POPULARITY
Yau shirin 'Mu Zagaya Duniya' shiri ne na musamman a kan ta'aziyyar abokin aiki, kuma mataimakin editan sashen Hausa na RFI, garba Aliyu Zaria, wanda Allah ya wa rasuwa a ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairu, 2022.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Garba Aliyu Zaria ya yi bitar labaran makon jiya da suka hada da, yadda dakarun Amurka suka kashe jagoran IS a Syria, da kuma gustiri tsoma da ke ci gaba da wakana da kungiyar tsaro ta NATO da Rasha a kan Ukraine, da dai sauran mahimman labaran da hali ya yi aka samu yin bitar su.
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya fara ne da bitar halin da ake ciki dangane da rikici tsakanin Rasha da Ukarine.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon da ke bitar manyan labarun da suka faru a makon da ya kare tare da Garba Aliyu Zaria, ya fara ne daga kasar Kazakhstan inda kazamin boren adawa da gwamnati.
Shirin 'Kasuwa a Kai Miki Dole' tare da Garba Aliyu Zaria ya yi tattaki zuwa babbar kasuwar kayan gwari ta Mile 12 da ke birnin Legas inda ya zanta da shugabannin kasuwar da sauran masu ruwa da tsaki kan halin da take ciki, bayan kawo karshen rigingimu a tsakanin kabilun da ke cudanya da juna.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Garba Aliyu Zaria ya waiwayi halin da ake ciki tsakanin hukumomin kasa da kasa dangane da kokarin dakile yaduwar annobar Korona da a halin yanzu aka gano wani sabon nau'inta da ya bulla a kasar Afirka ta Kudu, wanda kwararru suka sanyawa suna Omicron.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Garba Aliyu Zaria da ke bitar muhimman labarai, ko lamurran da suka wakana a makon da ya kare, ya maida hankali kan taron tsaro da Faransa ta karbi bakwanci, da kuma taron yanayi na Glasgowa a kasar Scortland.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Garba Aliyu Zaria da ke bitar muhimman labarai, ko lamurran da suka wakana a makon da ya kare, ya maida hankali kan ganawar karon farko tsakanin shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron don warware rikicin diflomasiyya dake tsakaninsu kan batun kwace cikinkin jirgin yakin karkashin teku na Australiya.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Garba Aliyu Zaria da ke bitar muhimman labarai, ko lamurran da suka wakana a makon da ya kare, ya maida hankali kan rarrabuwar kawunan Turai na wasu kasashen duniya kan taimakawa kasar Afghanistan da kudade.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Garba Aliyu Zaria da ke bitar muhimman labarai, ko lamurran da suka wakana a makon da ya kare, ya maida hankali kan harin baya-bayan nan da wuka da aka akaiwa wani dan majalisar dokokin Birtaniya, wanda jami'an tsaro suka tattabar da cewa ta'addanci.
Shirin al'adunmu na gado tare da Garba Aliyu Zaria ya yi duba kan yadda Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ke cika shekara guda cur akan mulkin masarautar ta Zaria.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Garba Aliyu Zaria da ke bitar muhimman labarai, ko lamurran da suka wakana a makon da ya kare, ya maida hankali kan harin baya-bayan nan a Afhanistan kan masallacin 'yan shi'a da ya kashe mutane da dama.
Shugabannin kasashen da binciken Pandora Papers ya bankado sunayensu na kokarin wanke kansu daga zargin rahoton kan mallakar tarin dukiya boye a wasu kasashen duniya. Rahoton na nuna akwai shugabannin kasashen duniya 35 da suka kunshi tsoffi da masu ci da suka gwanance wajen cin hanci, da halatta kudaden haram da kaucewa biyan haraji. Kan haka Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Muntaka Usman na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ga kuma tattaunawarsu.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Garba Aliyu Zaria da ke bitar muhimman labarai, ko lamurran da suka wakana a makon da ya kare, ya maida hankali kan ranar bukin tunawa da samun 'yancin kan Najeriya daga turawan mulkin mallakar Birtaniya shekaru 61 da suka gabata.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon, Garba Aliyu Zaria ya duba abubuwan da suka faru a sassan duniya a makon da ya gabata, musamman ma halin da ake ciki a Guinea bayan da ECOWAS ta gana da shugabannin sojin da suka gudanar da juyin mulki.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon, Garba Aliyu Zaria ya duba abubuwan da suka faru a sassan duniya a makon da ya gabata, musamman ma halin da ake ciki a Amurka dangane da guguwar Ida da ta mamaye wasu yankunan kasar.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon, Garba Aliyu Zaria ya duba abubuwan da suka faru a sassan duniya a makon da ya gabata, musamman ma halin da ake ciki a Afghanistan da sauran su.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon, Garba Aliyu Zaria ya duba abubuwan da suka faru a sassan duniya a makon da ya gabata, musamman ma halin da ake ciki a Afghanistan da sauran su.
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan rana tare da Garba Aliyu Zaria ya yi waiwaye kan wasu daga cikin muhimman bautuwan da suka auku a makon da ya kare, ciki har da halin da ake ciki a Afghanistan bayan fara janyewar dakarun kasashen waje, abinda ya baiwa mayakan Taliban kaddamar da gagarumin farmaki kan dakarun kasar.
Garba Aliyu Zaria ya kawo mana bitar labaran abubuwan da sukan gudana a makon da ya gabata da suka hada da halion da ake ciki a game da yaduwar sabon nau'in annobar Covid-19.
