wadda tawagar kwallon kafarta ta 'Dream Team' ta kasance ta farko a nahiyaar Afrika da ta lashe kofin kwallon kafa a gasar Olympiic a shekarar1996.Shirin ya samu damar tattaaunawa da wasu 'yan wasa da jami'ai da aaka dama da su a lokacin. TARIHIN GASAR WASANNI TA OLYMPICGasar motsa jiki ta Olympics an fara gudanar da ita ne a karni na 8 a kasar Girka, sai dai daga bisani aka dakatar da ita.Bayan dakatar da gasar na tsawon lokaci, a shekarar 1940, kwamitin shirya gasar Olympics na Duniya IOC ya zabi babban birnin kasar Finland Helsinki don gudanar da gasar, amma sai dai sanadiyar barkewar Yakin Duniya na 2 aka sake dakatar ita.Bayan kawo karshen yakin, a shekara ta 1946, IOC ya yanke shawarar sake farfado da harkar wasannin Olympics na zamani, inda aka fara gudanar da wasannin gasar a shekarar 1948 a birnin London na kasar Ingila, duk da cewa itama ta kasance kamar sauran kasashen Turai, ta na cikin yanayi na matsi, amma sai da aka sake gina birnin na London don gudanar da gasar wasannin Olympics.Fiye da 'yan wasa dubu 4 ne suka fafata a wasanni 136, sai dai ba a gayyaci kasashen Japan da Jamus ba, yayin da Tarayyar Soviet da aka gayyata ta kaurace wa gasar.Shekaru hudu bayan waccan gasar, birnin Helsinki na kasar Finland ta karbar bakuncin gasar, da aka yi wa lakabi da “gasa ta zamani”.An fara wasanni ne a ranar 19 ga Yuli zuwa 3 ga Agustan 1952, wannan gasa ta Olympics wacce ita ce karo na 15, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar bayan kammala yakin duniya na biyu.‘Yan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra'ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.Duk da cewar wannan gasar ba a farota da kasashen nahiyar Afrika ba, akwai wakilan nahiyar da suka shigo daga baya kuma suka nuna bajinta, musammanma a bangaren wasan kwallon kafa, inda a shekarar 1996 da kuma 2000 kasashen Najeriya da Kamaru suka taka rawar gani wajen lashe gasar.A shekarar 1996 ce Najeriya ta kafa tarihin samun nasarar lashe lambar zinari a bangaren kwallon kafar gasar, lamarin daya kara karfafawa sauran kasashen nahiyar gwiwa.A biyo mu a kashi na gaba don jin tagomashin da nahiyar Afrika ta samu a wannan gasa ta olympic.
Majalisar dinkin duniya ta bi sahun kungiyoyi da daidaikun jama'ar dake gabatar da bukatar gudanar da bincike na gaskiya a kan kisan gillar da aka yiwa mutanen kauyen Tudun Biri a Najeriya, sakamakon harin sama da sojoji suka kai wanda yayi sanaduyar salwantar rayukan mutane da dama. Ko a jiya sanda aka gudanar da zanga zangar lumana a Abuja da kuma Zaria domin kara matsin lamba ga gwamnati. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Naja'atu Muhammad, mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Najeriya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Kungiyar agaji ta OXFAM ta bayyana farin cikin ta da nasarar da aka samu wajen kafa asusun da manyan kasashen duniya zasu zuba kudade, domin tallafawa kasashe masu tasowa dake fuskantar matsalar sauyin yanayi. Wannan mataki ya biyo vayan amincewar da wakilan kasashe sama da 175 suka cimma a wajen taron sauyin yanayin Majalisar dinkin duniyar dake gudana a Dubai. Bashir Ibrahim Idris ya tatatuna da Daraktar kungiyar dake kula da nahiyar Afirka, Fati Nzi Hassan.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A yayin taron yanayi na 27 wanda Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a shekarar da ta gabata, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tashi ta sanar wa duniya cewa za ta dauki matasa masu jini a jika aikin dashen itatuwa har dubu dari 2 da 50 a duk shekara, a shirin da take na daukar mataki a game da sauyin yanayi. Shekara guda bayan wannan alwashi na gwamnatin Najeriya, bincike ya nuna cewa kusan an jefa wannan shiri a kwandon shara, a yayin da ya rage ‘yan kwanaki a bude taron yanayi na 28 da aka wa lakabi da COP 28.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin
Shirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan mako kaamar kowane mako, ya kawo muku tambayoyi ne da masu sauronmu suka aiko mana, inda ya samar da amsoshinsu daidai gwargwadon iko. Daga cikin tambayoyin da muka amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin yadda aka yi wasu kebabbun kasashe suka samu "kujerar naki' a Kwamitin Tsaro nna Majalisar Dinkin Duniya.
