POPULARITY
Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bukukuwan Easter, waɗanda ke matsayin tunawa da ranar da aka gicciye Yesu Almasihu da kuma tashinsa bayan kwanaki uku. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Reverand Andrew Dayyu, wanda ya yi masa ƙarin bayani a game da abin da ake nufi da Easter da kuma muhimmancinta ga mabiyar addinin Kirista. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawarsu.............
Al'ummar musulmi a sassan duniya na gudanar da bukukuwan Mauludi, domin tunawa da ranar da aka haifi annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah.To domin sanin muhimmancin wannan rana ga musulmi, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Sheikh Mansur Ibrahim da ke garin Kaduna a Najeriya.
Kwararru game da matsalar sauyin yanayi da kuma wakilan gwamnatoci da na ƙungiyoyi, sun fara gudanar da wani taron kwanaki uku a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, domin tattauna matsalar sauyin yanayi a Yankin Sahel da kuma Yammacin Afirka. To domin jin muhimmancin wannan taro, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Moussa Hassan Ousseini, jagoran ƙungiyar Jeunes volontaires pour l'environnement du Niger mai rajin kare muhalli a Jamhuriyar Nijar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.....
Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa a Najeriya, manazarta na ganin cewa ba wata hanya da za ta taimaka domin kawo wa jama'a sauƙi face bayar da damar shigar da kayan abinci da na masarufi daga ƙetare har zuwa cikin ƙasar har zuwa lokacin da lamurra za su daidaita. Alhaji Shehu Yaro Abdulkadir Jimoh, ɗan kasuwa ne kuma shugaban al'umma, na daga cikin masu goyon bayan wannan shawara, ga kuma abin da yake cewa a zantawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu
Matsalar tsaro a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da ɗaukar sabon salo lura da yadda ake samun ɓullar sabbin ƙungiyoyin tawaye da ke kai hare-hare, inda suke cewa suna yin hakan ne saboda neman a saki hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum. Bayan da ƙungiyar FPL ta kai hari kan bututun mai da ke sada ƙasar da jamhuriyar Benin, a ranar juma'ar da ta gabata kuwa, wata ƙungiyar mai suna FPJ ta kama da kuma yin garkuwa da kantoman mulkin soji na yankin Bilma da muƙarrabansa a jihar Agadez. Don jin dalilan bayyanar waɗannan ƙungiyoyi da kuma manufofinsu, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Mahaman Sani Roufa'i mai sharhi kan lamurran yau da kullum a Damagarm.Latsa alamar sauti don jin cikakkiyar zantawarsu.......
Mahukunta a Nijar sun ce ba za su bari motocin da ke ɗauke da lambar Jamhuriyar Benin damar tsallaka iyakar ƙasar da Najeriya domin shiga ko kuma fita daga Nijar ba, a maimakon haka, sai dai su zagaya zuwa cikin Burkina Faso da kuma Togo kafin komawa gida. Wannan dai alama ce da ke ƙara tabbatar da cewa alaƙa ta yi tsami a tsakanin ƙasashen biyu tun daga lokacin da aka kifar da gwamnati Mohamed Bazoum. Dan gane da wannan mataki, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Hima Barkire, sakataren tsare-tsare na ƙungiyar masu motocin dakon kaya a Nijar.Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawar ta su......
Duk da matakai da mahukunta a Najeriya ke cewa sun dauka domin tunkarar manyan matsalolin da kasar ke fama da su, da suka hada da na tsaro da kuma tsadar rayuwa, toh amma mafi yawan al'ummar kasar cewa suke yi a zahirance babu wani tasiri da wadannan matakai ke yi wajen shawo kan wadannan matsaloli. Toh sai dai Hon Muktar Ishaq Yakasai, daya daga cikin magoya bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ganin cewar ya kamata a yi wa shugaban adalci, lura da irin matsalolin da gwamnatinsa ta gada.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.....
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sake komawa a Yankin Gabas ta Tsakiya a ci gaba da kokarin da kasashen duniya ke yi don samar da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas. Daga farkon wannan rikici wanda ya barke a ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa yanzu, sau da dama Amurka na cewa tana yunkuri domin samar da tsagaita wuta a wannan yaki da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu 35 da kuma raba sama da milyan biyu da gidajensu. Farfesa Tukur Abdulkadir malami a jami'ar jimi'ar jihar Kaduna, na ganin cewa, da dagaske Amurka ke yi, da tuni an kawo karshen wannan yaki.Ku latsa alamar sauti don jin zantawarsa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.......
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka, tare da zargin cewa dakarun Amurka wadanda adadinsu ya zarta dubu daya na zaune a kasar ne ba a kan ka'ida ba. Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da wata babbar tawagar Amurka ta kamma ziyarar da ta kai Nijar ta tsawon kwanaki uku. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Farfesa Dicko Abdourahmane, masani tsaro kuma malami a jami'ar Damagaram Zinder, wanda da farko ya fara yin bayani a game da dalilan da suka sa mahukuntan Nijar suka dauki wannan mataki.Ku latsa alamar sauti don jin zantawarsu.......