A Najeriya, yanzu haka ana ta tafka muhawara game da batun biyan kudaden fansa ga masu garkuwa da mutane, ganin yadda wasu jihohi suka haramta biyan kudaden, duk da cewa an gaza daukan matakan ceto mutane da dama da ake garkuwa da su. Game da wannan al'amari Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Barr. Audu Bulama Bukarti, masani kuma mai nazari kan matsalolin ta'addanci a Najeriya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Garba Aliyu Zaria kamar yadda aka saba ya yi bitar wasu daga cikin muhimman labarun abubuwan da suka gabata a makon da ya kare, ciki har da yadda aka bankado wata manhajar kasar Isra'ila da ake amfani da ita wajen yiwa sama da mutane dubu 50 leken asirin wayoyinsu na Salula ciki harda shugabannin kasashen da fitattun 'yan jaridu.
Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Garba Aliyu Zaria ya fara waiwayar manyan labarun duniya a tsawon mako ne daga nahiyar Turai inda ambaliyar ruwa ta yi barna a kasashen Jamus da makwaftanta.
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Garba Aliyu Zaria ya kamar yadda aka saba yayi bitar wasu daga cikin muhimman labarun abubuwan da suka gabata a makon da ya kare, ciki har da yadda kasashen Turai suka soma amfani da takadar shaidar rigakafin Korona kafin yin balaguro.
A yanzu haka kasashen duniya da suka hada da Rasha da Turkiya da sauran kasashen larabawa na ta aikewa da sakonnin murna da fatan alheri ga sabon shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi bayan sanar da sakamakon zaben sa ranar Juma'a. Ebrahim Raisi mai shekaru 60 zai maye gurbin Hassan Rouhani wanda wa'adin mulkin sa ya cika. Dangane da wannan batu Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Dr Abdulkadir Mubarak mazaunin Tehran don jin wasu irin sauye-sauye ake fatan samu.
Shirin na wannan mako tare da Garba Aliyu Zaria ya waiwayi taron shugabannin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki na G7 da kuma taron kasashen kungiyar tsaro ta NATO, sai kuma Isra'ila da ta ce za ta mikawa Falesdinawa alluran rigakafin cutar Korona miliyan daya.
Gwamnatin Najeriya ta ware yau Litinin ta zama ranar hutu a fadin kasar don murnar ranar Dimokaradiya ta kowace ranar 12 ga watan Yuni. Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauya ranar ta Dimokaradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni don tuna zaben da aka yiwa Marigayi Mashood Kashimawo Abiola wanda ake kyautata zaton shi ne ya lashe zaben da Soja suka soke. Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dakta Jonathan Zangina Daraktan yakin neman zaben marigayi Abiola don sanin yadda suke kallon wannan rana.
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan rana tare da Garba Aliyu Zaria ya yi waiwaye kan wasu daga cikin muhimman bautuwan da suka auku a makon da ya kare, kamar yadda shirin ya saba yi kowane karshen mako. A yi sauraro lafiya.
A Najeriya, ganin yadda ake samun yawaitan hasarar rayukan mutane da dukiyoyi a yankunan kudu maso gabashin kasar Kungiyoyin Dattawa da ta Matasan Arewacin kasar sun bukaci mahukuntan kasar da su amince da bukatar masu fafutukan neman kasar ta Biafra. Garba Aliyu Zaria ya ji ta bakin Nastura Ashiru Sheriff shugaban komitin amintattu na gamayyar matasan Arewacin kasar kuma ga tattaunawar.
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' a wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya soma da waiwaye ne kan sabon dokar da shugaban Rasha Vladimir Putin ya kafa don hana 'yan adawa shiga zabukan kasar, sai kuma matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da shafin Twitter a kasar.
Rahotanni daga karamar Hukumar Katsina-Ala na jihar Benue a Nigeria na cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane akalla 100 a yankin Mbayongo. Kakin Rundunar ‘yan sandan jihar DSP Anene Sewuese Cathrine ta gaskata kai harin amman kuma ta ce suna dakon cikakken rahoton harin. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Malam Mamman Dan-tibi mazaunin yankin na Katsina-Ala don jin abin da ya yi zafi haka.
Kungiyar Dattawan Arewacin Nigeria ta ce ba ta adawa da duk wani kyakkyawan tsari da gwamnati za ta bijiro dashi don kyautata sha‘anin kiwo da makiyaya Fulani ke yi domin tafiya daidai da zamani. Sai dai kungiyar ba ta goyon bayan muzgunawa Fulanin makiyaya da sunan haramta musu kiwo. A kwanakin baya ne dai Gwamnonin jihohin kudancin Nigeria 17 suka gabatar da bukatar hana kiwo a jihohinsu, bayan wani taro da suka yi a garin Asaba na jihar Delta. Kan wannan batu Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dakta Hakeem Baba-Ahmed kakakin kungiyar Dattawan na Arewa.
Duk da kiraye-kiraye da manyan kasashen duniya ke ta yi don a tsagaita wuta a rikicin da ake yi tsakanin Israela da Palestinawa har yanzu babu alamun samun nasarar hana rikicin, yayinda ya ke ci gaba da lakume rayukan tarin fararen hular da basu ji ba basu gani ba. Koda a yau sai da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel da Sarki Abdallah na Jordan suka bukaci a gaggauta tsahaita wuta amman kuma lamarin babu sauki ko kadan. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Dr Abdulhakeem Garba Funtua mai sharhi game da harkokin siyasar duniya ko akwai mafita game da wannan rikici. Ga tattaunawar.