Yanzu haka wakilan kasashe 175 na Nairobi dake kasar Kenya, inda suke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a kan yadda za'a magance matsalar sharar robobi da suka addabi bil Adama wajen toshe magudanan ruwa da mamaye tafkuna da teku tare da yiwa jama'a da dabbobi illa. Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin manyan kasashen dake sarrafa robobin da wadanda ke shan radadin matsalar. Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar muhalli, Malam Marwan Yakasai, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
A daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke ci gaba da janye dakarunta na MINUSMA daga kasar Mali, bayanai na nuni da cewa fada ya sake barkewa tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyin ‘yan tawayen arewacin kasar da ke fafutukar kafa kasar Azawad. Shi dai wannan fada ya fi yin kamari ne a zagayen birnin Kidal da ke karkashin mamayar ‘yan tawayen yau fiye da shekaru 10. Shin me za ku ce a game da wannan rikici da ya kunno kai a Mali yayin da a wani bangare kasar ke fama da kungiyoyin masu da'awar jihadi? Me za ku ce dangane da shirun kasashen duniya a daidai lokacin da kasar ke neman sake tsunduma cikin sabon yaki?Ku latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta.
Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci a gaggauta tsagaita wuta a Zirin Gaza, tare da gargadin cewa lokaci na kurewa kasashe kan bukatar dakile yi wa Falasdinawa kisan kare dangi a yankin na Gaza. Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Filpipo Grandi ya bukaci mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar da su kawo karshen rarrabuwar kawunan da ke tsakaninsu, don tabbatar da an tsagaita wutar da za ta dakatar da salwantar rayukan Falasdinawa a Zirin Gaza.
Kwanaki 26 bayan barkewar yakin dake ci gaba da gudana ba tare da kaukautawa ba tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 10, ana fargabar yakin na iya fadada musamman ganin yadda kungiyoyi irin su Hezbollah da Houthi suka fara harba makamai a kan Israila. Masana na bayyana cewar ganin yadda Majalisar Dinkin Duniya kuma kasashen dake da karfin fada aji suka gaza samar da Shirin tsagaita wuta, yakin na iya daukan dogon lokaci. A kan haka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Bashir Nuhu Mabai na Jami'ar Dutsinma da ke Katsinan Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin yana zuwa muku ne da wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha, kuma a daidai wannan lokaci. A cikin Shirin wannan makon, zai amsar tambayar da ke neman Karin bayani a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma gazawarsa da ma majalisar wajen kawar da yake yake a duniya,
Majalisar Dinkin Duniya da kuma manyan kasashen duniya sun gaza cimma tsagaita wuta a yakin da ake ci gaba da fafatawa tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, wanda yanzu haka ya zarce kwanaki 12. Alkaluma sun bayyana cewar ya zuwa wannan lokaci an hallaka akalla mutane 5,000 a yakin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin siyasar Gabas ta Tsakiya, Dr Elharun Muhammed na Babbar kwalejin Fasaha ta Kaduna, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
Bayan jakada da kuma dakarun Faransa, a yanzu kuma sojoji da suka kwaci mulki a Jamhuriyar Nijar, sun umurci shugabar ofishin MDD da ta fice daga kasar a cikin kwanaki uku. Mahukuntan sojin na zargin jami'ar ce da yin kare tsaye a game da muradun jamhuriyar Nijar a matakin kasa da kasa. Abin tambayar shine, ko ya ya wannan takun saka tsakanin sojojin Nijar da kuma kasashen duniya za ta kasancdce? Anya kuwa hakan zai haifar wa kasar ta Nijar da sakamako mai kyau? Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya mayar da hankali ne kan hasashen masana kan yiwuwar daukewar ruwan damuna da wuri a wasu sassan Najeriya, lamarin da zai haddasa gagarumar matsala a tsarin samar da abinci. Wannan hasashe dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin samun kamfar abinci a sassan Najeriya musamman jihohin arewaci wadanda su ne ke samar da abinci ga kusan daukacin jihohin kasar.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin............
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kasashen yankin arewacin duniya za su ci gaba da ganin tsananin zafi sakamakon dumamar yanayi da ke ci gaba da ta'azzara, gargadin da ke zuwa a dai dai lokacin da tuni nahiyar Turai da arewacin Amurka da kuma wasu sassa a Asiya suka fara ji a jikinsu.A cikin shirin mu zagaya Duniya Rukkaya Abba Kabara ta dubi a kan wannan labari da wasu a kai.
Kasar Rasha ta sanar da janyewar ta daga cikin yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine domin kai shi kasashen duniya, matakin da tuni ya jefa fargaba a kasashe matalauta da ke fuskantar hauhawan farashin kayan abinci. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce miliyoyin mutane ne za su shiga cikin ukuba sakamakon daukar wannan mataki. Dangane da illar wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Abdulhakeem Garba Funtua na Babbar kwalejin Fasaha dake Kaduna, a tarayyar Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Kungiyar agaji ta OXFAM ta bayyana matukar damuwar ta akan yawan mutanen dake fama da yunwa a sassan duniya, wadanda aka ce yawan su ya kai miliyan 783 a shekarar 2022, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa adadin wadanda yunwar zata kassara na iya kaiwa miliyan 600 nan da shekarar 2030. Rahoton kungiyar ya kuma cacaki gwamnatocin kasashe da kamfanoni da kuma attajiran duniya da kawar da kai akan wannan matsalar. Abin tambayar shine, wadanne dabaru ya kamata gwamnatoci su yi amfani da su wajen magance matsalar karancin abinci a kasashensu? Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Ahmad Alhassan ya gabatar.