A Najeriya wata babbar matsala da ake fama da ita a kasar ita ce yawaitar satar kananan yara musamman a yankin arewacin kasar, inda bayanai ke cewa bayan sace su, ana safarar su ne zuwa wasu yankuna da ke kudancin kasar. Malam Ibrahim Yunusa Ibrahim da ke zaune a Gwagwalada kusa da Abuja, daya ne daga cikin gungun iyalai fiye da 50 wadanda aka sace ‘yayansa, kuma yanzu haka suke ci gaba da nema, ya yi wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal karin bayani a game da wannan matsalar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
Kwamitin da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka kafa domin bayar da shawarwari dangane da yadda za a inganta karatun firamire a kasar ya gabatar da rahotonsa ga ministar ilimi. Kafa wannan kwamiti da ya kunshi kwarari, ya biyo bayan lura da yadda aksarin yara ke kammala firamire amma ba tare da sun iya rubutu da karatu ba.A zantawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, Abdou Dan Neito mai fafutuka a cikin kungiyoyin fararen hula ke cewa ya zama wajibi a samar da wannan gyara.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar zantawarsu
Kusan watanni biyu kenan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ci gaba da bai wa ‘yan kasuwa da ke shigar da wasu kayayyaki fiye da 40 a cikin kasar damar samun dala cikin sauki daga babban bankin kasar, amma har yanzu bincike na nuni da cewa ba a fara aiwatar da umurnin ba. To sai dai a daya bangare an wayi gari da karin kudaden da ‘yan kasuwa ke biya a matsayin fito ko kuma harajin shigar da kaya a kasar ne saboda an bari kasuwa ta aikinta a fagen canjin Naira zuwa kudaden ketare.Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Zubairu Mele Abba-Ganamma, daya daga cikin shugabannin kungiyar masu aikin fito wato 'Transit Agents', wanda ya yi mana karin bayani a game da hakan.
A Najeriya, sakamakon da Jim Obazee, wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada domin binciken yadda tsohon gwamnan Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele ya gudanar da ayyukansa ya fitar, na ci gaba da haifar da muhawara a tsakanin jama'a. Tuni dai bankin na CBN ya fitar da wata sanarwa da ke yin kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu, domin kuwa ba abin da zai shafi kudadensu da ke ajiye a bankunan da rahoton mai binciken ke cewa tafka kura-kurai wajen sayar da hannayen jarinsu.Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani tattalin arziki Shu'aibu Mikati, a game da wannan rahoto da kuma abubuwan da ya kunsa.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar zantawarsu.
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta ce ba za ta bari a kwashe kayayyakin da aka sauke a tashar jiragen ruwan Cotonou zuwa Nijar ba, amma a maimakon haka za ta bai wa ‘yan kasuwar Nijar damar karkata akalar kayayyakin zuwa wasu kasashe, ta hanyoyin mota ko jiragen ruwa. A sanarwar da ta fitar karshen mako, hukumar kula da tashar jijagen ruwan Cotonou ta kuma bai wa ‘yan kasuwar Nijar damar sayar da kayayyakinsu a Benin idan har ba za su karkata akalarsu zuwa wata kasa ba. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Yacouba Dan Maradi, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da ke shigar da kaya a Nijar, domin jin yadda suke kallon wannan mataki. Ga kuma zantawarsu.
A Jamhuriyar Nijar, yau 26 ga watan Okotba, watanni 3 kenan da sojoji suka kifar da gwamnatin dimokuradiyyar da ke karkashin jagorancin Mohamed Bazoum, lamarin da ya sa kungiyar ECOWAS da kuma UEMOA suka kakaba wa kasar takunkumai da dama. Yanzu haka dai wannan lamari ya jefa al'ummar kasar a cikin hali na kunci saboda rashin kudi da kuma rashin kayayyakin masarufi. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ambasada Abubakar Cika, domin jin yadda yake kallon wannan rikici da kuma halin da Nijar ke ciki saboda wannan juyin mulki.
A yanzu haka dai al'ummar musulmi sama da milyan 2 da dubu 500 ne suka tururuwa domin tsayuwar Arafa, da ke matsayin babban ginshinki a aikin hajji, bayan kammala tsayuwar Araf a gobe laraba, musulmi a sassan duniya za su gudaanr da bukukuwan sallar layya, tare da yanka dabbobinsu a matsayin Ibada. Domin jin abin da ake nufi da layya da kuma dabbar da ta cancanci a yi layya da ita, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zantar da Sheikh Dakta Abubakar Hassan Dikko, malamin addinin musulunci a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar ta su..........
Al'amurran yau da kullum sun fara daidaita a birnin Moscow fadar gwamnatin kasar Rasha, bayan da jagoran kamfanin Wagner Yevgeny Prigozhin ya sanar da dakatar da boren da yake yi wa gwamnatin Vladimir Putin. Shugaban kasar Belarusse Alexander Loukochanko ne ya yi nasarar shawo kan shugaban Wagner domin jingine yunkurinsa na afka wa birnin Moscow, tare da amince wa ya bar Rasha zuwa Belarusse. Domin jin dalilin da suka haddasa tsamin dangantaka tsakanin Putin da Prigozhin, da kuma yadda hakan zai shafi makomar yakin Rasha da Ukraine? Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Janar Idris Bello Dambazau mai ritaya. A latsa alamar sauti don jin tattaunawar ta su.......
Hukumar sa-ido game da yadda ake hada-hadar kudade a Najeriya wato NFIU, ta ce daga ranar 1 ga watan Maris mai zuwa Gwamnatin Tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi, ba su da izinin fitar da tsabar kudi daga asusun ajiyarsu, amma suna da hurumin yin hakan daga bakin zuwa. A cewar shugaban hukumar ta NFIU Modibbo Tukur, ya ce wadanda suka karya wannan ka'ida za su iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari. Domin jin tasirin wannan tsari, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Kasimu Garba Kurfi, shugaban cibiyar hada-hadar hannayen jari na APT Securities and Fund Ltd da ke Lagos, ga kuma zantawarsu.