Shugabannin kasashen Afrika na halartar wani taro na musamman domin bunkasa tattalin arzikin kasashensu a Paris babban birnin kasar Faransa bisa gayyatar shugaba Emmanuel Macron. An fara taron ne da batun tallafawa kasar Sudan don tattalin arzikinta ya farfado bayan kwashe shekaru suna fama da rikice-rikice. Garba Aliyu Zaria ta tuntubi Farfesa Muntaka Usman na Jamiar Ahmadu Bello dake Zaria masanin harkokin tattalin arziki ko yaya yake kallon wannan taro.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon, Garba Aliyu Zaria ya yi mana bitar mahimman abubuwan da suka wakana a makon jiya, ciki har da luguden wuta da Isra'ila ke ci gaba da yi a yankin Falasdinawa. A yi sauraro lafiya.
A Najeriya, yau Alhamis ake dakon gabatar da dalibai 27 na kwalegin koyon Aikin Gona dake Kaduna da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata, bayan da aka yi nasarar kubutar da su jiya Laraba. Sakin daliban ya biyo bayan shiga lamarin da tsohon Shugaban kasar Olusegun Obasanjo da kuma fitaccen malamin addini Sheikh Dr Ahmed Gumi suka yi. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Usman Yusuf na hannun daman Sheikh Gumi wanda aka yi komi a gabansa, ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.
A cikin shirin "Mu Zagaya Duniya" na wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya yi bitar mahimman abubuwan da suka wakana a makon jiya, masamman nasarori da shugaban Amurka Joe Biden ya samu a kwanakin farko dari da yayi da kuma halin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya.
A yau Juma'a ne aka binne gawar marigayi Shugaban Chadi Idriss Deby Itno, kuma shugabannin kasashen duniya da dama ne suka halarci bikin. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Dr Abdulhakeem Garba Funtua, mai sharhi game da siyasar duniya yadda yake kallon Chadi bayan mutuwar Idris Derby Itno.
A cikin shirin mu zagaya Duniya ,Garba Aliyu Zaria ya mayar da hankali ga fadar Ingila,yan lokuta bayan da sanar da mutuwar Yarima Philip ya na mai shekaru 99 a Duniya. Mutuwarsa na zuwa ne a yayin da ya rage watanni kalilan a gudanar da bikin cikarsa shekaru 100 da haihuwa a cikin watan Yuni mai zuwa. Yariman ya auri Sarauniya Elizabeth a shekarar 1947, wato shekaru biyar kafin ta dare kan gadon sarautar Ingila, yayin da ma’auratan biyu suka kafa tarihin zama masu mulki mafi dadewa kan karaga a tarihin Birtaniya. Ma’auratan biyu na da yara hudu da jikoki takwas da kuma tattaba-kunni 10.
Kungiyar masu motocin sufuri ta Nigeria ta bukaci Gwamnatoci da su wadata matasa da ayyukan yi don kawo karshen rashin tsaro a manyan hanyoyin kasar da ke neman haifar da cikas ga matafiya. Shugaban kungiyar na Kasa Dr Musa Mohammed Maitakobi ya gabatar da bukatun kungiyar a tattunawa da Garba Aliyu Zaria. Ga tattaunawar.
Yayinda matsalolin rashin tsaro ke neman durkusarda harkokin yau da kullum a fadin Nigeria, bisa dukkan alamu lamarin ya kaima Gwamnatin Kasar wuya ayanzu, kuma ta sanar da Shirin tunkarar matsalar ayita ta kare. Ministan Tsaro Janar Bashir Magashi ya bada wannan tabbacia wani taro na musamman a Abuja da ya shafi harkan tsaron kasar. Garba Aliyu Zaria ya nemi ji daga bakin Dr Hakeem Baba-Ahmed kakakin Dattawan Arewa ko yaya su ke kallon wannan.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako, Garba Aliyu Zaria ya duba manyan labarai kan mahimman abubuwan da suka wakana a makon da ya gabata, ciki har da labarin mace ta farko da ta zama shugaban Tanzania, bayan mutuwar shugaba John Magafuli, da kuma yadda Tarayyar Turai ta amince da sahihancin maganin rigakafin cutar Covid-19 samfurin AstraZeneca.
Babbar Jamiyar adawa a Nigeria PDP ta yi tsokaci a game da lamarin rashin tsaro musammam satar mutane da ya zama babbar sana’a a arewacin kasar. Babban Sakaren Jam'iyyar ta PDP, Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya fadi a tattaunawar da suka yi da Garba Aliyu Zaria cewa sam, ba su yi likimo ba, lamarin ne ke basu mamaki da tsoro.
A cikin shirinmu na 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako, Garba Aliyu Zaria ya kewaya da masu sauraro sassa dabam-dabam na duniya don bitar mahimman abubuwan da suka wakana a makon jiya. Daga cikin abubuwan da suka auku, har ma da sace daliban kwalejin nazarin gandun daji a Kaduna, Najeriya da 'yan bindiga suka yi, inda gwamnatin jihar ke cewa an ceto 180 daga cikin wadanda aka sace.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dibawa ‘yan bindiga da suka hana sukuni a jihohin arewa maso yammacin Nigeria musamman Jihar Zamfara, wa’adin watanni biyu da su bada kai ko kuma ya sanya kafar wando daya da su. Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya gabatar da sakon shugaban kasar a jawabi ga al’ummar jihar. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Alhaji Tukur Mamu, dan Jarida, kuma mai sharhi gameda harkokin yau da kullum ko yaya yake kallon matakin.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya yi bitar mahimman abubuwan da suka wakana a makon jiya, masamman yadda kutun Faransa ta daure tsohon shugaban kasar Nicola Sarkozy tsawon shekaru uku, da kuma ziyarar da Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis ya kai kasar Iraki a karon farko, inda ya bukaci kawo karshen tsattsauran ra’ayi da rikice-rikice a duniya.