Majalisar Dinkin Duniya ta amince da matakin janye dakarunta dubu 13 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali bayan da gwamnatin sojin kasar ta yi matsin lamba don ganin an kawo karshen ayyunkan rundunar ta MINUSMA da ta shafe shekaru 10 a kasar. Yanzu haka gwamnatin Mali ta kulla alaka da sojojin haya na Wagner daga Rasha domin samar da tsaro a kasar. To ko mece ce makomar tsaro a kasashen yankin Sahel bayan kawo karshen aikin rundunar a Mali? tambayar kenan da Abdurrahman Gambo Ahmad ya fara yi wa Dr. Yahuza Getso, mai sharhi kan lamurran tsaro a Sahel.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu...
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa, ciki har da yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen zaman sojojinta na MUNISMA a Mali, bayan da suka kwashe tsawon shekaru 10 suna aiki. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa duk da kokarin wayar da kai da aka dauki shekaru 10 ana ayi, a zahiri babu wani sauyin da aka samu a fagen rage wariyar jinsi. Duk da cewa kowane jinsi na mata ko maza na fuskantar wariya, to amma mata ne suka fi fama da wannan matsala a cewar rahoto. Yaya ku ke kallon wannan rahoto na Majalisar Dinkin Duniya? A fahintarku, mene ne dalilin wannan wariya da wani jinsi ke fuskanta a tsakanin al'umma? Wannan shi ne maudu'in da shirin na Ra'ayoyin Masu Saurare ya tattauna a kai.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Muhammane Salissou Hamissou
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya saba waiwayar mahimman abubuwan da suka faru a duniya a cikin maako mai wucewa. Daga cikin abubuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon, akwai rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya bayyana cewar sojojin Mali tare da dakarun kasashen ketare da ke taimaka musu a yakin da suke yi da taa'addanci sun kashe daruruwan fararen hula a shekarar 2022. Zaloka, baangarorin da ke riki da juna a Sudan sun bada dama a shigo da kayayyakin agaji inda ake da bukata.
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi nazari ne kan sake bazuwar cutar kuturta a Najeriya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kasar ce ke kan gaba wajen yawan kutare a kasashen Afrika. Alkaluman Majalissar Dinkin Duniya sun nuna cewa, akwai kutare kimanin dubu 3 da 500 yanzu haka a Najeriya, abin da ya sa kasar ke kan gaba a nahiyar Afrika, a daidai lokacin da ake ci gaba da yakin kawar da wannan lalura daga dora-duniya.Shirin na Lafiya Jari Ce ya kuma yi nazari kan yadda za a iya magance cutar kuturta da zaran alamominta sun fara bayyana.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.
Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman kamar kowanne mako ya yi bita kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi, ciki har da rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa yaro guda na mutuwa a duk dakika hudu da rabi saboda rashin kulawar lafiya musamman a kasashe masu tasowa.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wanna makon ya ci gaba da kawo muku tarihin tsohon sakataren majalisar Dinkin Duniya ne, wato Koffi Annan wanda ya kasance bakar fata na farko da ya hau wannan kujera a shekarar 1997. Dan asalain kasar Ghana ne, wanda ya kwashe shekaru yana aiki a majalisar a matakai dabam dabam. Ya rasu a shekarar 2018.
Sama da mutane milyan 280 ne ke rayuwa a matsayin ‘yan ci-rani a sassan duniya, wannan kuwa sanadiyyar tashe-tsahen hankula da kuma sauran matsaloli irin na yau da kullum. Wadannan alkaluma ne da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar Lahadi 18 ga watan Disamba, ranar da ake kebe domin kula da matsalolin da ‘yan ci-rani ke fuskanta a sassan duniya. Abdoulkarim Ibrahim Shikal, ya zanta da Dakta Shehou Azizou, shugaban wata kungiya da ke taimaka wa matafiya a yankin Agadez da ke arewacin jamhuriyar Nijar. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin Tarihin Afrika na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda muke kawo muku tarihin tsohon babban jami'in diflomasiyar nan kuma tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wato Kofi Annan.Kofi Annan ya kara tarihin zama bakar fata na farko da ya zama Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1997, inda ya taka gagarumaar rawa a kan wannan mukamin.Ya rasu a watan Agustan shekara ta 2018.