Matsanancin sanyin huturu na cigaba da wanzuwa a kasashe da dama na sassan duniya ciki har da na nahiyar Afirka. Wannan dai lokaci ne da masana kiwon lafiya ke gargadi domin daukar matakan kariya musamman ga yara kanana saboda kaucewa kamuwa da wasu cututuka da ke nasaba da sanyin na huturu. Dr Rilwanu Muhammad, shugaban sashen kula da lafiyar al'umma a matakin farko reshen jihar Bauchin Najeriya, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal wasu daga cikin matsaloli na kiwon lafiya da ake cin karo da su a irin wannan lokaci na sanyin huturu.
Manoma a Najeriya sun bukaci mahukunta da su kara sanya ido, domin yaki da wadanda ke shigar da takin zamani maras inganci a cikin kasar. Alhaji Umar Ya'u Gwajo-Gwajo, daya daga cikin shugabannin kungiyar manoma a Najeriya, kuma shahrarren manomi a jihar Katsina, ya ce tabbas manoma na iya kokarinsu domin wadatar da kasar da abinci, amma duk da haka akwai bukatar gwamnati ta sanya ido domin samar da ingantaccen takin zamani a cikin kasar. Ga dai abin da ya shaida wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal a zantawarsu.
Duk da cewa Najeriya ta sanar da bude mafi yawan iyakoki tsakaninta da kasashe makota bayan da suka kasance a rufe tsawon kusan shekaru biyu, amma har yanzu zirga-zirga da kuma shige-da-ficen kayayyaki musamman tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Benin bai kankama ba. Alhaji Zubairu Mele Abba Ganama, daya daga cikin shugabannin kungiyar masu aikin shige-da-ficen kaya a iyakar Seme Border, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal irin matsalolin da suke ci gaba da fuskanta.
Kusan makonni biyu da fara amfani da sabbin kudade a Najeriya, amma yanzu haka tsoffin kudade ne ke ci gaba da yawo a hannayen jama'a hatta a cikin bankuna da kuma wuraren cire kudi da ake kira ATM. Wannan dai na faruwa ne duk da cewa tuni babban bankin kasar wato CBN ya kayyade lokacin da za a daina amfani da tsoffin kudin. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Kasimu Garba Kurfi na kamfanin APT Securities and Funds Limited da ke hada-hadar kudade a birnin Lagos. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A Najeriya, wasu bayanai na nuni da cewa gwamnatin Tarayyar kasar na shirin kawo karshen sassaucin biyan haraji da ta ke yi wa kamfanonin da ke gudanar da ayyukansu a karkara. Wannan mataki dai na kunshe ne a cikin sabuwar dokar kasafin kudi, wanda yanzu haka majalisar ke yi wa gyara kuma ake kyautata zaton cewa za a amince da ita a cikin wannan mako. Kan hakan Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Muhammad Magaji, Sakataren yada labarai na kungiyar manoman Najeriya.
A Najeriya rashin kyawun hanyoyi da kuma tsadar makamashi musamman diesel, na ci gaba da yin tasiri a kan farashin kayayyakin masarufi a kasuwannin kasar. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Umar Garba Alangawari, daya daga cikin masu motocin dakon kaya daga yankin kudu zuwa Arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Sama da mutane milyan 280 ne ke rayuwa a matsayin ‘yan ci-rani a sassan duniya, wannan kuwa sanadiyyar tashe-tsahen hankula da kuma sauran matsaloli irin na yau da kullum. Wadannan alkaluma ne da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar Lahadi 18 ga watan Disamba, ranar da ake kebe domin kula da matsalolin da ‘yan ci-rani ke fuskanta a sassan duniya. Abdoulkarim Ibrahim Shikal, ya zanta da Dakta Shehou Azizou, shugaban wata kungiya da ke taimaka wa matafiya a yankin Agadez da ke arewacin jamhuriyar Nijar. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Duk da cewa Majalisun Tarayyar Najeriya sun nuna fargaba a game da shirin sauya takardar kudin kasar da kuma adadin da za a iya cirewa a kowace rana, amma gwamnan babban bankin kasar Godwin Emiefele ya ce ba gudu ba ja da baya a game da wannan shiri da zai fara aiki a ranar 15 ga wannan wata na disamba. To sai dai a zantawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, Alhaji Ibrahim Ya'u Galadanci, daya daga cikin shugabannin matasa a Najeriya, ya bayyana fargaba a game da wannan shiri, musamman yadda zai iya kara jefa talaka wanda bai mallaki asusun ajiya a banki ba cikin matsala.
Bankunan Kasuwancin a Najeriya sun sanar da janyewa daga tsarin bai wa manoma rancen kudade da babban bankin kasar ke kan aiwatarwa da ake kira da suna Anchor Barrower, bayan da mafi yawan manoman da suka karbi wannan rance su ka gaza dawo da kudaden da aka ba su. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da sakataren yada labaran kungiyar manoman Najeriya Alhaji Mouhammad Magaji, domin jin inda wannnan matsala ta samo asali, da kuma yadda hakan zai shafi makomar shirin, gad ai zantawarsu.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da kawo karshen ayyukan rundunar Barkhane mai yaki da ta'addanci a yankin Sahel daga jiya laraba, to sai dai ya ce Faransa za ta fayyace sabon tsarin ci gaba da kasantuwar dakarunta a Sahel cikin watanni 6 masu zuwa. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Tahirou Gimba, masani tsaro, domin jin yadda yake kallo matakin rusa rundunar da kuma yadda ya kamata alakar tsaro ta kasance tsakanin Faransa da sauran kasashen yankin, ga dai zantawarsu.