A Najeriya ana ta cece - kuce kan kalaman shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ke tabbatarwa ’yan Najeriya cewa daga satar daliban Makarantar Sakandiren Gwamnati ta ’Yan Mata dake Jangebe a jihar Zamfara ba za a sake sace dalibai a makarantu ba. Kuma kan haka Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dakta Mainasara Umar Faskari masanin diflomasiyar kasa-da-kasa da tsaro.
Rahotanni daga sassan kudancin Najeriya na cewa yajin aikin da Hadaddiyar Kungiyar masu fataucin dabbobi da kayan abinci suka fara karshen makon da ya gabata na matukar shafar kayan abinci a kudancin kasar, wanda tuni suka shiga karancin nama da sauran kayan masarufi. Kasuwanni da dama yanzu haka na fuskantar matsalolin karancin kayayyakin abinci saboda matakin da kungiyar dake arewacin Najeriya ta dauka na kin kaiwa da kayayyakin abinci kudancin kasar saboda zargin muzguna masu da ake yi, kuma kan haka ne Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Comrade Mohammed Tahir shugaban kungiyar da suka kira yajin aiki.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya yi bitar mahimman abubuwan da suka wakana a makon jiya, masamman matakin manyan kasashen duniya ke yi wajen wadata kasashen matalauta da rigakafin annobar koronna sai kuma batun sake sace 'yan matan sakadare sama da 300 a jihar Zamfara.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon, Garba Aliyu Zaria ya yi bitar mahimman abubuwan da suka wakana a makon jiya.
A cikin shirin al'adunmu na gado, za ku ji yadda Garba Aliyu Zaria ya bibiyi nadin sarautar Dan Iyan Yamma Alhaji Abubakar a Ibadan, basaraken da ke matsayin dan asalin kasar Nijar na farko da zai rike mukamin.
An yi bikin rantsar da zababben shugaban Amurka Joe Biden a matsayin shugaban kasa na 46, tare da mataimakiyar sa Kamala Harris a Majalisar dokokin Amurka. Bikin da ya gudana a Majalisar dokoki Amurka kamar yadda aka saba, shine irin sa na farko da shugaba mai barin gado yaki halarta a cikin shekaru 150, ganin yadda shugaba Donald Trump ya haure takalman sa ya tashi zuwa Florida, bayan yayi jawabi a cibiyar soji ta ‘Joint Base Andrews’ inda ya shaidawa magoya bayan sa cewa zai sake dawowa ta wata hanyar, bayan nasarorin da yace ya samu. Garba Aliyu Zaria a cikin shirin Mu zagaya Duniya ya mayar da hankali kan rantsar da sabon Shugaban Amurka Joe Biden,Shugaba na 46.
Kungiyar Agaji ta kasa da kasa da ake kira International Red Cross ta bayyana gamsuwa da aiwatar da dokar haramtawa kasashen duniya mallaka, samarwa ko kuma amfani da makaman nukiliya daga yau. Shugaban Kungiyar agajin Peter Maurer ya bayyana matsayinsu cikin wata sanarwa a yau. Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Alhaji Aliyu Dawobe kakakin kungiyar ta Red Cross a Najeriya don sanin tasirin wannan mataki.
Rahotanni daga jihar Kaduna sun ce sama da ‘yan bindiga 500 ake sa ran za su tuba tare da ajiye makamansu, biyo bayan tattaunawa da fitaccen malamin addinin Musulunci Shiekh Ahmad Gumi a baya bayan nan. A kan haka ne Garba Aliyu Zaria ya tuntube shi, kuma ga yadda tattaunawarsa ta kasance.
A Nigeria duk da matakan tsaro da hukumomin kasar ke ikirarin suna dauka, ana ci gaba da samun yawaitan satar mutane ana garkuwa da su, a sassan kasar musamman arewaci inda wasu bayanai ke nuna matafiya da masu zaman gida duka basu tsira ba. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Dr Kole Shettima masani kuma mai sharhi dangane da lamurran tsaro a kasar. ko me ya sa aka gaza shawo kan matsalar.
Hukumar tsaron FBI a Amurka ta ce Magoya bayan Donald Trump na shirin gudanar da zanga-zanga a wasu jihohin kasar 50. Bayan tsige Shugaba Donald Trump na Amurka da majalisar wakilan kasar ta yi jiya laraba, a yanzu haka masu ruwa da tsaki game da dorewar siyasar kasar sun maida hankula ne wajen samun nasarar rantsuwar kama aiki na sabon Shugaba Joe Biden. Jamian tsaron kasar dai sun karfafa matakan tsaro don gudun kada a mamaye su. Majalisar wakilan kasar dake da rinjayen ‘yan jam’iyar Democrat ta kada kuri’ar amincewa da tsige shugaban, a karo na 2, kuma irinsa na farko a tarihi da yawan kuri’u 232 a kan 197 na wakilan dake goyon bayansa. A zauren majalisar, ‘yan jam’iyyar Republican 10 ne suka goya wa takwarorinsu na Democrat baya, cikinsu har da kusa a jam’iyyar, Sanata Liz Cheney. An zargi hamshakin attajiri, kuma shugaban Amurka mai barin gado, mai shekaru 74 wanda zai mika ragamar mulki a ranar 20 ga wannan wata na Janairu, da tunzura masu zanga zangar da suka mamaye majalisar dattawan kasar a ranar 6 ga wata domin hana tabbatar da zaben Joe Biden mai shekaru 78, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 5, ya kuma zubar da mutuncin demokradiyar Amurka. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Khamilu Sani Fagge na Jamiar Bayero dake Kano don jin yadda yake kallon dambarwar siyasar Amurkan.