Shirin Tarihin Afrika na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda muke kawo muku tarihin tsohon babban jami'in diflomasiyar nan kuma tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wato Kofi Annan.Kofi Annan ya kara tarihin zama bakar fata na farko da ya zama Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1997, inda ya taka gagarumaar rawa a kan wannan mukamin.Ya rasu a watan Agustan shekara ta 2018.
Gobe Asabar 3 ga watan Disamba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da mutanen da suke fama da wata nakasa a jikinsu ko kuma wadanda ake kira masu bukata ta musamman domin nazari akan halin da suke ciki da kuma samo hanyar taimaka musu gudanar da rayuwa kamar kowanne bil'adama. A sakon sa na wannan shekara, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci baiwa ire-iren wadannan mutane dama domin damawa da su a kowanne bangare na rayuwa, ciki har da samun guraban shugabanci a matakai daban-daban. Albarkacin wannan ranar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani fitaccen mawaki a Najeriya, Malam Yahya Makaho, wanda nakasarsa ba ta hana shi cimma burinsa a rayuwa ba. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyaar hirarsu.
Ranar 1 ga watan Disambar kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, domin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta Sida a fadin duniya, yayin da masu dauke da wannan cuta ke fuskantar tsangwama a wasu yankuna. Bugu da kari, rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kananan kasashe ne masu dauke da wannan cuta suka fi fuskantar matsaloli daga al'umma. Dangane da bikin wannan rana ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Abdullahi Ibrahim
Shirin Tarihin Afrika na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda muke kawo muku tarihin tsohon babban jami'in diflomasiyar nan kuma tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wato Kofi Annan.Kofi Annan ya kara tarihin zama bakar fata na farko da ya zama Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1997, inda ya taka gagarumaar rawa a kan wannan mukamin, sannan kuma ya lashe kyautar zaman lafiya taa Nobel a shekara ta 2001. Ya rasu a watan Agustan shekara ta 2018.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan al'ummar duniya ya kai biliyan 8. Shin ko ya ya ake yi a gane hakan, ganin cewa kasashe da dama sun dade basu kidaya al'ummar su ba?Dangane da hakka Michael Kuduson ya mika wannan tambaya daga cikin tambayoyin ku masu saurare a cikin shirin tambaya da amsa.
Wani rahoto da hukumar kididdiga ta Najeriya tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya suka fitar, ya nuna cewa kashi 63 cikin 100 na al'ummar Najeriya na rayuwa ne cikin tsananin talauci.Rahoton ya nuna cewa wadanda suka fi fama da talauci a kasar sun fito ne daga yankunan karkara, wanda ke dauke da kusan kashi 80 na adadin al'ummar ta. Kan dalilan da suka haddasa wannan matsala, Shamsiyya Haruna ta tattauna da Dakta Isah Abdullahi na sashen nazarin tattalin arziki a jami'ar Kashere da ke jihar Gombe.
Shirin Tarihin Afrika na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda muke kawo muku tarihin tsohon babban jami'in diflomasiyar nan kuma tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wato Kofi Annan. Kofi Annan ya kara tarihin zama bakar fata na farko da ya zama Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1997, inda ya taka gagarumaar rawa a kan wannan mukamin, sannan kuma ya lashe kyautar zaman lafiya taa Nobel a shekara ta 2001. Ya rasu a watan Agustan shekara ta 2018.
Shirin Tarihin Afrika na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda muke kawo muku tarihin tsohon babban jami'in diflomasiyar nan kuma tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wato Kofi Annan. Kofi Annan ya kara tarihin zama bakar fata na farko da ya zama Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1997, inda ya taka gagarumaar rawa a kan wannan mukamin, sannan kuma ya lashe kyautar zaman lafiya taa Nobel a shekara ta 2001. Ya rasu a watan Agustan shekara ta 2018. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya kawo muka tarihin Kofi Atta Annan jami'in diflomasiyyar kasar Ghana wanda ya zama babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na bakwai daga shekarar 1997 zuwa 2006. Amatsayin bakar fata na farko dan kasar Afirka ya dare wannan kujera, ya karbi kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2001. Ya koma ga Allah ranar 18 ga watan Agustan shekarar 2018.
Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashe da dama cikinsu har da Amurka da Birtaniya sun yaba da rawar da kungiyar kasashen Afirka ta dauka na sasanta rikicin kasar Habasha, wanda tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya jagoranta a Afirka ta Kudu. Masana na bayyana cewar wannan ya dada tabbatar da cewar 'yan Afirka na iya sasanta rikicin su ba tare da sanya hannu kasashen Yammacin duniya ba. Dangane da wannan nasara, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Abbati Bako, mai sharhi akan siyasar duniya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar kawo karshen cin zarafin da ake yiwa Yan Jaridu a duniya, lura da yadda ake afkawa manema labarai a sassa daban daban ana hallaka su. Hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya tace tsakanin shekarar 2006 zuwa 2020, Yan Jaridu sama da 1,200 aka kashe a duniya, kuma abin takaici shine ba'a hukunta akasarin masu aikata wadannan laifuffuka, abinda ke baiwa wasu mutane damar ci gaba da kai hari akan Yan Jaridun. Dangane da wannan rana, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren Kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya, Shuaibu Leman, kuma ga yadda zantawarsu ta kaya.