A rana ta biyu da fara taron duniya game da sauyin yanayi da ake kira Cop27 da ke gudana yanzu haka a Sharm el-Sheikh na Masar, Gidauniyar Bill Gates attajirin Amurka ta sanar da ware dala bilyan daya da milyan 400 a matsayin tallafi ga manoman Afirka da Kudancin Asiya. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Kabiru Ibrahim Matazu, na jami'ar Umaru Musa ‘Yar'adua, wanda da farko ya yi karin bayani a game da girman matsalar sauyin yanayi musamman ga bangaren noma a kasashen yammacin Afirka.
Lalacewar hanyoyin mota a Najeriya na ci gaba da haddasa matsaloli da dama da suka hada da tseko ga matafiya, hauhawar farashin dakon kaya da kuma barazanar tsaro ga matafiya. Wannan matsala ta lalacewar hanyoyi ta fi ta'azzara ne a jihar Niger da ke tsakiyar kasar, inda a wasu lokuta masu motocin ke share tsawon makonni kafin ratsa wannan jiha, kan hakan Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Umar Garba Alangawari, daya daga cikin masu motocin dakon kaya daga Lagos zuwa arewacin Najeriya, wanda ya bayyana mana girman wannan matsala.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya kawo muka tarihin Kofi Atta Annan jami'in diflomasiyyar kasar Ghana wanda ya zama babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na bakwai daga shekarar 1997 zuwa 2006. Amatsayin bakar fata na farko dan kasar Afirka ya dare wannan kujera, ya karbi kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2001. Ya koma ga Allah ranar 18 ga watan Agustan shekarar 2018.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya ci gaba da kawo muku tarihin fiitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a shekarar 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi na 2 daga 1981 zuwa 2001.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya ci gaba da kawo muku tarihin fiitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a shekarar 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi na 2 daga 1981 zuwa 2001. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
Shirin 'Tarihin Afrika' na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya ci gaba da kawo muku tarihin fiitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a shekarar 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi na 2 daga 1981 zuwa 2001.
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya ci gaba da kawo muku tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya ci gaba da kawo muku tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya ci gaba da kawo muku tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.
Har zuwa cikin daren jiya talata an ci gaba da kokari domin ceto tarin mutanen da da wani gini ya rufta a kansu, lokacin da su ke tsaka da hada-hadar kasuwanci a kasuwar Beirut da ke jihar Kano a Najeriya, duk da ya ke wasu sun yi korafi dangane da yadda aka fara gudanar da ayyukan ceton a makare. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana a jihar ta Kano wato PFS Saminu Yusuf Abdullahi.
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya ci gaba da kawo muku tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.
Shirin tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan makon ya faro tarihin fitaccen shugaban kasar Ghana dan gwagwarmaya John Jerry Rawlings da ya mulki kasar na gajartaccen wa'adi a 1979 gabanin sake shugabantar kasar a wa'adi 2 na daga 1981 zuwa 2001.
A kwana a tashin yau 15 ga watan Agusta, shekara daya kenan cur da ‘yan Taliban suka karbi ragamar mulki a Afghanistan bayan da Amurka ta janye dakarunta daga kasar. Taliban dai ta sake dawo kan karagar mulki ne bayan da kasashen duniya suka yi ma ta taron dangi karkashin jagorancin Amurka. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr. Muhammad Kabiru Isah na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, domin jin yadda aka yi ‘yan Taliban suka sake karbe ragamar mulkin Afghanistan. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
A Najeriya, yanzu haka akwai dimbin yara da ke karatu a cikin makarantun allo da ake kira tsangaya, kuma mafi yawansu na rayuwa ne a cikin yanayi na kunci saboda rashin abinci, ko muhalli balantana kula da lafiyarsu. A wannan yanayi ne aka kafa wata kungiya mai suna ‘'Sure For You'' don taimaka wa irin wadannan matakarantu da kuma tabbatar da cewa yaran sun samu kulawar da ta dace. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Mohammed Babandede, tsohon shugaban hukumar shige-da-fice ta Immigration a Najeriya wanda shi ne shugaban wannan kungiyar, domin jin abin da ya zaburar da su don daukar wannan mataki.
A Jamhuriyar Nijar, bayan da kungiyoyin kwadago da na fararen hula suka yi barazanar sanya kafar wando daya da gwamnati saboda karin farashin man dizil daga bisani shugaba Mohamed Bazoum ya gana da shugabannin kungiyoyin don yi musu karin bayani kan dalilan daukar matakin. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Maikoul Zodi, daya daga cikin shugaban Tournons la Page, daya daga cikin kungiyoyin fararen hular da suka halarci wannan ganawar da shugaban kasa, domin jin abin da suka tattauna akai.
Shirin Tarihin Afirka na wannan mako tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya dora kan na makon jiya game da tarihin dan gwagwarmaya na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Patrice Lumumba da ya taba rike mukamin Firaminista bayan samun 'yancin kai daga kasar Belgium.