Sashen hukumar yaki da fasa-kwauri na Najeriya da ke tashar jiragen ruwa na Apapa a jihar Lagos, ya sanar da kame kwantainoni 133 makare haramtattun magungunan asibiti ciki har da kwayar Tramol. A wani taron manema labarai da hukumar ta kira shugaban shiyyar Alhaji Mohammed Abba-Kura ya ce za su ci gaba da kara kaimi a yaki da ayyukan fasakwauri ta tashar ruwan. Ga dai yadda tattaunawarsu ta gudana da Garba Aliyu Zaria.
A Najeriya, ganin yadda matsalolin satar mutane don neman kudaden fansa ke kara taazzara, musamman a Arewacin kasar, Babbar Jamiyar adawa PDP ta dora laifin kan gazawar kan shugabanci na jam'iyya mai mulki wato APC, kuma Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Ambassador Ibrahim Kazaure jigo a jamiar adawar.
A Nigeria yayinda ake Shirin shiga sabuwar shekara alamu na nuna akwai karuwar mutane da ke harbuwa da kwayar cutar Coronavirus a duk rana. Wannan na zuwa ne a wani lokaci da manyan kasashen duniya ke ta kokarin fara gwajin alluran rigakafin wannan cuta da aka gano. Garba Aliyu Zaria ya nemi ji daga Dr Nasiru Sani Gwarzo kwararren likita a Nigeria ko me ke haifar da hauhawan.
Shiri na tattalin arziki na wannan mako zai leko kasuwar Mile 12 dake Lagos a kudancin Najeriya.Wannan kasuwa dai da ake kira kasuwar Mile 12 dake Lagos ta yi fice sosai bama a jihar Lagos ba, a kudancin kasar domin takan sami baki har daga wajen kasar musamman kasashen Togo, Benin Ghana da su Kamaru akan sami ‘yan kasuwa dake kawo kayan abinci daban-daban don saidawa. Garba Aliyu Zaria ya je kasuwar inda ya samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki aharkokin cinikaya a kasuwar Mile 12.
Yayin wata ziyara da Gwamnan Borno Babagana Zulum ya kai kauyen Jakana da Auno a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda aka sace matafiya 35 karshen mako, Gwamnan ya dora laifin rashin tsaron kan gazawar jamian tsaro wadanda aka zuba a kan hanyoyi. Sai dai kuma wata sanarwa da Sojan kasar suka bayar na cewa Kazafi ne Gwamnan yayi masu cewa suna karban na goro daga matafiya. A makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum ya gana da shugaban Chadi Idris Deby lokacin da ya ziyarci kasar domin ganin halin da Yan gudun hijirar Jihar sa ke ciki da kuma shirya yadda za’a mayar da su gida. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Khalifa Dikwa don jin yadda yake kallon wannan dambarwa.
Alummar jihar Borno dake arewa maso Gabashin Najeriya na cikin zaman makoki yanzu haka sakamakon kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai tare da kashe sama da mutane 100 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar, akasarinsu manuma shinkafa. Wannan ya kasance mafi muni a cikin hare-haren da mayakan kungioyar Boko Haram ke kaiwa duk da matakan da Gwamnatin kasar ke cewa ta na dauka. Dangane da haka, Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Mohammed Kabir Isa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, wanda ke bincike dangane da ayyukan Boko Haram.
Najeriya ta sake fadawa cikin matsin tatalin arziki a karo na biyu cikin shekaru 5 sakamakon annobar Covid 19 da faduwar farashin danyen mai, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta bayyana a ranar Asabar. To sai Masana harkokin tattalin arziki a Najeriya dai na ganin matsalar ba mai daurewa ba ce, kuma ya shafi kasashen duniya da dama, saboda yanayi na annobar korona da ya haifar da faduwar farashin man fetur. Dangane da haka ne Garba Aliyu Zaria ya tattauna Dakta Kasim Garba Kurfi masanin tattalin arziki a Najeriya.
Shirin Mu Zagaya Duniya da wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya tabo mayan labaran da ya kamata mai sauraro ya sani cikin makon da mukayi bankwana da shi, musamman labarin yunkurin karade duniya da maganin rigakafin cutar korona da wasu kamfanoni suka samar, da kuma tirjiyar da shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ke nuna kan rungumar kaddarar faduwa zabe.
Tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo ya bayyana fargabar cewa zaben shugagban kasar dake gudana a yau asabar na iya haifar wa kasar da tashin hankali, a tsokacin da ya yi a game da kasar tun da ya sauka daga mukamin shugaban kasa a shekarar 2011.Garba Aliyu Zaria a cikin shirin Mu zagaya Duniya ya mayar da hankali a kai tareda duba wasu daga cikin manyan labaraen Duniya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar mutane 69 suka mutu sakamakon tarzomar da aka samu lokacin zanga zangar adawa da cin zarafin yan Sanda, yayin da 37 suka samu raunuka, kuma adadin ya hada da fararen hula da jami’an Yan Sanda da kuma soji.Garba Aliyu Zaria ya mayar da hanakali a cikin shirin Mu zagaya Duniya.
Rohatanni daga jihar Legas a Najeriya na cewa gwamnatin jihar ta yi asarar kimanin Naira miliyan 400 sakamakon rikicin da ya barke a jihar, biyo bayan zanga-zangar EndSars da ake yi, duk da cewa har yanzu ba'a kammala bincika ba, yayin da Juma’an nan gwamnan Jihar Babajide Sanwo-Olu ya aki rangadin gani da ido na wuraren da aka yi ta'adi sakamakon tarzomar. Shugaban Cibiyar Kasuwanci Ta Legas, Muda Yusuf, ya shaidawa manema Labarai, cewa har yanzu ba'a kai ga tattara alkaluma kan kiyasin asarar da wannan tarzoma ta jawo ba, amma an yi asarar kimanin naira biliyan 400. Tarzomar da ta barke a Legas ta haifar da matsaloli da ta kai ga kona gine-ginen gwamnati da na al’umma. Cikin wuraren da aka kona tun a daren Talata kafin wayewar Laraba, sun hada da wani Babban Otel da wani asibiti baya ga ofisoshin ‘yan sanda. Yayin da ranar Laraba aka cinna wuta a cibiyar Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA, da kuma gidan talabijin na TVC da ke Legas din, tare da ofishin Hukumar kiyaye haddura da wani sashe na sakatariyar Legas. Kazalika, fusatattun masu zanga-zangar sun bankawa tashar motocin BRT na gwamnatin Lagas dake Oyingbo wuta, inda motocin Bus na safa-safa da dama suka kone, yayin da aka kai hari kan bankuna a wasu sassan birnin. A bangare daya, bayanai sunce ankuma kona gidan mahaifiyar gwamnan jihar Baba Jide Sanwo – Olu, yayin da suka farma gidan sarkin Lagas, wanda yasha da kyar, inda aka wawure kayayyakinsa da dukiyoyi. Dangane da wannan batu, Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Dr. Kasimu Garba Kurfi masanin tattalin arziki a Najeriya don jin yadda suke kallon irin hasarar da aka tafka.
Rahotanni daga Najeriya na cewa masu zanga zanga a wasu sassan kasar na ci gaba da yin fito na fito da jami'an tsaro, inda majiyoyi ke fadin an rasa rayukan akalla mutane 10 tare da kona ofishin 'yan sanda a jihar Edo da Legas da kuma hana walwala. Ganin irin halin d ake ciki, Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dokta Tukur Abdulkadir na jami'ar Kaduna ko yaya masana ke kallon wannan dambarwa.
A Najeriya an shiga rana ta takwas ana ci gaba da bore a wasu sassan kasar inda matasa ke neman Hukumomin kasar su aiwatar a zahiri ikirarin rusa ayarin ‘yan sandan yaki da ‘yan fashi da makami da ake kira SARS. Yayinda a wasu sassan kasar masu boren ke neman a soke rundunar ‘yan sandan, a yankunan arewa maso gabashin kasar da kuma Jihar Katsina masu boren na goyon bayan kada a ruwa ‘yan sandan domin su suke yakar ‘yan kungiyar Boko Haram. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Jibrin Ibrahim mai lura da lamurran kasar kuma ga bayanin da yayi.
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa dan sandan nan farar fata Derek Chauvin, da ake zargi da kisan wani bakar fata George Floyd, al’amarin da ya haifar da kazamin bore a sassan kasar, yanzu haka dai an bada belin sa kuma har ya fice daga gidan yari da ake tsare da shi. An bada belin dan sandan ne akan kudi Dalan Amurka miliyan guda, kan hakan Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Alhaji Garba Sulaiman Krako Saminaka mazaunin Amurka da ke bibiyar lamarin kuma ga bayanin da ya yi mana.
Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Garba Aliyu Zaria na wannan lokaci ya soma ne da lekawa birnin Paris a Faransa, inda aka sake kaiwa ofishin mujalar wallafa zanen barkwanci ta Charlie Hebdo da ta ci zarafin addinin Musulunci.
Kamar yadda aka saba a kowane mako, shirin Mu Zagaya Duniya tare da Garba Aliyu Zaria, ya waiwayi wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankula a makon da ya kare, cikinsu kuwa har da halin da ake ciki a sassan duniya bayan sake barkewar annobar coronavirus, musamman a nahiyar Turai.
Kungiyar direbobin tanka masu dakon man fetur ta baiwa ‘ya’yanta umarnin dakatar da jigilar man daga birnin Legas zuwa sassan arewacin kasar daga yau Alhamis har sai abinda hali yayi. Shugaban kungiyar direbobin tankar na Najeriya Otumba Oladiti yace tilas ne su yanke hukuncin, saboda matakin gwamnatin Niger na haramtawa dukkanin manyan motoci bin hanyoyin da suka ratsa ta cikin garin Minna, babban birnin jihar. Garba Aliyu Zaria ya tattauna da shugaban matuka motocin dakon man fetur din na arewacin Najeriya Comrade Abdulsalam Mohammad
A Najeriya, wasu manyan kungiyoyi biyar dake wakilcin manyan kabilun kasar da maradunsu, sun bayyana goyon bayansu ga shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo da ke zargin gwamnatin kasar da gazawa. Kungiyoyin sun hada da na Afenifere ta Yarbawa, da Ohaneze Ndigbo ta Inyamurai, da Kungiyar hada kan al’ummar yankin Niger Delta da Kungiyar mazauna jihohin tsakiyar Nigeria Kungiyar Dattawan Arewa. Garba Aliyu Zaria ya ji ta bakin Farfesa Jibrin Ibrahim dake daya daga cikin wadannan kungiyoyi ko me yayi zafi haka.