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako shirin ya mayar da hankali kan yadda wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ke nuna cewa Najeriya ke sahun gaba a yawan yaran da basa zuwa makaranta tsakanin takwarorinta kasashen Afrika.
Yau ake bikin ranar 'yaya mata da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, wanda ake nazari akan halin da yara mata ke ciki da irin matsaloli da suke fuskanta domin tattauna yadda za'a shawo kansu. Yankin arewa maso yammacin Najeriya a wannan lokaci, na daga cikin yankuna masu hadari ga rayuwar ‘yaya mata, ganin yadda 'yan bindiga ke afka garuruwa suna garkuwa da su da kuma yi musu fyade, abinda ke lalata musu rayuwa. Albarkacin wannan rana ta yau, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Khadija Suleiman Saulawa, daya daga cikin jami'an kungiyoyin dake kare hakkokin mata a jihar Katsina. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Firaministan Mali da sojoji suka nada ya caccaki Faransa da kuma Majalisar Dinkin Duniya a wani jawabin da ya gabatar mai cike da koke kan tabarbarewar tsaro a kasarsa. A makon da ya gabata ne aka nada Kanar Abdoulaye Maiga, a matsayin Firaministan rikon kwaryar Mali, wanda ya zargi Faransa da zamewa kasar sa kayar kifi a wuya. Abdoulaye Issa ya tattauna da Alkassoum Abdourahamane, mai sharhi kan lamuran zamantakewa da siyasar kasashen yammacin Afrika dangane da jawabin Firaministan kasar ta Mali.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Duniya Antonio Guterres ya bayyana fatan ganin an kawo karshen tsaiko da ake fuskanta dangane da batun fitar da cimaka daga Ukraine zuwa wasu kasashen Duniya. Hakazalika manyan kasashen duniya sun cika alkawura da suka dauka na bayar da tasu gudun mowa ga kasashe matalauta a yakin da dumammar yanayi ta yiwa illa. Guterres na fadar haka ne yayin tattaunawa da RFI. Latsa alamar sauti domin sauraron fassarar kalaman nasa.
Jiya Talata aka bude zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda shugabannin kasashen duniya ke gabatar da jawabi dangane da halin da ake ciki a duniyar da kuma gabatar da shawarwarin tinkarar matsalolin da ake fuskanta. Taron na bana na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar karuwar yake-yake da kuma matsalar tattalin arziki. Shugaban Majalisar na wannan karo Csaba Korosi, ya ce a halin da ake ciki yanzu, ana fuskantar amfani da makamin nukiliya sama da shekaru 40 da suka gabata. Dangane da taron da kuma rawar da majalisar ke takawa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. Elharun Muhammad, na babbar kwalejin fasaha ta Kaduna. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
Shirin Ra'ayoyin Masu Saurare na wannan rana ya tattauna ne kan wani raahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa, akalla mutane milyan 50 ne ke rayuwa a karkashin wani salon bauta na zamani a sassan duniya. Rahoton ya ce mata da kananan yara ne suka fi fuskantar ukuba a karkashin wannan sabon salo na bauta, da suka hada da auren dole, yin aiki na tsawon awanni ba tare da mutunta ka'idojin kwadago na duniya ba, yayin da ake tilasta wa wasu shiga karuwanci.
Rahotan Ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya na wannan shekara ya bayyana cewar duniya ta fuskanci koma-baya sakamakon annobar Korona, rahotan ya sanya kasashen Sudan ta Kudu da Chadi da kuma Nijar a matsayin jerin kasashe na karshe a duniya. Sai dai ga alama, rahotan bai yi wa wasu jama'a dadi ba, saboda yadda ya mayar da wasu kasashe baya. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Salah Habi, tsohon ayyuka na a Nijar. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
Yau ake kammala taron Hukumar kare hakkin Bil Adam ata Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, wanda yake tattauna batutuwan da suka shafi kare hakkin Bil Adama a kasashen duniya daban daban. Taron na kwanaki 3 ya samu halartar wakilai daga sassan duniya. Dangane da wannan taro, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Kalla Muntari, dan Majalisar dokoki kuma shugaban kwamitin kula da walwalar 'yan kasa a Jamhuriyar Nijar. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Yau shugabannin kasashen Afirka tare da ministoci da kuma masana harkar noma ke halartar taro a Kigali dake Kasar Rwanda akan yadda za'a bunkasa aikin noma da samar da abinci a nahiyar. Daga cikin mahalarta taron harda Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Muhammed. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Rabe Isa Mani, masanin harkar noma da kiwo a Najeriya, kuma tsohon Darakta a ma'aikatar noman kasar. Ga yadda zantawar su ta gudana.
Shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman da ke bitar muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata, a wannan karon shirin ya yi waiwaye kan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ke nuna yadda aka samu karuwar yaran da basa zuwa makaranta zuwa yara sama da miliyan 240 sai kuma yadda yara dubu 22 suka rasa rayukansu saboda gurbatar iska a jihar Lagos. Ayi saurare Lafiya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 31 ga watan Agustan kowacce shekara a matsayin ranar da ake mayar da hankali akan mutanen da suka bata, inda kungiyar agaji ta ICRC tace a nahiyar Afirka kawai ana da mutane dubu 64 da suka bata. Alkaluman kungiyar sun bayyana cewar a Najeriya kawai akwai mutane sama da dubu 25 da suka bata, kuma kusan dubu 14 daga cikin su yara ne kanana. Dangane da bikin irin wannan rana, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan yada labaran kungiyar ICRC a Najeriya, Aliyu Dawobe. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya yi duba kan yadda ake samun yawaitar yaran da basa zuwa makaranta a Najeiya bayan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa yara sama da miliyan 10 ne yanzu haka basa zuwa makaranta a sassan kasar wanda ya mayar da Najeriyar kasa ta farko mai yawan yaran da basa zuwa makaranta.
Shirin 'Ra'ayoyin Masu Sauraro' na wannan rana ya ba da damar tattaunawa ne akan rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya ce adadin mutanen duniya zai kai miliyan dubu 8 a watan Nuwamba mai zuwa, yayin da Najeriya za ta kasance kasa ta 6 mafi yawan al'umma a duniya da mutane miliyan 216. Hasashen ya kara da cewar nan da zuwa shekara ta 2050, yawan al'ummar Najeriya zai kai miliyan 375, wato kasa ta 4 mafi yawan mutane a duniya. Wasu dai na bayyana yawan al'umma a matsayin kashin bayan samar da ci gaba ga kowace kasa, yayin da wasu ke bayyana shi a matsayin nakasu.
Shirin ‘Mu Zagaya Duniya' yana tacewa gami da zakulo wasu daga cikin muhimman labarai ko rahotannin da suka gabata a makon da ya kare domin bitar su, dama kuma masu iya magana sun ce ‘waiwaye adon tafiya'. Daga cikin muhimman labaran da shirin wannan makon ya waiwaya akwai rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya ce ‘yan gudun hijira da suke tserewa hare-haren ‘yan ta'adda fiye da dubu 36 suka kwarara cikin Jamhuriyar Nijar a shekarar nan. Sai kuma taron Manyan Hafsoshin tsaron kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS domin Nazari akan matsalolin tsaron da suka addabi yankin yammacin Afirka.
Cikin shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Michael Kuduson za ji karin bayani kan ko akwai kasashen da ba sa cikin Majalisar Dinkin Duniya, da dalilansu da kuma abin da hakan ya tsinana musu. Sai kuma hanyoyin da ake bi wajen zaben gwarzon dan kwallon kafa na duniya mai lashe kyautar Balon d'Or.
YAU ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yaki da cutar AIDS ta duniya, da zummar nazari da kuma fadakar da jama'a halin da ake ciki game da cutar. A wannan shekarar Majalisar ta bukaci samun daidaito ne wajen kawo karshen cutar nan da shekara ta 2030. Dangane da wannan rana, mun tattauna da Dr Aliyu Gambo, shugaban hukumar yaki da cutar a Najeriya, kuma ga tsokacin da yayi mana akai.
Shirin 'Kasuwa a kai miki Dole' na wannan mako ya maida hankali ne kan wani gagarumin taro da kungiyar Masu Masana'antu ta Najeriya MAN ta shirya a birnin Lagos dake Kudancin kasar, yayin da take bukin cikar ta shekaru 50 da kafuwa. Kungiyar Masu Masa'antun Najeriya karkashin jagorancin Injiniya Mansur Ahmed ta shirya taron ne a katsaitacen otel din Intercontinental dake birnin Lagos, inda ta shirya muhawara mai matukar muhimmaci kan bunkasar Masana'antu da kuma ci gaba mai daurewa. Taken wannan taro dai shine, yadda”Masana'antu zasu zama Hanyoyin Cimma Manufofin Ci Gaba mai Dorewa" kamar yadda wani kudiri na Majalisar Dinkin Duniya ya tanadar, don haka aka gayyaci ƙwararru a fannin masana'antu da kuma masu ruwa da tsaki a sabgar, ciki harda Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Mohammed wanda ta halarci taron na Lagos kai staye ta fasahar Bidiyo, kuma ta yi tsokaci kamar haka.
Shirin Mu Zagaya Duniya da ke bitar muhimman labarai, ko lamurran da suka wakana a makon da ya kare, ya fara ne da lekawa zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, inda kasashen duniya ke taron kasa da kasa karo na 76.