A yau larabra 3 ga watan Agusta Jamhuriyuar Nijar ta gudanar da bukukuwan cika shekaru 62 da samun ‘yancin-kai, bayan share kusan shekaru 70 na mulkin mallakar Faransa. Kamar dai kowace shekara, daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan, a gefe daya ana amfani da wannan rana ta ‘yancin-kai domin dasa milyoyin itatuwa saboda yaki da gurgusowar hamada a duk fadin kasar. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Sani Roufa'i, mazauni birnin Damagaram da ke sharhi kan lamurran da suka shafi kasar. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da sauya wa kwamandojin da ke jagorantar manyan rundunoninta hudu wuraren aiki, a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar kasar. Wannan mataki dai ya zo ne sa'o'i kadan bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya gana da manyan hafsoshin tsaron kasar a birnin Abuja, yayin da kusan a kowace rana ta Allah ake ruwaito cewa ‘yan bindiga sun kai hare-hare kan jama'a da kuma kan shingayen binciken jami'an tsaro. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ibrahim Ya'u Galadanci, daya daga cikin shugabannin matasan Arewacin Najeriya, wanda ke cewa dole sai mahukunta su sake daura damara don tunkarar wannan matsala ta tsaro. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
A Najeriya, lura da tsadar makamashi musamman ma diezel da kuma man fetur, wannan ya sa kungiyar masu motocin sufuri da hadin gwiwar gwamnatin tarayya, ta fara jarraba amfani da iskar gaz da ake kira LNG da ake ganin cewa ya fi sauki a wajen farashi da kuma karancin gurbata muhalli. Tuni dai kungiyar masu motocin sufuri da ake kira Rtean ta kaddamar da motoci sama da dubu biyu da 300 da ke amfani da wannan sabuwar fasaha maimakon diesel, kamar dai yadda shugaban kungiyar Alhaji Musa Muhammad Maitakobi ya yi wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal karin bayani a zantawarsu.
Ministar kudi da tsare-tsare ta Najeriya Zainab Ahmed ta ce a shekara mai zuwa (2023) gwamnati za ta kashe Naira tiriliyan 6 da bilyan 700, wato kwatankwancin dala bilyan 16 a matsayin tallafi ga bangaren man fetur na kasar, wato karin kusan70% fiye da abin da gwamnatin ke biya a wannan shekara ta 2022. Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gwamnatin ta sanar da kammala sayar da hannayen jarin kamfanin mai na kasar wato NNPC, yayin da a hannu daya aka yi karin farashi a kan kowace lita ta mai a sassan kasar. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ibrahim Garba Wala, mai sharhi kan lamurran yau da kullum a kasar, inda da farko ya tambaye shi karin bayani a game da abin da ake nufin da kudin tallafi.
Shirin 'Tarihin Afirka' na wannan lokaci tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya cigaba da kawo wa masu sauraro tarihin tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara, wanda aka yi wa kisan gilla a bakin aiki. Marigayi Thomas Sankara na daga cikin jerin tsofaffin shugabannin nahiyar Afirka da aka yi amannar cewa suna cike da kishin kasa da kuma nahiyarsa, zalika yana kan turbar samar da gyara a tsarin shugabancin al'umma. Wannan shine kashi na karshe na tarihin wannan dan taliki.
Shirin 'Tarihin Afirka' na wannan lokaci tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya ci gaba da kawo wa masu sauraro tarihin tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara, wanda aka yi wa kisan gilla a bakin aiki. Marigayi Thomas Sankara na daga cikin jerin tsofaffin shugabannin nahiyar Afirka da aka yi amannar cewa suna cike da kishin kasa da kuma nahiyarsa, zalika yana kan turbar samar da gyara a tsarin shugabancin al'umma.
Shirin 'Tarihin Afirka' na wannan lokaci tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya cigaba da kawo wa masu sauraro tarihin tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara, wanda aka yi wa kisan gilla a bakin aiki. Marigayi Thomas Sankara na daga cikin jerin tsofaffin shugabannin nahiyar Afirka da aka yi amannar cewa suna cike da kishin kasa da kuma nahiyarsa, zalika yana kan turbar samar da gyara a tsarin shugabancin al'umma.
Shirin 'Tarihin Afirka' na wannan lokaci tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya cigaba da kawo wa masu sauraro tarihin tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara, wanda aka yi wa kisan gilla a bakin aiki. Marigayi Thomas Sankara na daga cikin jerin tsofaffin shugabannin nahiyar Afirka da aka yi amannar cewa suna cike da kishin kasa da kuma nahiyarsa, zalika yana kan turbar samar da gyara a tsarin shugabancin al'umma.
Yayin da aka share tsawon watanni biyar malaman jami'o'i na gudanar da yajin aiki a Najeriya, har yanzu babu wata alamar da ke tabbatar da cewa ana daf da kawo karshen wannan yajin aiki, duk kuwa da tattaunawar da aka sha yi tsakanin wakilan kungiyar malaman wato ASUU da kuma wakilan gwamnati. A watanni da suka gabata ,kungiyar malaman jami'o'I ta kasar ASUU ta sanar da tsawaita yajin aikin gargadin da ta tsunduma zuwa makwanni 12 a nan gaba saboda abin da ta kira rashin yunkuri daga gwamnati wajen kwatanta kokarin mutunta bukatun da ta shigar, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da sukar gwamnati kan yadda harkokin ilimi ke kokarin durkushewa a kasar To domin jin inda aka kwana, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Muhammad Adamu Babayo, daya daga cikin shugabannin kungiyar ta ASUU, ga kuma zantawarsu.
Masana tattalin arziki dai na ci gaba da yin kashedi dangane da yadda wannan yaki da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine ke neman haifar da talauci da wasu matsaloli musamman ga kasashe masu tasowa. A yau alhamis aka cika wata hudu da shiga yakin Ukraine da Rasha,sai dai duk kokarin manyan kasashe na kawo karshen wannan rikici ya cutura. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Farfesa Kabiru Isah Dandago, masani tattalin arziki kuma malami a jami'ar Bayero da ke Kano, domin jin yadda wannan yaki ke shafar kasashe musamman na Afirka.