Wata kotu dake Milan na kasar Spain ta bayyana ranar 21 ga wannan wata da muke ciki don sauraron bukatar Najeriya na neman a biya ta kudade da suka kai dala biliyan daya da miliyan daya daga cikin kudaden zamba wajen saida rijiyoyin mai a shekara ta 2011 ga kamfanonin mai na Eni da kuma Shell. Kuma dangane da wannan baatu ne dai Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Farfesa Muntaka Usman na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria don jin yadda masana ke kallon lamarin.
Kasashen Afrika da dama yanzu haka na fuskantar ambaliyar ruwan sama, iftila’in da tuni ya lakume rayuka da mamaye gonaki da rusa gidaje a wasu kasashen da suka hada da Nijar, Najeriya, Sudan, Kamaru da kuma Chadi. Ko yaya masana yanayi ke kallon wannan barna, tambayar kenan da Garba Aliyu Zaria ya yiwa Farfesa Adamu Tanko na Jami’ar Bayero dake Kano.
Shugaban gidauniyar yakar rashawa mallakin jagoran ‘yan adawar Rasha Alexie Navalny, Ivan Zhdanov, yace Rasha ce kawai za ta iya aiwatar da danyen aikin shayar da mai sukar nata guba, yayin da kasashen duniya da kungiyoyi ke caccakar aika aikar. Garba Aliyu Zaria ya duba mana halin da ake ckin a shirin mu zagaya Duniya.
Wani rahoton da Kamfanin man Najeriya NNPC ya fitar na cewa an kashe kudaden da suka kai Naira Biliyan 148 a matatun mai na kasar uku cikin watanni 13, sai dai har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Kan haka Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Alhaji Umaru Dembo tsohon Ministan mai a Najeriyar.
A karon farko a Najeriya, wata kotu ta zartas da hukunci kan masu fashin jiragen kan teku, al’amarinda zai nuna azahiri kasar da gaske take yi game da sauye-sauye ta fannin yawaitan fashi a teku. Kotun dake zama a Port Hacourt ta ci taran kudi Naira miliyan 10 kan kowannensu saboda laifin fashin jirgin ruwa a watan uku na wannan shekaran, inda suka karbi kudin fansa na dalar Amurka dubu 200 don sakin matuka jirgin ruwan. Dangane da wannan hukunci Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Alhaji Isa Tafida Mafindi Masani gameda sha'anin jiragen ruwa.
Shugaban majalisar Turai Charles Michel ya kai ziyarar aiki a yau asabar a kasar Lebanon domin jajanta wa al’ummar da ke alhinin mutuwar sama da mutane 150 sanadiyyar wannan fashewa da ta faru a ranar talatar da gabata. A lokacin wannan ziyara, shugaban na majalisar turai ya gana da shugaba Michel Aoun, da shugaban majalisar dokoki Nabih Berri sannan da firaminista Hassan Diab. A cikin shirin mu zagaya Duniya zaku ji halin da ake ciki a wasu kasashen Duniya tareda Garba Aliyu Zaria.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce yana da matukar wuya a samu maganin cutar Coronavirus duk da kokarin da kasashen duniya da kamfanonin harhada magunguna ke yi don samarda maganin cutar, dangane da wannan batu Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko kwararren likita dake Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria kan yadda suke kallon wannan hasashen.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako, Garba Aliyu Zaria ya zagaya da mu sassa dabam dabam na fadin duniya.
Sahugabannin kasashen kungiyar yammacin Africa biyar na kan hanyarsu ta zuwa Bamako na kasar Mali don shiga sulhu da ake yi na warware rikicin siyasar Kasar. Shugabannin kasashen biyar da suka hada da Cote d’Ivoire, Ghana, Senegal, Nijar da Nigeria za su yi wannan zaman tattaunawa ne gobe Alhamis. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Khamilu Sani Fagge na Jamiar Bayero dake Kano yadda yake kallon wannan zaman sulhu.
A cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' Garba Aliyu Zaria ya yi bitar mahimman labaran al'amuran da suka auku a sassan duniya, ciki har da kokarin da masana ke yi na lalubo magani da rigakafin cutar coronavirus da sauransu. A yi sauraro lafiya.
Bankin raya kasashen Afrika AFDB, ya ce tasirin da annobar coronavirus ke ci gaba da yi kan tattalin arzikin Duniya kan iya jeffa karin mutane kusan miliyan 50 cikin mummunan talauci a nahiyar Afrika. Garba Aliyu Zaria a cikin shirin Mu zagaya Duniya ya mayar da hankali ga muhiman batuttuwan da suka faru a cikin wannan mako.