Cikin shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Michael Kuduson, ya amsa tambayoyin masu sauraro kan batutuwa da dama ciki harda karin bayani kan kujerar dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.
Shirin na wannan makon ya zo daidai da ranar matasa ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ke warewa a duk shekara, inda a bana ta mayar da hankali a kan hikimar matasa.
Annobar cutar Covid-19 ta kawo tseko a harkar kiwon lafiya musamman a fannin kiwon lafiyar mata gurin haihuwa, inda annobar ta kawo tseko wa kimanin mutane miliyan 12 masu amfani da tsarin bada tazarar haihuwa a watan Maris a najeria. --- Send in a voice message: https://anchor.fm/devcoms-network0/message
Majalisar Dinkin Duniya ta kara wa'adin zaman rundunar ta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali da tsawon shekara guda, wato zuwa Yunin shekarar 2022. Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma jaddadawa sojojin Mali kiyaye 27 ga watan Fabarairu, lokacin da aka tsara za su shirya zaben mikawa farar hula mulki. Dangane da wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Kamilu Sani Fagge a tsangayar Kimiyyar Siyasa dake Jami'ar Bayero a Kano, Najeriya.
Bankin Duniya yace hauhawan farashin kayan masarufi a Najeriya yayi sanadiyar jefa jama'ar kasar miliyan 7 zuwa tsananin talauci. Rahotan bankin wanda ya yabawa hukumomin Najeriya saboda matakan da suka dauka na rage radadin matsalar da annobar korona ta haifar, ya kuma bukaci hukumomin da suka kara kaimi wajen dakile tsadar kayayyakin da mutane ke bukata na yau da kullum. Rahotan Bankin da yayi amfani da alkaluman Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Bada Lamuni ta duniya yace kashi 41 na Yan Najeriya ko kuma mutane miliyan 87 na fama da tsananin talauci wajen rayuwa a kasa da Dala 2 kowacce rana. Danna alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Dr. Isa Abdullahi, masanin tattalin arziki a Jami'ar Kashere ta Najeriya.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince ba tare da hamayya ba domin bai wa Sakatare Janar Antonio Guterres damar yin wa'adi na biyu domin ci gaba da tunkarar matsalolin da suka addabi duniya musamman rikice-rikicen da ake fama da su. Guterres wanda tsohon Firaministan Portugal ne ya karbi aikin jagorancin majalisar ne a shekarar 2017 daga hannun Ban Ki Moon, Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Dr. Abbati Bako mai sharhi kan siyasar duniya
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' a wannan makon ya soma da waiwaye ne kan shirin hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya na soma bincike kan zargin sojojin Isra'ila da aikata laifukan yaki yayin hare-haren da ta kaddamar kan birnin Gaza tsawon kwanaki 11 a cikin watan Mayu na wannan shekara.
Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar Kasashen Afrika da ECOWAS da wasu manyan kasashen duniya da suka hada da Faransa da Birtaniya da Amurka sun yi tur da juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin rikon kwarya a Mali, inda suka tsare shugaba Bah Ndaw da Firaministansa Moctar Ouane a barikinsu. A baya-bayan nan shugaban Faransa ya yi barazanar cewa, Kungiyar EU za ta lafta takunkumai ga Mali muddin lamura suka yi sauyawa a kasar. A game da wannan juyin mulkin, Abdurrahman Gambo Ahmad ya zanta da Farfesa Mohd Usman, shugaban Cibiyar Horas da ‘Yan Majalisar Afrika wanda ya ce, Faransa ce kadai za ta iya maido da zaman lafiya a Mali.
Yau ce ranar mata ta duniya, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware a kowacce shekara, inda ake nazari kan matsalolin dake fuskantar mata da kuma irin cigaban da suke samu. Yara mata na cigaba da fuskantar matsalolin samun ilimi a kasashe masu tasowa, kamar irin su Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Maryam Muhammad, malama kuma mai bincike a kasar Amurka, wadda ke nazari kan matsalolin matan.
Alummar jihar Borno dake arewa maso Gabashin Najeriya na cikin zaman makoki yanzu haka sakamakon kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai tare da kashe sama da mutane 100 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar, akasarinsu manuma shinkafa. Wannan ya kasance mafi muni a cikin hare-haren da mayakan kungioyar Boko Haram ke kaiwa duk da matakan da Gwamnatin kasar ke cewa ta na dauka. Dangane da haka, Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Mohammed Kabir Isa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, wanda ke bincike dangane da ayyukan Boko Haram.