Shirin 'Tarihin Afirka' na wannan lokaci tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya cigaba da kawo wa masu sauraro tarihin tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara, wanda aka yi wa kisan gilla a bakin aiki. Marigayi Thomas Sankara na daga cikin jerin tsofaffin shugabannin nahiyar Afirka da aka yi amannar cewa suna cike da kishin kasa da kuma nahiyarsa, zalika yana kan turbar samar da gyara a tsarin shugabancin al'umma.
Yayin da yakin Russia da Ukraine ke ci gaba da haddasa hauhawar farashin kayan abinci a sassan duniya, yanzu haka wasu kasashe na sun fara daukar matakai da kuma shimfida sabbin dubaru domin tunkarar wannan matsala. To sai dai ana iya cewa mafi yawan kasashen Afirka sun dogara ne da ketare don samun abinci da sauran kayan masarufi. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhajii Yakuba DanMaradi, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da ake kira SIN a Jamhuriyar Nijar, domin jin yadda yake kallon wannan matsala.
Hukumar Kula da Ayyukan Sadarwa a Najeriya, ta bayyana sunayen kamfanoni biyu wato MTN da kuma Mafab a matsayin wadanda suka cancanci fara aiki da sabuwar fasahar sadarwa ta 5G a kasar. Hukumar ta NCC, ta bayyana 24 ga watan Agustan wannan shekara a matsayin ranar da kamfanonin za su fara amfani da sabuwar fasahar. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Adamu Garba, na kamfanin IPI Solutions Group wanda yak ware a fannin ayyukan sadarwa, wanda da ya fara da yi masa bayani game da abin da ake nufin 5G.
Ranar talata 3 ga watan Mayu ake gudanar da bikin tunawa da zagayowar ranar ‘yancin aikinm jarida a duniya, inda wani rahoto da kungiyar kare ‘yan jaridu ta 'Reporters Without Borders' ya bayyana yadda kafafen sada zumunta ke neman gurbata aikin jarida ta hanyar yada labaran karaya da kuma wadanda ke tunzara jama'a. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Hon Muhammad Sani Zoro, tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida a Najeriya wato NUJ, wanda da farko ya fara yi masa bayani a game da muhimmacin kebe wannan rana.
An shiga wata na hudu da jami'o'in Najeriya ke ci gaba da kasancewa a rufe sakamakon yajin aikin da malamai suka tsunduma don neman gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Muhammad Danjuma Katsina, marubuci kuma mai sharhi kan lamurran yau da kullum, wanda ya yi mana tsokaci a game da tasirin wannan yajin aiki dangane da makomar matasa a Najeriya.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya wato NDLEA, ta bukaci a fara yi wa masu neman tsayawa takarar neman wasu mukaman siyasa ciki har na shugaban kasar gwaji domin tabbatar da cewa ba sa mu'amala da miyagun kwayoyi. Shugaban hukumar ta NDLEA Janar Buba Marwa mai ritaya ne ya bukaci a fara wannan gwaji a wasikar da ya aika wa jam'iyyun siyasar kasar. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Sule Ammani Yari, mai bin diddigin lamurran siyasar kasar domin jin yadda yake kallon wannan shawara da NDLEA ta gabatar.
Shirin 'Tarihin Afirka' kashi na 5/20 tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya kawo ci gaban tarihin Thomas Sankara, shugaban kasar Burkina Faso, wanda aka wa kisan gilla a bakin aiki.
Shirin 'Tarihin Afirka' kashi na 4/20 ya kawo ci gaban tarihin Thomas Sankara, shugaban kasar Burkina Faso, wanda aka wa kisan gilla a bakin aiki. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ne ya shirya, ya kuma gabatar da shirin, wanda yake zuwa muku duk ranar Asabar da maraice, a kuma maimaita ranar Lahadi da safe.
Wata tawagar manyan jami'an gwamnatin Chadi karkashin jagorancin ministan tsaro kasar Daoud Yaya Brahim ta gana da shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustine Archange Touadéra a birnin Bangui. Babban daliin wannan ganawa shi ne yadda za a sake bude iyakar kasashen biyu, wadda aka rufe tun 2014 a lokacin mulkin shugaba Idris Deby. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Idris Adamu Sarkin Hausawa daga kasar ta Chadi, dominm jin muhimmancin sulhuntawa tsakanin Chadi da makotanta.
A Najeriya yayin da bayanai ke nuni da cewa ‘yan bindiga da ke addabar jama'a a jihohin Arewa maso yammacin kasar sun shiga dimuwa saboda matsanantan hare-haren da suke fuskanta daga dakarun gwamnati, a daya bangare kuwa bayanai na nuni da cewa yanzu haka wata tawagar gwamnati na can tana ganawa da jagoran ‘yan bindigar wanda aka fi sani da suna Turji. A game da wannan lamari ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Shu'aibu Shinkafi, dan asalin jihar Zamfara mai fama da ‘yan bindiga, ga kuma zantawarsu.
Gobe asabar za a gudanar da zaben shugaban kasar a Gambia da ke yammacin Afirka, zaben da zai kasance na farko ba tare da tsohon shugaba Yahya Jammeh ba, wanda ya mulkin kasar tsaron shekaru 22 kafin kawar da shi a watan janairun 2017. Mutane 6 ne za su kara da juna a zaben na gobe ciki har da shugaba mai-ci Adama Barrow. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Sani Yahaya Janjouna, masani salon siyasar kasashen Afirka, domin jin yadda yake kallon wannan zabe na gobe, ga kuma zantawarsu.