Wasu rahotanni da kafofin sadarwa a Najeriya su ka wallafa sun bayyana cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kori mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magudu. Tun ajiya ne dai ake ta rade-radin jami’an tsaro na farin kaya na tsare da Ibrahim Magu Abuja babban birnin kasar. Garba Aliyu Zaria ya nemi ji daga Awwal Musa Rafsanjani na kungiyar kare hakkin bil’adama yadda su ke kallon matakin da Shugaba Buhari ya dauka.
Kamar yadda aka saba a kowane mako, sashin Hausa na RFI kan waiwaye kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Garba Aliyu Zaria ya soma bitar muhimman labarun ne daga Faransa, inda shugaba Emmanuel Macron ya nada sabon Fira Ministan bayan murabus din na da Edouard Philippe.
tsuguni bata karewa Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ba, ganin yadda magoya bayan bangaren Bola Ahmed Tinubu suka bayyana rashin amincewar su da rusa kwamitin zartarwa da kuma nada shugabannin riko a karkashin Gwamna Mai Mala na Jihar Yobe. Garba Aliyu Zaria ya duba tareda mayar da hankali ga manyan labaren mako daga nan sashen hausa na rediyon Faransa rfi.
Likitoci a Najeriya yau sun tsunduma cikin yajin aiki saboda abinda suka kira kin gwamnati na biyan su hakkokin su da kuma samar musu da kayan aiki, a daidai lokacin da annobar coronavirus ke cigaba da yaduwa a kasar, dangane da wannan batu ne Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dr Mohammed Askira shugaban kungiyar Likitocin Najeriya. Kungiyar likitocin tace 'ya'yan ta dake aiki da gwamnatin Najeriya sun yanke hukuncin fara yajin aikin domin nuna rashin amincewar su da matakin na gwamnati, sai dai sun ce yajin bai shafi takwarorin su dake aiki a cibiyar yaki da masu fama da cutar coronavirus ba. Akalla ma’aikatan lafiya 800 suka kamu da cutar coronavirus a kokarin da suke na yaki da cutar amma kuma gwamnatin taki biyan su hakkokin su.
Matsalolin rashin tsaro a yankunan jihohin arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da ciwa ‘yan asalin yankin tuwo a kwarya, kasancewar a duk rana sai kara samun munanan hare-hare ake daga ‘yan bindiga duk da matakan tsaron da ake dauka. Kan sha’anin tsaron ne Garba Aliyu Zaria ya tattauna da mai martaba Sarkin Gwandu na 19, kuma tsohon mai tsaron lafiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a zamanin mulkin soja, Alhaji Mustapha Haruna Jokolo, wanda yayi tsokaci kan halin da ake ciki da kuma mafita daga matsalar tsaron.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da Karin wa’adin hana zirga-zirga a tsakanin jihohin kasar da tsawon makwanni, gami da jinkirta daukan sauran matakan cigaba da sassauta takaita gudanar harkokin yau da kullum domin dakile yaduwar annobar coronavirus. Dangane da wannan mataki Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dakta Bashir Kurfi masanin tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kan tasirin matakin bisa tattalin arziki Najeriya.
Kamar yadda aka saba a kowane mako, sashin Hausa na RFI kan waiwaye kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Garba Aliyu Zaria ya soma bitar muhimman labarun ne daga birnin Kabul na Afghanistan, inda 'yan ta'adda suka kai mummunan hari kan wani asibitin kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF.
Kamar kowane mako, Sashen Hausa na RFI kan yi dubi game da wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karo ma, Garba Aliyu Zaria zai ba mu damar yin dubi a game da irin wadannan labarai cikin shirin Mu Zagaya Duniya.
Kamar kowane mako, Garba Aliyu Zaria na duba mana wasu daga cikin muhimman labarai da suka faru da wadanda ke faruwa a sassan duniya, A wannan mako mako ma ya yi tsamo wasu daga cikin irin wadannan labarai a cikin shirin ''Mu Zagaya Duniya''.
Kamar kowane mako, Garba Aliyu Zaria kan yi dubi a game da muhimman batutuwan da suka faru a duniya cikin wannan mako da ya kawo karshe.
Adadin mutanen da cutar Coronavirus ta kashe ya zarta dubu 5 a sassan duniya, kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Faransa ya tattaro daga alkaluman da mahukunta suka fitar. Wannan na zuwa ne a yayin da kasar Iran ta sanar da sabbin mutane 85 da cutar aika lahira a yau Juma’a, yayin da kasashen Turai da dama suka rufe makarantu har tsawon makwanni biyu don dakile yaduwar wannan annobar. Garba Aliyu Zaria ya duba wasu daga cikin manyan labaren Duniya cikin shirin mu zagaya Duniya .
Cikin shirin Muhimman labaran karshen mako ta cikin shirin Mu zagaya Duniya tare da Garba Aliyu Zaria, ya tabo manyan labaran da suka faru a sassa daban-daban na duniya, masamman halin da ake ciki dangane da annobar cutar murar Mashako ta Coronavirus ko COVID - 19 da ta bulla a China.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da yin kira zuwa kasashe don ganin sun dau matakan kariya daga kamuwa da cutar Mashako duk da tace babu shaidar dake nuna cewar cutar zazzabin da ta barke a China na yaduwa tsakanin Bil Adama a wajen kasar. Wasu bayanai daga hukumomin Turai kama daga Faransa da Austria na tabbatar da bulluwar cutar a yankunan su,haka zalika a Amurka da wasu kasashen yankin Asiya. Garba Aliyu Zaria a cikin shirin mu zagaya Duniya ya mayar da hankali a kai.