Kowace 2 ga watan Nuwamba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yaki da cin zarafin da ake yiwa 'Yan Jaridu, wanda ke zuwa a dai dai lokacin da kungiyar kare hakkokin 'Yan Jaridu ta duniya ke cewa a cikin shekaru 10 an kashe Yan Jaridu 277. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace muddin aka gaza wajen kare 'Yan Jaridu, duniya ba zata samu sahihan bayanan da za tayi aiki da su ba. Dangane da wannan biki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakatare Janar na kungiyar 'Yan Jaridun Najeriya Shuaibu Leman, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris, ya yi nazari ne dangane da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar samar da abinci ta duniya,wato kowace 16 ga watan Oktoba, wanda ke dauke da taken yadda za’a wadata jama’ar duniya da abinda da za su ci domin cimma daya daga cikin muradun karni.
Majalisar Dinkin Duniya tace kasashen Afirka sun yi asarar kudaden da suka kai Dala biliyan 836 ta hanyar fitar da su zuwa kasashen duniya ba bisa ka'ida ba a cikin shekaru 15. Hukumar dake kula da kasuwanci da kuma cigaba ta gabatar da rahoto akai, inda take cewa kudaden sun zarce Dala biliyan 770 da ake bin nahiyar baki daya a shekarar 2018.Dangane da wannan rahoto, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Isa Abdullahi na Jami’ar Kashere, kuma ga yadda zantawarsu ya gudana.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da yayi amfani da tattaunawa da kuma tafarkin siyasa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar. Babban Jakadan Majalisar dake Najeriya Edward Kallon ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar shugaban, inda yake cewa matsalolin tsaron da suka addabi kasar dake da sassa daban daban na da wahalar magance su. Dangane da wannan shawara Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon ministan ayyuka na musamman a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Yunkurin Sasanta rikicin Libya na cigaba da fuskantar zagon kasa daga kasashen dake goyan bayan bangarorin dake rikicin wanda ya kwashe dogon lokaci ana cigab da zubda jini akai. Janar Khalifa Haftar da ya sha alwashin kifar da gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ke goyawa baya na samun taimakon wasu kasashe, yayin da ita ma gwamnatin ke samun nata taimako. Yanzu haka Masar da Rasha na jagorancin wani sabon yunkurin samun tsagaita wuta a kasar. Dangane da wannan rikici, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Elharun Muhammed na Babbar Kwalejin Fasaha ta Kaduna, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane sama da miliyan 40 dake zaune a Yammacin Afirka zasu fuskanci karancin abinci a watanni masu zuwa sakamakon illar annobar coronavirus wadda ta tilasata killace mutane a cikin gidajen su. Wannan ya biyo bayan matakan da gwamnatoci suka dauka na tilastawa mutane zama a gida domin dakile yaduwar annobar coronavirus wadda ta shafi manoma da masu harkar samar da abinci. Dangane da wannan rahoto Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren yada labaran kungiyar manoman Najeriya kuma kwamishinan Gona a Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Magaji.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 3 ga kowane watan Mayu a matsayin ranar 'Yan Jaridu ta Duniya domin tunawa da karramma ‘Yan Jaridun da suka rasa rayukansu bisa gaskiya a bakin aiki, da kuma wadanda suka fuskanci cin zarafi ko tauye hakki. Taken bikin ranar ‘Yan Jaridun ta duniya na wannan shekara ta 2020, shi ne “Aikin Jarida ba tare da tsoro ko alfarma ba”. Dangane da wannan rana Ahmad Abba da shi ma ya taba fuskantan cin zarafi dangane da aikin, ya tattauna da Farfesa Umar Pate, na jami’ar Bayaro dake Kano.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da yin kira zuwa kasashe don ganin sun dau matakan kariya daga kamuwa da cutar Mashako duk da tace babu shaidar dake nuna cewar cutar zazzabin da ta barke a China na yaduwa tsakanin Bil Adama a wajen kasar. Wasu bayanai daga hukumomin Turai kama daga Faransa da Austria na tabbatar da bulluwar cutar a yankunan su,haka zalika a Amurka da wasu kasashen yankin Asiya. Garba Aliyu Zaria a cikin shirin mu zagaya Duniya ya mayar da hankali a kai.
Kungiyar agajin kasar Faransa ta Action Against Hunger ta sanar da kashe jami’an ta guda 4 da kungiyar Boko Haram tayi garkuwa da su tun a watan Yuli. Kisan ya gamu da suka daga Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma kungiyar agajin dake taimakawa mutane 300,000 da rikicin Boko Haram ya tagayyara. Kan wannan batu muka baku damar tattaunawa a wannan litinin.
Shirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan ranar tare da Micheal Kuduson, ya tattauna ne kan ranar 11 ga watan Yuli da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yawan al'umma ta Duniya, domin yin nazari kan batutuwa da yawan jama'a kan janyo domin magance wa.
Kowacce Ranar 16 ga watan Oktoba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ke warewa a matsayin ranar samar da abinci ta duniya. Taken bikin na bana dake gudana a birnin Geneva shi ne ‘Ana iya magance yunwa a duniya.’ Shirin Ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan lokaci, ya baku damar tofa albarkancin bakinku kan yadda harkar noma da samar da abinci ke gudana a yankunan ku.