Yanzu haka ana ci gaba da shiryes-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 24 ga wannan wata na disamba a Libya. To sai dai masu lura da lamurran da ke faruwa a kasar, na ganin cewa abu ne mai wuya a iya gudanar da wannan zabe a cikin kyakkyawan yanayi, lura da cewa har yanzu akwai dubban sojin haya da ke ci gaba da rike makamai a kasar. Kan hakan Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Hammi Souleyman, wani tsohon jami'in diflomasiyyar Nijar a birnin Tripoli, ga kuma zantawarsu.
Akalla mutane 3 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 18 suka samu raunuka a arangamar da aka yi tsakanin jami'an tsaro da kuma mutanen garin Tera da ke jihar Tillabery a jamhuriyar Nijar, wadanda ke nuna adawa da wani ayarin sojojin Faransa da ke hanyarsa ta zuwa kasar Mali. Tahirou Guimba, tsohon jami'in tsaro a Nijar, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal wasu daga cikin dalilan da suka sa jama'a ke nuna adawa da kasantuwar sojin Faransa a yankin Sahel.
Daya ga watan gobe na disamba ita ce ranar da gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bai wa ma'aikatanta domin su yi allurar kariya daga cutar covid-19, to sai dai alkalumma na nuni da cewa adadin wadanda suka karbi allurar sau biyu bai wuce 3% ba. To domin jin dalilan da suka sa mafi yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya suka ki karbar allurar, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Comrade Nasiru Kabir, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin kwadagon kasar, ga kuma zantawarsu.
Yanzu haka dimbin motocin sufuri da dama ne dauke da kaya suka tsaya cak a kan titunan Jamhuriyar Nijar, yayin da wasu suka makale a tashar jiragen ruwan Cotonou, sakamakon wani sabani da ya kunno kai tsakanin masu motocin sufuri na kasar da kuma wadanda aka bai wa kwangilar sufurin bututun man fetur da China ke shirin shimfidawa daga Nijar zuwa Jamhuriyar Benin. A kan wannan batu ne, AbdoulKarim Ibrahim Shikal ya tattauna da Alhaji Hima Barkire, daya daga cikin shugannin kungiyar masu motocin dakon kaya a jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sautin domin sauraren cikakkiyar hirar
Gwamnatin Jamhiryar Nijar ta ce yanzu haka akwai wasu da ke safarar mutane inda suke kai su kasashen ketare don yin bara. Ta ce za a zakulo wadannan mutane tare da gurfanar da su gaban kotu, yayin da ake shirin dawo da mabaratan zuwa gida. A game da wannan yunkuri na gwamnatin Nijar, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Moustapha Kadi, wani mai fafutukar kare hakkin dan adam a kasar.
Yayin da akasarin jihohin yankin Kudancin Najeriya suka sanar da kafa dokokin dake hana kiwon dabbobi a fili, yanzu haka wasu jihohi a arewacin kasar sun kaddamar da shirin karbar Fulani makiyaya a jihohinsu. Jihar Kano, na daya daga cikin jihohin da suka warewa filaye don bai wa Fulani damar gudanar da sana'arsu ta kiwo. Ishaq Mukhtar Yaksai, shi ne Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Kano, ya yi wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal karin bayani.
A Najeriya, babban batun da ke ci gaba da daukar hankulan jama'ar kasar shi ne yadda gwamnatin ta kaddamar da farautar jagororin masu da'awar raba kasar. Bayan tasa keyar Mazi Nnamdi Kanu da ke jagorantar ‘yan Biafra, daga bisani jami'an tsaro sun kaddamar da samame gidan Sunday Igboho da ke cewa zai kafa kasar Yarbawa, wanda yanzu haka yake boye. Dangane da wannan batu Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya tattauna da Sarkin Hausawan Lagos, Alhaji Muhammad Aminu Yaro Dogara, kuma kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikekkiyar hirar da sukayi.
A Jamhuriyar Nijar, an kulla wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Birnin Yamai da kuma wani kamfanin kasar Maroko mai suna YMMY Finance Holding, domin gina wata kasaitacciyar unguwa, da wata cibiyar da za ta kunshi rukunin masana'antu, wutar lantarki da kuma bunkasa ilimi a birnin. Kamfanin na kasar Maroko ya ce zai kashe Dala bilyan uku da milyan 300 domin gudanar da wadannan ayyuka da za a kammala cikin shekaru 8 masu zuwa. To domin jin muhimmancin wadannan ayyuka, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Yakuba Danmaradi, wanda mamba ne a majalisar ‘yan kasar kasuwar kasar ta Nijar. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu
Ana ci gaba da samun yawaitar hare-hare musamman a yankin kusurwar kan iyakokin Nijar, Burkina Faso da kuma Mali, inda mafi yawan lokuta fararen hula ne ke rasa rayukansu. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Boubacar Diallo, shugaban kungiyar makiyaya a yankin arewacin Tillaberi daya daga cikin yankunan da suka fuskantar irin wadannan hare-hare a jamhuriyar Nijar, ga kuma zantawarsu.
A yau litinin dubun dubatar mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a garin Idlib da ke matsayin tungar karshe ta ‘yan tawayen kasar Syria, domin tunawa da cika shekaru 10 da barkewar bore, wanda ya rikide zuwa yakin basasa. Alkaluma dai na nuni da cewa akalla mutane dubu 388 ne suka rasa rayukansu a wannan rikici. Dangane da wannan rikici ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Yunusa Muhammad Haruna malami a jami’ar jihar Katsina, kuma masani a game da kasashen Gabas ta Tsakiya.
A cikin shirin"Al'adunmu Na Gado" na wannan mako, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi dubi ne da al'adar tauri a kasar Hausa.
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi dubi ne game da rasuwar marigayi mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris wanda ya yi ban-kwana da duniya a karshen da ya gabata yana da shekaru 84.
Wata kungiya da ke fatan samar da zaman lafiya da ci gaba a tarayyar Najeriya ta nemi a gudar da bincike kan mutanen da ‘yan sanda suka kama a jihar Zamfara cikin kwanakin da suka gabata, bisa zargin cewa sun yi ganawar sirri da wasu tubabbin ‘yan bindiga da suka yi kaurin suna wajen aikata kisa da kuma yin garkuwa da mutane a jihar. To sai dai kungiyar ta yi zargin cewa sakamakon matsin lamba da kuma tsoma bakin wasu manyan ‘yan siyasa daga Abuja, ala dole jami’an tsaro suka saki mutanen 16. Dr Sani Abdullahi Shinkafi shi ne shugaban kungiyar, ga kuma abin da ya shaida wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal.
A Najeriya,sakamakon tsanantar cunkoson ababan hawa, masamman a birnin Lagos, mafi yawan mutane sun zabi yin amfani da hanyoyin sufuri na jiragen ruwa domin isa wuraren aiki da kuma kasuwancinsu.To sai dai wata matsalar da ake fuskanta ita ce yawan faruwar hatsurran da kan yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a wadannan jirage.To domin jin karin bayani game da tsarin sufurin ruwa a Lagos, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Ahmad Isma’il, wani da ke amfani da irin wadannan jirage domin kauce wa cunkoso, ga kuma zantawarsu.
Kungiyoyin kasa da kasa na ci gaba da yin tir da kuma Allah wadai da juyin mukin da sojoji suka yi wa shugaba Ibrahim Boubacar Keita na Mali, yayin da wani lokaci a Laraba Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da taron gaggauwa dangane da wannan lamari. Tuni dai sojojin da suka kwaci mulkin suka bayyana aniyarsu ta kafa gwamnatin rikon kwarya, tare da shirya zabubuka don sake mayar da kasar a kan tafarkin dimokuradiyya a nan gaba. A game da wannan lamari ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal na zanta da Alkassoum Abdourahman, masani siyasar kasar ta Mali.
A Talatar nan, al’ummar Chadi suka gudanar da bukukuwan cika shekaru 60 da samun ‘yancin kan kasar daga turawan mulkin mallakar Faransa. Sai dai bikin na bana ya sha bamban da na shekarun da suka gabata, domin kuwa an yi amfani da wannan rana wajen bai wa shugaban kasar, Idris Deby Itno mukamin Marshall, sakamakon rawar da ya taka don samar wa kasar ci gaba. Sarkin Hausawa N’djamena Mai Martaba Alhaji Mustapha Ibrahim Ahmad, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal muhimmancin wannan rana ga al’ummar kasar ta Chadi.
Mahukunta a Jamhuriyar Nijar, sun ce ko shakka babu za a sake bude makarantun bokon kasar a ranar litinin mai zuwa bayan share kusan kwanaki 70 a rufe sakamakon annobar coronavirus. Ministan ilimi mai zurfi na kasar kuma shugaban kwamitin da ya kunshi masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimi a kasar Yahouza Sadissou, ya bayyanawa Abdoulkarim Ibrahim Shikal irin matakan da gwamnati ta dauka kafin sake bude makarantun.
Masu manyan motocin dakon kaya a Najeriya, na zargin jami’an tsaro a wasu jihohi na kasar da fakewa da dokokin da aka kafa don yaki da cutar covid-19 inda suke tursasawa tare da lafka masu tarar makudan kudade. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Umar Garba Alangawari, daya daga cikin masu motocin dakon kaya daga Apapa da ke Lagos zuwa arewacin Najeriya, wanda ya bayyana wasu daga cikin jihohin da suka fi fuskantar wadannan matsaloli.
A ranar litinin 25 ga watan Mayu, aka gudanar da bukukuwan zagayowar ranar Tarayyar Afirka, wadda ta yi daidai da cika shekaru 57 da kafa kungiya ta farko don hada kan nahiyar ta Afirka AU. Ibrahim Yakubu, tsohon ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar, ya bayyana muhimmancin ranar Tarayyar ta Afrika, yayin zantawa da AbdoulKarim Ibrahim Shikal.
Coronavirus, annoba ce da ta shafi kusan kowace bangare ciki har da na tattalin arziki a duniya, a wasu kasashen kasashen kuma lamurra suka tsaya cak tsawon watanni biyu zuwa uku da suka gabata sakamakon wannan annoba. Sai dai a Najeriya, bangaren sufuri musamman na ruwa na daga cikin fannonin da gwamnatin kasar ta baiwa damar kasancewa a bude tsawon wannan lokaci. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta Kontrolan Kwastam a tashar jiragen ruwan Apapa, Muhammad Abba-Kura, domin jin ko watakila wannan matsala ta shafi aikinsu da kuma kudaden shigar da suke samarwa Najeriya a tashar ta Apapa dake birnin Legas.
Shirin Tarihin Afrika tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal a wannan Mako ya dora daga inda ya tsaya a kashi na 1 cikin tarihin tsohon shugaban kasar Mali Moussa Traore da ya yi gwagwarmaya da turawan Faransa.
A ci gaban shirin kasuwa a kai miki dole cikin wannan makon, tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, ya dora ne kan batun makomar aikin hakar makamashin Uranium a Jamhuriyar Nijar, wanda ke fuskantar barazanar samun koma baya.
A wannan makon muna dauke da kashi na farko na tarihin tsohon shugaban Jamhuriyar Congo Mubutu Sese Seko tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal. A yi saurare lafiya.